ta dafe goshinta da hannu daya, sannan ta furta da kyar,
“Nabeeha ba ‘yar Major General Dawud bace…”
Hajiya Karama da Hajiya Ladi suka zaro ido a tare.
"Me kike nufi?"
Hajiya Rumanah ta bude idanu, tana kallon su da tsananin firgici.
“’Yar Hajiya Zaytunah ce! Kuma tana gidan Major General Dawud ne… Amma ba ‘yar sa bace!”
Shiru ya biyo baya. Zuciyoyinsu sun cika da mamaki da firgici. Hajiya Ladi ta yi saurin fadin:
“Haba Rumanah! Wannan ba zai yiwu ba. Kin tabbata? Wannan bayanin ba kuskure bane?”
Hajiya Rumanah ta kada kai, hawaye na taruwa a idonta. "Ban san me ke faruwa ba… Amma idan haka ne, to lamarin ya fi yadda muke tunani. Wannan matsala ce babba!"
Hajiya Karama ta dafe kirjinta, tana kokarin kwantar da nutsuwarta. “Dole ne mu samo mafita da wuri. Kada mu bari wannan ya bata mana shiri.”
Amma Hajiya Rumanah ta kasa samun nutsuwa. Duk yadda suka so su lallasheta, tunaninta ya tafi nesa. Idan har Nabeeha ba ‘yar Major General Dawud bace, Toh ta tabbata yar Hajiya Zaytunah ce kenan... Zuciyarta ta sake harbawa da karfi…
Hajiya Rumanah ta kasa zama. Ta tashi tsaye, tana safa da marwa a cikin dakin, zuciyarta tana tafasa kamar ruwan dafawa. Idanunta sun kada, tana huci kamar wacce aka yi wa dukan tsiya.
"Wannan ba zai yiwu ba! Nabeeha 'yar Zaytunah ce? Amma me hakan ke nufi? Me yasa take gidan Major General Dawud? Yaki ya fito da ita. Shine gaskiar lamarin ne ko kuwa?"
Hajiya Ladi ta gyara zaman mayafinta, ta dubi Hajiya Karama da fuskar da ke bayyana damuwa.
"Yanzu, Rumanah, yaya za a yi?" Ta tambaya da karyayyen murya.
Hajiya Karama ta numfasa, ta saki wani murmushin dole.
"Ba mu da wata mafita illa mu sake duba lamarin da kyau. Mu tabbatar da gaskiyar al’amarin kafin mu dauki wani mataki."
Amma Hajiya Rumanah ta juyo da sauri, ta daga murya.
"Karama! Da me za mu sake duba lamarin? Ai an riga an tabbatar! Idan har Nabeeha 'yar Zaytunah ce, to tabbas muna cikin matsala! Me ya sa ba wanda ya gaya mana? Me yasa har yanzu Muhammad yake bibiyarta?"
Ta dafe goshinta da hannu daya, tana girgiza kai.
"Haka kawai na ji ba dadi! Na ji kamar muna cin amanar kanmu! Don kuwa lamarin backfiring zeyi. Komai tsawon lokaci sai gaskia ta fito mun kwashi kashin mu a hannu"
Hajiya Ladi ta yi gyaran murya, tana kokarin dan shawo kanta.
"Rumanah, ki kwantar da hankalinki. Muna da damar da za mu iya gyara komai."
"Yaya?" Hajiya Rumanah ta yi tsawa.
"Za mu ci gaba da bincike. Sai mun tabbatar da komai kafin mu dauki mataki."
Hajiya Karama ta jinjina kai.
"Eh, dole ne wannan"
Shiru ya ratsa dakin na wasu ‘yan dakiku. Sai dai zuciyar Hajiya Rumanah ta kasa samun natsuwa. Ta sake kallon wayarta, zuciyarta na bugawa da sauri.
"Dole in sake aika sakon tambaya! Ina so in tabbatar da abu daya..."
"To me yasa Muhammad ke son aurenta. Bashi ita akai ko ganinta yayi yana so?"
Hajiya Rumanah ta danna sakon cikin sauri, zuciyarta na dokawa da karfi. Hannunta na rawa, ta zuba ido kan wayar tana jiran amsa.
Hajiya Ladi ta lura da hakan, ta kalli Karama kafin ta dubi Rumanah da kulawa.
