dawo dasu ko yayan su idan yana gari. Eh su uku ne. Ita Zaytunah, sai Nabeeha. Sai Hammad. Hammad din shi bama anan yake karatu ba a oversea ne. Eh tabbas, muna tunanin yiwuwar an yi garkuwa da su."
A ɗaya ɓangaren, Brigadier General Mukhtar ya farka gaba ɗaya. Jin labarin ban mamaki da tu'ajjabi..
"Ranka ya daɗe! Za mu fara aiki nan take! Ko akwai wani bayani na ƙarin haske?"
Major General ya runtse idanuwansa yana kokarin dakile wani abu dake kokarin taso masa daga ciki mai zafi,
"No, Muna jiran su nema su zo nan asibitin alfirdaus specialist dinnan na outskirt of cikin gari dinnan.amma tun ɗazun ba su iso ba. Duk wayoyin su a kashe, Kaga kuwa. Wannan ba karamun abu bane, akwai wani abun a kasa"
"Mun fahimta! Bari mu tara jami’anmu don a fara bincike nan take!"
"Godia nake..." Ya katse wayar bayan sunyi sallama..
"Inshaa Allah yanzu zasu fara aiki Gwaggo... Yana ma duba jikin ki kafin ya iso yace"
"Toh Allah yasa mu dache... Ina amsawa nagode kwarai"
Major general baiyi kasa a gwiwa ba. Ya sake danno kiran wani yaron sa, Bayan sun gaysa ne yake tambayar yaron inda yake,
"Ina barracks yallabai!"
"Inaso ka jagoranci bincike kan motar number motar nan da zan turo maka, Daga nan ka yi coordination da Intelligence Unit don mu gano inda aka kwashe su."
"Za a fara aiki nan take, ranka ya daɗe!"
Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya. Amma har yanzu, zuciyarsa na bugawa da tsanani. Ya juya ga Gwaggo Hafsatu da Hajiya Hauwa Maijidda.
"Inshaa Allah, Duk yadda za a yi, sai mun gano inda suke..Allah ya shige mana gaba yasa mu dache Amin"
"Toh Allah ya amince"
"Aameen" suka amsa baki daya...
Ranar dai a dole likitan ya sallame su. Don gwaggo Hafsatu ta matsa kan ba zata kwana a asibitin nan ba. HANKALIn ta baya jikin ta. Nutsuwar ta da kwanciyar hankalin ta baki daya ya tattara ne awajen su hajia zaytunahh na rashin sanin takamaimai halin da suke ciki..
Hankalin Major General ya ƙara tashi fiye da yadda zai iya bayyanawa. Bai taɓa jin zuciyarsa ta yi nauyi haka ba. Hannunsa ya fara gumi, ya sake duba wayarsa. Bai san sanda ya miƙe tsaye da sauri ba. Ganin lokaci ya sake zartawa.. Amman ba wani labari daga dukkanin wadanda ya saka aikin bincike...
Gwaggo Hafsatu ta dubi dan nata, idanuwanta cike da tsoro.
"Dawuda, ka ce wani abu! Ka ce ba wata matsala!"
Hajiya Hauwa Maijidda ta dan matsa kusa da shi.
"Kayi shiru! Me ke faruwa?"
Muryarsa ta ɗauka da ƙarfi. Bai masan ya furta,
"Wannan abu ba daidai bane! Ba abu ne na hatsari ba. Ba daidai bane gaba ɗaya!"
hajiya Hauwa Maijidda ta ɗaga wayarta da sauri, tana sake ƙoƙarin kiran Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad. Amma duk wayoyin a kashe suke.
"Subhanallah!" Ta furta, jikinta na rawa.
Major General Dawud ya haɗa fuska, ya danna wata lamba a wayarsa. Cikin daƙiƙa biyu kacal aka ɗauka.
"Captain!" Ya kira da kakkausar murya.
"Na’am, ranka ya daɗe!"
"A gaggauce ka bi sawun brid. Gen. Mukhtar, Ka temaka musu ku tsananta binciken nan da gaggawa"
"Ina nan a kan hakan, ranka ya daɗe."
Ya kashe wayar batare da wata magana ba.
Gwaggo Hafsatu tasake fashewa da kuka. Wannan karon muryarta har wani rawa takeyi,
"Dawuda, ka taimake ni! Kar dai wani abu ya same su!"
