KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   3 / 40

6K to 9K   out of 119.4K words

bin sawun coordinates da ka aika. Muna shirye don ɗaukar mataki."

"Thank you" Fawaaz ya fada yana katse kiran... Airpods ya zura a kunnuwansa saboda saukin amsa kira ba sai yata latsa wayar sa ba.

Gabansa na tsananta bugawa ayayinda yaketa kokarin kiran sauran maaikatan dake gudanar da bincike. Wani bangaren na zuciyar sa yana samun saukin radadi ganin tracking devices sun fara aikin kokarin gano inda su Nabeehan sa suke...

🎀🎀🎀

A wajen da suke a tsare , Nabeeha, da Hammad da Hajiya Zaytunah da ta daidaita tana addu’a cikin shiru. Zuciyarta ta cika da fargaba, amma ta yi ƙoƙarin ƙarfafa ƙwarai domin ba 'ya'yanta damar samun kwanciyar hankali.

A wannan lokacin, Hajiya Zaytunah a cikin ɗakin da aka tsare su, ta fara kallon sama cikin dogon nazari.

"Allah ya tsare mu, ya kawo mana agaji," ta yi ta addu’a, tana fatan cewa Allah zai kawo musu sauki ba tare da bata lokaci ba.

Daya daga cikin tawagar binciken Fawaaz ta fara motsawa cikin dazukan, suna amfani da kayan zamani na bincike da fasahar tauraron dan adam, tare da makamin CCTV da na'urorin sa ido. Daga cikin wannan tsari, Captain Fawaaz ya kasance cikin cikakken natsuwa... ko da yake zuciyarsa na bugawa da karfi a cikin rufin jikinsa, ba ya bari damuwarsa ta bayyana a fili.

"Mu tashi, mu shiga aikin ceto. Ba zan bari wannan muguntar ta kare ba," in ji shi a cikin murya mai kwarin gwiwa.

A nan, lokacin ya fara ƙurewa, kowane sakan na tafiya yana nuni da muhimmancin daukar mataki cikin gaggawa. Fawaaz ya kafa hannunsa a kan na'urar, yana tura bayanai zuwa rundunar musamman da aka kebe domin irin waɗannan lamurra.

Yayin da tawagar binciken ke matsowa cikin ƙaramar ƙofar daji, Captain Fawaaz ya ƙara jaddada umarni,

"Ku kasance masu faɗakarwa, duk wani motsi mara kyau, ku sanar da ni kai tsaye. Mu tabbatar babu wata hanyar da za su iya ɓoye mu a ciki."

Duk da kasancewarsa mutum mai ƙarfi da rashin bayyana jin zafi, cikin zuciyarsa ya cika da kishi da ƙwazo na ganin su Nabeeha sun dawo lafiya. Duk abin da ya faru, shi ba zai yarda da wannan mugunta ta ci gaba ba, daga nan zai tashi don daukar duk wani mataki mai tsauri.

Tsohon gidan da ke tsakiyar dajin ya fara bayyana a nesa, kamar wani guri mai shakku da duhu. Wannan shi ne wurin da na'urar tracking ta nuna, kuma tawagar binciken ta fara shiryawa tsaf don shiga cikin aikin ceto.

Captain Fawaaz Dawud ya ɗauki numfashinsa da zurfi, ya tsayar da tafiyarsa a wani wuri mai nisa, yana auna kowane alamun motsi a taswirar digital.

"Mu shirya. Lokaci yayi da za mu tunkari wannan wuri," in ji shi cikin muryar soja mai cike da umarni, yayin da zuciyarsa ta ci gaba da bugawa ba don bayyana damuwa ba, amma saboda kishi da kwarin gwiwa na son ganin su Hajiya Zaytunah sun dawo lafiya cikin koshin lafiya.

Sai dai lokacin da suka karasa shiga cikin dokar dajin..sun Sha tsananin mamakin ganin wuta tanaci da bukkoki tamkar da mutane acikinta. Amman ba kowa awajen wayam. Kenan yan fashin backup sukayi musu don su zata suna nan da su Hajiya Zaytunah a tsare..

"God damn it! " Captain fawaaz ya fada yana cijan yatsansa.