"Rumanah, ki kwantar da hankalinki. Kina acting kamar kin san komai, alhali ba mu gama fahimtar lamarin ba."
Hajiya Rumanah ta juyo, idonta cike da bacin rai.
"Ladi, wannan ai ba wasa ba ne! Idan har Nabeeha 'yar Zaytunah ce, kuma take tare da Major General Dawud, muna cikin matsala!"
Hajiya Karama ta yi ajiyar zuciya, ta gyara zaman hijabinta.
"Kin ce haka, amma har yanzu ba ki tabbatar da komai ba. Idan har Muhammad ita din yake so Kuma an tabbatar , ya kamata mu gano me yasa."
Hajiya Rumanah ta sake duban wayarta, tana huci. Kafin su samu damar ci gaba da tattaunawa, amsar sakon ya shigo.
"Nabeeha ba 'yar Major General Dawud bace. 'Yar Hajiya Zaytunah ce, wadda ke zaune a gidan Major General Dawud."
Wayar ta sulale daga hannun Hajiya Rumanah, zuciyarta ta buga da karfi. Kamar an tsikare ta, ta dafe kirjinta, zuciyarta na bugawa da mugun sauri.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!"
Hajiya Ladi da Hajiya Karama suka matso da sauri, suka tsare ta da ido.
"Me ya faru?" Karama ta tambaya da damuwa.
Hajiya Rumanah ta nuna wayar da yatsa, idanunta sun ciko da matsanancin tashin hankali.
"Kun ga? Nabeeha 'yar Zaytunah ce! Kuma suna gidan major general dagaske"
Shiru ya ratsa tsakani na wasu dakiku, kowacce daga cikinsu tana kokarin fahimtar wannan ruɗanin da ya kunno kai.
"Ko dai akwai wani abu da ba mu sani ba?" Hajiya Ladi ta furta a hankali, tana mai jin gabanta yana faɗuwa.
Hajiya Karama ta share gumin da ya keto mata.
"Rumanah, muna bukatar karin bayani! Me yasa take a gidan Major General Dawud? Kuma me yasa har yanzu ba mu san hakan ba. Shin su alhaji sunada masaniya ko kuwa?"
Hajiya Rumanah ta jingina jikin kujera, zuciyarta tana ci gaba da tafasa. Wannan batu ya fi ƙarfin yadda take zato!
Tana jin kamar zuciyarta zata tarwatse. Abin da ta fi tsoro yana kokarin zama gaskiya!..
🎀🎀🎀🎀
A cikin wani tsohon gida da ke tsakiyar daji, an ajiye su Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad a ɗaki mai duhu. Hannayensu da ƙafafunsu an ɗaure su da igiya mai ƙarfi, yayin da wasu daga cikin yan fashin suka tsaya a bakin ƙofa suna gadinsu.
Nabeeha ta kalli mahaifiyarta da damuwa, hawaye na kokarin cika idanunta. “Ammi, su wanene waɗannan mutanen? Me su ke so da mu?”
Hajia Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon ɗiyarta da ƙoƙarin kwantar mata da hankali.
"Ban sani ba, amma abin da na sani shi ne dole mu ci gaba da yin addu’a.”
Hammad ya runtse idanu, zuciyarsa na tafasa da takaici. Bai iya jure ganin mahaifiyarsa da yayar sa cikin wannan hali ba. Ya ce da ƙasa da murya,
"Su wane ne suka aikosu? Wane irin mugunta ce wannan?”
A dai-dai lokacin, kofar ɗakin ta bude da karfi, daya daga cikin yan fashin ya shigo. Fuskar sa a tamke, idonsa na cike da ƙeta. Ya kalli su hajia zaytunah da wani irin murmushin mugunta.
“Kuna bukatar ruwa ko abinci?” Ya tambaya da wata murya mai cike da zolaya.
Hajiya Zaytunah ta ɗago idonta, tana kallon sa da tsananin tsoro amma ba tare da ta nuna rauni ba. Ta ce da ƙarfi,
“Me kuka ke so da mu? Ku gaya mana, me muka muku?”
Dan fashin ya bushe da dariya.
"Ba ke ce matsalar ba. Amma fa idan ba a bi umarnin mu ba, sai mun koya muku darasi.”
Sai ya juya ya fice, ya bar su cikin damuwa da rashin tabbas. Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah da Hammad, zuciyarta na bugawa da karfi.