Zuciyar Major General tana bugawa, amma ya daure kansa. Ya kalli mahaifiyar sa, gwaggo Hafsatu cikin muryar ban tausayi da rarrashi yace,
"Inshaa Allahu zasu kubuta, Za'a ceto su gwaggo, Zaa gansu. Ki bar zubar da hawayen ki dan Allah.."
Major General ya rufe idanuwansa na wasu dakiku, yana shakar iska mai nauyi.
Nan take ya ɗauki waya, ya kira Control Room na sojoji.
"Ina so a fara bincike! A duba ko an samu wani rahoto na motar da ta bar gida tun dazun!"
A ɗaya ɓangaren, wani yaron sa ya kira shi.
"Tracking ɗin motar yana nuna an bar hanya mai tsaro. Motar ta shiga cikin wani yanki da ba a saba wucewa da ita ba!"
Kamar an caka wa Major General ƙwalla da wuka, haka zuciyarsa ta ji.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!"
Ya dafe goshinsa, hannunsa na rawa.
Gwaggo Hafsatu ta kama rigarsa.
"Ka ce ba a sace su ba, Dawuda! Kar dai yan fashi ne!"
Zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Bai iya cewa komai ba. Amma zuciyarsa na jin 'An sace su!'
Ya dan kakaro murmushin kwantar da gwaggon HANKALI yace,
"No akan na'urar aiki ne ta katse. Inshaa Allah komai zai daidaita Gwaggo..ki kwantar da HANKALIn ki"
🎀🎀🎀
Duk da an jima ana tafiya, babu wata gajiyar da Fawaaz ke ji. HANKALIn sa gaba ɗaya yana kan abu ɗaya wato Nabeehan sa...
Tunda suka fara tafiya daga base, tunaninsa ya kasa barin fuskar Nabeeha, Yanayin tsarin halittar jikin ta, sanyayyar muryarta, Kai komai nata ma, Yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa da soyayyarta, yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da son ya ganta a zahiri, ya fuskance ta, ya faɗa mata abin da ke ransa.
Ya gama yanke hukunci, yau ba zai kwanta ba tare da ya fuskance ta ba. Duk da miskilancinsa da kamun kansa, ya yanke shawarar faɗa mata gaskiyar zuciyarsa. 😂
Sai ga direban nasa yana sanar da shi,
"Yallaɓai, yanzu zamu hau babban titi har cikin gari"
Yana shirin bayar da umarni, sai wayarsa ta fara ringing. Mahaifinsa ne. Wato, Major General Dawud.
Nan take bugun zuciyarsa ya sauya. Ya duba fuskar wayar, yana jin kamar numfashinsa na ɗaukewa, Mahaifinsa ba mutum ne mai yawan kiran sa ba, sai dai idan da wani lamari mai muhimmanci.
Ya ɗaga wayar da sauri.
"Morning sir! Barka da war haka Baba!"
Muryar mahaifinsa ta fito da ƙarfi da girmamawa, amma kuma da wani yanayi na tashin hankali da bai saba jin sa da shi ba.
"Fawaaz! Ba lokaci, muna da matsala! An sace su Hajiya Zaytunah, Nabeeha da Hammad!"
Zuciyarsa ta tsaya cak. Duk duniya tamkar ta tsaya cak a kunnensa.
"M... menene?"
"An sace su akan hanyar zuwa asibiti! Gwaggo an kwantar da ita as of then , su kuma an sace su! Duk wayoyinsu a kashe! Babu wanda ya san inda suke!"
A wani lokaci dabam, Fawaaz zai iya sarrafa kansa, amma yanzu zuciyarsa ta gama harbawa da tashin hankali! Ya ji wani sanyi yana ratsashi daga ƙasa har sama. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi.
"Nabeeha..." ya furta a hankali, yana jin yadda wani abu mai tsananin zafi ke ciwo a KIRJIN sa.
Tunanin cewa Nabeeha tana hannun wasu mutane ya kusa gigita shi. Ita da ke ransa da zuciyarsa, ita da yake shirin faɗa wa gaskiyar zuciyarsa, ita ce aka sace?
"Kana jina kuwa, Fawaaz?!" Mahaifinsa ya ɗaka masa tsawa.
Ya rufe idanunsa, yana kokarin daidaita numfashinsa. Ya sanya hannunsa yana dafe kansa.
"Sorry sir. Yes sir! I'm all ears..Ina sauraron ka... gashinan zan dawo gidan yanzu! Babu wanda zai kwana ba tare da an san inda suke ba inshaa Allah !"
Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya.
