KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   19 / 40

54K to 57K   out of 119.4K words

ta tsaya a harabar gidan a hankali, amma babu wanda ya yi yunƙurin fita daga ciki.

Shiru ya ratsa tsakanin su, sai dai sautin numfashinsu da aka kasa ɓoyewa.🤭

Fawaaz ya kafe idanunsa a kan gaban motar, amma zuciyarsa na wani wuri. A zuciyarsa, yana jin tamkar bai so su koma gida ba. In da za a ce lokacin zai tsaya cak, ya kasance tare da ita har abada, babu shakka da ya yi hakan.

Sai dai rayuwa ba haka take ba.

Ya juyo a hankali, idanunsa suka sauka a kanta.

Nabeeha tana zaune da mayafinta da ya zame a gefe, yana bayyana fuskar da ya daɗe yana gujewa kallon kai tsaye. Amma yau…

Yau zuciyarsa ba ta iya daurewa ba.

“Nabeeha.”

Muryarsa ta fito a kasalance, amma cike da nauyin da bai saba da shi ba.

Ta dago idanunta a hankali, idanunta masu launin hazel sun ratsa nasa. Duk wani ƙoƙarin da take yi na guje wa kallonsa ya gagara, saboda yadda idanunsa suka kulle nata gaba ɗaya.

Fawaaz ya dan matsa, yana jin wani abu na fisgarsa da ƙarfi.

Bai san lokacin da hannunsa ya kai ya riƙo nata ba. Hannunta ƙanƙani ne cikin nasa, amma dumin da ya ji ya fi duka sojojinsa cusa masa jini a cikin gangar jikinsa.

Nabeeha ta runtse ido. Ta san cewa idan har ta sake kallonsa, tabbas za ta nutse a cikin abin da take ƙoƙarin guje wa.

Sai dai hakan bai hana ta jin yadda zuciyarta ke bugu da sauri ba.

A hankali, Fawaaz ya ɗago da ɗayan hannunsa, ya sanya yatsansa a gefen fuskarta. Bai sani ba, amma yana jin tamkar zuciyarsa ta ɓarke da wani irin shauƙi da bai taɓa fuskanta a rayuwa ba.

Ta buɗe idanunta a hankali.

Idanunsu sun haɗu, zuciyoyinsu suka yi shiru, amma jikin nasu na furta dukkan abin da suke ji.

Fawaaz ya saki ajiyar zuciya mai nauyi.

Ina ma ita ce tasa.

Ina ma yana da ita tamkar yadda yake buƙatar ta.

A hankali ya matsa, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. Yana jin yadda idanunta ke kiran nasa, ba tare da wata kalma ba.

Labbanta sun jike da ɗan sauƙin numfashi. Suka kasance jajaye kamar furannin wardi, suna kiran nasa da wani irin nutsuwa da tsoron zuciya.

Tamkar Ya kai karamin sumba a hankali.

Sai da ya ji yadda duk wani zafin da zuciyarsa ke ji ya narke a take.

Nabeeha ta lumshe ido. Bai da ƙarfin ja da baya. Bai da ƙarfin barin abin da zuciyarsa ta riga ta aminta da shi.

Fawaaz yaji tamkar ya jingina goshinsa da nata, yana mai jin tamkar wannan ne farkon tafiyar da bai san inda za ta tsaya ba.

Yana jin zuciyarsa na bugawa, amma ba da tsoron soja ba—da tsoron so.

Soyayyar da ba zai iya furtawa ba.

Fawaaz ya kashe motar, amma bai yi yunƙurin buɗe ƙofa ba. Hannayensa suna kan sitiyari, amma zuciyarsa tana wani wuri.

Zuciyarsa tana tare da ita.

Nabeeha tana gefensa, zaune kamar yadda ta kasance tun farkon tafiyar. Sai dai yanzu, shiru ya mamaye tsakanin su.

Wani irin sanyi ya ratsashi. Bai san dalili ba, amma zuciyarsa na faɗin abu ɗaya,

"Ina ma halaliyata ce, inama tawa ce mallaki na ce.."

"Ina ma zan iya riƙe ta cikin kaina, ba tare da wata shakka ba.inama ace matata ce"

Ya dan juyo, idanunsa suka sauka a kanta.

Ta daɗe da sunkuyar da kai, tana wasa da yatsunta cikin nutsuwa.

