Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
*TAURIN KAI*
*ZAHRA ROYAL STAR*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*
*Tsokaci*
Littafin *Taurin Kai* na ɗauke da wani babban darasi na rayuwa, musamman ga iyaye mata da ‘ya’ya mata. Yana bayani ne kan yadda rashin tarbiyya da son duniya ke iya lalata rayuwar yara, musamman idan uwa ta gaza fahimtar nauyin da ke kanta.
A cikin labarin, an nuna irin yadda wata uwa ke amfani da ‘ya’yanta mata wajen cimma burinta na duniya, ba tare da la'akari da tasirin hakan ga rayuwarsu ba. Wasu daga cikin su har matan aure ne, amma hakan bai hana ta raba su da mazajensu ba, domin kawai su dawo gidan iyaye su rika zama abin amfani gareta.
A daya hannun, akwai ɗaya daga cikin ‘ya’yan da ta ƙi bin wannan tafarki, duk da ƙoƙarin da aka yi na lalata ta. Wannan kuwa shine babban sako na littafin — cewa duk da yadda yanayi zai kasance, mutum na iya tsayawa da gaskiya da akida idan har yana da imani da kai da kuma goyon bayan Allah.
*Taurin Kai* ba wai kawai labari bane, darasi ne mai zurfi da ke haskaka illar rashin tarbiyya, kwaɗayi da sakacin uwa, da kuma ƙarfafa gwiwar waɗanda ke ƙoƙarin tseratar da rayuwarsu daga mummunan tasiri.
PAGE 1
*Ƙofar Marusa, Katsina state Nigeria*
Sanye dake take da kayan Islamiyya a jikinta, Hijab ɗin har ƙasa dan har tana jan ƙasa idan tana tafiya. Tana tafiya a hankali kamar mai tunanin wani abu daban, sai dai gabanta take kallo inda ta hango Aunty Haja tsaye da wani jifgegen mutum a ƙofar gidansu.
Lumfashi kaɗan ta sauke tana bin wata Mota dake parke a ƙofar gidan. Jingine suke jikin motar suna fira da hara kamar wa'inda suka daɗe da sanin juna.
Tana zuwa ƙofar gidan taja ta tsaya tana girgiza kai zatai magana Aunty Haja ta wani ɓalla mata wani mugun kallo haɗe da hararara tana nunata da yatsa ta ce.
"Ahir ɗinki bakin nan naki ya furta wani lafazi wallahi, dan kin san Allah yau mai raba ni dake a gidan nan sai Allah kawai"
"Amma Aunty Haja abunda kike ya dace kenan ace da au...
"A'a wai kune dama a tsaye a ƙofar gidan ne?. Ai kamata yayi ke Haja ki shigo daga ciki, kin san unguwar ne akwai fa ƴan sa ido"
Ammi ta faɗa tana yin wuff ta katse lafazin da Hannah ke son furzarwa.
"Ammi kiyi ma Hannah magana bana son tana shigar min hanci, zan fyato ta ne wallahi"
"Dalla rabu da ita. Ke zo ki wuce ciki shashasha marar zuciya kawai, wacce ta gado ƙashin tsiya wajan ubanta"
Wani malolan baƙin ciki ne ya tokare maƙoshin Hannah tana duban yadda Ammin ta fito daga ita sai wani yalolan mayafi wadda da kyar ya iya rufe mata jiki, kuma daga ita sai ɗaurin ƙirji.
Shi ko ƙaton mutunen dake tsaye tare da Aunty Haja sai satar kallon Hannah yake, dan ba ƙaramin tafiya tayi da imaninsa ba, saboda duk cikin ƴaƴan Ammi Hannah ɗin tafi su kyau nesa bama kusa ba, kusan za'a ce ita ce ta kwaso kyan Mahaifinsu wadda ya kasance Fulanin asali ne irin na daji, duk da itama Ammi ɗin bafullatana ce amma mahaifinsu Hannah yafita kyau nesa ba kusa ba.
"Zaki zo ki wuce ne ko sai nazo miki kina tsaye nan kamar wata gunki?"
Jiki a sanyaye ta taka ƙafarta ta wuce cikin gidan nasu da ko arziƙin ƙyaure bai samu ba. Ginin ƙasa ne irin nada wadda aka shafe shi da sumunti. Ƙasan gidan ƙasa ce, amma gidan tsaf-tsaf yake dan kwata-kwata Hannah bata son ƙazanta, kusan duk ita ce mai gyaran gidan, da kauda duk wani abu.
