Taurin Kai Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 47

48K to 51K   out of 140.3K words

ganin Fannah ta ce.

"Yawwa Aunty Fannah please ɗakko min ɗayan shima yana nan masu shi sunzo shima"

Da to ta amsa tana shiga ciki saita yafa wani mayafin Abayar dake jikinta kawai ta ɗakko ta biyo bayan Hannah data riga ta ƙarasa wajen.

Da murmushi masu amsar Cake suka amsa suna mata godiya gaba ɗaya, kowanne yazo da Motar shi dama ya shige suka bar ƙofar gidan.

Hannah tana murmushi ta sauke ajiyar zuciya a bayyane tana cewa.

"Wallahi karki ji yadda naji daɗi dana sauke nauyin nan"

Fannah zatai magana suka ji muryar Kawu Sani akansu.

"Gaskiya ne yaran nan wato ku dai baku da aiki saina tara Maza da mata ƴan iska ko?"

Hannah na shirin gaida shi Fannah ta diri ta ce.

"Kawu Sani kamar ya bamu gane ba?"

"Zaki gane ne dan ub*anki, ni kike ma wannan tabbayar ta rashin kunya?"

Fannah ta fara ƙunƙuni tana faɗin badai nata ub*an ba wallahi ta ƙare magnar zucin tana harararsa ta juya ta shige gida.

Hannah ma ganin kamar Kawu Sanin da faɗa yazo yasa ta shigewa kawai ya kuma biyo bayansu sai ɓaɓatu yake na ɓorin kunya.

"A'a hayaniyar mi nake ji ne Fannah a waje?"

Ammi ta ƙare maganar tana kallon Fannah data shigo gidan tana turo baki ranta a ɓace.

"Waye fa idan banda kamar muryar Kawu Sani nake ji, kamar dai shine"

Maryam ta faɗa tana tashi zaune sosai itama akan tabarmar da suke zaune.

"Shine mana Ammi ƴan...

Shigowarsa kusan tare da Hannah data fara shigowa yana take mata baya ne yasa Ammi tashi tsaye itama ba shiri, dan yadda taga ya shigo to ba lafiya ta kawosa ba.

"Yaya Sani lafiya dai?"

"Ita ce zata kawo haka ai?"

"A'a kaga Ubangiji ya baka hakuri daga tabbaya?"

"To nida gidan ɗan uwana da ƴaƴansa a ciki dan nazo sai a rinƙa tabbayata lafiya?"

"Ai yadda naga ka shigo ɗin ne kamar ba lau ɗin ba"

Maryam kam zaune saita taɓe baki tana faɗa ƙasa-ƙasa yadda baji zaiyi ba ta ce.

"Yo dama su lafiya na kawo su ne?, sai idan tashin hankali ne ko biyan buƙatar ransu"

"Zuwa nayi na sanar dake mun gaji da irin zaginmu da ake yi a gari akan wa'innan yaran naki, da suke so su gagari ub*an kowa a garin nan, kullum cikin zaginmu ake mu dangin uban nasu, dan haka haƙƙinmu ne dama mu aurar dasu, dan haka nazo na shaida miki mun yanke hukuncin haɗa Aysha aure da ɗan waje na Abdullahi, sai kuma ita wannan marar kunyar Maryam da Sulaiman ɗan wajan Sama'ila, da kuma...

Da wani irin rikitaccan sauti Ammi ta shiga cewa.

"Kaga banfa gane ina wannan zancan naka ya dosa ba yawwa, tatsuniya ce kake yi ne ban gane ba?"

"Tabɗi jam da waye za'a haɗa ni auren Sulaiman?, ai wallahi idan na yarda Ubangiji ya tsi....

"Kinga daina ma ɓata yawun bakinki Maryam, ai abunda bazai taɓa yiwuwa bane wallahi, ko za'ai yaƙin duniya na biyu ku ɗin nan baku isa kun zaɓar ma ƴaƴana mijin wai da zasu aura ba, iyaka ci ku bari su zaɓa da kankin kansu a kawo magana gareku ku jagoranci ɗaurin aure shine dama dole sai anzo an same ku, amma wai maganar ku zaɓar masu miji ma bata taso ba wallahi bazai kuma yiwuwa ba, wannan ma magana bamai yiwuwa bace na faɗa na sake faɗa"

"Ohhh hakama zaki ce?, wato kin fara nuna mana cewar ƴaƴan nan ba dai namu bane, ba jininmu bane?"