Fawaaz ya kafe ta da ido, yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Wani ƙarfi ne ya lulluɓe shi, yana ƙoƙarin fisgarsa.

Ya ma rasa dalilin da ya sa hakan ke faruwa.

Hannunsa ya dan motsa, yana so ya kai ga nata. Amma ya dakata.

Ba ta tashi ba.

Ba ta yi magana ba.

Haka shima bai ce komai ba.

Bai san yaushe ya juyo da fuskar sa sosai ba, yana kallon yadda hasken fitilar gidan ke sauka saman fuskarta.

Ta haɗiye yawu a hankali, tana jin idonsa akan ta kamar wuta.

Fawaaz ya sake numfasa, yana jin yadda zuciyarsa ke faɗin abu ɗaya,

"Ina ma zan iya rungumarta a kaina."

"Ina ma zata iya jin yadda zuciyata ke bugawa saboda ita."

Sai dai…

Ba halaliyar sa bace.

Ba mallakinsa ba ce.

Zuciyarsa ta amince da hakan, amma gangar jikinsa ta ƙi.

Ya lumshe ido, yana mai jin yadda wannan tunanin ke ƙara masa raɗaɗi.

Ya ɗauki lokaci kafin ya matsa baya kadan, ya jingina da kujera, yana mai kakkabe duk wani tunani da ke ransa.

Soja ne shi.

Dole ne ya riƙe kansa.

A hankali ya ce,
“Mun iso.”

Muryarsa ta fita da sanyi, ba tare da ƙarfin da ya saba da shi ba.

Nabeeha ta daga kai a hankali, suka yi ido biyu. Sai dai kafin ta samu damar cewa komai, ya riga ya buɗe ƙofar motar ya fita.

Ya riga ya rufe komai cikin zuciyarsa....









Dan wahala 😂🤭🧑‍🦯







MX🧕

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*


_PAGE:31_



A cikin babban falon gidan Major General Dawud, kowa ya hallara. Gwaggo Hafsatu na zaune a tsakiyar kujerar da take da alfarma, tana daura tafukan hannunta a saman cinyoyinta. Fuskar ta na bayyana alamar tunani mai zurfi, tamkar tana jin nauyin wani babban yanke hukunci.

Major general dawud mafia na daga gefen ta yana kallon kasa da shiru. Duk da cewa shi mutum ne da ke da karfi da iko, yau ya kasa daukar mataki ba tare da jin ra’ayin Gwaggo Hafsatu ba. Yana jin nauyin amanar da ta rataya a wuyansa—amanar Zaytunah da ‘ya’yanta.

A gefe guda, Hajiya Zaytunah na zaune da kai a kasa, zuciyarta cike da tunani. Shekaru da yawa da suka shude, ta san ba za ta iya komawa gidan Alhaji Uzairu ba a tunanintaa, kuma yanzu da aka buɗe sabon shafi a rayuwarta, dole ta yanke shawarar da ta dace. Nabeeha da Hammad kuwa suna zaune kusa da ita, suna kallon kowa da kowa a falon, ba tare da sanin abin da ke tafe ba.

Gwaggo Hafsatu ce ta katse shiru da wata kakkausar murya,

“wannan hutun mai dogon zango. Inshaa Allah a birnin mawii zamuyi shi.”


Kowa ya kalleta. Major general yadan gyara zamansa, yana jiran jin dalilinta.

"Dawuda yana da katafaren gida a can, gida ne da zai iya daukar su Zaytunah da ‘ya’yanta cikin kwanciyar hankali. Babu wanda zai takura musu ko ya binciko su, babu wanda zai dinga bibiyar rayuwarsu. Idan muna so su sami sabuwar rayuwa, to Mawii shine mafita.”

" hakan zai fi dacewa,” ya fada a hankali. “Ni kaina ba na so su zauna a nan, saboda idan SIRRIN ya tonu, za mu shiga matsala.”

Hajiya zaytunah ta dago kai a hankali.

"Gwaggo, kina nufin mu bar noka gaba daya?”

“Eh, Zaytunah,” Gwaggo Hafsatu ta fada da karfin gwiwa. “Dole mu fice, saboda noka ba wurin da zai ba ki kariya bane. Na gama magana da Dawuda, ya shirya mana komai.”

Nabeeha ta kalli mahaifiyarta da mamaki. Komawa wani gari daban? Wata sabuwar rayuwa? Ta kalli Hammad, shima yana kallon ta, tamkar yana jiran jin ra’ayinta.

