KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   9 / 40

24K to 27K   out of 119.4K words

rayuwa.

Amma yau? Ita ce ta bayar da umarnin a kama ta? Ita ce ta so a nakasta Hammad? Ita ce ta nemi a cire wa Nabeeha mutuncinta?

Hajiya Zaytunah ta rike kanta da hannaye biyu. Kamar zuciyarta za ta faso KIRJIN ta. Hawaye suka tsinke daga idanunta, suka gangaro kan fuskarta.

“Wai Rumanah ce? Ita ce ke kokarin ganin an kashe ni da ‘ya’yana?”

Ta girgiza kai cikin matsanancin firgici. Kamar mafarki take ji. Mafarki mai cike da tsoro da tashin hankali. Idan aka ce ta fada mafarkin da zai firgita ta, wallahi ba ta taba tunanin wannan ba.

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, ta fashe da wani sabon kuka mai tsananin radadi.

“Rumanah, me na miki?”

Sai a lokacin ta fara tuna wasu abubuwa da suka faru a baya. Kodai tun tuni take ginin kiyayya a zuciyarta? Ta cika da tsananin mamaki!

Wata zuciya ta ce mata “Idan har Rumanah ta kai ga bayar da umarnin a bata Nabeeha, hakan na nufin babu wani abu da ba za ta iya yi ba.”

Zaytunah ta dago, idanunta sun yi jajir.

“Dole ne a dauki mataki!”

Hajiya Zaytunah ta yi shiru na tsawon lokaci, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi, tamkar zata faso kirjinta. Hawaye suka ci gaba da gangarowa daga idanunta, hannayenta sun yi sanyi, jikinta ya dauki rawa.

"Rumanah?" Ta sake maimaitawa cikin rauni. "Ashe ke ce kika kulla wannan makircin? Ke ce kika so a bata Nabeeha? Ke ce kika so a nakasta Hammad?"

Wani irin sanyi da radadi ya ratsa ta. Babu abinda ke kara huda zuciyarta kamar tunanin yadda ita da Rumanah suka taso tare, suka raba komai, suka rayu tamkar yan biyu.

"Wai har kin kai matsayin da ba kya jin tausayin jinin ki? Har kin kai matsayin da zuciyarki ta zama kamar dutse, babu tausayi ko kadan?"

Ta runtse ido, tana jin yadda numfashinta ke fita da kyar. A zuciyarta, tambayoyi sun yi mata caa.

Zaytunah ta dago kai, ta share hawayen da ya cika fuskarta. Duk da bakin cikinta, zuciyarta ta fara kallon wannan matsala a wani sabon salo.

Idan har Rumanah ta aikata haka, hakan yana nufin cewa akwai wani abu a zuciyarta tun tuni da ba su fahimta ba. Me ya sa ta tsane su haka? Me yasa take ganin su a matsayin abokan gaba?

"Ina jin akwai wani abu da zan gano." Ta furta a hankali.

Dole ne ta fahimci SIRRIN Rumanah, ta gano dalilin kiyayyar da take yi musu. Kuma kafin ta dauki mataki, dole ta tabbatar da cewa komai a fayace.

Ta numfasa da kyar, ta juyo ta kalli su Gora da suka gama sanar da ita SIRRIN da suka samu. Ta yi shiru na dan lokaci, sannan ta ce da su cikin murya mai tsanani,

"Kun ce min Rumanah ce ta dauke ku aiki?"

Gora ya gyada kai cikin girmamawa. "Eh, Hajiya. Ita ce ta biya mu, ta ce mu tabbata mun bata miki rai. Ta ce mu yi duk mai yiwuwa domin mu tabbatar da cewa kin yi nadamar rayuwa."

Wani takaici ya sake turnuke zuciyar Hajiya Zaytunah. Ta numfasa a hankali, sannan ta ce:

"Ba damuwa. Na gode da gaskiyar da kuka gaya min."

Ta juya tana kallon kofar da ke gabanta, zuciyarta na cike da sabbin tunani. Wannan abu ba zai kare haka ba. Dole ne ta dauki mataki.


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
**KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE: 14_


Captain Fawaaz ya jinjina kai, bai ce komai ba. Idanunsa sun sauka kan na’urar tracking da ke gabansa, ya tuno da sakonnin daya turawa Nabeeha, Wannan yana nufin cewa a wannan lokacin layinta yana bisa sabis, kuma hakan na iya basu damar gano inda suke.