"Godiya nake, Fawaaz. Mun baza jami’an bincike, amma kana da ilimi da kwarewa wajen gano abubuwa. Sauran jami’ai na kan aikinsu, amma ina bukatar ka waiwayo gidah yanzu don taimakawa wajen gano su."
Fawaaz ya sunkuyar da kansa, yana jin yadda zuciyarsa ke ƙuna da damuwa.
"Inshaa Allah baba...." Major general ya katse wayar..
Cikin muryar sa mai cike da damuwa yace da direban,
"Kara gudu ! Please... I beg you!"
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:4_
Gaba daya tunda Captain Fawaaz Dawud ya karɓi kiran mahaifinsa, Major General Dawud, hankalinsa ya yi matuƙar tashi, amma a zahiri ba a iya karanta komai a fuskarsa. Yana daga cikin mota tare da direbansa lokacin da kiran ya shigo. Duk da cewa tunaninsa yana kan Nabeeh.. masoyiyar da bai furtawa kalaman yana kaunarta ba a zahiri. Sai gashi labari mafi muni ya riskesa alokacin daya gama tsarawa zuciyarsa da labbansa yanayin yarda zai furta mata komai na kaunar da yake mata. Mummunan labarin an sace su ya doki kofofin kunnuwan sa..
“An sace su Hajiya Zaytunah akan hanyar su ta zuwa asibiti duba gwaggo,” Ya tuno mahaifinsa ya sanar da shi da kakkausar murya...
Fawaaz ya ɗauki sakanni kaɗan yana nazari, ba tare da wata hayaniya ko wata alama ta firgici ba.
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Gabansa na tsananta bugawa, Ahankali ya zura hannu ya zare katin kuɗi mai nauyi daga aljihunsa, ya miƙawa direban nasa, sannan ya ce,
“gashi ba yawa, ka tafi gida ka huta, Na gode.”
Direban ya ji mamakin yadda Fawaaz bai nuna wata damuwa ko firgici ba. Lalle wannan shi ne Captain Fawaaz Dawud Mafia. Soja mai cikakken ikon sarrafa kansa... Direban ya sauka ahankali yana yana sake yiwa captain fawaaz godia. Idanuwansa sun cika da ruwan hawayen kyautar kudi masu yawa da fawaaz din ya masa,
"Nagode ranka ya dade. Allah ya saka maka da alkhairi. Ya yi riko da hannuwan ka. Allah kuma ya shiga cikin lamuran ku Kai da zuriyar ka. Ya kawo karshen dukkanin matsaloli"
"Aameen, Ni ne da godiya" captain fawaaz, Bai jira komai ba, ya shiga cikin motarsa ya ja da gudun wuce kima, har sai da tayoyin suka yi ƙara akan titin. Hannunsa yana kan sitiyari, idonsa yana kan hanyar da ke gabansa, amma zuciyarsa tana can waje guda kawai.,
Nabeeha.
Sai yanzu ya fahimci cewa damuwar da yake ciki ba saboda kowane mutum ba ne sai ita. Duk da kasancewarsa mutum mai natsuwa da miskilanci, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi saboda ita.
Amma ba lokacin tunani ba ne. Yanzu aiki ya rage masa.
Yana tafe yana amfani da na’urorin binciken sojoji na zamani, yana tuntuɓar abokan aikinsa ta SIRRI. A matsayin soja, ya san hanyoyin gano mafakar masu aikata laifi, kuma ya san yadda ake bibiyar mutum ta hanyoyin zamani.
Yana tuki da gudu fiye da kima, yana kauce wa motocin da ke kan titin, yana kwana cikin gaggawa. Da wani irin zafi yake tuƙi, tamkar idan har ba zai isa ba nan take, zai iya karya ƙa'idojin duniya gaba ɗaya don kawai ya isa.
Wani lokaci ne da bai taba jin kansa a haka ba cikin tsananin gaggawa da tsoro mai yawa.
"Waye ya sace su? Me suke nufi? Me yasa?!"
A yanzu, babu wani abu a duniyarsa da ya fi muhimmanci fiye da gano inda Nabeeha take.
A zuciyarsa, yana jin wani sabon irin fushi da ba kasafai yake jin sa ba. Idan har wani ne ya kuskura ya cutar da ita... to wannan zai kasance babban kuskuren rayuwarsa.
Fawaaz ya cigaba da tuƙi da gudun tsiya, tamkar zai tarwatse da zuciya. Bai damu da harbin hanyoyi ko ƙa'idojin hanya ba, burinsa guda ɗaya ne isa gida cikin gaggawa!