"Roger that, captain yanzu ya zamuyi what's next? "

"Muyi grouping into 4,. Ku nan ku yanki dajin kudu, ku kuma dajin yamma, Ku Kuma nan haka gabas zakuyi. Kai da Kai da Kai muyi arewa. Let's go.no time ...move it soldiers.."

"Aye aye captain" suka amsa shi cikeda zafin nama da Kuma girmamawa. Motocin su suka shisshiga suka fara barbazuwa cikin dazukan don neman su Hajiya Zaytunah..

Captain fawaaz suna tafiya acikin mota yana jera tsaki ba adadi. Ya sauke numfashi Mai zafi yana dartse lebensa. Mahaifinsa ya kira a awaya ya sanar masa yadda suke ciki ya karkare da,

"Amma mun rabu wings hudu sir, yanzu haka Muna mota ma zamuyi arewa. Inshaa Allah su aunty, Hammad da Nabeeha zasu dawo gidah cikin koshin lafiya in Allah ya yarda"

"Allah ya amince captain. Sannu ku da kokari" major general ya amsa a sanyaye a nasa bangaren..

Gwaggo Hafsatu da tunda suka fara wayar take dubansa ganin sun kammala wayar bai ce komai ba ya sata cewa,

"Wani abune ya faru?"

"Aa inshaa Allah kalau Gwaggo. Ai sun barbazu ma cikin dazukan kudu da arewa, gabas da yamma. Su Hajiya Zaytunah zasu dawo gidah cikin koshin lafiya inshaa Allah"

"Toh Allah ya amince dawuda. Allah ya yarda dawuda. Allah ya kawo karshen wannan mummunan labari Amin"

"Aameen Gwaggo.. Aameen"

Yana rufe bakinsa. Wayar sa ta fara Kara. Ya dauka ganin chief judge Abdulfatah ne. Bayan sun gaysa yake sanar dashi dazu jikin Gwaggo ne ba lafiya. Ankwantar da ita a asibiti ma amma sun dawo gidah..

"Toh shikenan babu damuwa... Allah ya kawo su lafiya. Okay kai baka nan ma? Ayyah ehh. Supreme court. Toh Allah ya bada saa. Alright sai munyi magana. Nagode. Zataji inshaa Allah yauwa sai ka dawo"

Ya katse Kiran yana hurar da iskar bakinsa Mai tsananin zafi..ya dubi gwaggo yache,

"Abdulfatah ne. Yana duba jikin naki. Yana miki sannu yace na gayshe ki idan ya dawo zai zo ya dubaki inshaa Allah. Wai shugaban kasa ne yake neman su da gaggawa kan shari'ar nan ta supreme court."

"Allah sarki... Nagode kwarai. Allah yabada saa"

"Aameen gwaggo. Sai Kuma yake sheda mun mahaifan Muhammad mai neman Nabeeha sun taho suna kan hanya zasu karaso gidah"

Ya karasa fada yana duban gwaggon da itama shi take kalla. Allah yaso su biyu ne a parlorn. Daga ita sai shi. Hajiya Hauwa ta tashi.

"Tohh fa... Allah ka kawo mana sauki... "

"Aameen Gwaggo. Yanzu ya zamuyi kenan?"

"Dawuda ni kaina banida abun cewa.. Bamuda wani abun fada. Kaga dai halin da muka tsinci kanmu aciki ma. "

"Ko ca za'ai musu sunyi tafiya basa nan? Nabeehan"

"Toh kadai san me zaka sanar musu... Allah zai shiga cikin lamuran namu in Allah ya yarda"

"Aameen gwaggo. In shaa Allah"

Bai karasa rufe baki bayan maganar da yayi. Horn din dake jikin gate din gidan mai bada sauti ga bakin motocin da suka dososhi ne zasu shigo ya farayi ba kakkautawa. Inda masu gadin kafin su danna permit button sai da suka kira intercom na sashen major general dawud suka sanar masa. Nan yace abude musu bakin sane...

A lokacin da su Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Muhammad, Gwaggo Zainabu, da mai aikinta suka iso gidan Major General Dawud, an shigo da su ta babban kofar gidan, inda masu gadin gidan suka gaishe su cikin ladabi. A nan ne suka zarce zuwa cikin babban parlour, inda aka sauke su domin jiran Major General Dawud.