Ya matsa wani maballi a kan na'urar, ya duba taswirar da ke gabansa. Hanyar da suka bi tana da wahala, sai dai a haka ma ba zai yi kasa a gwiwa ba. Yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Ko da yake ya saba da irin wannan aiki, wannan yana da bambanci , Yana nufin ceto most beloved love of his life, Wato Nabeeha.

"Kayi tracking ɗin network ɗin nata?" Lieutenant Ibrahim ya tambaya.

"Eh," Fawaaz ya amsa, yana duba wani karamin screen a gefen dashboard. Ya kara danna wasu maballan sannan ya ce,

"Anan sakon ya shiga, daga nan zuwa wani wuri a kusa da gabar rafin Chida."

"To, akwai wata gada kusa da wannan rafi, amma an ce tana da matsala, babu wanda ke amfani da ita," Warrant Officer Suleiman ya kara da furtawa, yana duba bayanai a cikin wata ƙaramar kwamfuta.

"To lallai sun bi waccan hanyar," Fawaaz ya yanke hukunci.

Sai ya kara gudun motarsa a hankali, yana bin alamar da suka samu. Sauran motocin biyu da ke biye da su suma suka kara saurin tafiya, dukkansu cikin shiri. Su na ci gaba da tafiya cikin dajin, tayoyin motocin su na dannan ciyayi da ƙurar dajin.

Kusan mintuna talatin suna tafiya, sai na’urar tracking ɗin ta soma nuna wani matsayi kusa da su. Zuciyar Fawaaz ta buga da sauri.

"Alhamdulillah suna nan kusa," ya furta da wata murya mai ƙarfi.

Yana tsayar da motarsa a hankali, sauran motocin suma suka tsaya. Dukkaninsu suka kama bindigoginsu suna shirin fuskantar duk wani haɗari.

"Mu fita a hankali. Kar mu yi saurin motsi har sai mun tabbatar da yanayin da muke ciki," Fawaaz ya umarta, yana kokarin danne tsananin kwadayin da yake ji na ganin Nabeeha.

Sai suka rarrafa cikin dajin da taka-tsantsan, kowannensu yana duban gefen daji. Bayan kusan minti goma da shiru-shiru, sai suka jiyo wata murya daga baya,

"Da alama su ne can!"

Fawaaz ya zura zooming tool. Ya na ware ido, zuciyarsa na dukan uku-uku. A cikin wata ruguwar kwantaccen ciyayi da wasu tsofaffin bishiyoyi, ya hangi wasu mutane suna zaune kusa da wata karamar bukka. A tsakiyarsu, su Nabeehan sa ce!

Haj. Zaytunah tana zaune a gefe, tana rike da hannun Hammad da ke jin tsoro sosai. Nabeeha kuma tana a gefe, idonta cike da damuwa. Sai kuma wasu mutum biyu, Gora da Bala, waɗanda suke kallon gefe-gefe, suna jin wani irin damuwa.

Fawaaz ya dan zaro iska daga bakinsa, yana kokarin nutsuwa. Amma a zuciyarsa, yana jin wani irin ƙarfi da ƙwazo sun lullube shi.

"A shirya!" ya furta cikin sassanyar murya. "Zamu yi aiki mai tsabta. Nabeeha da sauran su na bukatar mu."

Babu wanda ya musa. Sun san cewa wannan aiki ne da ba za su bari ya gaza ba.

Fawaaz ya gyara rike bindigarsa, idonsa ya fi komawa kan Nabeeha. Ko da yake ba ta ganshi ba tukunna, amma ya san cewa cikin 'yan dakikoki, zai yi duk mai yiwuwa don ganin sun fita daga wannan wuri lafiya!

Fawaaz ya dan sunkuya yana lura da yanayin wurin. Binciken idanuwansa ya nuna masa cewa mutanen da suka yi garkuwa da su Nabeeha ba su da yawan makamai, amma hakan ba yana nufin ba su da hatsari ba. Ya san cewa su Gora da Bala mutane ne masu dabara, kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa wajen yaƙar su ba.