"Tohm gwaggo abunda kika yanke shi za'ai. Allah dai ya Saka muku da alkhairi. Yasa komawar tamu canne mabudin alkhairan mu gaba daya Amin"

"Aameen" suka hada baki wajen amsa ta.

___-----____

Bayan kwana biyu da tunani da shawarwari, Major General Dawud ya yanke shawarar kira Alhaji Amiru domin su yi wata muhimmiyar ganawa. A lokacin yana zaune a cikin ofishinsa, cikin tsanaki ya dauki wayarsa ya danna lambobin Alhaji Amiru.

Da alama yana jiran kiran, domin kuwa cikin ‘yan kara-kaushe Alhaji Amiru ya daga wayar.

"Salamu alaikum, Major General." Muryarsa da karfin gwiwa kamar yadda aka santa, sai dai akwai dan nutsuwa cikin ta.

"Wa’alaikumus salam, Alhaji Amiru. Ina fata kana lafiya?"

"Alhamdulillah. Yaya aiki?"

"Alhamdulillah. Akwai magana da nake so mu yi, idan baka da wani uzuri, acikin tsukukun nan. Zan neme ka"

Shiru na dan lokaci ya biyo baya. Alhaji Amiru ya fahimci cewa maganar dole ce, kuma ba zai yi mata rikon sakainar kashi ba.

"Babu matsala, Major General. in Allah Ya yarda."

"Shikenan.sai ka jini."

Bayan kammala kiran, Major General Dawud ya sauke numfashi. Yana da tabbacin cewa wannan ganawar za ta tsayar da shawarwarin da suka dauka a gida game da Zaytunah da ‘ya’yanta.

....
A yini biyu da suka gabata, an yi zaman shawarwari mai tsawo a gidan Major General Dawud. Gwaggo Hafsatu ce ta sake kira zaman, inda ta bukaci a zauna a sake tattauna batun komawar Hajiya Zaytunah da iyalanta zuwa wani wuri mafi tsaro da kwanciyar hankali.

"Na dade ina addu’ar Allah Ya yi mana jagora," cewar Gwaggo Hafsatu, tana kallon Major General Dawud da Hajiya Zaytunah. "Duk da haka, ba zan yanke hukunci ba sai da amincewarki, Zaytunah."

Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi, tana dan gyara zamanta. "Gwaggo, ni babu abin da nake so sama da kwanciyar hankali ga ‘ya’yana. Amma har yanzu ba zan iya komawa gidan Alhaji Uzairu ba. Komai yana nan yadda na bari."

"Mun fahimta," Major General Dawud ya katse shurun da ya biyo bayan maganarta. "Akwai wani wuri da muke son mu kaisu, Birnin Mawii. Gida ne da aka tanada tun tuni kamar yadda aka fada a baya, amma yanzu ne zai fi dacewa da su."

Hajiya Zaytunah ta daga ido tana kallonsa. "Birnin Mawii?"

"Eh. Gida ne mai tsaro da kwanciyar hankali. Ba kowa zai iya gane su can ba, kuma za su sami damar sake farawa da sabuwar rayuwa."

Shiru ya sake ratsa dakin, kafin daga bisani Hajiya Zaytunah ta gyada kai a hankali. "Idan hakan ne mafi alheri gare mu, to na amince."

Washegari kuwa, aka fara shiri don fice wa cikin SIRRI da kwanciyar hankali.

🎀🎀🎀

Major General Dawud mutum ne mai kamun kai, wanda ya fi so abubuwa su tafi yadda ya tsara su. Bai cika barin wayarsa a ko’ina ba, domin yana da matukar kula da SIRRIN SA. Amma yau, kwatsam, yana dawowa daga sashen mahaifiyarsa, Gwaggo Hafsatu, ya shiga dakinsa ne ba tare da tsammani ba, sai ya ci karo da wani abin da ya kada masa gwiwa.

A kusa da gadonsa, Hajiya Hawwa Maijiddah na zaune da wayarsa a hannunta. Ba wai tana kallonta ba ne kawai, a’a, Tana rubuta wata lamba a nata wayar!

Da farko, bai ce komai ba. Ya tsaya a bakin kofa, yana nazarin lamarin. Ya lura yadda ta mayar da hankali sosai, tana ta dannawa cikin hanzari kamar wacce ke tsaka da wata gaggawar aiki.