"Afayi haƙuri ranka ya daɗe, yaran ne sai a hankali"
Murmurshi ya saki kawai yana saka hannunsa a aljihun wandonsa ya zaro ƴan ɗari biyar-biyar bandir guda.
Ido waje Ammi ke kallon kuɗin ita ko Aunty Haja sai ta wani maze tana haɗiyar miyau, dan ji take kamar ta warce kuɗin.
Miƙa ma Ammi yayi. Jiki na rawa ta miƙa hannu tun kan ya ce wani abu ta amshe kuɗin ta washe baki kamar gonar auduga.
Ai sai ta zube ƙasa tana kwasar godiya kamar bakinta zai zage dan godiya.
Har sai da Aunty Haja ta ɗan taɓe baki tana kallon Ammi ta ce.
"Kinga Ammi ya isa haka dan Allah, kije gida kawai haka nan"
Washe baki Ammi ta ƙarayi tana ƙara damƙe kuɗin ta ce.
"To ƴar albarka sai kin shigo ɗin. Alhaji munfa gode Allah dai ya baka abunda kake nema duniya wa lahira wallahi"
Ta ƙare maganar ta idasa shigewa cikin gidan.
"Baby gaskiya ƙanwar nan taku fa tayi. Da ace zata bada haɗin kai ai ba ƙananun kuɗi zata jawo maku ba. Wannan kyawu nata ai ko ina za'aje da ita"
Taɓe baki Aunty Haja tayi tana dubansa sosai ta ce.
"To ka ganta nan babu irin huɗuba da bamuyi mata ta waye amma ina, gata nan kamar bagidajiya, ba abunda ta sani"
"To amma babu yadda za'ai ku jawota cikin harkar nan ta arziƙi, dan gaskiya sai ta fiku kawo wuta nake gaya miki, da ace zata yarda zuwan da zamuyi Abuja dake nanda sati ɗaya mu wuce da ita, wato ko Haja ba ƙaramin kuɗi zaku dawo dashi ba daka ke har ita, dan wannan gidan naku tabbas sai kun saka an rushe maku shi an sake maku sabon gini na zamani"
Ɗan fiddo ido Aunty Haja tayi tana kallonsa sosai kamin ta ce.
"Allah Alhaji na?"
"Sosai ma kuwa. Wai duk ɓuɗewar idonku baku taɓa fita irinsu Abujar nan ba da Logas haka?, ai can ake samo manyan kaya ba wai ku zauna a nan ba, ai nan ba manyan kwari"
Dariya Haja ta saki tana cewa.
"Kuma fa haka ne maganar ka wallahi, yawanci duk ƴan ƙarya sunfi yawa. Ai ni na ƙagara naje Abujar nan fa dan....
Maganarta ce ta maƙale hango Umar tafe ta layin gidan nasu.
Tun nesa ya gane wacece tsaye.
Wani kalar baƙin ciki ne ya ciwo Umar yana ƙarasowa, ransa a mugun ɓace yake duban Haja.
Nunata yayi da yatsa yana cewa.
"Haja da auren nawa a saman kanki kike tsayawa da wani ƙaton garɗi?"
Murguɗa masa baki tayi tana baƙin cikin zuwansa wajan a ranta.
"Kaga Mlm ka manta miye ka ce min ne?. Cewa fa kayi na tafi gidanmu har sai lokacin da ka neme ni, dan haka na taho gidan namu. Kusan yau wata na ɗaya gida, baka neme ni ba, na ɗauka ko sakin nawa kayi ban sani ba, haka kawai zaka ce na taho gida?, kai baka ƙara waiwayata ba sai kuma na zauna ni shikenan na mutu a haka nan?, saboda ga sakarai wacce bata san ciwon kanta ba ko?, dan haka ni dan Allah Mlm ka rabu dani, Allah ma yasa takarda ka zo kawo min ta saki"
"Saki Haja?"
