dayan kuma yana shafa gashin kansa a hankali, tamkar wanda yake tunanin matsala mai wuyar warwarewa.
Idanunsa a rufe, amma zuciyarsa ba ta huta ba. Duk da shiru da duhun dakin, tunaninta yana nan da shi. Yana jin numfashinta a cikin tunaninsa, yana ganin murmushinta a cikin duhun da ke rufe idanuwansa.
Ya juyo da gefen jikinsa, yana jin nauyin zuciyarsa kamar tana cike da wani abu da ba zai iya furtawa ba.
Yana son ta.
Ya san hakan.
Ya tabbatar da hakan fiye da yadda yake tabbatar da komai a rayuwarsa.
Amma yana gudu. Yana gudun furta abin da zuciyarsa ke ji.
Yana tsoron idan ya fadi, idan ya bayyana, me zai faru?
Me zai faru idan zuciyarsa ta bayyana sirrinta?
***
A cikin duhun dakin, idanunsa a rufe, yana iya hango ta kamar tana kusa da shi.
Yadda idanunta ke haskakawa idan tana magana. Yadda take dan taɓa hancinta idan tana tunani. Yadda take murmushi har dimples dinta su bayyana.
Ya tuno yadda take kokarin hana dariyarta fita idan wani abu ya bata dariya. Yadda idan tayi murmushi, zuciyarsa ke tafasa da wani yanayi da ya kasa misaltawa.
Kamar yana jin kamshin turarenta a kusa da shi. Wannan turaren da ya saba jin kamshinsa idan ta wuce kusa da shi, ko idan tana kusa da shi a dakin gaisuwa.
Ya runtse idanu da karfi.
Me yasa bai iya barin tunaninta ya fita daga zuciyarsa ba?
Ko zai yi bacci, da ita yake kwana.
Ko zai farka, tana nan cikin tunaninsa.
Ko yana aiki, yana jin kamar zata fito daga wani wuri ta sake ce masa, "Yaa Fawaaz."
Muryarta tana da laushi, tana da wani irin sauti da ke sanya shi tsayawa tunani ko da kuwa yana cikin gagarumin aiki.
***
Ya kai hannu ya dauki wayarsa, yana kallon fuskar wayar na tsawon lokaci. Bai san dalili ba, amma sai da ya bude chat dinsu.
"Me yasa ka siya min ita?"
Tun jiya take jiran amsa. Tun jiya take son jin dalilin da yasa ya bata kyauta.
Shiru yayi yana kallon rubutun. Zuciyarsa na bugawa da karfi.
Yana da abubuwa da yawa da zai ce.
"Saboda kina da muhimmanci a wajena."
"Saboda na riga da na saba da kasancewarki kusa da zuciyata."
"Saboda... ina son ki, Nabeeha."
Sai ya dafe goshinsa a hankali.
Zai iya cewa haka?
Zai iya bude zuciyarsa da kansa?
Wani sashe na zuciyarsa yana son rubutawa. Yana son furta gaskiyar da yake boyewa tun farko.
Amma wani sashen yana hana shi.
Fawaaz ya kashe wayar, ya sake kwanciya, yana jin zuciyarsa tana bugawa kamar zai ji kalmomin da bai iya furtawa suna fitowa da kansu.
Zai iya boye zuciyarsa daga mutane.
Amma ba zai iya boye ta daga kansa ba.
Kuma babu shakka—wata rana, watakila daga bakin ta ko daga nashi, amma wata rana, wannan gaskiya da yake gujewa za ta fito fili.
....
Yana tsaye a cikin duhun bishiyoyi, yana boye jikinsa da kyau domin kada su gan shi. Daga inda yake, yana iya hango su Hajia Karama, Hajia Ladi, da Hajia Rumanah suna tsaye a gaban wani tsoho mai dogon gemu da jajayen idanun da ke cike da alamun sihiri.
A hankali ya matso da kunensa domin jin abin da suke fadi.
"Ba mu son kuskure wannan karon," cewar Hajia Karama, tana hadiye yawu.
"Dole a tabbata an shafe su gaba daya," Hajia Ladi ta ce tana girgiza kai. "Idan Zaytunah da yaranta sun wanzu, to wallahi, mu za mu zama matsala a idanun duniya."
Bokan ya kada sandarsa mai bakin ƙaho. "Kun tabbata ba wanda ya biyo ku?"
