rasa komai. Ba ni da mafita, kuma a lokacin, Hajiya Ladi da Hajiya Karama sun makantar da Alhaji Uzairu da zargin karya akaina. Na san idan na tsaya, da za a kashe ni ko kuma na rasa hankalina."
Hammad ya dafa hannun mahaifiyarsa. "Ammi, na fahimta. Amma me yasa sai yanzu ake sanar mana?"
Gwaggo Hafsatu ta gyara zamanta.
"Saboda lokaci yayi. Har yanzu ana neman mahaifiyarku. Duk wanda ya mata wannan asiri, ba ya so ta dawo cikin iyalinta. Sai dai hakan ba zai canza gaskiyar lamarin ba."
Nabeeha ta runtse ido, zuciyarta cike da mamaki. Hammad kuma ya dafe goshinsa. Amma abu mafi tayar musu da hankali shine kalmomin da Gwaggo Hafsatu ta kara fadi,
"Sai Muhammad manemin ki Nabeeha, Da ne ga Alhaji amiru. Wato dan gidan hajia rumanah. Hajia rumanah Kuma da mahaifin ta da mahaifin mahaifiyar ku uwar su daya uban su daya, sannan rana daya aka haifi hajia rumanah da hajiya Zaytunah... atakaice dai Muhammad Hammad dan Alhaji Amiru Muhammad ne dan yayan mahaifin ku Alhaji uzairu!"
Wani mugun shock ya saukarwa Hammad da Nabeeha. Idanunsa suka firfito, yana kallon su duka.
"Dan Hajiya Rumanah ne?"suka hada baki wajen tambaya idanuwan su sun furfuto waje cike da mamaki ..
Gwaggo Hafsatu ta gyada kai.
"Eh, dan Alhaji Amiru da Hajiya Rumanah ne. "
Wani irin nauyi ya saukarwa Hammad da Nabeeha. Don Nabeeha kuwa, numfashinta ya fara hawa da sauka. ..
Major general dawud mafia yana daga gefen da yake zaune yana hankalce da komai gefe daya dinbin mamaki da sanyin jiki sun dabaibaye shi... Yana tausayin su sosai .
"To yanzu me zai faru?" Hammad ya tambaya, yana kokarin daidaita kansa.
Gwaggo Hafsatu ta dube shi da kulawa.
"Atakaice dai mahaifiyarku Hajiya Zaytunah tana son ku. Ta yarda da kaddara, kuma tana rokon Allah ya bayyana gaskiya. Abin da ya fi shine ku cigaba da rayuwar ku da hakuri da biyayya."
A wannan lokaci, dakin yayi shiru. Idanun Nabeeha da Hammad sun cika da kwalla, zuciyoyinsu suna cike da rudani. Rayuwarsu ta canza a cikin dare daya. Sun san iyayensu, sun san asalin su. Kuma sun san cewa komai da suka sani a baya—ya canza...
MX🧕
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞
*PG :29*
*AREWABOOKS VVIP:👇*
https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb
Tashin motar Fawaaz kadai ke karan kunne a kofar gidan Major General Dawud. Baba . Wato Major general dawud ne yace ya dauki nabeeha ya kaita workshop din da sukeyi na wani course na su na makaranta. Yana jingine da kujerar motar, hannayensa rike da sitiyari, yayin da zuciyarsa ke tafasa da tunanin wacce zai dauka a yau....
Nabeeha.
Ya lumshe ido a hankali, yana jin bugun zuciyarsa na karuwa da wani irin salo da ba kasafai yake jin sa ba. Bai san me ke damunsa ba, amma abu daya ne yake a fili—ya makara. Ta dade a shirye, kuma shi ke bata lokaci.
Daga cikin gidan, Nabeeha ta fito a nutse, sanye da riga da siket na atamfa mai launin royal blue, wanda ya kara fidda kyawun fatarta. Dogon gyalen kanta ya tsaya tsaf akan kafadunta, yana sauka daidai gadon bayanta.
Fawaaz ya dago idonsa daga sitiyari, idanuwansa suka sauka a kanta. Ya hadiye yawu.
Ya san cewa Nabeeha kyakkyawa ce. Amma a yau, akwai wani abu a tare da ita da ya kasa fassara.
"Sorry na bata lokaci," ta fada a hankali, tana kokarin bude kofar mota.
Fawaaz bai ce komai ba. Sai kawai ya juya yana kallon gaban motar, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wani irin nauyi.
Tana shiga, ya danna wani button, motar ta rufe da kanta. Ya daidaita sitiyari, sannan ya kunna motar, suka fara tafiya.
