Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
ɗin banza da baza'a iya bugun naki ba, ke ɗin wacece ma?"
Wata shegiyar dariya ta saki harda su tafa hannu zatai magana Mimi ta ce.
"Kinga Maryam dan Allah kiyi hakuri haka nan zo muje ciki"
Taja ta suka bar wajan zuwa cikin bedroom nata, suna iya juyo yadda Shamsiyya ke sakin maganganu ƙawar nan tata na ƙara taya ta.
"Mtsww ke yanzu haka kika zauna suka raina ki?"
"Haba dai ƙawata ai kema kin san bazai taɓa yiwuwa ba, ita mai gidan baki ga yadda ta tsaya kamar wata sakarai ba?"
"Hmm ai ni ce ke na rantse da tuni nayi sanadin girgiɗe mata auren da take taƙama dashi"
"Nima wani ɗan abu kawai nake jira, dole ne ma sai Mimi tabar gidan nan na maye gurbinta"
"Ahh yo har sai kin bari ta fice sana zaki wani gurbinta?, ai ina ki bari ki shigo tana gidan ta yadda zaki ji daɗin gasa mata aya a hannu, da ƙafarta zata bar miki gidan wallahi, mune fa ai duk wadda yaci tuwo damu miya yasha wallahi"
"Allah ko ƙawata?"
"Ah eh mana"
Suka ƙare maganar suna fashewa da wata muguwar dariya suna tafa hannu da sakin shewa.
"Ke kinga na sha'afa Ayrah wallahi mun baro masu kiɗan nan a waje"
Shamsiyya ta ƙare maganar tana kallon ƙawar tata wacce ta kira da Ayrah.
"Ke nima bana mance ba, bari naje nasa su shigo ai ko?"
"Eh ki shigo dasu, a nan harabar gidan zasu shirya komai"
"Tom shikenan bari na dawo sai muzo a fiddo Cake ɗin da mukayo Order shi a wajan Hannah"
"Kai ai kin san yarinyar ta iya Cake duk cikin garin Katsina tafi sauƙin yinsa ga daɗi ga cika alƙawari shi yasa kawai ina ganin posting nata nasa tana saka pics na Cake nata a Instagram banyi ƙasa a gwaiwa ba wajan saka Order ba gashi har ya iso ba yau"
"Ai gaskiya ko ni na bikina wajanta zan saya, kuma kin san har Yayarta Sa'a tana abincin biki kama dana taro su duka sun iya sun huta wallahi"
Ayrah ta ƙare maganar tana wucewa waje da sauri ta shigo da iyayen masu ƙida a harabar gidan.
Daga cikin bedroom Maryam ce bakin window tana kallon abunda ke faruwa a tsakar gidan ta waigo cike da mamaki ta ce.
"Mimi miye akeyi a cikin gidanki baki sani ba?"
Da sauri Mimi ta taso daga zaunan da take a tsakiyar gado tazo bakin window ɗin itama tana kallon abunda ke faruwa.
"Wai karda wannan yarinyar da gaske take birthday party zata haɗa a gida na?"
"Au dama party take shirin haɗawa kenan?, hhhh a lallai tsakani da Allah Shamsiyya ta samu ɗaurin gindin zama a cikin gidanki, ba shakka?"
Maryam ta ƙare maganar tana riƙe baki cike da mamaki.
Da sauri Mimi ta matsa jikin window ɗin tana neman wayarta da sauri.
Hango ta ajiye a bakin madubi yasa ta ɗakkota da sauri neman numbersa ta fara yi tana daga tsaye tana cije baki Allah-Allah kawai take ya ɗauka. Saida ta kusan tsinkewa kamin ya ɗauki kiran nata.
Cike da wani irin rikitaccan sauti ta shiga sanar dashi abunda Shamsiyya ke ƙoƙarin yi mata a cikin gida daga ƙarshe ta ce.
"Dama koda saninka zata shirya wani birthday party?"
"Haba dai Love ya za'ai na bari wannan marar hankalin ta shirya min wani party a gida?, ta tara mun maza da mata, ni bamuyi haka da ita ba ko kaɗan, bari yanzu nasan matakin da zan dauƙa ai ina zuwa"
Yanke wayar yayi yana hucin ɓacin rai kai tsaye ya canza akalar kiran ga Shamsiyya da zai kira Hajja ne sai yaga kiran Hajja ma kamar ɓata lokaci ne, dan ba yarda zatai Shamsiyya tayi laifi ba.