Hajia Rumanah ta dan saki murmushi. "Babu. Mun fito a hankalce sosai. Muna son a yi aikin da babu wanda zai taba sanin mu ne muka aikata."
"Toh ai na gaya muku," cewar bokan yana mai kada kansa. "Idan za a yi aikin, sai kun kawo mini wani abu da ke jikin wannan Zaytunah. Na biyu, dole a samo wani abu da zai shafi yaranta—wanda suka fi amfani da shi kullum."
Hajia Karama ta kalli Hajia Ladi, sai ta ce, "Zan samu mayafinta. Ni na san yadda zan yi hakan."
"Ina da kofin shan shayi da take amfani da shi kullum a baya" Hajia Rumanah ta kara da cewa.
Bokan ya kada kansa. "Duk wannan yana da kyau. Amma ku sani, idan har kuka biya kudin da ake bukata, to babu komai. Za a shafe su daga doron kasa."
Hajia Ladi ta zaro kudade masu yawa ta aje a gabansa. "Idan kudin ne, babu matsala. A tabbata aikin an yi shi yadda ya kamata."
Suka tsaya suna ci gaba da tsara yadda za a aikata abin da suke shiryawa.
Amma Haruna, daya daga cikin ma’aikatan gidan Alhaji Uzairu, yana jin komai daga inda yake laɓe.
Sun manta cewa idanun wani yana kansu.
Suna gamawa, suka fice cikin dare.
Haruna ya saki ajiyar zuciya, yana jin yadda gumi ya lulluɓe shi.
A cikin zuciyarsa, ya san wannan lamari yana da matukar hatsari. Idan har bai yi abu akai ba, to ba zai yafe wa kansa ba.
Dole ne ya sanar da Alhaji Amiru...
***
Alhaji Amiru yana zaune a cikin falonsa, yana nazarin wasu takardu, lokacin da Haruna ya shigo da sauri.
Da yake ya san shi a matsayin ma’aikacin gidan Alhaji Uzairu, sai ya kalle shi da mamaki.
"Haruna, lafiya kuwa?"
Haruna ya duka a gaban sa, yana kokarin daidaita numfashinsa.
"Alhaji... akwai matsala babba! Wata babbar fitina ake shiryawa!"
Alhaji Amiru ya jingina da kujera, yana jiran karin bayani.
"Alhaji," Haruna ya ci gaba da cewa, "Ni ne da idona na ji, da kunnuwana na saurara. Su Hajia Karama, Hajia Ladi, da Hajia Rumanah... sun je wajen boka domin a kashe su Zaytunah gaba daya! Sun bada kudi, sun kuma tsara yadda za a aikata hakan."
Zuciyar Alhaji Amiru ta buga da karfi.
Ya kafe Haruna da ido na sakanni da dama.
"Wani irin abu kake fada haka?" Ya tambaya, yana jin wani abu yana taso masa a KIRJI.
"Wallahi da gaskiya nake magana, Alhaji!" Haruna ya kara tabbatar da cewa ba karya yake ba. "Sun ce za su kawo wani abu da ke jikin Hajiya Zaytunah da yaranta domin a kammala aikin."
Alhaji Amiru ya shafa fuska da hannunsa, zuciyarsa na tafasa.
Ya san cewa su Hajia Karama suna da tsananin kiyayya, amma bai taba zaton za su kai ga irin wannan mummunan nufi ba.
Dole ne ya dauki mataki.
Bai tsaya wata-wata ba, ya dauki waya ya kira Alhaji Uzairu, sannan ya kira mahaifiyarsu, Gwaggo Zainabu.
***
A lokacin da suka zauna a babban falon gidan Alhaji Uzairu, shiru ne ya ratsa bayan Alhaji Amiru ya bayyana musu duk abin da ke faruwa.
Alhaji Uzairu ya girgiza kai, yana jin kamar ba a duniya yake ba.
"Babu yadda za a ce matana sun je wajen boka saboda su kashe Zaytunah!" Ya ce da karfi.
Alhaji Amiru ya kafe shi da ido. "Uzairu, ka tabbata da hakan? Ka tabbata da cewa su Hajia Karama ba su da irin wannan niyyar?"
Shiru ya biyo baya.
Gwaggo Zainabu ta sauke ajiyar zuciya.
"Idan da gaske ne wannan magana," ta ce cikin yanayi mai nauyi, "to dole ne mu dauki mataki kafin su aikata abin da suke so."