"Kware kuwa ka sake ni Mlm ana dole ne?. Daɗi na ma ɗaya ba haihuwa mukai dakai ba, dan haka ba yaro bare goyo ka sake ni kawai Mlm na ce"
"To bazan sake kin ba na ce"
"To kuwa zaka ga yadda ake wallahi, zaka san wacece Haja"
"Yo miye baki gama nuna min ba a cikin baƙaƙen halayenki Haja?, ai nayi dana sanin saninki wallahi Haja"
"To idan har kayi dana sani ka sake ni man"
"Na ce bazan sake kin ba. Ke bari ma kiji, wallahi duk yadda zakiyi sai dai kiyi babu saki a tsakaninmu"
"Kaga Alhaji nah, sai munyi waya da kai kawai, wannan shashashan ya zo ya ɓata mana bajat"
Alhaji yana murmurshi ya ce mata.
"Kin san shi talaka haka yake baƙin ciki ne cike da cikinsa kullum, yaga zaki ci gaba dole ya nuna miki ainafin shi talaka ne mai baƙar zuciya. Kai bawan Allah yanzu wannan idan banda ƙaddara ai ba kalar ka ba ce, kalar masu kuɗi ce wallahi"
Wani kalar baƙin ciki ne ya ciyo Umar, dan haka bai san lokacin daya watsa ma Alhajin wani mugun kallo ba yana sake nunasa da yatsa ya ce.
"Kai fasiƙi marar tsoran Allah ya isheka haka. Wallahi kaji tsoron Allah. Na ɗauka da kaji cewar akwai aure a kanta kaja baya da ita, ka nuna rashin dacewar abunda tayi na tsayawa da kai, amma sai ka nuna ma ko a jikinka, tsabar dama ka kware wajan neman har matan auren. Kai dama daga ganinka baka tsoron Allah wallahi"
Alhaji zaiyi magana Aunty Haja ta fara lallaɓasa dan taga shima ya hau sama komai na iya faruwa tsakaninsa da Umar ɗin.
Bayan Alhaji ya hau Mota ya tafi har lokacin Umar nata ɓaɓatu yana zagin Alhaji kamar zai ari baki.
Wani mugun tsaki Haja taja zata shige gida Umar ya shiga gabanta.
"Miye haka Mlm?"
Ta faɗa tana watsa masa wani banzan kallo.
"Kiji tsoron Allah wallahi Hajar"
"Hmm au da tsoronka nake ji ne idan bana tsoron Allahn?. Kaga Mlm idan kana son kanka da arziƙi ka kawo min takardar saki na har gida, ina nan ina jiranka"
Zata raɓasa ta wuce ya sake tare mata gaba.
Aysha ce ta sawo kai a zauren gidan zata fita. Sai taja ta tsaya tana bin Umar da wani kallon uku saura kwata.
Ta shiga nuna Aunty Haja da hannu tana faɗin.
"Wai Aunty Haja jiran mi kike da wannan mijin naki da baza kiyi masa akuyanci ba ya baki takardar sakin ki?. Hmmm ni wallahi da ni ce da tuni an wuce wajan kin sani. Gashi nan kamar bushashshan buredi ko aukin jiki babu kike tsayawa yana baki ciwon kai"
"Duk ƙarshenta haka zan masa ne Aysha wallahi tunda shi baya da zuciya a ƙirjinsa. Ko kuma na makasa a Kotu kamar yadda Aunty Sa'ade tayi ma nata tsohun mijin"
"Mtswww sakarai kawai ba. Ai Aunty Sa'ade dama nasan zatayi fiye da hakan, dama ita badan taso akai auren nan nata ba, lokacin tun Baba na raye ne, itama inda Allah yasa babu ɗa ko jika bare a kawo mata ciwon kai har gida wallahi"
Aysha ta faɗa tana raɓa su zata wuce Umar ya wani tsaida ita wajan cewa.
"Keeee Aysha ni zaki kalla ina mijin Yayarki kina kira na da sakarai?"
Wani birki taja tana dakatawa ta ɗan dawo baya kaɗan ta shiga masa kallon sama da ƙasa, kamin suga ta kwashe da wata shegiyar dariya.
Nunasa da yatsa ta ce.
"Au a hakan kai har wani kallon kanka kake a matsayin mijin Yayata?, to sannu na ce Mlm Garba. Gaskiya fa Aunty Haja kina fama. Ni dama na sani za'ai hakan ai keda Aunty Sa'ade kuna ganin jalala, waye ya gaya muku yanzu ana saurin fiddo da mijin aure ne?, ai kun bari ku gama cin duniyarku da tsinke tukunna, yanzu mu baga mu ba babu ɗa namijin da zai rinƙa tare mu yana mana wata shashashar tabbayar da aurensa akanmu ba, hmm ai wallahi kunyi ganganci, koda yake gara Aunty Sa'ade ta rabu da ƙaya kam saura ke ya rage"
Aysha ta ƙare maganar tana wuce su tana dariya.