Shamsiyya ko dake tsaye a ɗakin da aka sauƙeta Ayrah na ɗaura mata kallabi tayi mata kwalliya da yake ta iya kwalliya sosai saita koma kamar wata babyn roba, kwata-kwata kwalliyar batai mata wani kyau ba kamar ƴar aljanu haka ta koma.
Cike da yanga ta ɗauki kiran nashi, sai dai abunda taji yana faɗa ne yasa ta miƙewa ba shiri.
"Ko miye kike shirin shirya min a cikin gida ki tabbatar kin tattara inaki-inaki kun barmun cikin gida, idan ba haka ba Shamsiyya wallahi wallahi zan miki abunda banzan tunanin nan naki bai taɓa zata ba na gaya miki, na baki awanni kaɗan ki tabbatar daga ke har ƴan iskan da kike shirin tara min su a gida kun bar min cikin gida"
Yana ƙare maganar taji ya datse kiran, ai a zabure tabi wayar da kallo kawai.
"Mike faruwa?"
Ayrah ta faɗa da sauri tana jefa Shamsiyya wani kallo.
"Inafa lafiya, ƴar iskar matarshi ta kirasa ta gama gaya masa ƙarya da gaskiya akan partyn nan dana shirya, wai faɗa min yake fa na tattara ku mubar masa gida. Hhhh wallahi Mimi zaki san wacece Shamsiyya har yanzu baki san shu'umanci na bane, shi yasa har kike ƙoƙarin shigar min hanci"
Tana ƙare faɗar hakan ta shiga kiran number ɗin Hajja.
Hajja na ɗaukar wayar saita fashe da wani kalar kukan tausayi a lokacin saika rantse da Allah wani abun akai mata na rashin kirki.
Daga cikin wayar Hajja ta fara tabbayarta mike faruwa a ruɗe.
Shamsiyya saida ta ci kukanta kamin ta shiga ɗauke ajiyar zuciya tana cewa.
"Hajja wai ni Ya Jafar zai kira yau wai sai na bar masa gida?"
"Ki bar masa gida kamar ya ban gane ba?, wanin abun ne ya sake faruwa?"
"Hajja kin san ina yin birthday yau to shine na tara mutane zamuyi addu'a aci asha taro ya watse, shine kawai daga ganin hakan matarshi ta ɗauki waya a gabana ta shiga kora masa ƙarya da gaskiya shi kuma ya yarda ya kira ni. Karki so jin yadda yayita zagi na da cin mutumci na saina tattara na bar masa gida"
"Shi Jafar ɗin ne yayi haka?, wato har matarshi ta isa ta kira waya ta gaya masa ƙarya akan ƴan uwansa harya yarda?, wato an fara shanye min yaro kenan tun kan aje ko ina?"
"Wallahi Hajja sai abunda fa take so yake mata, komai Mimi komai Mimi, data kirasa ta gaya masa magana shikenan kamar asiri ya ɗauka ya yarda. Hajja wai kinji yadda yake bata haƙuri ma kuwa, sai ka ce wani laifi nayi mata"
"Shikenan ki barni dasu, zanyi maganin abun ai. Kuma kiyi zamanki ku shirya duk wani abu da kikai niyya ni na ce haka"
Hajja na ƙare maganar ta yanke kiran.
Wani kalar tsallan murna ta daka tana sakin ihun murna.
Ayrah dake murmushi da dariya ta shiga nuna Shamsiyya da hannu tana cewa.
"Gaskiya ne ƙawata kin iya haɗa bomb wallahi, wannan irin abu haka?, ai ni saina koma ƴar kallo kawai kin goge min hadda"
Dariya Shamsiyya ta ƙara saki tana zama akan wata kujera dake ɗakin guda ɗaya tana ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya ta ƙara sakin wata dariyar kamin ta ce.
"Kina wasa dani ne Ayrah, amma na wuce duk wani hasashanki, na rantse da Allah saina saka Mimi ta koma abar tausayi a cikin gidan nan, zata zan ni take shigar ma hanci da ƙundindine, saita gwammace dama yau bata ɗauki waya ta kira Jafar ta shaida masa abunda na shirya ba wallahi"
Ta ƙare maganar cike da wani irin baƙin ƙuduri a cikin ranta, dan har wani cije baki take tana zaro ido waje.........
