Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
dashi shine ita Hajja ɗin tasa dole ya tura matan, shine ni kuma ya kira ni yana faɗa min, na ce masa kawai ya tura mata tunda har Hajja ce ta bada umarnin haka"
"Tabɗi jam anya-anya Mimi haka nan suka bar Hajja kuwa?"
Da sauri Mimi ta waiga saitin bedroom ɗin da Shamsiyya take jin kamar motsin fitowarta yasa Mimi saurin rufe ma Maryam baki tana sauke lumfashi ganin Shamsiyya ce ta fito sanye take da wasu irin matsiyatan kaya matsatstsu, sosai suka matse ta dan da kyar take iya tafiya, ga ub*an ɗuwawukanta sun mugun bayyana kirjinta ma a bayyane duk rabinsu ana gani.
Sakin baki da hanci kawai Maryam tayi tana bin Shamsiyya da kallo kamar wata sakarai.
Tana binsu da wani kalar kallo na wulaƙanci ta wuce su tana wata rangwaɗa haɗe da faɗin.
"Anzo gulma da kilbibi"
Maryam kamar zatai magan sai kuma ta girgirza kai tana yin kwafa kawai tana cije baki suka bita da kallo harta fice daga parlon da alamar ma fita zatai gaba ɗaya daga gidan.
"Tabɗi jam ke kina zaune kina gani kuma take irin wannan shegiyar shigar a gidanki?"
"Haba dai Maryam baki ga fita zatai ba, idanma tayi wallahi babu ruwana kanta tayi mawa, ita ce zata zubarwa da kanta mutumci, ni dai abu ɗaya na faɗa mata karta sake idan har zama zatai ta rinƙa min shigar banza a cikin gidana, amma naga kamar maganar ma dana faɗa matan baji tayi ba, dan ɗazu wasu riga da wando naga tasaka ta zauna min a parlo tana kallo harda ƙure min ƙara tana jin waƙa hankalinta kwance kuma"
"Ahh to ya kike so ki ganta?, ai kece dama ake so aga an tayarwa da hankalin ai"
"Yanzu dan Allah micece mafita ne Maryam?, dan ni kaina ya kulle na rasa ya zanyi da ita wallahi"
"Ai nima na rasa abun cewa, dan Shamsiyya naga ta wuce duk yadda nake tunanin ta yanzu, da alamar a shiryenta tazo kawai so suke dole da tsiya sai Jafar ya auri Shamsiyya ɗin shine kawai ƙudurinsu wallahi"
Gaban Mimi ne ya wata irin faɗuwa rasss har saida ta rufe idonta da sauri tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa da sauri da sauri.
Gani halin data shiga yasa Maryam dafata da kyau tana kallonta cike da son kwantar mata da hankali ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki, kuma shawara ɗaya zan baki, shine duk tsiya karki bari yarinyar can ta raina ki, ki ɗaure ki cire tsoro ki kwaci ƴancin kanki, gida ne naki ne kuma mijin ma naki ne, dan haka dole ki rinƙa taka mata birki, duk wuya karki sake taka gazawarki na gaya miki, kuma duk wuya karki bari taga hawayenki, karki sake na gaya miki, idan kikaga abun yaƙi ci yaƙi cinyewa kawai ki dawo gida shine iyayenki su san da maganar"
Girgirza kanta kawai Mimi tayi da sauri tana jin cewa babu ma yadda za'ai ta fara kai wata matsalar gidanta a gidansu, saboda kusan irin wannan su Abba ke gudar mata, sun gudar mata haihuwar mai sikila zaisa su shiga matsalar rayuwa, sai gashi tun kan ma su haihun ga matsala nan nata kunne kai ta ɓangaren dangin Jafar ɗin.......
PAGE 30
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
Tsinkar zogale take tana yi tana waƙe-waƙenta.
Sallamar da aka kwaɗa ce tasa ta ɗagowa tana bin ƙofar fita da kallo.
Na'ima ta shigo tare da Musa biye a bayanta.
Taɓe baki Mubeena tayi dake binsu da wani kallon takaicin Na'ima ɗin.
Iya ce ta ɗaga labulen ɗakinta ta fito dai-dai lokacin da suka ƙaraso ƙofar ɗakin.
Iya ta sakarma Musa murmushi tana cewa.