A lokacin da ya kusa isa, ya hango daya daga cikin masu gadin gidan yana buɗe babbar ƙofar shiga. Wani saurin fakin ya yi, motar na kusan sulalewa ta tsaya cak! Bai ko kashe injin ba, ya fice da matuƙar sauri.
Da sauri da gudu gudu yana shigewa cikin gida da hanzari. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
Yana shiga cikin babban falo, ya hango mahaifinsa, Major General Dawud, tsaye cikin damuwa, yana waya da wasu mutane. A gefe kuma Gwaggo Hafsatu zaune, hannayenta a dage a sama, kamar tana addu’a. Damuwa ta bayyana a fuskarta,
"Baba! Sir! " Fawaaz ya furta, zuciyarsa na harbawa.
Major General Dawud ya waiwaya da sauri, idanunsa sun nuna yawan tunani da damuwa.
"Fawaaz, an sace su! An sace su akan hanyar zuwa asibiti!"
"Subhan'Allah!" Fawaaz ya kusan faɗuwa saboda girgiza da tashin hankali. "Who did this?! Waye yayi haka?!"
Gwaggo Hafsatu ta dago idanunta da suka cika da hawaye. "Ya Allah, ka tsare su! Ka kubutar da su cikin aminci!"
Major General Dawud ya ajiye wayarsa, yana jan numfashi.
"Ba mu san su waye ba, amma tun dazun muna kokarin bincike. Har yanzu babu wani sahihin labari daga jami'an tsaro."
Fawaaz ya runtse idanunsa da ƙarfi, numfashinsa yana ƙara nauyi.
"Father... Su Nabeeha fa? Ta ina suka tafi da su?"
Major General ya gyara tsayuwarsa, yana daidaita muryarsa da ƙyar. "Bamu san inda aka tafi da su ba, amma mun tabbatar an sace su a kan hanyar zuwa asibiti. Mun kira wayoyinsu, duk a kashe."
Fawaaz ya dafe kansa, yana jin ƙarar zuciyarsa na bugawa kamar zata faso kirjinsa ta fito.
"Ba zai yuwu ba! Oh no no no no..!"
Ya juya da sauri, yana lalubo wayarsa. "Ba za su iya ɓacewa haka kawai ba! Dole akwai mafita!"
Fawaaz ya riƙe wayarsa da ƙarfi, numfashinsa yana saurin hawa da sauka kamar wanda ya yi gudun fanfalaki. Tashin hankali ya cika zuciyarsa, tunaninsa ya rabu biyu, Ina Nabeeha? Me ke faruwa da ita a wannan lokacin? An sace su a yanayin da yake matukar bukatar ta don sanar mata labarin zuciyar sa..
Ya sa hannu ya share gumin da ya taru a goshinsa, ya danna lambar wasu daga cikin ma'aikatan sa domin tabbatar da wani abu, amma babu wanda ya ɗaga.
"Damn it!" Ya furta, yana jan numfashi mai nauyi.
Major General Dawud yana tsaye kusa da shi, hannunsa cikin aljihun wandonsa, fuskarsa cike da kaffara da damuwa.
"Fawaaz, ka kwantar da hankalinka." Muryarsa ta fito da nutsuwa mai cike da umarni.
Fawaaz ya juyo da sauri, idanunsa sun kada kamar wutar lantarki.
"Baba, Ta yaya zan iya wani kwantar da hankalina? Nabeeha na hannun wasu mutane da bamu san ko su wanene ba! Wannan ba lokaci bane na nutsuwa!" Fawaaz ya fada acikin zuciyar sa..
"Allah ka kubutar da Nabeeha" ya fada batare da yasan subatar bakin da yayi ba.
Major general ya lura dashi yana dan bubbuga kafadar sa yache
"It shall be well inn shaa' Allah"
Gwaggo Hafsatu ta sauke numfashi mai nauyi, tana girgiza kai.
"Ya Allah! Ka tsare mana su. Allah ka dawo mana da su lafiya!"
Major General ya ɗauki wayarsa, ya sake kiran sauran jami’an tsaro domin a tura jami’ai don bincike da gaggawa.
Captain Fawaaz ya tsaya cak, idanuwansa sun ɗauki wani irin kalar tsananin tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci, kwakwalwarsa ta fara hango hanyoyin da zai bi don gano su Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad.
Ya juya ga mahaifinsa, Major General Dawud, cikin cikakkiyar murya mai ƙarfi.