Da sauri ya kutsa cikin dakin, zuciyarsa na bugawa. "Hawwa!" Ya kira da murya mai karfi, amma ba tare da hayaniya ba.

Da sauri ta daga kai, idonta cike da firgici. Kafin ta samu damar ɓoye abin da take yi, ya karaso ya kwace wayarta.

"Meye haka?" Ya tambaya da karfi, yana kallon wayarta.

Tana kokarin mayar da nutsuwa, amma jikinta ya nuna cewa an kamata. "Uh… Ni dai kawai… na duba wani abu ne."

"Duba wani abu?" Ya maimaita, yana duba fuskar wayarta. ya duba fuskar wayar Hajiya Hawwa Maijiddah, idonsa ya tsime kan jerin sakonni da ta tura. Bai tsaya bata lokaci ba, ya danna kiran baya (recent messages). Cikin ikon Allah, sakon da ta tura bai riga ya goge ba.

A yayin da ya karanta, fuskar sa ta nuna tsananin bacin rai. Har gaban zuciyarsa yaji wani irin daci.

"Wannan shine babban shirin su. Za a mayar da ita da ‘ya’yanta wani area dake garin ku na mawi.. Gida ne na SIRRI da aka tanada tun tuni, amma yanzu ne za a kaisu. Za a yi tafiya cikin SIRRI."

Hannunsa ya fara matse wayar da karfi, idanuwansa suka kada.

Ya dago kai a hankali, yana kallon Hajiya Hawwa Maijiddah da take kokarin boye firgicinta.

"Hawwa, wa kike tura wa wannan sakon?"

Muryarsa cike da tsawa, da wata irin natsuwa mai hade da fushin da ba kasafai ake ganin shi da shi ba.

"Ni… Ni… Wallahi… Ba wani abu bane" Ta fara kokarin magana, amma muryarta na rawa.

"Ba wani abu bane? Kina fadawa wani SIRRIn da ni da Gwagggo muka dauki tsawon lokaci muna kiyaye shi, sannan kice ba wani abu bane?!"

Ya nuna mata wayarta da ke hannunsa, yana mai nuna mata sakon da ta tura.

"Daga ina kika samu wannan number.. shinma Wa kike turawa, Two face?? Fuska biyu hauwa?!"

Tayi shiru. Jikinta har rawa yake yi. Idanuwanta sun cika da ruɗani. A yadda ta san shi, idan yana cikin fushi irin wannan, babu mai iya hanashi daukar mataki.

Ya dauki tsawon lokaci yana kallonta, zuciyarsa na tafasa. Wata zuciyar tana gaya masa ya mata tambayoyi da ladabi, wata kuma tana gaya masa cewa babu sauran lokacin sassauci.

Ya kai hannu ya dauki wayarsa, yana dubawa don ganin ko ta duba wasu bayanai a cikinta. Bai jima ba, ya gano cewa ta shiga cikin saƙon wayarsa, tana duba sakonninsa da kuma lambobin da suka shafi Zaytunah da iyalanta.

"Whattttttt!" Ya furta a hankali, amma muryarsa ta kara tsananta.

Yayi kokarin bin lambobin da ke cikin wayarta, yana nazari kan wanda take tura wa wadannan sakonni. Amma hakan bai samu ba cikin sauki. Amma abu daya ya bayyana, wannan lambar ba sabuwa bace. Wani mutum ne da take da alaƙa da shi tun baya.

Da sauri ya kalle ta, yana kokarin gano amsar tambayoyin da zuciyarsa ke yi.

"Waye wannan? Waye kike turawa wannan bayanai?"

Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kanta, tana kokarin kaucewa kallon idanunsa.

"Daga yau, kada ki kuskura ki kara taba wayata!" Ya furta da kakkausar murya, yana jefar da wayarta akan gadonta.

"Duk wani abu da kike shiryawa, na tabbatar ba zai yiwu ba."

Ya juya, zuciyarsa cike da tunani. Wannan abu ba zai wuce haka kawai ba. Zai bincika komai ko da kuwa hakan yana nufin zai bankado wani SIRRI mafi muni fiye da wanda ya gani yanzu. Shi ya Saka ma ba zai dauki hukunci ba anan take. Sai ya gama bincike ya futarda sakamakon bincikensa...