PAGE 34
*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*
Iya ce ta fito tsakar gidan tana kwala kiran Inna.
Inna dake wanki a tsakar gidan tayi saurin tsame hannunta da take wankin dashi tana cewa.
"Iya gani nan fa"
Iya ta kalleta da kyau tana cewa.
"Ohhh ashe ke ce a nan?, ai na ɗauka ƴaƴan nan ne"
"Eh Iya ni ɗin ce dai"
"To ki same ni a ɗaki ke da marar kunyar nan Mubeena ina son magana daku ne yanzun nan"
Gaban Inna ne ya yanke yayi wata irin faɗuwa, har saida ta rufe idonta da ƙarfe tana tsaye tsawon minti biyu bata fargaba har saida ta fara jin maganar Iya na sake ce mata.
"Wai baki ji miye na ce bane Binta?"
Inna kamar wacce ta dawo daga duniyar tunani haka ta ɗan firgita kaɗan tana saurin girgiza kai haɗe da cewa.
"Iya naji mana, yanzu zaki ganku tare da ita"
"To yayi ina jiran naku"
Iya ta ƙare maganar tana shigewa ɗakinta, tabar Inna da zullumin abunda Iyar ke son ƙullawa.
Tana sauke wani goran lumfashi ta taka a hankali ta shige ɗakinta, dasu Mubeena ke kwance suna ƴar fira tun ɗazu.
Tana shiga ta iske Mubeenar harta fara baccin ranar data saba a ƴan kwanakin.
"Ke Mubeena tashi na ce"
"Inna lafiya dai?"
"Hmm inafa lafiya Iya na son ganina dani da wannan marar jin"
Inna ta ƙare maganar tana nuna Mubeena data ɗan miƙe zaune tana murje idonta dake cike da bacci.
"To ni Inna miye nayi kuma yanzu?"
"Yo waye yasan miye kikai?, ai kinfi kowa sanin abunda yasa Iyar ke son ganin naki, kin mance furucin da kikai na hana auren ƴar uwarki Na'ima ne?, ai akan hakan take son ɗaukar mataki a kanki, domin dai karki bata matsala, kuma dama nasan wacece Iya bata taɓa bari wani abu ya shige mata gaba muddun dai zai bata matsala a shaaninta to tabbas duk yadda zatai sai tasa an kauda mata shi"
"To amma Inna tsakani da Allah mu kenan bamu da yadda za'ai muyi gaban kanmu, sai ace kawai Iya ce kawai keda ikon yanke hukunci akan rayuwarmu?, kuma shikenan idan ta ce abu sai anyi?"
"Hmm Khadija kenan to ya zanyi, tunda har ku ɗin suna da iko akanku, ke dai kawai ni ina maku addu'a kullum Ubangiji ya yanke maku wannan zaman kowacce tayi aurenta, dan ni idan kukai auren ma bar mata gidan zanyi, dama saboda ku ne naƙi tashi wallahi, saboda kuma ba inda zan iya zuwa idan na ce zan tafin, banda kowa sai ƴar uwata Zubaida to itama tayi nesa dani"
Shiru sukai su duka kamar jikinsu yayi sanyi yadda Innar ke magana cike da sanyin jikin itama.
"Kinga Mubeena taso ki biyo ni"
Inna ta faɗa tana yin gaba.
"Ki tashi kije mana"
Tashi tayi tana kallon Na'ima datai maganar tana daga kwance itama.
A hankali ta doshi ƙofar ɗakin Iya da Inna ta rigata shiga tun ɗazu.
"Ohh wato ita shafaffa da mai ɗin saita ga dama zata zo kenan?"
"A'a Iya ai gata nan ma zuwa"
"Mtsww wallahi Binta kina bani mamaki, ace yara ke juya ki kamar waina, yanzu ni da ni ce dan ub*nta ba dole ta biyo ni ba, amma ji sai yanzu taga damar zuwa"
Ita dai Inna bata sake magana ba, sai Mubeena data shigo ta samu waje ta zauna ta zafga ma Iya hararara kamar idonta zasu faɗo.