"Sir, ina buƙatar cikakken bayani. Wa ya san tafiyarsu? Wani lokaci suka bar gida? Wane irin shiri aka yi don tsaron su?"
Major General Dawud ya gyara tsayuwarsa, yana jin alfahari da yadda ɗansa ya saba da aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
"Mun san dai sun taho asibiti ne, amma ba su iso ba. Wayoyinsu duk a kashe. Motarsu ba a gani a asibiti ba basu iso ba. Ba kuma ta gidah alamar sun bar gidah kenan. Sannan bata dukkanin inda ake tunanin zasu je. Muna da sakon da mahaifiyar ku ta aika musu kafin tafiyarsu, amma bayan haka babu wani bayani daga gare su."
Gwaggo Hafsatu, da hawaye ke ƙoƙarin taruwa a idanunta, ta ce cikin shashsheƙar murya,
"Fawaaz, Ku tsananta bincike,... Nabeeha... Hammad... Zaytunah... har yanzu ba a san inda suke ba. Ka yi wani abu, dan Allah."
Fawaaz ya kalli kakarsa da idanunsa masu ƙayatarwa, sannan ya rankwafa a gabanta
"Gwaggo, zan dawo da su. Inn shaa' Allah na miki alƙawari."
Bai ƙara bata lokaci ba, ya fice da sauri zuwa sashen sa ya ɗauko wata na'urar gano siginar wayoyi ta sojoji daga cikin akwatinsa. Nan take, ya fara aiki.
"First step, gano waje karshe da aka yi amfani da wayoyin su." Ya ce a hankali, yana duba bayanan da suka fara bayyana a na'urar.
Ya latsa wani maballi, na'urar ta yi ƙarar ɗan motsi, sannan ya fara samun sakonni,
Last known signal: kusa da hanyar asibiti.
Next movement: ba a iya gano shi.
Possible jamming detected: wani abu yana toshe siginar wayoyin su.
Fawaaz ya rufe idanunsa na sakanni kaɗan, yana ƙoƙarin fahimtar abinda ke faruwa. Duk alamu na nuna cewa wannan ba kawai batan hanya ba nez tabbas an sace su.
Ya buɗe idanunsa a take, yana jan numfashi da zurfi. Sannan ya juyo yana fuskantar mahaifinsa.
"Sir, ba hatsari suka yi ba. Wannan shiri ne aka yi don a sace su. Ina buƙatar izinin amfani da dukkan hanyoyin tsaro don gano su."
Major General Dawud ya gyada kai ba tare da wata gardama ba. "Permission granted. Ka yi duk abinda zai dace, Captain."
A nan Fawaaz ya danna wani maballi a na'urar hannunsa, yana aika da bayanai zuwa wata runduna ta musamman da ke taimakawa a irin waɗannan lokuta. A lokaci guda kuma, ya ɗauki wayarsa yana dailing wata lamba, wanda zai iya taimaka masa fiye da kowa a wannan yanayi.
Yanzu dai lokaci ya fara ƙurewa,duk wani mataki da za su ɗauka dole su ɗauka da gaggawa.A cikin zafin nama, Fawaaz ya fice ya nufi parking lodge tuni har masu gadin sun shigar masa da motar, Ya karbi makullin motar tasa yana musu godiya..
Ya buɗe motarsa ya shiga da sauri, zuciyarsa cike da tsananin tashin hankali da fargaba.
Bai tsaya tunani ba, ya danna motar da gudun tsiya. Takalminsa ya danna kan accelerator da ƙarfin tsiya, yana tukin cikin fushi da tsoro.
"Nabeeha! Kar ki bari wani abu ya same ki!" Ya furta cikin sauti mai ƙarfi, zuciyarsa na bugawa da mugun sauri.
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 5_
Captain Fawaaz Dawud ya naɗe hannayensa da ƙarfi akan sitiyarin motarsa, idanunsa sun cika da girmamamman al'amarin da ke gabansa. Hankalinsa ya ƙara tashi lokacin da ya duba taswirar wayarsa, ya ga cewa siginar tracking na inda akai amfani da wayar karshe tana motsi yanaa nufin an wuce da su!
Ya danna kira ga tawagar bincikensa. "Bravo Team, target yana motsi! Sigina yana nuna suna tafiya cikin wani yanki da ba a fiye amfani da hanyarsa ba. Dole mu gaggauta kafin su kauce daga tracking range!"
Wani daga cikin sojojinsa ya amsa, "Roger that, Captain! Muna