"Ko kaɗan ƴaƴa naku ne, amma miye kuka taɓa tsinana masu a rayuwar nan?, sai kuma kawai na bari rana tsaka ku wani ce kun zaɓa masu miji?, haka kawai salon a tarwatsama yarana rayuwa?, to bazan taɓa yarda da wannan ba, na faɗa ko kotun ƙoli zamuje daku wallahi bazan taɓa amincewa ayima ƴaƴana auren dole ba"

Cike da borin kunyar data rufesa ya fara cewa.

"Ohh wato auren zumuncin da muke son haɗawa ne kike ce ma auren dole?, duk ba a taru a rufama juna asiri bane?"

"To ai ni da wannan auren haɗin bari kaji Yaya Sani gara zumuncin gaba ɗaya ya lalace asirin ya tono ba ruwana, da dai na bari a tarwatsa kan yarana"

"Subhallahi zumuncin da Ubangiji ya haɗasa kike cewa gara ya tarwatse?"

Taɓe baki tayi tana jinjina kai, saima ta koma ta zauna dan hankalinta a kwance, dan wallahi tasan ba wadda ya isa ya ɗaga masu yatsa a cikin dangin Mahaifin ƴaƴan nata, dan ita yanzu ta fara ganin hassada ce kawai da ƙyashi kesa suna yo mata sallama cikin gida suna son ɗaga mata hankali ne kawai ba wani abuba, dama kuma ta daɗe da samun labarin harda su ke ƙara haɗa cewar ƴaƴanta na tara maza suna yawon iskanci, duk daga garesu ne maganar ke fitowa, suna yaɗa cewar ai sunfi ƙarfinsu ne shi yasa suka kasa taka masu birki masu ganin kowannensu da gashi, duk sune suka bawa mutane ƙofar zagin nasu ai ta daɗe da sanin hakan.......

PAGE 32

"To idan har mun isa da ƴaƴan nan basu da sama da wa'inda muka zaɓa masu, wannan shine magana kuma mun zauna mun gama yanke hukunci"

"To ai ko wannan hukuncin bazai taɓa yiwuwa ba"

Su duka waigawa sukai suna kallon Aunty Haja da tayo sallama ta shigo gidan riƙe take da key na Mota a hannunta sai jakar dake riƙe a ɗayan hannun nata.

"Keeee har kin koyo rashin tarbiyya kema wato da rashin kunya?, ni kike kallon tsabar ido na kike gaya ma haka?"

Tana ƙarasowa inda suke taja ta tsaya tana sake duban Kawu Sani ta ce.

"Kawu Sani kayi hakuri amma bawai rashin kunya nayi maka ba, kowacce nan da kake ganinmu tana da mijinta a hannu, wani ɗan abu muke jira kamin mu kawo su gareku ayi maganar aure bawai auren ne ai bazamuyi ba ko wai mun rasa mijin bane a'a akwai su"

"Kuma a wannan zamanin ma anyi auren soyayyar ya aka ƙare da auren bare kuma bana soyayya ba?"

Aunty Sa'a ta faɗa itama suna fitowa daga kitchen ɗinta bayan sun gama aikin abinci, Aysha dake biye a bayanta ɗauke da sauran abincin da suka rage wadda za'a raba suci a gidan ta aje shi gefen Ammi rufe yake a kula tana kallon Ammi ta buɗe baki zatai magana taji maganar Kawu Sani na maida ma Aunty Sa'a maganar da tayi masa.

"Ke kin san kan maganar ne da har zaki sakowa mutane baki?, ko duka kun san akan mi ake magana ne?"

"Bamu sani ba kawai mun ɗan tsinta ne"

Aunty Haja ta ƙare faɗar hakan tana cire gyalen jikinta ta kai ta zauna a kusa da Ammi tana dubanta ta ce.

"Ammi mike faruwa ne?"

Ammi ta taɓe baki tana hararar Kawu Sani ta ce.