"Kai amma naji daɗin zuwan naka yau. Shigo kawai zamuyi wata magana ne da kai mai mahimmanci ma kuwa"
Zata juya zuwa cikin ɗakin taji Musa na cewa.
"To amma Iya da Masoyiya zamu shigo ko?"
Tsayawa tayi tana juyowa gaba ɗaya ta ɓalla masa wata hararar wasa tana cewa.
"A'a kai kaɗai na ce ka biyo ni, suma muna gama maganar da kai zan kira uwar tasu na gaya mata abunda na yanke"
Jinjina kai yayi yana bin bayan Iya data shige ɗakin.
Na'ima dake tsaye ta sauke lumfashi tana dawo da dubanta inda Mubeena take zaune.
Khadija ce ta fito daga banɗaki tana ɗauraye hannunta tana cewa.
"Wai muryar waye nake ji kamar Musa?"
Mubeena na taɓe baki ta saki wani tsaki mai sauti tana cewa.
"Yo shine mana, ya wani shigowa ma mutane gida sai rangaji yake, da wasu shegun kaya wando duk ya zame, wai shi nan gaye"
"Hmm waya ga gayu tab"
Cewar Khadija tana dariya ƙasa-ƙasa.
Na'ima ta matso kusa dasu zata shige ɗakinsu ta ɗan tsaya tana dubansu da takaici ta ce.
"To waima ina ruwanku ne a ciki?"
"Haba Ya Na'ima?, mufa wallahi muna gudar miki auren Musa ne da abunda ka iya zuwa ya dawo"
"Kinga Khadija bana son maganar komai, kuma babu wani abunda zaije ya dawo da izinin Ubangiji, tunda har Inna tasa min albarka wannan ma kaɗai ya wadatar dani"
Ta ƙare maganar tana shigewa cikin ɗaki.
"Kiji ta ba?, wallahi ni tausayi ma take bani"
Khadija ta faɗa tana bin ƙofar da Na'ima ta shige da kallo.
Mubeena dake ci gaba da aikin da take yi ta ce.
"Ana tausayinta ne ai bata tausayin kanta, amma wallahi ko yanzu sai naga bayan auren nan, sai naga ba'ayisa ba, ina wata dacewa a tare da Ya Na'ima da Musa fisbilillahi?"
"Dan Allah idan baki ga bayan auren ba baki cika sunanki Mubeena ba, kinji ko?"
Da sauri suka ɗago suna duban Inna data fito daga kitchen na gidan dama sanwa take yi.
"Bani aikin dana saki. Ko ki maida hankali kiyi min aikin dake gabanki amma kin tsaya wani furucin banza, wadda bazai taɓa yiwuwa ba"
"To ni Inna ba....
"Rufe min baki na ce, kuma wallahi na sake na sake jin kalma wacce ta danganci irin wannan lafazin a bakinki zaki gane Allah ɗaya ne wallahi, zaki ga ɓacin raina wadda baki taɓa ganinsa ba"
"Amma Inna ni banga abunda Mubee..
"Kema kiyi min shiru na ce duk ba bakinku ɗaya ba?, dan haka ban san sake jin wata magana a bakinku gaba ɗaya. Wa'inda basu san ciwon kansu ba kawai"
Inna ta ƙare maganar tana ɗaukar zogalen da Mubeena taci rabin gyaransa ta koma cikin kitchen ɗin da take sanwarta ta barsu da binta da kallo kawai na mamaki.
"Iya ina jinki"
"Yawwa ɗan albarka, dama tuni nake so muyi maganar nan da kai"
"Wacce magana ce haka Iya?"
"Ni kam Musa har yanzu kana samun labarin Zubaida?"
"Zubaida?"
Ya faɗa iya laɓɓansa yana jinjina kai da mamaki ya akai suke son sanin inda Zubaida take daga Iyar harsu Na'ima?.
"Kayi shiru Musa?"
"Ai Iya abun naku ne ke ban mamaki fa, su Na'ima ma shekaran jiya dana zo ta tabbaye ni wai ko yanzu ina da number da za'a iya samun Zubaida?, dana yi mata kallon tuhuma sai ta ce min kawai Inna ce ke son sanin halin da take ciki ne, saboda sun rufe shekaru uku rabon da suji labarinta, tunda dai na dakata da zuwa Logas"
Iya da mamaki ta sake cewa.
"Suka tabbayi number Zubaida?"