Shiru ya ratsa tsakanin su. Kamar kullum.
Nabeeha ta dan matsa jikinta gefe, tana kokarin tsaida zuciyarta daga bugun da take yi. Tunanin cewa yau Fawaaz ne zai kaita makaranta kadai ya ishi zuciyarta gamsuwa. Amma a lokaci guda, ya tuno mata da yadda shi mutum ne da ba ya taba magana da ita.
Ya kwana biyu yana wani iri. Yana kamar yana da damuwa, amma ba zai taba fada ba.
Sannu a hankali, karar kidan da ke fitowa daga stereo ya fara cika motar.
"Can’t help falling in love with you…"
Muryar Elvis Presley ta ratsa cikin motar a hankali, tana karawa yanayin shurun dake tsakaninsu nauyi.
"Wise men say… only fools rush in… but I can’t help… falling in love with you."
Fawaaz ya murza sitiyari da hannunsa, yana jin yadda kida ke mamaye zuciyarsa.
"Like a river flows… surely to the sea… darling so it goes… some things are meant to be."
Ya cije lebe, yana kallon titi amma tunaninsa yana kan wacce ke kusa da shi. Nabeeha.
Yana jin dadin kasancewarta kusa da shi. Yana jin shaukinta. Amma ba zai taba iya furta hakan ba.
Wakar dake fita itake bada sautin labarin dimbin kaunar da yake mata a birnin zuciyar sa..
Nabeeha ta juyo a hankali ta kalle shi. Idanunta sun sauka a kan hannayensa da suke kam da na soja, cike da layukan karfi. Sai kuma fuskarsa, wacce ke cike da natsuwa da miskilanci.
Hawaye ne suka taho mata, amma ta mayar. Kamar yadda ya saba mata miskilanci, shima zata saba.
"Take my hand… take my whole life too…"
Sai dai bata san cewa a zuciyarsa, Fawaaz yana juyawa kalmomin wannan waka ne a kansa.
"For I can’t help… falling in love with you."
Ya dauke numfashi a hankali, yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa. Ba zai iya cewa komai ba. Kuma ba zai iya dakatar da zuciyarsa daga jin abinda take ji ba.
Ya san abu daya ne kawai.
Shi fawaaz Dawud mafia yana son Nabeeha.
Amma zai iya furta hakan?
Fawaaz ya dan gyara zama, hannunsa na dama yana murza sitiyari a hankali. Wakar da ke tashi a cikin motar na dada saukar da wani irin shauki a zuciyarsa.
"Take my hand… take my whole life too… for I can’t help falling in love with you."
Yana jin wakar tamkar ita ce ke fassara zuciyarsa. Duk da miskilancinsa, zuciyarsa na cike da zafi—zafin soyayyar da ya kasa furtawa.
Idanunsa sun dan sauka a kan Nabeeha, wacce ke kallon titi ta window, hannayenta suna rungume da juna. Duk da bata ce komai ba, ya san tana jin wani abu.
Da alama ita ma tana kokarin boye abin da take ji, kamar yadda shima yake yi.
Hannunsa ya kara murza sitiyari.
"Kin shirya test ɗin?" Ya tambaya a hankali, muryarsa na fita da natsuwa.
Nabeeha ta juyo tana kallonsa da mamaki. Bai taba tambayarta wani abu makamancin hakan ba.
Ta dan saki murmushi, sai dai yana dauke da alamun damuwa. "Eh, ina kokarin karatu sosai."
Fawaaz ya gyada kai, sannan ya cigaba da tuki a shiru.
Shi kadai ya san yadda yake jin dadin jin muryarta. Amma me zai yi? Idan har yana jin wannan kauna mai tsanani a zuciyarsa, me yasa yake jin tsoron furtawa?
Kayi shiru! Ya fada a zuciyarsa. Kar ka sake. Ba dole sai ka fada ba.
Amma a lokaci guda, zuciyarsa na fada masa cewa yana makara.
Nabeeha ta dauke kai, zuciyarta na bugawa da sauri. Idanunsa sunyi mata kyau sosai yau. Tana son yadda uniform dinsa na yan sanda ke sake fidda kyawunsa. Iya kyan mutum!
Ta lumshe ido a hankali.
"Ina jin wani shiru," ta ce a hankali, bata san ta fada ba.
Fawaaz ya juyo da dan mamaki, sannan ya dauke kansa daga kanta.
"Me kika ce?"
Nabeeha ta girgiza kai, tana murmushi. "Ba komai."
