suka yanke hukunci cewa ni ce na watsar da su?"
Gwaggo Hafsatu ta murmusa, tana shafa hannunta cikin kwantar da hankali. "Zaytunah, su Alhaji Uzairu da sauran su ba yara ba ne. Sun yi shekaru suna neman ki, da basa kaunar sake sanya ki a idanuwan su ai duk tarin shekarun nan da ba zasu dinga neman ki ba.., suna neman hakikanin abin da ya faru. Wannan shi ne lokacin da za su ji gaskiya daga bakin ki. Babu wanda zai zarge ki idan suka fahimci matsalar da kika shiga."
Hajiya Zaytunah ta jinjina kai a hankali, tana jin wani sanyi a zuciyarta. Duk da haka, fargaba ba ta gushe ba.
A wancan lokacin, a gefen Alhaji Uzairu, zuciyarsa tana tafasa. Tun bayan da suka bar falon Major General Dawud jiya, ya kasa samun natsuwa. Tunani ya hana shi barci. Shin zai sake ganin Zaytunah? Shin zata gane shi? Shin zata yarda ta dawo da komai kamar da?
"Uzairu," murya ta katse masa tunani. Alhaji Amiru ne ke magana, yana dubansa da kulawa. "Kana da yakinin cewa kana shirye ka fuskance ta?"
Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa na harbawa. "Ya Amiru, ba wai tambayar ko na shirya ba ce. Tambayar ita ce—shin zata yarda da ni? Shin zata fahimce ni?"
Alhaji Amiru ya dan murmusa, yana dafa kafadar shi. "Zaytunah ba matar da zata manta da kai haka kawai ba. Idan da hakan ne, da tuni ba ta damu da ciwon da take fama da shi ba. Ka yi hakuri, ka bari lokaci ya yi aiki."
A can gefe, Major General Dawud ya fito daga sashensa yana kallon su duka. A yau ne suka shirya haduwar da suka jima suna jira. Ya kalli Gwaggo Hafsatu, wadda ta jinjina kai, tana nufar su Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru.
"Lokaci ya yi." Ta fada a hankali.
Alhaji Uzairu ya mike, ya gyara rigarsa. Zuciyarsa na bugawa da sauri. Wannan haduwar ba zai taba mantawa da ita ba.
Duk da sanyin gari, idanun Alhaji Uzairu sun cika da zufa. Yayi nisa a tunani har sai da suka iso bakin kofar dakin da Hajiya Zaytunah take.
Gwaggo Hafsatu ta ja numfashi sannan ta tura kofar a hankali.
Cikin nutsuwa, Hajiya Zaytunah ta dago daga inda take zaune, idanunta cike da tsoro da fargaba. Kamar dai yadda take a daren jiya, zuciyarta ta kasa natsuwa.
A hankali, Alhaji Uzairu ya taka zuwa ciki, yana kallonta da ido. Tsawon shekaru bai ganta ba, amma yau, gashi a gabansa.
"Zaytunah..." Muryarsa ta fito cikin karyewa.
Hajiya Zaytunah ta sake kakkarwa, zuciyarta na bugawa. Ta dauke kanta gefe, tana jin yadda numfashinta ke rikicewa.
Alhaji Uzairu ya matsa kusa, amma ba tare da matsawa fiye da kima ba. Ya lura da yadda take a tsorace, hakan yasa ya daidaita kansa.
"Zaytunah, ni ne. Uzairu. Ki kalleni."
Idanunta sun cika da kwalla, amma ta kasa dago su. Babu abin da take ji sai bugun zuciyarta da wani irin sanyi a gabanta.
"Ban taɓa mantawa da ke ba." Ya fada a hankali, hawaye suna taruwa a idonsa. "Ban san me ya faru da ke ba. Ban san inda kika shiga ba. Amma ban taɓa dena tunaninki ba."
Hawayenta sun gangaro, amma har yanzu bata iya motsi ba.
"Idan har da gaske kika manta da ni, idan har da gaske kika manta da rayuwarmu..." Ya runtse ido, yana jin yadda zuciyarsa ke suya. "To zan tafi. Amma da fatan za ki gaya min gaskiya, menene ya faru?"