Alhaji Amiru ya mike tsaye, yana jin zuciyarsa na harbawa da karfi.
Idan har matan gidan suna da wannan mugun nufi, to dole a dakatar da su.
Domin ko ba komai, Zaytunah da ‘ya’yanta suna da hakkin rayuwa.
Ba za a bari wani ya shafe su daga doron kasa ba!
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞
*PG :25*
*AREWABOOKS VVIP:👇*
https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb
___
Shiru ya ratsa falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa tana tafasa.
Alhaji Uzairu ya jingina da kujera, yana girgiza kai tamkar wanda ya kasa yarda da abinda kunnuwansa suka ji.
"Subhan'Allah, Yaya Amiru," ya furta a hankali, yana dafe goshi. "An tabbatar da gaske Ladi da karama sune suka je wajen boka domin kashe Zaytunah?"
Alhaji Amiru ya cije lebe, yana kafe shi da ido. "Uzairu, ya kamata ka gane cewa kai ba ka san matanka ba. Kawai kana zaune kana tunanin komai lafiya kalau, alhalin wasu suna neman shafe daya daga cikin matan ka da ya’yan ka daga doron kasa!"
Gwaggo Zainabu ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
"Yanzu me za a yi?" Ta tambaya, tana kallon Alhaji Amiru.
Alhaji Amiru ya kalli Haruna, wanda ya yi ta bayani a baya, ya kuma tabbatar da cewa abin da ya ji da kunnensa ba karya ba ne.
Daga bisani, ya kalli Alhaji Uzairu.
"Uzairu, ya kamata ka dauki mataki kafin lokaci ya kure," ya fada da kakkausar murya.
Alhaji Uzairu ya numfasa, zuciyarsa na tafasa da tunani iri-iri. Bai san cewa haka matansa suke ba. Bai taba tunanin cewa za su iya aikata irin wannan mummunan abu ba.
"Amma... ina bukatar hujja," ya ce cikin kasala.
"Kana bukatar hujja?" Alhaji Amiru ya tambaya yana kallonsa da mamaki. "Shin har yanzu baka yarda da abinda aka fada ba?"
"Ba wai ban yarda ba bane," Alhaji Uzairu ya ce, yana shafa fuskarsa. "Amma dole ne a tabbatar da komai kafin a dauki mataki."
Haruna ya gyara zama, yana fuskantar Alhaji Uzairu.
"Alhaji, wallahi da idona na gani, da kunnuwana na ji," ya fada cikin tabbaci. "Idan kuwa kuna bukatar wani shaida, zan iya komawa har wajen bokan domin a tabbatar."
"Ba dole sai ka koma ba," in ji Alhaji Amiru. "Dole ne mu dauki mataki tun kafin lokaci ya kure."
Gwaggo Zainabu ta jinjina kai.
"Amma su kansu ba su san an tona musu asiri ba, ko?"
"A’a," Haruna ya amsa. "Babu wanda ya san cewa na bi su, babu wanda ya san na ji komai."
Shiru ya sake ratsa falon.
Alhaji Uzairu ya dafe kansa, yana jin yadda zuciyarsa ke karyewa. Shin haka matansa suka zama? Su ne da suka daɗe suna tare da shi?
Gwaggo Zainabu ta yi gyaran murya, sannan ta kalli Alhaji Amiru.
"Yanzu me za ku yi?"
Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya.
"Muna bukatar mu fara da kare su Zaytunah," ya ce. "Dole ne mu tabbatar cewa sun fi kowane lokaci a cikin kariya."
"Ta yaya?" Gwaggo Zainabu ta tambaya.
Alhaji Amiru ya gyara zama. "Za mu samu Major General Dawud," ya ce. "Shi kadai ne zai iya tabbatar da cewa ba za a cutar da su ba. Idan har akwai wanda zai iya daukar mataki cikin gaggawa, to shi ne."
Gwaggo Zainabu ta gyada kai. "Hakan yayi. Amma fa, ba za mu bari su Karama su fahimci cewa an tona musu asiri ba."
"Tabbas," in ji Alhaji Amiru.
Sannan ya juyo ga Alhaji Uzairu.
"Uzairu, dole ne ka kara lura da matanka," ya ce cikin tsananin takaici. "Idan har ka barsu da wannan mugun nufi, to za su iya aikata abinda ba za ka taba yarda da shi ba."
Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin tamkar kansa zai fashe.
Bai san cewa matsalar ta kai haka ba.
Amma yanzu, babu abin da ya rage face daukar mataki....
Shiru ya sake ratsa falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa cike da tunani mai nauyi.
Gwaggo Zainabu ta dafa gefen kujera, ta dubi Alhaji Uzairu da idanuwanta da ke dauke da damuwa.
"Uzairu, lokaci ya yi da za ka tsayu ka fuskanci gaskiya," ta fada cikin nutsuwa. "Idan ka yi sakaci, abin da zai biyo baya ka iya zama mafi muni fiye da yadda kake tunani."
Alhaji Uzairu ya bude ido, yana kallonta. Har yanzu zuciyarsa ba ta gama karbar gaskiyar abin da ake fada masa ba. Sai dai yana jin nauyinsa sosai.
Alhaji Amiru ya yi gyaran murya.
"Maganar gaskiya, ba zamu jira har su sake kokarin cutar da Zaytunah ba," ya ce da kwarin gwiwa. "Dole ne mu kai rahoto wajen Major General Dawud. Shi ne kadai zai iya magance wannan matsala cikin gaggawa."
Gwaggo Zainabu ta jinjina kai.
"Hakan daidai ne," ta ce. "Amma kada mu manta cewa idan suka fahimci cewa an gano su, to ba abin da ba za su iya aikatawa ba domin su kare kansu."
Haruna ya gyada kai.
"Tabbas, su Karama da kishiyoyinta ba za su yi kasa a gwiwa ba idan suka ji cewa an bankado SIRRIN su," ya ce. "Wannan shine dalilin da ya sa dole a yi komai a hankali, ba tare da sun fahimta ba."
Alhaji Uzairu ya gyara zamansa, ya dubi Alhaji Amiru da Gwaggo Zainabu.
"To yanzu, ya za ayi?" ya tambaya cikin damuwa.
Alhaji Amiru ya yi shiru na dan lokaci, kafin ya kalli Haruna.
"Ka shirya ka sake tafiya wajen boka?" ya tambaya.
Haruna ya yi ajiyar zuciya, ya kalli su duka.
"Idan hakan zai tabbatar da cewa muna da cikakken shaida, zan sake komawa," ya ce cikin karfin hali. "Sai dai, dole a yi HANKALI kada su fahimci cewa ana bincikensu."
Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu.
"Uzairu, kana da tabbacin cewa za ka iya hada kai da mu wajen ganin an yi adalci?"
Alhaji Uzairu ya dago idanuwansa, yana kallon kowa daya bayan daya. A zuciyarsa, yana jin radadin cewa iyalinsa sun fi kowa cutar da shi. Bai taba tunanin cewa akwai wata rana da za a gaya masa irin wannan abu ba.
Ya numfasa, sannan ya gyada kai.
"Na amince," ya ce a hankali. "Ba zan bari su kashe min iyali ba."
Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
"To, lokaci bai yi ba da za mu tafi wajen Major General Dawud ba?"
Gwaggo Zainabu ta gyada kai.
"Yanzu ne lokaci. Ba za mu jira har sai wani abu ya faru ba."
Alhaji Amiru ya mike tsaye.
A nan suka yanke shawarar tafiya wajen Major General Dawud, don a dauki matakin kare Zaytunah daga mummunar makarkashiya da kishiyoyinta suka kitsa...
Suna fitowa daga falon, kowanne daga cikinsu zuciyarsa cike da tunani. Alhaji Uzairu yana bin su da baya, har yanzu kansa a kulle yake da abubuwan da suka faru. Bai taba tunanin cewa wata rana zai fuskanci wannan matsala daga matansa ba.
Haruna ne ya dauki nauyin tukin motar, yayin da Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu suka zauna a bayan mota, kowanne cikin nitsuwa. A lokacin da motar ta bar harabar sashen Gwaggo Zainabu, shiru ya ratsa cikin su.
Alhaji Uzairu ya lumshe idanu, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi. Abin da ke faruwa ya girgiza shi matuka.
“Uzairu, ka tabbatar cewa kana da ƙarfin zuciyar fuskantar abin da zai biyo baya?” Alhaji Amiru ya tambaya, yana dubansa.
Alhaji Uzairu ya bude idanu, ya dubi dan uwansa. “Dole na yi hakan, Yaya Amiru,” ya ce da karfin hali. “Ba zan iya bari su hallaka min ‘ya’ya ba.”