Shi ma ya dan saki murmushi, amma cikin zuciyarsa yana jin abinda ta fada.
Eh, yana jin shiru. Shiru ne ke tsakanin su, shiru ne ke bayyanawa zuciyarsa dukkan abin da yake ji.
Amma zai iya furta hakan?
"Like a river flows… surely to the sea… darling so it goes… some things are meant to be…"
Wakar na cigaba da tashi a hankali, tana bayyanawa zuciyarsa abin da bai da karfin furtawa.
Ya lumshe ido na dakika daya, sannan ya bude. Bari ya cigaba da yi shiru. Zuciyarsa kadai zata fassara abin da take ji.
Sai dai, har zuwa yaushe?
Motar Fawaaz na tafiya cikin nutsuwa, tana yanke iskar titin da ke cike da shuke-shuke masu kyan gaske. An makara sosai, hasken rana ya fara dusashewa, yana barin wani launin orange mai kyau a sararin samaniya.
Nabeeha ta lumshe idanu a hankali, tana jin sanyin A.C na motar yana ratsa fuskarta. Sai dai, ba sanyin ne ya fi shigar ta ba—yana nan kusa da ita. Duk da shiru ne tsakaninsu, tana jin wani nauyi yana cika zuciyarta.
Fawaaz.
Idanunta sun sauka a kan hannayensa, wadanda ke rike da sitiyari da cikakken control, kamar yadda ya saba. Miskili ne, amma yana da nutsuwa. Kuma yana da wani abu da yake jan hankali ba tare da yana kokarin hakan ba.
Ta dauke kanta da sauri, saboda tsoron kada idanunta su bayyana abin da take ji.
Fawaaz a nasa bangaren, yana kallon titi amma zuciyarsa na wani irin tafasa. Bai saba da wannan yanayin ba.
Me yasa yake jin wannan abu a jikinta?
Me yasa shaukinta ke shigar sa sosai, har ma ya fi yadda ya zata?
Ya dan murza sitiyari, yana jin yadda numfashinsa ke sauka da nauyi. Sai dai duk da haka, ya ki bude baki.
Ya ki furta wani abu.
A zuciyarsa, yana jin kalmomin da bai da karfin furtawa,
"Nabeeha, ina matukar kaunar ki. Har tana yi min yawa. Amma ba zan iya furtawa ba."
Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta dafa glass din motar. "Zan yi kokari in gama wannan course din cikin lokaci."
Fawaaz ya dan juyo, ya kalle ta a gefe. "Kin san sai an yi kokari."
Ta gyada kai. "Ina kokari."
Ya dan lumshe ido na dakikoki biyu. Ta na kokari, amma shi fa?
Shima yana kokarin boye soyayyarsa?
Shiru ya sake cika motar, yayinda wakar da ke fitowa daga speakers take dada shiga zuciyarsu,
"For I can’t help… falling in love with you…"
Kamar wanda ya saba da hakan, Fawaaz ya daidaita mirror din motar, yana dan gyara gefen hularsa ta soja( beret/military cap). Nabeeha ta juyo da sauri tana kallonsa.
Idanuwanta sun tsaya cak a kan shi.
Ya kara kyau fiye da yadda ta zata. Wannan shigar tasa ta sojoji ta kara masa wani irin kamala da take jin zuciyarta tana tsalle idan ta kalle shi.
Sai dai, sai ta sunkuyar da kai cikin sauri. Bata son yayi tunanin wani abu daban.
Amma kuma, me zai yi idan ya gano?
Fawaaz bai kula da kallon da take masa ba. Bai san cewa yana kara burgeta da miskilancinsa ba. Abinda ya sani kawai shine, zuciyarsa na tafasa.
Yayi kokari ya cigaba da tukinsa, amma ya kasa.
A hankali ya sake rage gudun motar, zuciyarsa na bugawa da sauri.
Da alama yana makara.
Ya san cewa idan bai furta ba, zuciyarsa za ta iya fashewa.
Sai dai, me zai ce?
Fawaaz Dawud ya saba da jan aji. Amma yana iya cigaba da jan aji akan soyayya?
Nabeeha ta juyo tana kallonsa. Yana daure fuska, amma hakan bai hana shi kyau ba.
Ya san cewa idan ya ci gaba da yi shiru, soyayyar za ta yi nauyi fiye da yadda yake zato.
Da wannan tunanin, ya dan gyara murya.
"Ina fatan test din zai tafi daidai," ya ce, ba tare da ya kalle ta ba.