A wannan lokacin ne zuciyar Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Kamar wacce ta sha ruwa mai sanyi, ta fashe da kuka.
"Uzairu..." Muryarta na rawa. "Ban guje ku ba. Ban manta da kai ba. Ban manta da komai ba."
Alhaji Uzairu ya kafe ta da ido, zuciyarsa na suya da karaya. "To me ya faru? Menene ya hana ki dawowa?"
Hajiya Zaytunah ta runtse ido, tana jin yadda hawayenta ke bin fuskarta. Cikin wani irin shesshekar kuka, ta furta kalmomin da suka kasa fita tsawon shekaru.
"Asiri aka min, Uzairu. An rabani da ku da sihiri da tsibbu. An tursasa min tafiya, aka hana ni dawowa. Ban yi hakan da kaina ba!"
A take zuciyar Alhaji Uzairu ta buga, ya dafe kirjinsa kamar wanda aka caka wa mashi. Idanunsa suka firfito da mamaki.
"Asiri?" Ya tambaya cikin rawar murya.
Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin yadda zuciyarta ke kunshe da zafi. "Kurciya aka yi min, Uzairu. An kulle ni cikin wani hali da bai barni na koma gare ku ba. An sace rayuwata."
Shiru ya ratsa dakin. Alhaji Uzairu ya dafa goshinsa, yana jin yadda nauyin abu ya hau kansa. Idan har wannan gaskiya ne, to hakan na nufin shekaru da dama na rashin sanin hakikanin abin da ya faru.
Bai san lokacin da hawaye suka gangaro daga idonsa ba. Bai san lokacin da zuciyarsa ta fashe da raɗaɗi ba.
A hankali, ya matsa kusa da ita. Babu kalma da zai iya furtawa, sai ya tsugunna gabanta, yana kallonta da ido.
"Zaytunah..." Ya kira sunanta cikin rawar murya.
A hankali, ta dago ta kalle shi. Idanun su cike da hawaye.
"Kin dawo gare ni?"
A wannan lokacin ne zuciyarta ta fashe, ta sunkuya, ta boye fuskarta cikin tafukan hannunta, tana kuka mai karfi.
A wannan lokacin ne Alhaji Uzairu ya fahimta duk tsawon shekarun da suka shude, duk radadin da suka sha, wataƙila wannan ce ranar da za a fara farfaɗowa daga ciki.
Ranar da komai zai fara gyaruwa...
MX🧕
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:36_
Hawaye suka ci gaba da sintiri a fuskar Hajiya Zaytunah. Hannunta yana rawa, zuciyarta na bugawa da karfi. Ta kasa motsawa, ta kasa yarda da cewa yau, gashi da gaske Alhaji Uzairu na a gabanta.
"Yaya uzairu..." Ta sake furta sunansa cikin raunaniyar murya, kamar mai neman tabbaci.
Alhaji Uzairu ya gyada kai, yana kallonta da ido mai cike da tausayi. "Eh, ni ne, Zaytunah. Na zo, na zo gare ki. Amma kina nufin shekaru duka wadannan ba ki san yadda za ki dawo ba? Ko da sandar sako?"
Hajiya Zaytunah ta runtse ido, wani sabon hawaye na gangarowa.
"Ba ku fahimta ba, Uzairu. Ba wai kawai an rabani da ku ba ne. An tsare ni a wani hali na kurciya da ba zan iya bayyana ba. Wataƙila har yanzu ba ku san cewa har cikin barcin ku an danƙa min tsinuwa da tunzuri akan kin waiwayar gidah ba"
Alhaji Uzairu ya dafe goshinsa, zuciyarsa na kuna. Wani irin tausayin Zaytunah ya lulluɓe shi, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. Duk da shekara da shekaru da suka shude, ba zai iya musanta cewa wannan matar da ke gabansa ita ce zuciyarsa, soyayyarsa, iyalinsa da ya dade yana nema.
A hankali ya kalli cikin idanunta da suka cika da hawaye.