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*


_PAGE:32_



Major General Dawud ya yi numfashi mai nauyi, zuciyarsa na tafasa da tunani. Bai taba zaton Hajiya Hawwa Maijiddah zata iya aikata irin wannan ba. Ya san cewa ba ta cika jin dadin zaman Zaytunah a gidan ba, amma bai yi tsammanin cewa za ta kai ga tona SIRRIN da aka dauki lokaci ana boyewa ba.

Yana tsaye a tsakiyar dakin, yana kallonta da idanuwansa masu nuna tsananin takaici. Hajiya Hawwa Maijiddah ta sunkuyar da kai, tana kokarin kauce wa kallonsa. Duk da cewa a zuciyarta ta san cewa bata da wata hujja mai kwari da zata iya kare kanta da ita, har yanzu tana kokarin boye gaskiyar lamarin.

"Hawwa," ya kira sunanta da murya mai cike da natsuwa, amma hakan bai sa zuciyarta ta daina bugawa da karfi ba.

"Daga ina kika samu wannan bayanin? Waye yake ba ki shi? Waye kike tura wa wannan sakon?"

Ta dinga hadiye yawu, tana jin tsoron bayyana gaskiya. Idan har ta fada masa komai, tabbas hakan zai kara dagula al’amura.

"Dawud, wallahi ba wani abu bane… Ni dai kawai… kawai ina son sanin abubuwan da ke faruwa ne. Na tsinci labari ne daga inda ba zan iya bayyanawa ba."

Ya saki murmushin takaici, yana jin yadda zuciyarsa ke kara tafasa.

"Kin san mene?" Ya kalle ta kai tsaye. "Bani da bukatar jin wani karin bayani daga gare ki, domin abinda nake gani ya ishe ni."

Ya juya, ya dauki wayarta yana sake duba sakonnin da ta tura. Yayi mamakin yadda ta samu cikakken bayani game da shirin komawar Zaytunah da ‘ya’yanta. Wannan ya tabbatar masa da cewa dibar rahotan komai take tana barbadawa..

"Hawwa, ni da ke muka zauna a wannan gidan tsawon shekaru, amma ban taba tunanin cewa wata rana za ki iya cin amanata haka ba."

Hajiya Hawwa Maijiddah ta dago kanta a hankali, idanunta cike da hawaye. "Wallahi ba hakan bane, Dawud… Ni dai kawai—"

"Ya isa!" Ya katseta da muryar da ta firgita ta. "Na ce ki bani amsa, ba na son jin wata ‘yar magana maras amfani."

Ta yi shiru. Idanunta sun kada da tashin hankali, amma ta kasa furta komai.

Major General Dawud ya runtse idonsa na wani lokaci, yana kokarin kwantar da fushinsa. Amma hakan ba abu ne mai sauki ba. A zuciyarsa, ya fara tunanin duk wata hanya da zata iya fallasa bayanan SIRRIN da suka dade suna kokarin rufewa.

Idan Hajiya Hawwa Maijiddah ta iya sanin wannan labari, hakan na nufin cewa akwai wanda ke ba ta bayanai a cikin gidan. Ko kuma ta samo su daga wajen wani da ke da masaniya game da lamarin.

Ya dauki wayarta, yana kokarin ganin idan zai iya gano wanda take turawa sakonni. Amma abin mamaki, lambar da ta aika wa sakonnin ba ta da suna. Wata lamba ce da ba a rubuta mata suna ba, wata sabuwa ko wata da aka boye.

Wannan ya kara tabbatar masa da cewa akwai wani abu mai girman gaske da ke faruwa.

A take ya juya, ya dubi Hajiya Hawwa Maijiddah da idanuwansa masu nuna bacin rai.

"Na dauki alkawari, babu wanda zai taba Zaytunah da ‘ya’yanta ba tare da sunan Allah ya tabbata akai ba. Idan har kina da hannu a cikin wani shiri na cutar da su, to ki sani, ba zan taba lamunta ba."

Ya wuce zuwa kofar fita, amma kafin ya fita, ya tsaya ya sake dubanta.

"Ki tanadi amsa, domin zan dawo."

Ya fice daga dakin, zuciyarsa na cike da tunani. Wannan batu ba zai tsaya nan ba. Dole sai ya gano wanda ke bayan wannan al’amari—da kuma abinda ya kawo hakan.


Major General Dawud yana fita daga dakin, zuciyarsa cike da tunani. Bai yi kokarin rufe kofa

19 / 40