KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   40 / 40

117K to 119.4K   out of 119.4K words

same ta tana zaune a falo, tana kallon cikin ta da murmushi.

Ya durkusa a gabanta, ya dafa cikinta da tafin hannunsa. "Yaya babyna?"

Ta kalle shi tana murmushi. "Babynka yana cikin kwanciyar hankali. Yana jin sanyin addu’o’inka."

Ya lumshe ido, yana fadin: "Allah ya sauke ki lafiya, Nabeeha. Allah ya ba mu ikon tarbiyyar wannan yaron daidai da yadda zai zama mai amfani a duniya."

Ta furta cikin radadi da kauna: "Ameen, Fawaaz. Allah ya kara mana soyayya."

Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta a kirjinsa. "Soyayyarmu ba zata taba raguwa ba, Nabeeha. Sai dai ta kara girma har abada!"

Haka rayuwarsu ta ci gaba, cikin kulawa, addu’a, da soyayya ta gaskiya..

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*
_(Completed)_


*_PAGE:65_*
_(shafin karshe/The end/Episode Finale)✅_


______
A daren ranar, duhun dare ya lullube garin, amma zuciyar Fawaaz tana cike da fargaba da fatan alheri. A cikin asibiti yake zaune, hannunsa rike da na Nabeeha, wanda ke jin radadin nakuda. Idanunta sun lumshe, hawaye na sauka daga gefen kumatunta, amma har yanzu murmushi yana manne a fuskarta.

"Ya fawaaz…" ta kirasa cikin wata murya mai rauni.

Ya matsa kusa da ita, yana share mata gumi. "Nabeeha, ina nan. Ki kasance da ƙarfin zuciya. Kiyi haƙuri, kin kusa samun nasara."

Idanunta suka cika da soyayya, ta furta cikin rauni,

"Na gode… na gode da ka kasance tare da ni a koda yaushe. Ba zan iya misalta irin kaunar da nake maka ba."

Hannunsa ya kara damke nata, yana girgiza kai. "Kada ki ce haka, Nabeeha. Ina tare da ke har abada. Allah ya sa wannan ranar ta zama mafi albarka a rayuwarmu."

A wannan lokacin, likitoci suka bukaci Fawaaz ya fita domin su ci gaba da taimaka wa Nabeeha wajen haihuwa. Ya kasa matsawa daga kusa da ita, sai da aka lallashe shi sosai sannan ya yarda ya fita.

Bai daina addu’a ba. Bai daina salati ba. Bai daina rokon Allah da zuciya daya ba.

"Ya Allah! Ka sauke ta lafiya. Ka ba mu wannan jaririn cikin sauki. Ka raya mana shi cikin shiriya da albarka. Ya Allah, kada ka jarabceni da rashin Nabeeha. Ita ce numfashina."

Lokaci yana tafiya, amma a cikin zuciyar Fawaaz kamar shekaru ne ke wucewa. Har sai da wata karamar nurse ta fito tana murmushi.

"Captain Fawaaz?"

Ya mike da sauri. "Na’am! Yaya matata take?"

"Alhamdulillah! Allah Ya albarkace ku da ɗa namiji. Matarka ta sauka lafiya, kuma danta yana cikin koshin lafiya."

Duk wani nauyi da ke kan zuciyar Fawaaz ya dauke a take. Idanunsa suka cicciko da hawaye, amma wannan ba hawaye ne na damuwa ba, sai na tsantsar farin ciki. Ya durkusa a kan guiwowinsa, ya dora goshinsa a ƙasa, yana sujjadar godiya.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah ya Rabb! Na gode maka, Ya Allah!"

Bayan ya gama addu’a, ya mike da sauri, yana bin nurse ɗin da take jagoranta zuwa dakin da Nabeeha take.

A lokacin da ya shiga dakin, ya tsaya yana kallonta. Nabeeha na kwance da ƙarfinta ya rage, amma duk da haka akwai murmushi a fuskarta. A gefenta ne aka ajiye jaririn da ta haifa, an nade shi cikin fararen kaya..

Hankalinsa ya fara tafiya kan Nabeeha. Ya zauna kusa da ita..

Fawaaz ya zauna a gefen gadon, zuciyarsa tana cike da tsananin kauna da godiya. Ya shafi gashinta da kulawa, yana kallonta da idanunsa masu cike da shauƙi.