"Zaytunah..." Ya kira sunanta da wani irin sanyin murya, yana jin yanda kalmomin suka makale masa a makoshi. "Kina nufin duk wannan lokaci kina raye da kike fama da wannan hali?"
Zaytunah ta lumshe ido, tana jin zuciyarta na rawa. "Uzairu, ba abu ne mai sauƙi ba. Wallahi ba zan iya bayyana azabar da na sha ba. A kowace rana ina jin kaina a cikin duhu. Akwai lokutan da nake jin kamar na salwanta, kamar rayuwata ta kare."
Ta runtse ido, hawaye suna sintiri a kumatunta.
"Ban san yadda zan iya komawa gare ku ba. Ko da na so, ba zan iya ba. Duk hanyoyin da zan bi an toshe min su."
A can gefe, Gwaggo Hafsatu ta dafa hannun Zaytunah, tana girgiza kai.
"Ai mun san hakan, Zaytunah. Mun san cewa ba da kanki kika bar su ba. Muna tare da ke, mun sha wahala wurin fahimtar abin da ya faru."
Alhaji Amiru ya dubi Major General Dawud, yana dan gyara zamansa. "Wannan abu da aka yi mata ba ƙaramin zalunci ba ne. Na sha bincike a baya, amma ban taɓa tunanin cewa har tsibbu da asiri ne aka yi mata ba."
Gwaggo Zainabu, wadda tun farkon maganar take kallonsu da damuwa, ta numfasa. "Wai shin waye ya yi wannan asirin? Su waye suka shirya wannan makircin?"
Shiru ya ratsa falon. Kowa ya juya yana kallon Zaytunah, amma sai ta kauda kai gefe. Akwai abubuwan da ba za ta iya faɗa yanzu ba.
Major General Dawud ne ya dubeta da kulawa. "Zaytunah, babu abinda zai faru idan kika faɗa gaskiya. Wannan lokaci ne na yanke hukunci akan abin da ya faru da ke. Idan har akwai wanda yake da alhakin hakan, to dole ne mu san shi."
Zaytunah ta dan lumshe ido, ta sake jan numfashi. Sannan cikin wata irin murya mai rauni, ta furta: "Kishiyoyi hadi da wasu daga cikin yan uwana na ne suka yi min wannan asirin. Sun haɗa kai da wasu bokaye suka kulle ni da tsibbu da kurciya, suka hana ni komawa gidana... ."
Wata irin faduwar gaba ta kama Alhaji Uzairu. Ya kafe ta da ido, yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. "Wannan gaskiya ne, Zaytunah?"
Ta gyada kai, hawaye suna cika mata ido.
"Yaya Uzairu, wallahi gaskiya nake faɗa. Su ne suka yi min haka. Su suka raba ni da kai, suka sa na bar gidan da Muhammad wanda yake Hammad a yanzu da mai sunan Gwaggo da muke kira da Nabeeha a yanzu."
Alhaji Uzairu ya rintse ido, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. Bai taba tunanin cewa matan sa za su iya aikata hakan ba. Bai taba zaton cewa makircinsu zai kai haka ba.
"Allah ya isa!" Ya furta cikin zafin rai.
Gwaggo zainabu ta dafa kafadar sa, tana kokarin kwantar masa da hankali. "Uzairu, ba fushi za mu yi ba. Abinda ya fi dacewa shi ne mu yi tunanin matakin da za mu ɗauka a yanzu."
Major General Dawud ya gyara zama, yana kallon su gaba ɗaya.
"Tabbas dole ne a yi abu akan wannan lamari. Amma kafin komai, dole ne mu tabbatar da cewa Zaytunah da iyalinta sun samu kariya daga duk wani abu da ka iya faruwa nan gaba."
Gwaggo Zainabu ta jinjina kai. "Eh, haka ya kamata. Mun dade muna neman ta, amma yanzu da Allah ya kawo mu gare ta, ba za mu ƙyale ta sake shan wahala ba."
A hankali, Alhaji Uzairu ya sauke ajiyar zuciya. Ya kalli Zaytunah, zuciyarsa na cike da raɗaɗi da kauna a lokaci guda.
"Ba zan taɓa barin ki sake fuskantar irin wannan ba, Zaytunah."
Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, hawaye suka sake gangarowa daga idanunta. A karo na farko tun shekaru da dama, ta ji wata irin nutsuwa a cikin zuciyarta. Wataƙila, wannan ce ranar da za ta fara dawowa da kanta.
Shiru ne ya sake ratsa falon, kowa cikin dogon tunani. Wani irin nauyi ne ya danne zuciyar Alhaji Uzairu, amma dauriya kawai yake yi. A gefe guda yana ji kamar ya fusata, amma a dayan bangaren kuma zuciyarsa na cike da shauƙi da ƙauna, saboda a gaban sa ne matar da ya dade yana mafarkin ganin ta.
A hankali ya numfasa, ya kalli Zaytunah da idanunta suka cika da hawaye. A shekarun da suka wuce, ya yi tunanin cewa watakila ta manta da shi, watakila ta samu wani rayuwar daban, amma a yau, gashi da idanunsa yana jin labarin abin da ya raba su.
"Zaytunah..." Ya kira sunanta a hankali, kamar wanda ke jin tsoron ta ɓace masa.
Ta ɗan juyo, amma ba ta iya kallonsa kai tsaye ba. Numfashinta na fita a hankali, tana jin zuciyarta kamar zata fito waje.
"Kin dade a cikin duhu. Kin sha wahala. Amma na rantse da Allah, daga yau ba zan ƙyale wani ya sake cutar da ke ba." Muryarsa na nuna yadda zuciyarsa ta gama cika da alhini.
Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, tana jin yadda kalamansa suka saukar mata da wani irin sanyi a zuciya. Daga lokacin da ta bar gidansa zuwa yanzu, ba ta taba jin irin wannan nutsuwa ba.
Gwaggo Hafsatu ta numfasa, ta kalli su duka da kulawa. "A yanzu, abin da yafi dacewa shi ne mu yanke shawarar yadda za a ci gaba. Zaytunah, ke dai kin shirya komawa gidan mijinki?"
Shiru ya ratsa falon. A hankali, Zaytunah ta dago kai, ta kalli Gwaggo Hafsatu.
"Ba wai ba na so ba, Gwaggo, amma ina jin tsoro. Ina jin tsoron komawa cikin wannan rayuwar, saboda har yanzu ba mu san abin da zai biyo baya ba."
Major General Dawud ya gyara zama, yana kallonta da kulawa. "Ba ke kadai kike jin hakan ba, Zaytunah. Amma muna tare da ke. Duk wanda ya sake kokarin cutar da ke, zai gamu da hukuncin da ya dace da shi."
Alhaji Amiru ya jinjina kai. "Haka ne. Kuma ba za mu tsaya a nan ba. Dole ne a bi wannan lamari a shari'ance. Mutanen da suka yi miki haka dole ne su fuskanci hukunci."
Alhaji Uzairu, wanda ya kasa jurewa, ya kalli Major General Dawud. "Ina bukatar taimakon ka, Janar. Ina so a yi bincike sosai a gano wadanda suka hada baki akan wannan mugun nufi."
Gwaggo Zainabu ta gyada kai cikin goyon baya. "Haka ya dace. Wannan ba abu ne da za a kyale ya wuce haka ba. Mun dade muna cikin duhu, amma yanzu gaskiya ta bayyana."
Hajiya Zaytunah ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon su daya bayan daya. A karo na farko, ta fahimci cewa ba ita kadai ce. Tana da mutanen da suke tare da ita, wadanda za su kare ta, za su tsaya mata.
Ta juya, ta kalli Alhaji Uzairu. A karon farko tun bayan shigowarsa, ta kalle shi da tsananin kauna da tausayawa.
"Yaya uzairu..." Ta kira sunansa da wata irin nutsuwa. "Ina so ka fahimta cewa ba na manta da kai ba. Ban manta da kauna da zaman mu ba. Amma ina bukatar lokaci… Na shirya dawo wa, amma ina bukatar in tabbatar cewa babu hatsari."
Alhaji Uzairu ya fahimci tsoronta. Ya matso kusa da ita, yana dubanta da tsantsar soyayya. "Zaytunah, na amince da komai. Ba na matsa miki dole. Amma zan jira ki. Na jima ina jira, don haka babu matsala idan zan jira ki har sai da kika shirya."