Nabeeha ta dan zaro ido da mamaki. Wannan shi ne karo na farko da Fawaaz yake nuna mata wata alama ta kulawa, ko da kuwa kadan ne.
Sai ta saki murmushi, zuciyarta na bugawa da sauri.
"Ina fata haka," ta amsa a hankali.
Fawaaz bai sake cewa komai ba. Bai san me zai ce ba.
Bai san ko yana da karfin fadin abinda zuciyarsa take fada ba.
Sai dai abu daya yana a fili.
Shi captain fawaaz yana son Dr. Nabeeha.
Kuma yana jin hakan yana yi masa nauyi fiye da yadda ya zata....
MX
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:30_
Motar na cigaba da tafiya a nutse, iskar dake fitowa daga A.C na motar na yawo cikin cikinta, yana ratsa jikinsu da sanyin da bai kai ya isa ya rage zafin da zuciyarsu ke ciki ba.
Fawaaz ya lumshe ido na wuni dakikoki kadan, sannan ya budesu, yana sauke numfashi a hankali.
Ya dade yana kokarin hana zuciyarsa bayyana soyayyar da take da ita. Ya dade yana kokarin boyewa, amma yanzu ya fara jin kamar yana makara.
Kamar dai yadda wakar da ke fitowa daga speakers take fada masa:
"Wise men say… only fools rush in… but I can’t help falling in love with you."
Ya dan matsa hannunsa a kan sitiyari, yana ji kamar yana jin zafin da zuciyarsa ke yi a fatar tafin hannunsa.
Nabeeha a daya bangaren, ta kara daidaita zamanta. Duk da sanyin dake cikin motar, tana jin wani irin dumin shauki yana ratsa zuciyarta.
Tana jin kamshin turarensa yana kara hadewa da sanyin da ke fitowa daga motar, yana sakata jin wani irin natsuwa mai dauke da tsananin shauki.
Sannu a hankali, zuciyarta na tafiya da wani irin salo da ta kasa fassarawa.
Ta dago a hankali, tana kallonsa daga gefe.
Ya kyau…
Sai dai ta sunkuyar da kai da sauri, zuciyarta na dokawa da sauri.
Meye haka, Nabeeha?
Sai dai a cikin zuciyarta, bata da amsar tambayar.
Fawaaz kuwa, sai ya cigaba da tukinsa, yana ji kamar zuciyarsa na kokarin doke duk wata ka’ida da ya gindayawa kansa.
A hankali, ya dan juyo yana kallonta. Ta bace cikin tunani, hakan ya bashi damar kare mata kallo.
Ya lura da yadda fuskarta ke da annuri, ko da yake idanuwanta cike suke da tunani.
Ya san cewa tana burgesa fiye da yadda ya zata.
Ya san cewa yana jin zuciyarsa tana tafasa a duk lokacin da yake kusa da ita.
Amma hakan ya isa ya furta mata?
Sai ya dauke kai, yana hadiye wani nauyin da yake ji a KIRJI.
Kai, Fawaaz! Ba dole sai ka fada ba!
Sai dai zuciyarsa na sake fada masa akasin haka.
Nabeeha a nata bangaren, ta kasa dauke zuciyarta daga kansa. Wannan shine karo na farko da take tafiya tare da shi, babu kowa sai su kadai, a cikin wannan yanayi na shiru mai cike da ma’ana.
Kuma yana kyau fiye da yadda ta zata.
Ta kalli hannayensa da ke rike da sitiyari. Me yasa suke burgeta haka?
Sai ta rufe ido, tana jin kamar tana kokarin kaucewa soyayyar da take ji.
Sai dai, shin yana yiwuwa?
Wakar dake fitowa daga motar ta sake mamaye zuciyarsu:
"Take my hand… take my whole life too… for I can’t help falling in love with you."
Fawaaz ya lumshe ido a hankali.
Nabeeha, me kike so na yi?
Ina jin ki. Ina jin ki fiye da yadda na zata. Amma ba zan iya furtawa ba.
Ya gyara zaman hularsa ta soja (Beret/Military cap), yana jin yadda soyayyar ke kara cika zuciyarsa da nauyi.
Nabeeha ta dago da sauri, tana kallon sa.
Shigarsa ta kara burgeta fiye da yadda take zato.
Ba ta san lokacin da murmushi ya subuce mata ba.
Fawaaz kuwa, ya lura da murmushin, amma sai ya dauke kai.
Idan ya ci gaba da kallo, zai iya furta abin da zuciyarsa take fada.
Sai dai a zuciyarsa, yana jin kamar yana makara.