“Ya Allah, ka kawo mana agaji.” Ta furta cikin sanyin murya...
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 9_
Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwanta da ƙarfi, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi. Kamar yadda ta taɓa jin irin wannan firgici a baya, haka take ji yanzu, amma wannan ya fi komai muni. Ta dubi gefenta, tana kallon Nabeeha da Hammad da ke a daure kamar yadda ita ma take. Sun yi shiru ba tare da sun furta uffan ba, amma idanuwansu sun bayyana tsananin tsoro da damuwa.
Ta juya idanunta cikin ƙwaryar ɗakin da ake tsare da su. An ajiyesu ne a wani wuri da ya yi kama da tsohon daki, katako ne ke rufe jikin bangon, kuma kowane lungu cike yake da ƙura. Abin da ya fi damunta shine sanin cewa har yanzu ba su san waye ke da alhakin wannan Kamen nasu ba, kuma ba su san me suka yi da har hakan ta faru da su ba.
Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, zuciyarta cike da addu’a. Shin wannan tashin hankalin zai ƙare lafiya kuwa?
A daidai wani dare mai tsananin duhu, cikin wani lungu da baƙin duhu a wani yanki na barikin da suka fake, wani guntun mutumi dake cikin yan fashin ya taho da waya a hannunsa, daya hannun nasa rike da torchlight. Ya mikawa daya daga cikin 'yan fashin da suka kama Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha. Takardar da aka rubuta da dogayen kalmomi masu nauyi, wato in bold letters ta turo text message din Suna ɗauke da umarni daga wacce ta fi kowa kula da lamarin - Hajiya Rumanah.
Kuna cikin bakin aiki, kuma babu wani kuskure da zan lamunta daga gareku. Haka nan, babu wasa a cikin wannan danyen aiki da aka damka muku. Zan yi muku magana ta gaskiya, kuma dole ne ku aikata abin da nake so cikin gaggawa.
Ga umarni na a gareku,
Na farko,
Za ku yanke gashin wannan annamimiyar (Hajiya Zaytunah) ku aiko mini da shi. Gashin kanta dole ne ya iso hannuna. Babu buƙatar yawan tambayoyi ko ɓata lokaci. Idan har ta ƙi yarda, ku tabbatar kun yanke shi da karfi da yaji. Idan ta yi ihu, to ku ƙara mata azaba!
Na biyu,
Kada ku sake a bar wannan ƴar wulakancin (Nabeeha) ta kubuta cikin salama. Idan har za ta rayu bayan wannan dare, to dole ne a ɗauke mata mutuncinta! Ku tabbatar an shanye duk wani alamar mutunci daga jikinta kafin ku bar ta ta numfasa. Idan ta mutu cikin tsananin azaba, to hakan ma zai zama alheri.
Babu wani kuskure da zan yarda da shi! Idan kun yi sakaci, ku sani cewa rayuwarku ce za ta biyo baya. Ku sanar da ni idan kun kammala.
Mutumin ya gama karanta sakon, zuciyarsa ta cika da kasala. Duk da ya saba da aikata muggan laifuka, ya san cewa wannan umarni ya wuce gona da iri. Kallon wasu daga cikin abokan aikinsa ya yi, kowanne yana jiran a ce komai. Daga ƙarshe ya kalli wanda ya kawo sakon ya ce:
"Wannan matar ba zata taɓa yin imani da ƙwaƙwalwarmu ba. Ita ba ta kula da komai sai mugun nufinta!"
Daga gefe, wani daga cikin 'yan fashin da ke jin maganar ya murmusa, yana kaɗa kai,
"Dama mun san cewa akwai wani abu da ke ƙasa da wannan lamarin. Ba so kawai ake su mutu ba, ana son a bar musu tarihi da abin da zai ruguza su tsawon rayuwarsu."
Duk da haka, babu wanda ya ce uffan na tsawon lokaci. Shirun ya yi yawa, sai ƙarar wata tsuntsuwa da ta ketara ta wuce cikin duhun dare. Daga bisani, babban shugaban 'yan fashin ya gyara zamansa, ya saki numfashi mai nauyi sannan ya ce,
"Za mu bi umarninta. Amma idan wata matsala ta taso, sai mu yi tunani kafin mu dauki mataki."
Suka yi shiru na wani lokaci, kafin wani daga cikinsu ya tashi tsaye ya ɗauki wani almakashi, yana kallon shi da kyau kamar yana nazari.