Ya yi alama ga abokan aikinsa su zagaya ta bangarori daban-daban domin su mamaye yankin da dazukan uku da suka rage, kudu, gabas dana yamma, Lieutenant Ibrahim da Warrant Officer Suleiman sun kama hagu, yayin da sauran suka kama dama. Fawaaz ya cigaba da lurawa da yadda ake tafiyar da abubuwa daga inda suke..

Nabeeha tana zaune a gefen Hajiya Zaytunah, idanunta cike da damuwa. Hammad yana nan rike da hannunta, yana ta kallon gefe cike da tsoro. Gora yana tsaye kusa da Bala, yana magana da wani karamin walkie-talkie, yana kokarin tuntubar wani a waje.

"Hello...."

Daidai lokacin, Nabeeha ta ji zuciyarta tana wani irin bugawa. Ta rufe idanuwanta na wasu dakiku, tana jin kamar numfashinta zai dauke. Amma cikin wannan yanayi na tsoro, sai wani tunani ya fado mata… Fawaaz!

Bata ankara ba, sai kawai ta ji karar wani abu yana kara kusa da su ,kamar motsin mutane cikin daji. Idanunta suka kai kan Gora, wanda shima ya ji motsin.

"Me ke faruwa?" Bala ya tambaya yana kai hannu kan bindigarsa.

A daidai wannan lokacin, Fawaaz ya bayar da umarni cikin walkie-talkie,

"Roger that soldiers..Yanzu! Mu Shiga!"

Cikin gaggawa, sojojin suka fantsama daga bangarori daban-daban! Wani dan karamin fashewar hayaki ya biyo baya, wanda ya sa Bala da Gora suka rude, suna kokarin zaro makamai.

Fawaaz bai bata lokaci ba, ya shiga ta babban kofar bukkar cikin matsanancin sauri, bindigarsa a hannu, idanunsa suna kan Gora da Bala.

"Kada ku motsa!" ya daka musu tsawa.

Bala ya yi kokarin daga bindigarsa, amma kafin ya ankara, sai Lieutenant Ibrahim ya karbe bindigar daga hannunsa. Gora kuwa ya yi kokarin tserewa ta bayan bukkar, amma kafin ya iya, Warrant Officer Suleiman ya cafke shi da karfi, ya buga shi kasa.

Fawaaz bai damu da su ba, idanunsa sun sauka kai tsaye kan Nabeeha!

Zuciyarta ta buga da karfi, tana jin kamar numfashinta zai tsaya. A karo na farko, ta ji wani irin kwanciyar hankali da ta dade tana jira.

Fawaaz ya taka kusa da ita, yana kallonta ido cikin ido. Babu wanda ya ce uffan. Ya mika mata hannu a hankali, idanunsa cike da nutsuwa.

"Kin ji tsoro?" ya tambaye ta da murya mai laushi.

Nabeeha ta girgiza kai, amma idanuwanta sun nuna cewa ta ji tsoro fiye da yadda zata iya furtawa.

Ba tare da wata shakka ba, ya kama hannunta ya rike da kyau.

"Don't be...Ssshhh is okayy" ya furta.

A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwa, tana fitar da ajiyar zuciya. Hammad kuwa ya ruga ya rungume Captain Fawaaz da karfi, yana kuka da murna.

Fawaaz ya dan matsa daga gefe, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Sauran sojojin sun riga sun kama Gora da Bala, sun daure hannayensu da igiya, sannan suka rufe musu baki domin su guji yin hayaniya. A gefe guda, Lieutenant Ibrahim yana duba motar da masu garkuwar suka kawo, yana tabbatar da cewa babu wani abin fashewa ko tarkon da zai iya kawo hatsari.

Nabeeha har yanzu tana tsaye a wurin, zuciyarta na harbawa da karfi. Idanunta sun cika da ruwaye, ba wai saboda tsoro ba, amma saboda yawan damuwar da ta sha. Har yanzu tana jin yadda hannun Fawaaz ke rike da nata , rikon da ya tabbatar mata cewa yanzu tana cikin aminci.

Fawaaz ya dan sunkuya yana shafa kansa, sannan ya ce, "Su daina damunki, Zamu mika su hannun hukuma, za su fuskanci hukuncin da ya dace da su."

Hammad ya dan yi shiru na wasu dakiku, sai daga baya ya jinjina kai. "Mungode, Captain brother!"