"Wani zance nan yazo min dashi akanku, wai sun yanke hukunci sun maku miji miye da miye. Ke kiji mun wannan magana dan Allah? an taɓa haka dama? a zauna a wani yanke hukunci ba tare da sanin wacce ta kawo su duniya ba?, abun naku ma gani nake yana so ya wuce gona da iri ne kawai"

"Ai ban taɓa ɗauka ƴaƴan nan ba namu bane sai yanzu, kuma kin nuna min cewar ba jinin namu bane, bamu isa dasu ba. To bari kiji na rantse da Allah daga yau zamu iya zare hannunmu daga duk wani al'amarinsu idan ya taso, koda na auren ne kuwa, sai suje can su nemi wa'inda zasu tsaya masun wajan bada auren nasu, ai dai da dangin uba ake ado, to munga yadda za'ai suyi auren, Mazaje ne ga wa'inda muke so su aura idan ba haka ba kuma babu mu babu su"

Baki sake su Aunty Haja ke bin Kawu Sani dake wannan furucin da kallon zallar mamaki, Maryam kam taɓe baki tayi a ranta ko a jikinta, danta rantse koma miye zai faru bazata taɓa bari ta auri wadda suke ikirarin wai sun zaɓa mata ba.

Ammi kam miƙewa ta sake yi a hargitse tana watsa hannayenta tana faɗin.

"To Yaya Sani sai miye idan kun zare hannun naku daga duk wani al'amarin ƴaƴana?, nake ganin dama ai ko yanzu miye kuke tsinani masu?, ai babu, dan haka wallahi ko a kwalar rigata, da dai ma kuna ciyar dasu sai naji hankali ya tashi, amma ƴaƴan nan gasu nan sune ke sana'arsu tuƙuru suke riƙe damu, har kuma kuna lallaɓowa kuna yagar arziƙi, dan haka wallahi ba wani abu a tafi a hakan"

"To ai shikenan idan auren nasu ya tashi sai ki auren dasu mu gani, tunda mace na auren da yaranta, sai a fara ta kanki mu gani"

Yana ƙare maganar ya wani bushi iska ya wuce fuuuu zaibar gidan da ƙarfi yadda zai iya juyota Ammi ta ce.

"Yo sai mine ai idan inyi duniya don Manzon Allah ƴaƴan nan zai sun zama yadda bakwa tunani ko hasashe, kuma aure ne koda ku koba ku sai sunyi shi, ai kawai bayin Allahn da zan iya tura abun garesu su jagoranci lamarin auren nasu ba dole sai da ku ba wallahi, kun daɗe baku zaren hannun naku daga lamarin ƴaƴana ba, aikin banza kawai"

"Dan Allah Ammi zauna haka nan kiyi hakuri"

Zaman Ammi tayi tana jin yadda kanta ke sara mata saboda hayaniyar da tayi sosai tana cewa.

"Haba Hajara ai dole nayi faɗa, ya za'ai kawai Mlm su wani zo suce wai sunma gama yanke hukunci akan aurar daku?, yo hauka ma ake kenan?. Mutanen nan basu san cinku ba bare shanku, ba abunda suka sani naku, idan rashin lafiya ce basu sani ba, ko zaku mutu da yinwa ku kwana da ita basu sani ba, ke ko karuwanci zanyi na ciyar daku babu fa ruwansu, suka ɗauke ƙafa daga gidan nan basa zuwa ko fa ƙofar gidan nan ne, sai yanzu kuma sunga babu ran Mahaifin naku shine suke son fara tsirfo min da wata maganar banza, to ni ba sakarar uwa bace ba kuma shashasha bace, da ilimina suka ganni kuma har yanzu ina a yadda suka sanni wallahi a baya"

"Kinga Ammi ki kwantar da hankalinki, ai wallahi ma basu isa ba, haka kawai yo haka ake yi ma"

Aunty Sa'a ta faɗa tana jawo kujera ta samu ta zauna tana sauke lumfashi.

Aysha kam abun fa mamaki yake bata ainun, dan a tsaye take ma ta kasa zama, zuwa can ta ce.