A cikin duhun dare, aka fara tsarawa domin aiwatar da mugun aikin da Hajiya Rumanah ta bayar...
A cikin dakin da aka kulle Hajiya Zaytunah da Nabeeha, ana iya jin numfashinsu yana fita cikin sauri da tsoro. Wutar fitila guda daya ce ke haskaka dakin, tana bayyanar da inuwa a bangon da ke nuna yanayin tsoron da ke tattare da su.
Hajiya Zaytunah tana zaune a gefe, hannayenta daure da igiya, idanunta sun kada saboda tsananin damuwa. Nabeeha kuma tana a gefenta, jikinta yana rawa, zuciyarta cike da tsoron abin da zai biyo baya.
A waje kuwa, daya daga cikin 'yan fashin ya dubi shugabansu, yana girgiza kai cikin shakku.
"Mun san aikinmu ne, amma wannan ai ya yi yawa."
Shugaban ya kalle shi da idanun da suka cika da rashin jin tausayin komai.
"Hajiya Rumanah ba za ta ji daɗin jin cewa ba mu aikata abin da ta umurce mu ba. Kuma ba na son jin bayanin kowa. Za mu aiwatar da umarnin nan da aka bayar!"
Ya juya yana duban wani daga cikinsu, wanda aka fi sani da Gora, ya ce da shi,
"Kai ne za ka shiga ka yanke mata gashi."
Gora ya haɗiye yawu, yana jin wani irin sanyi yana ratsa zuciyarsa. Duk da kasancewarsa da ƙwarewa a aikata laifi, wannan lamarin ya ɗauke shi a matsayin wani mummunan aiki da zai bar tarihi mai muni.
Ya ɗauki almakashin da aka ba shi, sannan ya sa hannu ya tura ƙofar dakin. Kamar yadda ya zata, idanun Hajiya Zaytunah sun zazzaro da ganinsa, tana kallon almakashin hannunsa.
"Mene ne kake shirin yi?" Ta tambaya da muryar da ke rawa.
Gora bai ce komai ba. Ya matsa kusa, zuciyarsa na dukan uku-uku. Ya tsugunna a gabanta, yana kallon gashinta da ke nade cikin mayafi. Ya san cewa wannan ba abu ne mai sauki ba, amma ya san cewa idan bai aikata ba, rayuwarsa tana cikin hatsari.
Hajiya Zaytunah ta fahimci manufarsa nan take. Ta motsa a inda take daure, tana kokarin janye kanta.
"Kada ka kuskura!" Ta ce, idanunta sun cicciko da hawaye.
Gora ya runtse ido yana shirin saka almakashin a cikin gashinta, amma zuciyarsa ta gaza. Sai ya sauke almakashin a kasa, yana jan numfashi mai nauyi.
A waje, sauran 'yan fashin suna jiran jin motsin da zai tabbatar da an yi aikin. Shugaban ya daka tsawa:
"Meye ya tsaida ka?"
Gora ya goge zufar da ta bayyana a goshinsa, sannan ya dubi shugabansu da fuskar da ke nuna rashin yarda da lamarin.
"Ba zan iya ba," Ya ce cikin sauti mai ƙasa.
Shugaban ya fusata, yana matsowa kusa da shi.
"Kana nufin kana ƙin yin abin da aka umurce mu?"
"Ba haka bane," Gora ya amsa, yana kokarin kare kansa. "Amma wannan abu ya wuce gona da iri. Wannan matar ta riga ta wuce wahala. Me yasa ba za mu yanke kanta gaba daya mu huta ba?"
Shugaban ya kara harzuka, sai ya finciki almakashin daga hannun Gora.
"Ka matsa gefe!" Ya ce da tsawa.
Ya shiga dakin cikin sauri, ya kama gashin Hajiya Zaytunah da karfi, yana kokarin yankewa.
A take, Nabeeha ta tashi tsaye, tana kiran cikin kuka,
"Don Allah, kada ku yi haka, Dan Allah !"
Shugaban bai saurare ta ba, sai kawai ya ci gaba da yankewa. Gashin da ya faɗi daga kanta ya shiga cikin wani farin leda da aka tanada, sannan ya kalli wasu daga cikin 'yan fashin.
"Ku shirya, za a aika da sakon nan zuwa wajen su."