"Eh sun tabbaya kuma na basu, amma gaskiya har yanzu number da wuya idan ta shiga, dan number ta ce ta da, kuma ina kyautata zaton ƙila bata amfani da layin a yanzu, dan ta zama mai kuɗi"
Iya ta taɓe baki tana cewa.
"To wata ƙila dai kawai tana so taji ina ƴar uwarta take shine kawai. Ni abunda nake neman jin labarin nata da inda take daban. Ka gane bikin nan naku da kai da Na'ima nake so kamin lokacin bikin zansa a tura Mubeena Logas ɗin can wajan Zubaida ɗin ta zauna kamin wani ɗan lokacin da zaku gama fahimtar juna bayan auren naku"
"Amma Iya saboda mi duk wannan?"
Ya faɗa da mamaki.
"Hmm kai kamar baka san wacece Mubeena ba?, nan-nan shekaran jiya da kyar na rabaku faɗa na iske sai gaggaya maka magana take ba?"
"To ai ni Iya da kin barni lokacin saina ɓarar da ita wallahi, saita gane shayi ma ruwa ne, dan ni kin san bana jure ana ɗaga mun murya"
"Na sani amma hatsabibancinta ya wuce duk yadda kake zato. Dan cewa tayi idan har tana nan bazata taɓa bari ayi auren nan naku ba kaida Na'ima, koma anyi ɗin sai tasan yadda tayi ta kashesa, shi yasa na kira ƙawata ta bani shawarar kawai nasa a kauda min ita daga garin nan bayan anyi biki da kwanaki masu dama sai nasa ta dawo, kuma ni na yanke hukuncin ko ba'a samu lambaɗin ita Zubaidar ba kawai na yanke kaine zaka je ka kaita Lagos ɗin ai kasan inda za'a iya samun Zubaida kai tsaye ai ba dole sai an sanar da ita tun a nan ba cewar za'a kawo mata Mubeena ba, gara ma kawai ta ganku kwatsam sai yafi, amma ya kake gani dai?"
"Ai hakan ma shine dai-dai Iya, amma fa Iya gaskiya kuɗin Motar zuwa Lagos yanzu fa sun ƙaro na rantse da Allah nida ita zamu iya kashe naira dubu ɗari"
"Ɗari kuma Musa? Haba dai Musa ina laifin dubu hamsin, itama kayan gonar dana noma ne zansa aje kasuwa a saida buhun waken soya a baku kuɗin Motar"
"Wallahi Iya da gaske, kin san dai ai sai mun riƙe kuɗin abinci daban suma, kuma a haka babbar Mota zamu bi tafi sauƙin kuɗi ai, kuma nake jin waken soyar kamar ya ƙara kuɗi ma dan buhun zai iya kaiwa dubu ɗari ɗin Iya"
"To ai shikenan ba damuwa zan baka shi zuwa juma'a kasuwar dake ci a ranar aje a sayar dashi ɗin, ranar litinin sai kawai ku kama hanyar tafiya, dan satin sama ne ta kama bikin naku ai, gara azo ayi komai da jiki dan ban san miye take ƙudurtawa a cikin ranta ba, wannan yarinya mai idon rashin kunyar"
Musa ya saki murmurshin mugunta dan shi kaɗai yasan miye ya shirya mata a wannan tafiyar da zasuyi a tare tana jinjina kansa ya miƙe yana ma Iya sallama ya fice bayan sun gama tattauna komai.
Lokacin da zai fito Inna ma na fitowa daga ɗaki tana kallonsu Mubeena da har lokacin suke zaune a tsakar gidan suna fira jefi-jefi.
Fitowar Musan yasa Mubeena binsa da wata hararara cike da jin haushinsa, shi kam binta yayi da wani kalar kallo mai cike da gargaɗi.
Sai Inna taji gabanta ya ɗan faɗi da irin kallon da taka suna aikama juna.
Ta kasa haƙuri bayan Musa ya fice daga gidan ta dubi Mubeena tana cewa.
"Mubeena wai ban hanaki wannan harare-hararen ba?, shi ba Yayanki bane, bana son fa rashin kunyar nan irin taki tom"
Tana turo baki ta ce.