"Wato ma su Kawu Sanin nan sun matuƙar raina mana hankali kawai zance. Yo idan banda haka kawai mun mallaki hankalin kanmu sai rana tsaka wai an mana miji, a lallai wallahi sun gama ganin inda muke kwana amma nan gaba kaɗan koda kuɗi aka ce suzo suyi mana wannan cin fuskar baza suyi ba"

"Hmm aunty Aysha bari ke dai, to ni ai da muka fara ganinsa a waje cewa yayi mana wai mun zama ƴan iska mun fara gagarar uban kowa, muna tara maza da mata ƴan duniya a ƙofar gida bamu da aiki sai haka"

"Ai dama ni ce ya haɗu da itan a ƙofar gidan Fannah daya ji magana ɗaya bayan ɗaya wallahi, ke wallahi dangin Babanmun nan basu da mutumci basu da ta ido"

"Ko kaɗan kuwa ai ta idon ma basu santa ba, basu da kunyar abun magana, kuma wannan maganganun da ake yaɗawa a cikin unguwar nan duk daga fa gare su suke fitowa su kuma mutane su biye masu suna zaginmu, amma ba komai ai duniya ce kuma ta isa ta nuna masu komai, kuma ni maganar mutane da tasu bata damuna, saboda dai nasan ƴaƴana basa iskancin da aketa yayatawa dan haka ko a jikina, ai dama sai an maka hassada kake ƙara ci gaba, wallahi suyi ta yin hassadar su ai hassada gamai rabo taki ce"

"Ai ni Ammi abunda ya tsaya min ma a rai wai bazasu amshi lamarin aurenmu ba, ni abun ya tsaya min a rai, kenan sai wa'inda suka zaɓa mana ne kawai zasu jagoranci abun?"

"To sai mine Haja har da zaki dami wani kanki akan maganarsu?, yo karda Ubangiji Allah yasa su amshi auren naku mana, babu mutane ne a duniyar?, ai basu kaɗai bane, kuma koda su koba su sai kunyi aure da yardar Ubangiji, shi dai aure ba shaidu yake buƙata ba kawai?, to kuma kwantar da hankalinku ni nasan miye zanyi idan maneman auren sunzo. Amma zansa su fara zuwa wajan su dangin Mahaifin naku idan suka ɓillo da wata maganar ni nasan inda zan sake tura abun ayi auren ba tare da sun sani ba"

"To ai Ammi banga dalilin fara tura su wajan nasu ba kuma"

"Akwai dalilin yin hakan Sa'a, saboda idan ba'a tura su ba farko abun zai zo ayi ta ƙananun maganganu kenan a unguwar nan, gara a fita haƙƙin nasu a basu dama suma, amma idan sukai wasa da damar tasu ni nasan inda zan tura abun"

"Hakane kuma Ammi, amma lamarin su Kawu Sama'ila akwai gyara, taya za'ai kawai rana tsaka kazo ku wani ce kun yanke hukunci ga abunda kuka yanke akan yaran da babu abunda kuke masu a duniya, sai abu yazo ku nuna ai kunfi kowa isa da gadara dasu"

Aunty Haja ta faɗa tana riƙe baki.

Hannah dake tsaye har lokacin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana girgiza kanta tana faɗin Allah ya kyauta kawai zata juya ta wuce taji wayarta kira na shigowa.

Da sauri ta ɗauki wayar tana karawa a kunnenta.

"Wayyo Sorry dan Allah wallahi sai yanzu naga kiran naki, wani abu ne ya ɗan ɗauke min hankali, amma zaku iya zuwa Cake ɗin ya zama radi"

Daga cikin wayar aka amsa ta sake cewa.

"Okey harma wai kun ƙaraso kenan?"

Daga cikin wayar aka ce.

"Muna ƙofar gidanku ma, tunda muka iso nake kiran wayar taki ba'a ɗauka"

"Dan Allah kuyi hakuri wallahi ina cikin hayaniya ne amma bari yanzu nazo na kawo maku ai na gamasa tun ɗazu dama ku nake jira kawai"

Hannah ta ƙare maganar haɗe da katse kiran ta dawo da dubanta wajan da Fannah take tsaye ta ce.

"Aunty Fannah dan Allah taho ki taimaka min da ɗaukar Cake ɗin nan can, kin san yana da girma da yawa"

Bin bayanta tayi kawai tana ɗaga mata kai alamar to, suka bar wajan zuwa cikin Kitchen ɗin.

Suna shiga ta ƙofar baya suka ɗauki Cake ɗin a hankali suka fitar dashi ta ƙofar waje.

Suna tsaye kuwa a bakin Motar da suka zo da ita.