Fawaaz bai ce komai ba, sai ya mike tsaye, ya nuna musu hanyar da za su bi zuwa motocin su. Sauran sojojin sun bi sawu, suna rike da Gora da Bala da aka daure su.

A daidai lokacin da suka fara tafiya, sai Fawaaz ya lura da yadda Nabeeha ke tafiya a hankali, kamar wacce ba ta da kwari sosai. Bai yi wata-wata ba, ya dan riko hannunta, yana tafiya tare da ita.

"Kin gaji?" ya tambaya, amma yana kallonta cikin ido.

Ta dan yi murmushi kadan, sannan ta ce, "Kadan dai."

Sai da suka soma tafiya kafin Nabeeha ta iya furta wani abu.

Fawaaz bai ce komai ba. Amma a zuciyarsa, ya san cewa zai iya yin komai don ganin cewa ba ta sake fuskantar irin wannan hatsari ba har abada.

Zuciyar Fawaaz tana daka da sauri fiye da yadda ya saba ji. Hannunsa yana rike da nata, amma har yanzu ba ya jin hakan ya wadatar. Idanunsa na tafiya a fuskarta, yana nazarin ta, yana neman wani alamun ciwo ko wahala.

Idonta ya lumshe na wani lokaci, sannan ta bude su a hankali, tana jin yadda dumin hannunsa ke ratsata. A duk tsawon rayuwarta, bata taba ganin Fawaaz a irin wannan yanayin ba. Idonsa na bayyana damuwa da tsananin kauna, amma duk da haka yana kokarin boye hakan a karkashin miskilancinsa.

Ya dan tsugunna kadan gabanta, yana kallonta sosai. “Nabeeha…” ya kira sunanta da wata murya da bata saba ji ba, murya mai cike da soyayya da fargabar rasa ta.

Ta dago idonta ta kalle shi.

“Yaya Fawaaz…”

Ya dan rufe idonsa na dan lokaci, yana kokarin daidaita numfashinsa, saboda yadda sanyayyar muryarta Mai kama da ana busa sarewa ta doki kofofin kunnuwansa. sannan ya bude su da karfi, kamar wanda ya yanke shawarar cewa ba zai kara boye abin da yake ji ba.

“Ban taba jin tsoro irin na yau ba.”Ya fada a hankali, amma tare da zurfi..''Ban taba tunanin za a dauke ki ba, ban taba jin fargabar rasa wani kamar yadda na ji akan ki ba.”

Nabeeha ta kalle shi da sauri, zuciyarta na bugawa da karfi. Tana iya jin gaskiyar da ke cikin muryarsa. Bata taba jin Fawaaz yana magana da irin wannan zafin rai ba.

Ya dan sosa keyarsa yana jin yadda zuciyarsa ke tashi da wani irin yanayi da bai saba ba.

“Kin san me yasa na san daidai inda kike?” Ya tambaya, yana kallon cikin idanunta.

Ta girgiza kai a hankali.

Ya dan sauke ajiyar zuciya, sannan ya saki murmushi kadan,

“Saboda na riga na turawa zuciyarki saƙo.” ya fada cikin zuciyarsa.

Sai Kuma yace,

"Tracking device" a fili..

Idanunta suka cika da mamaki. “Saƙon dama turo fa?”ta furta a kasan zuciyar ta

"Ohh" tace a fili..

Ya gyada kai. “Eh. Na san da cewa idan har da gaske akwai soyayya a zuciyarki, to da zarar kin karanta sakon nan, sai zuciyata ta ja ni zuwa inda kike.”ya furta a kasan makoshi ..

"You're loved..."

Hawaye suka cika idon Nabeeha. Bai taɓa furta mata soyayya a fili ba, amma wannan maganar ta fi duk wata soyayya da take zato.

Fawaaz ya zare safar hannunsa a hankali, ya cusa mata acikin hannunta. Saboda yadda sanyi ke kadata. Ya zare coat din jikinsa ya dora mata akan kafadarta yana dubanta cikeda kulawa yace,

“Nabeeha…” ya furta sunanta da wata irin murya mai daɗi. “Kin ji wani rauni a jikinki? Sun miki wani abu?”

Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. “A’a… Ni lafiya lau nake.”

Amma Fawaaz bai yarda da hakan ba. Ya matsa kusa da ita, yana dubanta sosai, yana nazarin yadda jikinta yake.