"Eh ba shakka ai da hararar nan da kike aiko min da kawai zuwa kikai kika rufe ni da duka ai, sai nasan kin isa kin kuma kai, kinga ba sai ki rage jin haushin nawa da kike yi ba hamshiƙiya?"
Zatai magana harta buɗe baki Inna ta jefa mata wani kallo girgaɗi yasa ta haɗe maganar dake bakinta tana turo baki harda sakin ƙunƙuni.
"Ki faɗi abunda ke ranki mana, ya zakiyi shiru kuma?, ai nasan dai wannan shirun ba dan Allah ki kai ba"
"Yanzu dai dan Allah Iya kiyi shiru haka nan, gamu dai munzo ai"
"Ke nifa Binta naga kema yanzu kamar kina shirin fara yaɓa min magana marar daɗi fa, ko dai ƴaƴan naki sun fara hure miki kunne ne banda labari?"
Girgiza kai Inna tayi zatai magana Mubeena ta kasa haƙuri ta ce.
"Shin wai Iya miye na duk wannan ne?, ba magana zakiyi damu ba wai?, to munzo ki ɗakko maganar data sa kika taso mu mana?, idan kuma baza kiyi ba wallahi ni zan miƙe nabar wajan nan haba"
"Lahhh haula, ni kike kallon tsabar idona Mubeena kike gayan magana har haka?. Koda yake ba mamaki ai tunda yanzu kin gama fitsarewa, wacce tafi hakan ma zaki furtata ne ai ba mamaki, fitsararra kawai"
"Yanzu dai Iya muna sauraronki dan Allah duk ya isa hakan ayi hakuri"
Iya ta wani sauke lumfashi tana sake gyara zama babu wasa ko dariya yanzu ta fara magana tana cewa.
"Na yanke hukunci zan tura Mubeena can wajan z....
Da wani irin sauri Inna ta katse Iya gabanta na faɗuwa sosai ta ce.
"Iya dan girman Allah kiyi hakuri akan abunda Mubeena tayi miki, amma karki tura ƴata wani wajan daban, wallahi duk maganar da take faɗa faɗarce kawai amma bawai iyawa zatai ba"
"To sannu masu ƴa, ni ai ba tawa ba ce ai ko?, kuma ma ai kin bari kiji hukuncin dana riga na yanke ai ko?. Kuma babu fashi wallahi sai Mubeena tabar gidan nan kinji na gaya miki ma, ni nafi ki ma sanin wacece ƴar taki, idan wannan mai ibilishin a saman kai ta ce zatai abu to da wahala bata yisan ba wallahi"
Iya ta ƙare maganar tana nuna Mubeena da yatsa.
Mubeena tabi Iya da wani mugun kallo tana murguɗa mata baki.
"Amma Iya...
"Kinga ba wani abu na yanke ba sai na tura Mubeena Lagos wajan ƴar uwarki Zubaida taje can ta kwana biyu kamin a gama bikin nan sai ta dawo, amma fa bawai zama zatai can ta wani daɗe ba, A'a zansa aje a dawo da ita, ta dawo itama mu duba wadda ya dace da ita ayi mata auren itama, tunda naga yanzu tashen balaga take yi ai, dan naga yanzu dai-dai take da kowa take gani"
Wata irin ajiyar zuciya Inna ta sauƙe ai bata taɓa kawo hakan a ranta ba itama, ta ɗauka ko wani wajan daban Iyar zata ce a tura Mubeena ɗin, sai gashi ra'ayinsu ya zo ɗaya da Iya ɗin, to amma itafa zata tura Mubeena ne badan ta dawo yanzu ba gaskiya, tana so taje can ta samu kyakykyawar rayuwa, harta kaita da samun miji a can ɗin, ita fatanta ma ace aure ne kawai zai dawo da ita garin, kuma zata san duk mai yiwuwa Mubeena ɗin idan har tabar garin ba yanzun ba dawowarta.......
PAGE 35
*HAJA POV*
"Bana jin daɗi ne Ammi bazan iya yin komai ba yau"
Cewar Aunty Haja tana kwance akan tabarma dake shinfiɗe a tsakar gidan.
Ammi ta ce.
"Wai mike damunki ne Hajara?"
Taja lumfashi kaɗan tana tashi zaune kaɗan ta ce.