"Nabeeha…" ya kira sunanta da murya mai rauni.

Ta bude idanunta a hankali, tana kallonsa da murmushi. Duk da gajiyar da ta sha, hakan bai hana hasken farin ciki bayyana a fuskarta ba.

"Ya Fawaaz… mun samu ɗa." Ta furta a hankali, hawaye masu ɗumi suna gangarowa daga idanunta.

Ya girgiza kai, yana share mata hawayen da yatsunsa. "Nabeeha, kin zama tauraruwa a rayuwata. Kin cika min burina. Na rasa yadda zan misalta irin godiyar da nake miki. Na gode da kika kawo min wannan baiwa daga Allah."

A hankali ya kama hannunta, ya rike da karfi. "Na sha alwashin kare ki da shi da dukkan rayuwata. Ba zan taba bari ku shiga cikin wata wahala ba, Nabeeha. Ke da wannan jaririn duk abin da nake da shi a duniya."

Ta kalli jaririn da ke gefenta, zuciyarta cike da tsantsar soyayya. "Ya Fawaaz, ka ɗauke shi."

Fawaaz ya tsaya na wani lokaci, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Wannan ne karon farko da zai ɗauki dansa a hannunsa. Ya matsa kusa, yana mika hannayensa da nutsuwa. Yana ji kamar idan ya ɗauke shi, zai ji wani yanayi na daban da bai taba jin irinsa ba.

A hankali ya ɗauki jaririn, yana jin sa a hannunsa da sanyin fatar jikinsa. Yaron ya motsa kadan, sannan ya yi wani ƙaramin gyatsa. Fawaaz ya kasa tsayawa da murmushi, yana jin wani irin farin ciki da bai taba ji ba. Kamar su daya da fawaaz din sak..sai dai idanuwan sa na Nabeeha ne da sumar kansa ta fulanin usul.

Ya rungume shi a kirjinsa, yana lumshe ido.

"Muhammad Dawud…" ya furta da murya mai rauni. "Sunan mahaifina zan saka masa, domin ya zama jarumi irin sa."

Nabeeha ta dube shi da murmushi, ta gyada kai. "Sunan ya dace da shi. Allah ya albarkace shi, ya tsare rayuwarsa."

Fawaaz ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da soyayya. "Ya Allah! Na gode maka da wannan baiwa. Ka sanya shi cikin shiriya, ka ba shi rayuwa mai albarka da tsawon kwana. Ka sa ya zama mai amfani ga addini da al’umma."

Ya dawo da kallonsa kan Nabeeha, yana matseta a jikinsa tare da jaririn. "Daga yau, soyayyata gare ki ta kara ninka fiye da yadda take. Na fi kaunarki fiye da yadda zan iya furta wa."

Ta lumshe ido, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da kwanciyar hankali. "Na gode, Ya Fawaaz. Allah ya kara mana soyayya da fahimta."

Nan da nan dama surprise (bazata) sukeso suyiwa dangi. Sai dai kawai aji haihuwar ta..nan da nan fawaaz ya fara Kiran dangin nasu a waya.

Asibitin ya cika da dangi anata farin ciki. Likitan ya tattara ya sallame su yace su koma gidah.

Ranar suna kuwa. Anyi suna hamshaki na masu farcinan susa. Babu ce kawai baa ci ba a sunan nan. Nabeeha ta koma gidan gwaggo Hafsatu bisaga jagorancin gwaggon da hukuncin data zarce...

A wannan yanayi, rayuwar su ta canza gaba ɗaya. Sabuwar soyayya, sabuwar rayuwa, sabuwar nasara. Kuma daga nan ne suka fara renon jaririnsu cikin kulawa da kauna..

Bayan dawowar su gida, rayuwar Fawaaz da Nabeeha ta cika da farin ciki da sabuwar soyayya. Duk da cewa su biyun sun saba da juna tun farko, hakan bai hana sabon salo na kauna shiga tsakaninsu ba. Yanzu Nabeeha ta zama mahaifiya, kuma hakan ya kara wa Fawaaz ƙaunarta fiye da tunaninta.

A kullum yana lallaba Muhammad Dawud, amma duk da haka yana da wata ‘yar kishi da ke ƙunshe cikin zolaya. Yana ganin kamar Nabeeha ta fi son danta fiye da shi.