Wani iri Umar yaji dama yasan indai Aysha ce zata faɗi abunda yafi haka ma, saboda duk tafi su iya rashin kunya ta kuma fiso buɗewar ido cikin ƴan matan gidan, dama kuma ita can lokacin da za'ai aurensu bata wani aminta da auren ba, dan bama ta nan akai bikin saida ta dawo ake gaya mata taita yi ma Haja faɗan taje ta shige ma faƙiri talaka, zatai dana sani ne.
"Kaga matsa ka bani waje zan wuce, ko kuma wallahi nasa ƙarfi na ture ka na wuce"
"Kai Haja ni ne fa Umar ɗinki?"
Wani kallo tabi sa dashi na sama da ƙasa tana cewa.
"Koma waye kai, ai da yake idon nawa tuwo ne a ciki da ban san waye tsaye a gaban nawa ba mtswww"
Ta ƙare maganar tana raɓawa ta gefensa ta wuce da sauri har tana bangaje masa kafaɗa.
Sake da baki ya bita da kallo......
*To jama'a bana kuma ina maku faɗo?. Labarin ya banbanta da wadda na saba kawo maku, yanzu aka fara tafiyar fa, kawai ku gyara zama masoya.......✍️*
*TAURIN KAI*
*ZAHRA ROYAL STAR*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.......*
PAGE 2
*HANNAH POV*
"Amma ammi dan Allah dan Annabi ya dace Aunty Haja na irin wannan abun da aure akanta?"
Wani kallo Ammi ta juyo tana jefama Hannah shi na tsabar jin haushinta dama cike take da ita ta shigo gidan.
"To wai ke ina ruwanki ne Hannah?, kefa wallahi kin fiye shiga abunda bai shafe ki ba haba"
"Yanzu fisbilillahi Aunty Sa'a kema haka zaki ce?"
Taɓe baki Aunty Sa'a tayi tana gyara zamanta akan kujera ƴar zugunne da take zaune akanta a tsakar gidan nasu.
"Rabu da ita Sa'a wallahi Hannah idan baki fita daga ido ba saina mummunan ɓata miki rai. Ace ayo ki ke kaɗai cikin gidan nan kin fita daban, wai ko dai canza min ke akai a asibiti ne ban sani bane?"
Turo baki Hannah tayi tana kallon Ammi zatai magana Aunty Haja ta shigo cikin gidan.
"Yawwa Ammi kiyi ma wannan ƴar taki gargaɗi na rantse ba ruwanta dani. Bazai yiwu ba ace yarinya ta zo tana ɓata min bajat ba. Shima wannan ƙaton banzar Umar ya zo yana neman ɓata min rai"
"Fatan dai ya baki takardar sakin ki?"
Aunty Sa'a ta faɗa da sauri.
Zama kusa da ita Aunty Haja tayi akan wani turmi tana yaye gyalen data yafa a jikinta ta ce.
"Inafa ɗan wahala, nayi-nayi amma yadda kasan sake zugasa ma nake naƙin sakin nawa"
"Mtsww wallahi sai kin tashi tsaye, ni yanzu ba gashi ba dana na ce zan makasa a kato dole ya biyo ni da tawa takardar ba"
"Uhm ni duk ƙarshenta ba rabuwar daɗi....
"Haba Aunty Haja, anya kuna towa da duk macen data nemi saki a wajan mijinta Ubangiji yana fushi da ita, sana shi sakin kansa idan aka yisa al'arshil Allah girgiza yake fa"
Hannah ta katse Aunty Haja tana faɗin hakan.
Ammi ce ta saki tagumi tana bin Hannah da kallo kawai zuwa can ta kasa haƙuri ta ce.
"Hannah ki kiyaye ni wallahi. Wai ni kam ya ake so nayi da wannan jarababbar ƴar ne?. Ke shikenan duk abunda mutum yayi sai kin kawo wani wa'azi naki?"