"Ammi yau fa kusan sati ɗaya da gama aikin nan amma shiru kake ji, abun ne ke damuna Ammi"
Ammi ma tayi shiru tana jinjina kai zuwa can kamar zatai maganaa Aunty Sa'a ta fito tana zama kusa da Aunty Haja ta dafata tana cewa.
"Ki kwantar da hankalinki please aikin nan fa saiya cisa, kawai kiɗan ƙara hakuri"
"Haba dai Aunty Sa'a yau fa sati ɗaya da gamawa kuma nayi komai yadda aka ce min, kawai ni abun mamaki ma yake bani fa"
"Akwai mamaki kam gaskiya ko ni ma mamakin nake yi ai, amma tabbas asiri ai gaskiyar mai shi, kuma ni a yadda ya ce mana ai kina gamawa zai fara nemanki da kansa, to ya akai haka zata faru kuma?"
"Yawwa nima abunda yake bani mamaki kenan da tsoro ai"
Maryam dake fitowa ta zauna itama sai ta ce.
"Karki wani damu Aunty Haja tashi zakiyi anjima muje wajan wani Malami da ƙawata ta taɓa kaini wajansa amma rakata nayi, shima daga gani aikin nasa nayi wallahi, nasan inda yake bama sai na gaya ma ƙawar tawa ba, zuwa kawai zamuyi na kaiki wajansa, ko Allah zaisa a dace da aikin nasa yayi"
Sauke lumfashi mai zafi Aunty Haja tayi tana jin wata ƴar kwarin gwiwar na zo mata.
"Shikenan Maryam ai ko yanzu ma zan iya tashi na shirya muje kawai"
"Shikenan to ki tashi ki lallaɓa ki shirya ɗin"
Cewar Maryam tana ɗan tashi itama ta shige ɗakinsu domin shiryawar itama.
"To hankali ya kwanta ko?"
Ammi ta faɗa tana kallon Aunty Haja dake tashi tsaye da kyar kamar wacce ta shekara tana ciwo.
"Hmm Ammi ai ni hankalina bazai taɓa kwanciya yadda nake so ba har sai Alhaji Ma'aruf yazo hannu yazo an gama maganar aurenmu kawai shine zan iya samun kaina dai-dai, ni nasan hakan, wallahi har cikin raina nake jin Alhaji Ma'aruf sai ka ce wani aikin asiri fa"
"So ne kawai kuma bai miki adalci ba"
"Hmm bari Aunty Sa'a ni kaɗai nasan yadda nake ji"
Ta ƙare maganar tana wucewa zuwa ɗaki domin shiryawar ta barsu suna magana akan matsalar.
"Wai Aunty Haja ina zaku je ne haka kuke ta shiri keda Aunty Maryam?"
"To tambai ina ruwanki?, wai ban hanaku shiga irin wannan abun ba?"
Turo baki Fannah tayi dake zaune gefe tana kallon Aunty Maryam datai maganar.
Aunty Haja na saka kaya itama ta ce.
"Ba inda zamuje zamu fita ne ta kaini asibiti ai kin san bana jin daɗi ko?"
Ɗaga kanta kawai tayi daga nan ta miƙe tana ficewa daga ɗakin dan bawai dan ta yarda asibitin zasu je ba.
"Mtsww ayo mutum sai tabbayar tsiya?"
Aysha dake kwance akan katifa tayi murmushi tana kallon Maryam datai maganar ta ce.
"Ai so take ƙila kuje da ita duk inda zaku je ɗin, kin san Fannah akwai son yawo ba kamar Hannah ba da ba ruwanta, dan ita idanma yawon kake son zawa da ita to sai ta ɓata maka lokaci, amma Fannah da son ganin gwaf"
"Ai shi yasa wani lokacin ma Hannah ta fita daɗin sha'ani fa"
"To ai ita Hannah bata cika saka baki a irin wannan ba, barta dai da sako baki ta ce zatai ma mutane wa'azi shine kawai, shima saita fahimci idan abunda ake bai dace ko ba dai-dai bane"
Aysha ta faɗa tana miƙe zaune sosai kamar zata sauka daga katifar sai kuma ta zauna sosai tana kallon yadda suka gama shiryawa tsaf zasu fita ta ce.
"Ina zuwa ne wai, nima nayi ta Fannah ɗin?"
Ta ƙare maganar tana sakin dariya.
"Hmm bari Aysha zuwa zamuyi