“Babu inda kike jin ciwo?” Ya sake tambaya, yana kiran sunanta cikin kwantar da murya.

Nabeeha ta dan lumshe idonta, sannan ta ce, “Kai ne kake bani ciwo, Fawaaz.” ta furta batare da ta sani ba..

Ya dan zaro ido kadan, zuciyarsa na harbawa. “Me kike nufi?”

Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta bude idanunta ta kalle shi.

"Babu.”

Fawaaz ya dan yi shiru, yana jin kalmomin nata na ratsa zuciyarsa. A koyaushe yana miskilanci, yana boye abubuwan da yake ji. Amma yau, ba zai iya musanta gaskiya ba.

Ya dan yi murmushi a hankali, sannan ya ce, “Kin san wani abu?”

Ta girgiza kai, tana jiran jin me zai fada.

Ya dan matsa kusa da ita sosai, har numfashinsa yana haduwa da nata.

“A duk tsawon lokacin da nake boye abin da ke raina, sai da aka zo kusa da dauke ki ne na fahimci cewa… Babu sauran boyewa.”

Ta lumshe ido, tana jin nauyin kalmomin nasa a zuciyarta.

“Da gaske kake,Yaa Fawaaz?” ta tambaya cikin wata murya mai taushi.

Ya murmusa, yana dubanta da wani irin so da babu wanda ya taba gani a idanunsa.

“Ba zan taba barinki ba, Nabeeha.” Ya furta da karfi. “Koda zai zame min zunubi, 🤭koda zai haifar min da matsala, koda duniya za ta juya min baya, ba zan taba barinki ba.”

A lokacin, wani hawayen farin ciki ya sulale daga idon Nabeeha. Tana kallon Fawaaz, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin shauki da bata taba ji ba.

Bata taba sanin cewa shi ma yana jin haka ba. Bata taba sanin cewa kaunar da take masa na da girman haka ba.

A hankali, ta daga hannunta, ta matse yatsunta tana jin yadda dumin tafin hannunta ke bata kwanciyar hankali.

“Nagode, Yaa Fawaaz.”

Ya dan lumshe ido, yana jin yadda wadannan kalmomi suka bugi zuciyarsa fiye da komai. Bai taba jin farin ciki irin wannan ba.

A yanzu, ba shi da shakka. Nabeeha ita ce ransa. Ita ce zuciyarsa. Ita ce rayuwarsa.kuma daga yau, ba zai taba barinta ba.





_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE: 14_


Captain Fawaaz ya jinjina kai, bai ce komai ba. Idanunsa sun sauka kan na’urar tracking da ke gabansa, ya tuno da sakonnin daya turawa Nabeeha, Wannan yana nufin cewa a wannan lokacin layinta yana bisa sabis, kuma hakan na iya basu damar gano inda suke.

Ya matsa wani maballi a kan na'urar, ya duba taswirar da ke gabansa. Hanyar da suka bi tana da wahala, sai dai a haka ma ba zai yi kasa a gwiwa ba. Yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Ko da yake ya saba da irin wannan aiki, wannan yana da bambanci , Yana nufin ceto most beloved love of his life, Wato Nabeeha.

"Kayi tracking ɗin network ɗin nata?" Lieutenant Ibrahim ya tambaya.

"Eh," Fawaaz ya amsa, yana duba wani karamin screen a gefen dashboard. Ya kara danna wasu maballan sannan ya ce,

"Anan sakon ya shiga, daga nan zuwa wani wuri a kusa da gabar rafin Chida."

"To, akwai wata gada kusa da wannan rafi, amma an ce tana da matsala, babu wanda ke amfani da ita," Warrant Officer Suleiman ya kara da furtawa, yana duba bayanai a cikin wata ƙaramar kwamfuta.

"To lallai sun bi waccan hanyar," Fawaaz ya yanke hukunci.

Sai ya kara gudun motarsa a hankali, yana bin alamar da suka samu. Sauran motocin biyu da ke biye da su suma suka kara saurin tafiya, dukkansu cikin shiri. Su na ci gaba da tafiya cikin dajin, tayoyin motocin su na dannan ciyayi da ƙurar dajin.

Kusan mintuna talatin suna tafiya, sai na’urar tracking ɗin ta soma nuna wani matsayi kusa da su. Zuciyar Fawaaz ta buga da

9 / 40