Da wannan umarni, wani daga cikin 'yan fashin ya ɗauki ledar, ya fice daga dakin, yana shirin aika da sakon.
A waje kuwa, wata matsala mai girma ta taso saboda wasu daga cikin 'yan fashin sun fara nuna shakku akan abu na biyu da aka umurce su da su aikata…
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 10_
A cikin dakin da aka kulle su, Hajiya Zaytunah ta kasa motsi yayin da idanunta ke zub da hawaye. Numfashinta ya tsananta, zuciyarta tana harbawa da sauri. Duk da azabar da aka yi mata da yankar gashinta, wani abu mafi muni ya fi tada hankalinta, wato abin da zai biyo baya...
Nabeeha ta kankame jikinta, tana jin gabanta yana faduwa da wani irin tsoro da ba ta taba jin irinsa ba. A zuciyarta, tana rokon Allah ya kawo mata mafita. Idanunta sun cika da hawaye, amma ta kasa kukan da zai sa su nuna rauni.
A waje kuwa, shugabansu ya sake duban sauran ‘yan fashin, yana furta abin da ya fi rudani.
“Ku tabbata an aiwatar da abu na biyu da Hajiya Rumanah ta bukata.”
Da jin haka, gaba daya ‘yan fashin suka yi shiru. Wasu sun zuba masa ido, wasu kuma suka dauke kai. Ko da sun saba da aikata miyagun ayyuka, hakan ba zai sa su yi wannan aikin da ya zama wulakanci ba.
Wani daga cikinsu, mai suna Bala, ya kalli shugaban da ido kamar yana tunani.
“mu dan dakata mu dauki lokaci kafin mu aiwatar da wannan,” Bala ya ce, yana kokarin kaucewa matsalar.
Shugaban ya dube shi da harara.
“Wane lokaci kake nufi? Ko dai mu aiwatar da shi ko kuma mu kashe ta gaba daya.”
Gora, wanda ya riga ya nuna rashin yarda tun da farko, ya sake matsowa.
“Wannan ba abu ne da zan iya aikatawa ba,” ya furta da karfi.
Shugaban ya kalle shi da fuska mai nuna rashin hakuri.
“Kai ne zaka zaba, ko dai ka aikata, ko kuma kai ma ka fuskanci hukuncin Hajiya Rumanah.”
Gora ya kara hararar shugaban, zuciyarsa cike da bacin rai. Ya jima yana rayuwa da laifi, amma bai taba zuwa inda aka ce ya wulakanta mace ba. Bai taba yi ba, kuma ba zai fara da wannan ba.
Ya sauke numfashi, sannan ya ce,
“Idan wannan shine abin da kuka shirya, to ni ba zan kasance da ku ba.”
Shugaban ya yi dariyar takaici, yana girgiza kai.
“Dama nasan kana da wata zuciya mai laushi. Ba ka dace da wannan aiki ba.”
Daga cikin sauran ‘yan fashin, wasu suka fara hada ido da juna, kamar suna tunanin cewa Gora yana da gaskiya. A wannan lokaci, an samu rarrabuwar kawuna.
A gefe guda kuma, Bala ya kalli dakin da aka kulle su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Yana jin zuciyarsa tana bugawa da wani irin yanayi da bai taba ji ba.
“Idan muka aikata hakan, me zai rage mana?” Bala ya fada a hankali. “Mu ‘yan fashi ne, amma ba azzalumai ba.”
Shugaban ya yi fuska, yana kallon Bala da Gora da mamaki. Bai zata cewa matsalar zata yi girma haka ba.
“Ina jin dai kun manta cewa mun karbi kudi a wannan aiki,” ya fada cikin bacin rai. “Kuma duk wanda ya ki aikatawa, to shi da kansa zai fuskanci hukunci.”
A wannan lokaci, Bala ya dauki mataki na rashin zato ya zaro bindigarsa!
Gaba daya ‘yan fashin suka ja da baya, sai wasu suka zaro makamai suma. Rikici ya fara tasowa, kamar tafasasshen ruwa.
Bala ya kalli shugabansu ido cikin ido, sannan ya ce da kakkausar murya:l,
“Ba zan bari ka wulakanta su ba. Idan haka ne, to sai dai ka kashe ni.”
Hakan ya tada hankalin sauran ‘yan fashin. Gora ma ya janye daga gefe, yana