Da sauri wacce sukai waya da ita tazo inda suke ta kama masu aka shigar da Cake ɗin cikin Mota.

Tana murmushi ta ce.

"Kai amma naji daɗi wallahi, na ɗauka ma ko ba'a samu yin Cake ɗin bane shi yasa ma baki ɗauki wayar tawa ba"

"Haba ai idan na ci zanyi ina yi, kawai ina can wani abu ne ya hanani ɗaukar wayar"

"To mun gode sosai sis, sai wani jiƙon kuma"

Sallama sukai suna shiga Mota suka barsu.

Hannah ta sauke ajiyar zuciya ta dubi Fannah ta ce.

"Abun nan ne ya ɗauke min hankali wallahi"

"Hmm keda ma kowa na tofa albarkacin bakinsa amma banji kince komai ba. Koda yake kefa abun ba wani damunki zaiyi ba ai"

Fannah ta ƙare maganar tana sakin tsaki tayi cikin gida tabar Hannah da binta da kallon mamaki. Girgiza kai kawai tayi tana bin bayanta itama da murmushi akan fuskarta a zuci take faɗin (kai Aunty Fannah akwai rigima, wata rana ayi daɗi wani lokacin ayi rashin mutumci da ita)........

PAGE 33

*MIMI POV*

"Bazai yiwu ba Maryam na fara kaiwa su Abba kukan gidan aurena tun yanzu, uhum bazan iya ba gaskiya, sai dai ko ki sake bani shawara"

Maryam dake mata kallon tsanake ta ce.

"Daga wannan shawarar bana jin zan iya baki wata, kwata-kwata kwakwalwata ta toshe nima, dan abunda Shamsiyya ke aikata miki cikin gida ya fara goge min hadda"

"Kema kenan ko?"

"Hmm ai ni da ni ce na rantse miki da tuni tabar min gida na, dan wallahi sai nayi mata haukan da zata gane eh ni ɗin ba kanwar lasa ba ce, ai wallahi ni bazan iya ɗaukar wannan rainin wayon nata ba, tabɗi jam kema kyale ta kikai ai"

"To Maryam ya kike so nayi mata?"

"Yo ai ni da ni ce da dukan mutuwa zan mata, sai taji a jikinta na rantse da Allah"

Saurin girgiza kai Mimi tayi tana cewa.

"Ni kina ganin mukai haka da ita ai ƙara rainani zatai, gara kawai a tsaya iya cacar bakin, shima sai dan dole, dan kar tagama ko tsoronta nake ji ne yasa kawai nake maida mata magana dai-dai da abunda ta faɗa min"

"To ni kinga....

Maganar ce ta maƙale jin motsin shigowar Shamsiyya tare da wata ƙawarta suna shigowa cikin parlon babu ko arziƙin sallama, kawai sun shigo ne suna shewa da dariya.

"Haba Malamai ya da haka kuma babu ko sallama sai ka ce gidan kafurai muke?"

Maryam ta kasa haƙuri ta faɗa cike da wani irin takaicinsu gaba ɗaya.

"Mtswww to fa harda su Ohhh-ohh kaji mun mata da karere dan Allah?, ita kuma wannan ɗin wacece ita, nake jin ai ga matar gidan nan ai ko Ƙawata?"

Wacce suke tare da Shamsiyya ta faɗa tana wani nuna Maryam da hannu cike da wulaƙanci.

Shamsiyya ta taɓe baki tana taunar chingum dake a cikin bakinta ta wani saki kwai tana hurasa ya fashe, kamin ta wani ɗan jefa masu wata uwar hararara ta ce.

"Hmm ai kin san dama irinsu sun fiye zaƙewa da yawa, wacece ita kuwa idan banda banza a banza ba kowa ba ce, dan ni duk familynmu banga irin mai kama da wannan ba"

A mugun zabure Maryam ta miƙe har Mimi na riƙe mata hannu ganin yadda ranta ya ɓaci ta shiga nuna su da yatsa tana cewa.

"Keee Shamsiyya hawainiyarki ta kiyayi rama ta wallahi, ni ba Mimi ba ce da zakiyi mata abu ta shanye, ni bazan ɗauki wannan iskancin naki ba wallahi"

"Au dan Allah?, to bismillah ai gani ko zan bugu ne?"

"Sosaima kuwa ke

17 / 47