"Kuma wallahi Ammi da ace zata waye da sai duk tafi mu samun naira da hutu, amma da yake bagidajiya ce taƙi fahimtar hakan"
"Komi za'a ce min ace min amma bazan taɓa ɗaukar irin wannan rayuwar taku ba wallahi"
"Ai kin mutu a tsiya cen ki kuwa, da wannan saurayin naki Ya Ustaz kuke ce masa ko mi, ba abunda ya aje, shima da kyar yake samu ya ciyar da kansa da ƙannansa. Nifa wallahi kunya ma kike bani, tun wuri Ammi ya kamata ki ɗau matakin rabasu wallahi, kashe mata rayuwa zaiyi kawai"
Wani kalar tashin hankali ne ya ziyarci Hannah dake tsaye har lokacin, dan tasan Ammi dama bata iya abun kanta Yayyan nan nata suna faɗin abu to kuwa sai ta yisa.
Wata hararara Hannah ta ɓallama Maryam data fito daga ɗakin da suke kwana ta nunata tana cewa.
"Aunty Fannah ba ruwanki a ciki, bana son irin haka gaskiya"
"Ai ke kinji matsalarki, ana hango miki makomarki amma kina botsarewa, kika sake kika auri wannan Ya Ustaz ɗin wallahi kinga yadda Ammi ta koma kamar tsohuwar data kusa shekara ɗari ko tamanin haka zaki koma kema"
Fannah ta ƙare maganar tana nuna Ammi dake zaune akan tabarma tana dubansu.
"Kefa Fannah baki da kunya yanzu ni ce na tsufa kamar wacce ta shekara ɗari?. Ai talaucin Ubanku ne ya maida ni hakan nan, shi yasa bazan taɓa bari ku auri irin ubanku ba wallahi. Ita kuma Hannah ɗin ai shi Ustaz ɗin zai zo har ƙofar gidan nan ne ya same ni, da kaina zan fita na gaya masa ya fita harkar ƴata ba sa'ar yinsa bace"
Bubbuga ƙafa Hannah ta fara yi tana son sakin kuka tana cewa.
"Ni dai wallahi Ammi ina sonshi a hakan, a barni dashi, ai ni zan zauna dashi ba wani ba ko?"
Tsintsinyar dake kusa da Ammi ta ɗauka tana jefama Hannah tsintsinyar, sai akan jikinta Ammi cike da fushi ta ce.
"Dalla sakarai kawai, yo dama waye zai zauna miki dashi ɗin ai ke ce, amma bazan bari kiyi mutuwar tsaye ba, kinji na gaya miki. Ni ɓace min da gani ma ko yanzu na tashi na ƙara ɓata miki rai yanzun nan"
Hannah na ƙunƙuni harda wasu guntun hawaye akan fuskarta ta juya tana nufar ɗakinsu tana jin wani irin baƙin cikin kasancewar gidansu irin haka, kuma duk mutuwar Babansu ce yasa Ammi ta koma hakan, da kuma laifin danginsa da nata, da babu ruwansu dasu, tunda ɗan uwansu ya mutu kowa ya daina shiga harkarsu, musababin ƙara taɓarɓarewar gidan nasu kenan, dama kuma gashi can dama haka ƴan gidan nasu suke da son duniya da kuma kyale-kyalen cikinta, mutuwar Mahaifin nasu saita ƙara bauɗe masu tunani. A cikinsu su shidda ita ce auta ƙarshen haihu, daga ita ne Ammi bata sake haihuwa ba har Babansu ya kwanta dama, kuma babu namiji ko ɗaya cikin ƴaƴan nata, duk mata ne.
"Mtsww tana tafiya simi-simi"
"Wai wama ya canza tunaninta ne haka?, ai da a sanina itama idan muka rotsata tana ɗaukar shawara, amma yanzu ta koma Malamar ƙarfi da yaji"
Faɗin Aunty Sa'a.
"Hmm yo waye fa yake hure mata kunnen idan banda Ustaz ɗin nan Malamin Islamiyar da take zuwa duk shine fa. Kuma wallahi Ammi da gaske idan baki raba su ba sai ya tarwatsa mata rayuwa. Yo ni da ace ni keda kyau irin na Hannah hmm wohoho da ansha kallo, wato zan rinƙa ɗaukar hankalin mutane ne na bala'i ma, gata da duk tafi mu kyan jiki dana sura"
Aunty Fannah ta faɗa tana miƙewa ta nufi wata tukunya dake bakin murhu.
"Ai ki barni da ita zata ga matakin da zan ɗauka ne daga ita har shegen Ustaz ɗin nata"
"Wai