"Ni fa Inna ba abunda nayi masa, baki ga shima wani kallo da yake min ba"
"Ba dole ya kalle ki ba, yaga kina watsa masa wannan mugun kallo, ai dole shima ya kalle kin"
Shiru kawai Mubeena tayi tana jin takaici da haushin Musa daga shi har Iya dama Na'ima ɗin data riga ta amince, itafa da Na'ima zata bi shawararta wallahi da ita ce tabi Aunty Zubaida Lagos ta gudarma auren Musa ɗin, bawai ita a kaita Lagos ba.........
PAGE 31
*HANNAH POV*
A hankali ta lakaci Cake ɗin data gama tana sakawa a baki, ta jinjina kai tana murmushi.
"Yawwa a bani nawa Cake ɗin na ɗanɗana nima"
Fannah ta ƙare maganar tana shigowa kitchen.
"Uhmm wallahi kitchen ɗin nan ƙamshi kawai ke tashi mai daɗi na abinci tako ina"
Fannah ta ƙara faɗa tana shigowa gaba ɗaya ta samu kantar kitchen ɗin ta haye ta zauna, tana kallon yadda Cake ɗin aka shiryasa har guda uku yayi masifar kyau gaba ɗaya kowanne kuma da kalar nasa.
"Harkin gama ƙunshin ne?"
"Eh Hannah na gama masu tun ɗazu ma, na tsaya na gyara mana ɗaki dan yau ko albarkacin gyaran bai gani ba sai yanzu"
"Aiki ne yayi yawa Fannah ai yau"
"To ai naga ma ke da sauran guda ɗaya da baki idasa haɗawa ba ko?"
"Eh shima na kusa na wacce zasu aiko zuwa ƙarfe ɗaya ne"
"Ke matso ki tayani saka abincin nan a takeaway ɗin nan"
Aunty Sa'a ta faɗa suna zaune da Aysha suna zuba abincin da suka kammala a takeaway ɗin dake jifge a gabansu masu yawan tsiya.
Tasowa Fannah tayi tana matsowa kusa dasu wata kujera ta samu ta zauna ta kallon abincin da yayi kyau sosai yayi shar dashi. Shinkaface aka dafa ta dafa duka taji naman rago a ciki, tayi wara-wara kuma shar da ita, ga kayan yanke-yanke dake gefe su kabeji ansa kwai dasu kokonba a ciki harda bama akasa, idan aka saka shinkafar a gefe sai wata taliya itama da aka dafa ta tayi kyau taji kayan lanbu itama, sai a ɗakko naman Kazar da yaji jar soya asa a gefe sai wannan kabejin shima daya ji kayan haɗi asa shima a gefe, haka suke yi a cikin takeaway ɗin suna zubawa ana rufewa sai asa a cikin wata leda fara mai kyau irinta ƴan gayu.
"Wai sannunku ai naga ma kamar kun kusa gamawa ko?"
"An dai kusan saura na mutum ɗaya, kusan guda ɗari da hamsin"
Aysha ta faɗa suna ci gaba da zubawa Fannah a amsa tana sakawa a ledar.
Wayar Aunty Sa'a aka kira yasa ta kallon Hannah dake ƙarama Cake ɗin da take haɗawa kwalliya ta dube ta tana cewa.
"Ɗan miƙo min wayata gata nan a kusa dake"
Wayar ta ɗakko ta kawo mata ta koma.
Tana ɗaukar ganin masu Order abincin bikin ne ɗaya daga cikinsu yasa ta ɗauka tana murmushi.
"Okey eh zaku shigowa ta ƙofar wajen, dan na gama sai a fara jidar abincin kawai"
Ta faɗa tayi saurin sauke wayar tana tashi tsaye ta buɗe ƙofar wajen.
Ta dubi Fannah ta ce.
"Taso please fara ɗebo wa'innan dana ware guda ɗari da hamsin gasu nan matso dasu kusa, masu su sunzo yanzu zasu tafi dasu"
Tashi tayi ta fara yin kamar yadda ta ce ɗin.
Wani yaro ne matashi yayo sallama cikin kitchen ɗin ya shigo ta ƙofar waje.
Gaisawa sukai da Aunty Sa'a a mutumce yana masu Fannah sannu suka amsa ciki-ciki suna ci gaba da aikin dake gabansu shi kuma Aunty Sa'a ta nuna masa takeaway ɗin dage gefe a cikin leda ya fara ɗauka yana kaiwa cikin Motar da suka yi parking ɗinta a ƙofar shagon.