Hajiya Zaytunah ta lumshe ido, ta dago cikin nutsuwa. "Nagode, Yaya Uzairu."
A gefen Gwaggo Hafsatu, Major General Dawud ya numfasa, yana jin wani nauyi ya sauka daga zuciyarsa. A yau, an warware wata babbar matsala da ta daɗe tana hana su sukuni.
Sai dai, wannan ba ƙarshen al’amari ba ne. Wannan ne farkon sabon babi a rayuwar su.
Sabon babi da ba za a iya hasashen yadda zai kaya ba....
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:37_
Duhu ne ya mamaye dajin, iska mai sanyi na busawa yana tayar da ganyaye suna faduwa bisa kasa. Tsuntsaye sun daina rerawa, kamar sun san wani abu mai girma zai faru. A tsakiyar dajin, akwai wata bukka, daga gefe wuta tana tashi a cikin kwanon karfe, tana daukar wani irin hayaƙi mai wari. A cikin wannan bukkah ne Haruna ya hangi su Hajiya Rumanah, Hajiya Ladi, da Hajiya Karama zaune, suna fuskantar wani dattijo da ke rike da babban bokiti mai cike da ruwa.
Haruna ya dan tsuguna a bayan wata bishiya, zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai taba zaton haka ba. Ya zo dajin ne don ya duba irin ayyukan da boka yake yi wa mutane, sai gashi ya hangi matan gidan Alhaji Uzairu cikin tsananin tawaya, suna rokon boka da yayi musu aiki.
“Me kuke so na yi muku?” Bokan ya tambaya da wata murya mai sautin tsoro.
Hajiya Rumanah ta dubi sauran matan, sannan ta ce, “Muna son ka kashe Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta,Muhammad da Zainab. Wanda sunansu ya koma Nabeeha da Hammad! Ba mu son su dawo gidan Alhaji Uzairu, ba mu son su rayu ko kadan!”
Hajiya Ladi ta gyara zamanta, ta matsa kusa da boka. “Muna son ka hana ta komawa gidan. Idan har ta yi niyyar dawowa, sai ka kashe ta da wani mummunan ciwo.”
Hajiya Karama ta kara da cewa, “Dole ka tabbatar da cewa Nabeeha da Hammad ba su rayu ba. Muna bukatar su bace daga doron kasa.”
Bokan ya yi dariya, wacce ta girgiza zuciyar Haruna.
“Aiki ne mai sauki,” ya ce yana hada wasu magunguna cikin bokitinsa. “Zan musu tsibbu da kurciya. Matar ba za ta taba dawowa gidan mijinta ba, kuma idan har ta kuskura ta yi niyyar dawowa, to za ta halaka da kanta. Iyalanta kuwa, za su gamu da masifar da ba za su taba tsira da ita ba!”
Ya dauko wani farin foda ya yayyafa cikin ruwan da ke cikin bokiti. Wata irin hayaki mai duhu ya tashi, yana zagaye bukkarsa. Sai ya dauki wata kwarya ya dora a kan wutar. Daga nan ya fara karanta wasu munanan surkulle, yana hura iska cikin hayakin.
Haruna ya runtse idanuwansa, zuciyarsa na tafasa. Ya san cewa wannan bayani yana da matukar mahimmanci, dole ne a dauki mataki akai. Bai yi wata-wata ba, ya juya a hankali, yana kokarin barin wurin ba tare da sun gano shi ba.
Bayan Haruna ya sanar da Alhaji Amiru abin da ya gani, cikin sauri suka hada mutane suka shirya tafiya dajin. Sun san cewa dole ne a cafke wannan boka domin a gano gaskiyar lamari.
Suna isa bakin dajin, jami’an tsaro su goma sun rufe gefuna. Alhaji Amiru na gaba tare da Haruna, a gefensa akwai wasu manyan dattawa masu fada a ji. Kafin su karasa, sai suka hangi boka yana kokarin arcewa da wata kwarya a hannunsa.
“Kama