Wata rana yana zaune a gefen gado, yana kallonta yayin da take shayar da ɗan su. Ya rangwada a gefenta, yana me ƙifta ido.

"Nabeeha?" ya kira sunanta da wata murya mai laushi.

Ta ɗago, tana kallonsa da murmushi. "Na’am, My Captain?"

Ya gyara zamansa, ya shagwabe fuska kamar yaro. "Kin daina sona, ko?"

Ta zabura, ta girgiza kai. "Subhanallah! What? Me yasa kake cewa haka?"

Ya nuna yaron da ke kwance a jikinta. "Tun da wannan yaron ya shigo duniya, kin daina kulawa da ni. Ko kallona ma ba kya yi da kyau."

Ta fashe da dariya, ta ɗora hannunta a ƙirjinsa. "To ai wannan yaron naka ne. Ya kamata ka ji dadin yadda nake kulawa da shi."

Ya sake matsawa kusa, yana matse rikon hannunta. "Ban ce bana jin dadi ba. Amma ki tuna, ni ne farkon soyayyarki."

Ta kwantar da kanta a kafadarsa, tana me murmushi. "Fawaaz, kai ne ginshikin rayuwata. Kauna ta gare ka ba zata taba raguwa ba. Shi Muhammad Dawud jinina ne, amma kai ruhina ne."

Ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin soyayyarta. "Na gode, Nabeeha. Har abada zan ci gaba da ƙaunarki fiye da komai a duniya."

A haka suka cigaba da rayuwa, cike da soyayya da ƙaunar juna. Duk da su biyun ba masu yawan magana bane, amma sukan fahimci juna ta hanyar kallon ido da kallon zuciya.

A wani dare, Fawaaz yana zaune a cikin bedroom, Nabeeha na kwance a jikinsa. A lokacin Muhammad Dawud yana barci a gadon sa. Wurin yayi tsit, sai saukar numfashin su kadai ake ji.

Sai da yayi shiru na wani lokaci sannan ya kamo hannunta, yana murza yatsunta a hankali.

"Kin san wani abu?" ya tambaye ta cikin wata murya mai nauyi.

Ta kalle shi, tana murmushi. "Me kenan?"

Ya dora hannunsa akan ƙirjin sa, ya rufe idanunsa. "Na sake tabbarwa da KIRJI ba MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA ne"

Ta ƙura masa ido, tana jiran cikakken bayani.

Ya ɗora hannunta a kan zuciyarsa. "AKWATIN SIRRIN na yana nan, a cikin zuciyata. Amma kin san waye SIRRIN? Ke ce. Ke ce SIRRINa, ke ce rayuwata, ke ce duk wani abu da nake da shi."

Ta lumshe ido, tana jin nauyin maganarsa yana shiga cikin zuciyarta.

"The vault of your secret...."

"The vault of his secret indeed... Amma kawai ina so ki sani, Nabeeha. Ko da waye zan kasance a duniya, ko da menene zan samu, har abada, ke ce AKWATIN SIRRINa."

A wannan dare, Fawaaz ya lumshe idanunsa, yana jin wani irin natsuwa da bai taba ji ba. Duk da yawan shekarun da suka shafe tare, soyayyarsa ga Nabeeha tana karuwa ne maimakon raguwa. Yana kallonta a kusa da shi, idanunta sun lumshe cikin barcin gajiya, amma fuskarta na bayyana nutsuwa da kwanciyar hankali.

Ya dan rankwafa, yana shafar gashinta a HANKALI. "Ke ce AKWATIN SIRRINa," ya sake nanatawa a kasan makoshinsa, yana jin nauyin soyayyar da take cike da zuciyarsa.

Sai da ya dan tsaya na wani lokaci, yana jin numfashinta yana tashi da sauka a hankali, sannan ya dora tafin hannunsa a saman cikinta da har yanzu bai gama komawa daidai ba bayan haihuwa.

"Kin ci gaba da bani darasi, Nabeeha," ya fada murya a raunane. "A baya na dauka cewa zuciya ce ke dauke da SIRRIN mutum, sai daga baya na fahimci cewa HANKALI shi ne ginshikin komai. Amma yanzu, na kara fahimta cewa akwai wani abu da ya fi duka. Wurin da SIRRIN mutum ke boye, ba a zuciya yake ba, ba a HANKALI yake ba. AKWATIN SIRRIN mai HANKALI yana hannun wanda ya cancanta."