Har saida wani yazo ya idasa taimaka masa suka kwashe sauran. Daga ƙarshe ɗayan yazo wadda sukai waya da Aunty Sa'a yana ce mata.
"To ranki ya daɗe bari na idasa tura miki cikon kuɗinki, munfa gode sosai da cika mana alƙawari wallahi"
Ya faɗa cike da jin daɗin yadda ta cika alƙawari sunzo basu wani zauna ba.
"Haba ba komai ai kyautatama costumer ɗina ai kamar wajibi ne a waje na"
Yana murmurshi ya jinjina kai ya fiddo da wayarsa nan take ya tura mata cikon kuɗin nata.
Nan ta duba har sun shigo daya ke Opay to Opay ne.
Tana dubawa ta zaro ido tana kallonsa da mamaki ta ce.
"Ai cikon dubu hamsin ne fa kawai"
"Eh na sani na baki dubu ɗari ne kawai dan naji daɗin yadda baki ɓata mana lokaci ba, dai-dai lokacin da muke so muka zo kuma muka samu, dan haka harki ji komai nina ƙara miki kin cancanta ne Hajiya, mun gode sai kin sake jinmu da wata Order ɗin insha Allah"
Murmushi itama ta saki tana sake masa godiya suka ja Motarsu suka tafi.
Tana sauke lumfashi ta koma cikin shagon.
"Yawwa muyi sauri dan Allah mu ƙarasa wannan ɗin, suma nasan suna kan hanyar zuwa"
Ta ƙare maganar tana zama suka ci gaba aikin.
Hannah dake tsaye tana ƙarasa kwalliyar Cake ɗin guda ɗaya wadda bata gama ba na cikon na huɗun wadda za'a amsa ƙarfe ɗaya taji wayarta na ƙara alamar kira ne ya shigo.
Hannu tasa tana ɗaukar wayar dake aje akan wani katako dake kitchen ɗin.
"Okey gani nan fitowa"
Ta faɗa kawai haɗe yanke kiran. Da sauri ta fice waje ɗakinsu ta shiga tana ɗakko Hijab ɗinta har ƙasa tasa ta fito zata koma kitchen ɗin taji Aunty Maryam na cewa.
"Ke idan kin koma ki ce ma Aunty Sa'a ta zubo min abincin nan dan yinwa nake ji, kamin kizo please ki ɗora mana abincin gida muma"
"Ai inaga abincin da sukai yi ya isa har muci basai an sake dafa wani ba, so take su gaba zubawa a takeaway ɗin kamin wadda yayi saura ta zubama kowa"
"To naji amma dai ni dai ki ce ta zubo min nawa"
Ɗaga kanta tayi tana amsawa da to tabar wajan suna fira da Ammi jefi-jefi, masu ƙunshin da Fannah tayima ne suka gama cire ƙunshin suna so a zuba masu ruwa zasu wanke ƙunshin.
Tashi Maryam tayi ta zuba masu ruwan tana cewa.
"Bari na kira Aunty Sa'a ta turo yarinyar nan Fannah tazo masu ƙunshin nata na shirin tafiya tunda wankewa zasuyi ya kama"
"Tana can tana surutu yanzu haka, Allah yasa ma tana tayasu aikin"
Maryam ta kira Aunty Sa'a bayan ta sauke wayar saiga Fannah riƙe da takeaway guda ɗaya tazo tana miƙema masu ƙunshin nata.
Da kamar bazasu amsa ba saida Ammi tasa baki tukunna suka amsa suna godiya, bayan sun wanke ƙunshin babbar cikinsu ta buɗe jakarta tana cewa.
"Dubu biyar-biyar ne ko?"
"Eh sis hakane"
"Ai kina da sauƙin ƙunshi ma wallahi"
Murmushi kawai Fannah ta saki tana kallon yadda ta buɗe jaka ta ɗakko kuɗin masu yawa ƴan dubu-dubu bugun Abuja, ta ƙirga 15k ta miƙa mata tana sake mata godiya, suka kwashi sauran kayansu da takeaway ɗin da aka basu suka nufi ƙofar waje suna masu Ammi sallama.
Fannah ma har ƙofa ta rako su bayan ta amshi kuɗin ta riƙe.
Suna tafiya ta dawo ta shiga ɗaki ta adana kuɗin ta koma cikin shago.
Hannah ce ta fito riƙe da wani farin kwali wadda ake saka Cake a cikinsa tana