Haruna ya cigaba da tuƙi cikin nutsuwa, yana bin titin da zai kaisu gidan Major General Dawud.
MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RES:
A lokacin da suka isa, an shigo da su kai tsaye zuwa falon ba tare da wata matsala ba. Major General Dawud yana sanye da kayan gida, yana zaune bisa kujerar da ke gefen babban falonsa. Da gani, yana cikin shirin hutawa ne kafin su shigo.
Ya kalli su daya bayan daya, kafin ya maida kallonsa ga Alhaji Amiru.
“Kun zo da gaggawa, Amiru,” ya fada a hankali. “Ina sauraronku.”
Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara bayanin komai dalla-dalla. Ya fada masa yadda Haruna ya bi matan Alhaji Uzairu har wajen boka, yadda ya ji su da kunnuwansa suna tsara kashe Zaytunah, da yadda Alhaji Uzairu ya kasa yarda da hakan har sai an kawo hujja mai karfi.
A lokacin da Alhaji Amiru ya kai karshe, fuskar Major General Dawud ta nuna tsananin ɓacin rai.
“Kun tabbatar da cewa wannan maganar gaskiya ce?” ya tambaya, yana duban Haruna da tsananin ido.
Haruna ya gyada kai. “Wallahi, babu shakka akan haka, ranka ya dade,” ya ce da tabbaci.
Major General Dawud ya jingina da kujera, yana tunani na wani lokaci.
“Idan haka ne, lamarin yana bukatar gaggawa,” ya ce a hankali. “Ba zan bari komai ya same su Zaytunah ba. Fata dai a same sun..”
Ya dubi Alhaji Uzairu da kyau. “Uzairu,” ya kira sunansa da kakkausar murya. “Kana da tabbacin cewa ba za ka yi wata-wata wajen daukar mataki akan wannan lamari ba?”
Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin Major General Dawud. Da farko, yana jin kamar abin kamar mafarki ne, amma yanzu ya san babu gudu ba ja da baya.
“Na tabbatar,” ya amsa cikin muryar da ke nuna yanke shawara.
Major General Dawud ya mike tsaye. “To, ku jira ni,” ya fada.
Ya yi gaba zuwa wani daki, sannan ya fito cikin uniform dinsa, yana daure da damara. Fuskar sa a daure take, alamun ya gama yanke shawara akan abin da zai yi.
“Za a tsaurara tsaro Inn shaa' Allah"
Ya kalli su duka, sannan ya dauki wayarsa. “Kuma ba zan tsaya nan ba. Sai mun tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan makirci.”
Alhaji Uzairu ya runtse ido, zuciyarsa cike da nauyi. Ya san cewa daga wannan rana, rayuwar sa ba za ta kara zama kamar yadda take a da ba...
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:26_
Da Alhaji Uzairu ya iso gida, bai wuce kai tsaye zuwa dakinsa ba. Maimakon haka, ya tsaya a babban falon gida inda matansa, Hajiya da Hajiya Karama, suke zaune suna tattauna wasu batutuwa a tsakaninsu. A ganinsa, kamar dai suna magana ne da nutsuwa, amma da zarar suka hango shi, sai suka yi shiru tamkar wadanda aka kama da laifi.
Ya zuba musu ido na dan lokaci ba tare da ya ce komai ba. Sai da ya zauna a kujera ya dora kafa daya kan daya, sannan ya gyara zama, yana jin nauyin da ke cikin zuciyarsa.
"Hajiya," ya kira sunan matar sa ta farko, "yau na wuni a gidan Ya Amiru."
Hajiya ta kalle shi cikin kulawa. "Lafiya dai? Ka dawo da wuri yau."
"Eh, ai ba wani abu," ya fada, yana juyawa zuwa ga Hajiya Karama.
"Mun yi doguwar hira da Alhaji Amiru da Gwaggo Zainabu. Sun yi tambayoyi da yawa game da rayuwar mu."
A take, Hajiya Karama ta hadiye yawu. "Tambayoyi irin na menene kuma?"
Alhaji Uzairu ya girgiza kai. "Kawai dai wasu tsofaffin batutuwa ne… da kuma wasu abubuwan da suka shafi rayuwar mu a baya."
Hajiya ta dube shi da dan tsoro. "Rayuwa ta baya fa?"
Sai ya gyada