Ya kalleta, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da matsananciyar kauna. "Kuma ke ce kikafi cancanta, Nabeeha. Kin rike SIRRINa, kin rike zuciyata, kin rike rayuwata. Ke ce mace daya tilo da zan iya mika dukkan amana ta gare ta."

A hankali ta bude idanunta, kamar wadda ta jima tana jin maganarsa a mafarki. Sai ta dan turo baki, tana murmushi. "To sai me?"

Ya yi dariya, yana dora goshinsa a nata. "Sai dai in ci gaba da nuna miki cewa bazan taba sauya tunani ba. Ke ce SIRRINa, kuma har abada, ke ce AKWATIN SIRRINa."

Ta lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da nishadi. "Kuma kai ne komai nawa, Fawaaz. Ba zan taba iya rayuwa babu kai ba."

Ya kama hannunta, yana dora mata kiss a bayansa. "Ko bayan rayuwa ma, soyayyata gare ki zata ci gaba da wanzuwa. Zuciyata ta kasance taki ce har abada, Nabeeha."

Duk da maganar tana da nauyi, sai da ta yi murmushi. "Ka fiye soyayya, Captain. Yanzu dai ka barni in ci gaba da barci, saboda Muhammad Dawud na iya farkawa da dare."

Ya jinjina kai, yana sake kwantar da ita. "To Allah ya sa mafarkin ki na da dadi."

"Amin."

A hankali ya rufe idanunsa, yana rungume ta da kwanciyar HANKALI. Cikin zuciyarsa, yana jin wani irin nutsuwa da bazai iya misaltawa ba.

HANKALI ya kasance cikin KIRJI, amma SIRRI yana da nasa mazauni. Kuma a karshe, Fawaaz ya fahimci cewa ba KIRJI bane ke dauke da SIRRIN MAI HANKALI, ba HANKALI bane ake ajiye shi. SIRRIN mai hankali yana hannun wanda aka mallaka masa zuciya da rayuwa gaba daya. Kuma gareshi, wannan mutum daya tilo ce, Wato...Nabeeha uzair Muhammad..Mrs Fawaaz dawud mafia..

Ta rungume shi da ƙarfi, tana jin tsantsar soyayyarsa yana ratsa zuciyarta. "Kauna ta gare ka ba zata taba gushewa ba, Ya Fawaaz dina." A haka bacci mai nauyi ya dauke su...

A wannan dare, soyayyarsu ta cika, zuciyoyinsu sun hadu, kuma SIRRIN su ya ƙare cikin ƙauna da aminci.



°°°°°
_Alhamdulillah! Duk da gajiyar tafiya, da ƙalubalen rubutu, da neman kyakkyawar mafita ga labari, a yau na kammala littafin KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA) gaba ɗaya._

_Na fara wannan tafiya da zuciya cike da burin bayar da labari mai ma’ana—wanda zai ƙunshi soyayya, sirri, hakuri, da yarda da kaddara. A ƙarshe, labarin ya zama fiye da haka. Ya zama tafiya ta soyayya da ƙaddara. Tafiya ta sirri da amana. Tafiya ta mutum da zuciyarsa, da wanda ya cancanci ya zama Akwatin Sirrinsa._

_Ina roƙon Allah Ya sa albarka a cikin wannan aiki, Ya yafe mun da ku duk wani kuskure da na rubuta, Ya kuma saka lada ga duk wanda ya karanta da niyyar neman nishaɗi ko darasi._

_Dukkan halaye da aiyuka na kyawawan jaruman wannan littafi ina fatan su zama abin koyi. Kuma kuskuren da suka aikata ya zama izina gare mu. Ina rokon Allah Ya gafarta mana, Ya sa mu zama cikin waɗanda suke koyi da alheri, su kauce wa sharri._

_Na gode da soyayya, goyon baya, da addu’o'in da aka yi mun a wannan tafiya. Sai littafi (zafafa paid books) na gaba, idan Mai Duka Ya kai mu!_

_Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_ _Alhamdulillah!_

_wannan littafi na kudi ne, wato daya daga cikin jerin littattafan zafafa biyar... Nera dari biyar N500 ne ga duk mai son mallakar sa.... Domin karin bayani sai a tuntubeni ta 09134848107_


_Taku: Nana hafsatu... (Mss xoxo)_

40 / 40