Yana makara kafin soyayyarsa ta fishe shi, har ta gagara ɓoyuwa.
Fawaaz ya kafe idanunsa a kan titin da ke gabansa, hannayensa na riƙe da sitiyari da cikakken iko. Motar na tafiya cikin nutsuwa, iska na tashi daga A.C, tana ratsa su da sanyin da bai iya kashe wutar zuciyarsu ba..
Yana sanye da kayan sojoji—khaki mai kyau da tsari, da hular soja (beret) da ya gyara a gefen kansa. Dogon hannun rigarsa ya bayyana ƙwarewa da ƙa’ida irin ta sojoji, lambar sunansa ta manne a gefen ƙirjinsa.
Nabeeha ta ji zuciyarta ta buga da sauri da ta sake kallonsa. Yana da kyau sosai a haka…
Amma hakan bai dame shi ba.
Yana tukinsa cikin shiru, fuska a daure kamar yadda ya saba. Sai dai ta lura da yadda jaw-line dinsa ke motsi—alamar yana taƙure wani abu da bai so ya bayyana ba.
Shiru ya fi magana sau dubu.
Sai dai ita kanta tana cikin tunani. Ba ta san me yasa zuciyarta ke dukan wata irin guda ba.
Ba ta son ya fahimta.
Sai dai, shin yana yiwuwa ya riga ya fahimta?
Wakar da ke tashi a hankali daga motar (Slow Love Song) ta cika zuciyarta da wani irin nutsuwa mai sanyi, amma da sauƙin da ke ɗauke da nauyi..
"I don’t wanna say goodbye…
Even when the night is over…
I just wanna hold you close…
Even if we’re lost forever…"
Ta dan lumshe idanu a hankali.
Tana jin shaukinsa na ratsa ta.
Hankalinsa na kan titi, amma zuciyarsa na wani wuri daban. Wurin da aka kulle shi da soyayyar da ba zai iya furta wa ba.
Fawaaz ya gyara zamansa a kujerar direba, yana matsa yatsunsa a kan sitiyari. Numfashinsa na fita a hankali, amma zuciyarsa na tafasa.
A gefensa, Nabeeha ta sake gyara zaman mayafinta, tana ƙoƙarin kwantar da zuciyarta. Sai dai hakan ya gagara.
Kafin ta fito daga gida, ta yanke shawarar cewa ba za ta sake kallonsa da wani irin kallo ba. Ba za ta bari zuciyarta ta bayyana abin da take ji ba.
Amma yanzu…
Yana da kyau…
Yadda kayan sojoji suka zauna masa daidai, sun bayyana cikakken ƙuruciya da ƙwarewarsa. Beret ɗinsa na gefen kansa, yana ƙara masa kwarjini. Idanunsa kuwa, ko da bai kalleta kai tsaye ba, akwai wani irin zurfi da take ji idan ta kalle su.
Zuciyarta ta ja da baya da sauri.
Wani sanyi ne ya ratsa ta lokacin da ta sake jin wakar da ke tashi a hankali daga speakers ɗin motar.
"I will always, always love you…"
Wata irin zufa ta keto mata a goshinta.
Ta san cewa ba kawai kalmomin waka ba ne ke ratsa ta.
Soyayyar da take jin yana ɓoye wa ne ke ratsata.
Fawaaz ya juyo da dan kallo, a hankali. Bai yi magana ba, amma idanunsa sun fada mata duk abin da bakinsa ya gaza furtawa.
Ta yi saurin dauke kai.
Zuciyarta na tsalle tamkar za ta fito waje.
Me yasa ba zai yi magana ba?
Me yasa ba zai furta abin da yake ji ba?
Ya jima da sanin cewa soyayyarta ta mamaye shi.
Ya jima da sanin cewa yana cikin matsala idan bai gaggauta daukar mataki ba.
Sai dai… yana jin tsoron furta hakan.
Hannunsa na dama ya dan dunkule sama da sitiyari, yana jin wani irin nauyi a KIRJI.
Fawaaz, kai soja ne.
Kai namiji ne.
Amma kuma me yasa soyayyarta ke galaba da kai?
Sai ya sake kallonta da gefen ido.
Sai dai ta kau da kanta, kamar yadda shima yake ƙoƙarin kau da zuciyarsa daga shaukinta.
Zuciyarta ta furta abu guda.
Duk da shiru ya yi yawa, zuciyoyinsu sun san gaskiya.
A haka ya karasar da ita zuwa inda zasuyi aikin... Ya jirata har suka kammala sannan ya dakkota suka koma hanyar gidah..
Motar