A yayin da suke zaune, ma’aikatan gidan suka shiga da kayayyakin da suka kawo. Manya manyan ledoji shake da kaya. Da kwalaye. Harda Karin wasu akwati guda biyu...

Akwatinan da suka ƙunshi kayan kyauta da wasu kayayyakin alatu, da manyan kwalaye.. Akwai ma wasu ledodi na kaya da aka mika wa wata daga cikin masu aikin, wadda ta shigar da su zuwa ɗakin da Gwaggo Hafsatu ke amfani da shi.

A hankali, an gama sauke komai, sannan aka tabbatar da cewa babu wani abu da aka bari a waje. Duk da cewa ma’aikatan ba su fahimci dalilin kawo kayan ba, sun kasance cikin girmamawa da kwarewa, suna kokarin yin komai ba tare da hayaniya ba...

Bayan ma’aikatan gidan sun gama shigar da kayan cikin tsari, daya daga cikinsu ya iso kusa da Alhaji Amiru cikin ladabi, yana sanar da su cewa an kammala jera kayayyakin a inda ya dace.

Gwaggo Zainabu ta ɗan zubawa parlourn ido, tana nazarin yadda gidan yake. Ita kanta ta san cewa gidan ba ƙaramin gida ba ne, kuma tsarinsa yana nuna cewa yana ɗauke da duk abubuwan jin daɗi. Sai dai hakan bai hana ta jin wani ɗan ɗaci a ranta ba, saboda tunani da damuwar da take ciki.

Muhammad ya matsa kusa da mahaifinsa, yana dan shafa KIRJIN sa da hannunsa kamar mai son yin magana amma yana kokarin kame kansa. Alhaji Uzairu kuwa, ya ɗan lumshe ido na wani lokaci, yana jin shiru da yanayin gidan ya lullubesu.

Gwaggo Zainabu ta kalli mai aikinta, wadda ke tsaye cikin nutsuwa kusa da ita, sannan ta ce da ita da sassanyan murya,

"Samu waje ki zauna kema.. sannu da kokari"

"To Hajiya," mai aikin ta amsa a ladabce, sannan ta juya zuwa hanyar wani dan corridor da kujera a wajen ta zauna tana nazarin kawataccen parlorn dayaci kayan kudi ya lashe..

A dai-dai wannan lokacin, wata daga cikin masu aikin gidan ta iso kusa da su cikin nutsuwa, sannan ta rusuna cikin girmamawa tana cewa,

"Barkan ku da zuwa. Yallabai yana zuwa yanzu."

Alhaji Amiru ya jinjina kai kawai ba tare da ya ce komai ba. Amma yana cikin zurfafa tunani. Ya san cewa wannan zama ba sauki ba ne, kuma ya shirya yin duk abin da zai yi don tabbatar da cewa an warware matsalar da ya kawo su.

Gidan ya kasance cikin tsananin shiru, kowannensu yana cikin tunaninsa, har sai da aka fara jin alamun takun mutum yana matsowa daga waje...



_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE: 6_

  A hankali, cikin kasaita da nutsuwa, Major General Dawud ya taka zuwa cikin babban falon gidan nasa, inda bakin suka hallara. Yana ɗauke da wani irin kwarjini da kamun kai da suka dace da mutumin da ya saba da shugabanci.

Da zarar idonsa yana sauka kan Gwaggo Zainabu, wadda ke zaune cikin kamala da haiba, sai ya taka da girmamawa, yana sunkuyawa kaɗan cikin dattako. A matsayinta na babbar macen data Isa ta haife shi, kuma dattijuwa mai cikakken daraja, ya san dole ya gaisheta da irin gaisuwar da ta dace da ita.

A nutse, cikin ladabi da haiba, ya ɗan rusuna kaɗan, yana faɗin da murya mai zurfi da cike da girmamawa,

“Ranki ya daɗe, Hajiya barka da wannan lokaci. Kun zo kalau?. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana. Allah Ya ƙara girma da daraja.”

Gwaggo Zainabu ta kalle shi da murmushin jin daɗi, tana jin daɗin yadda ya girmamata kamar yadda ya kamata. Ta amsa cikin kulawa da jin daɗi,

“Alhamdulillah! Sannu da kokari. Yaya aiki? Allah Ya ƙara maka nasara da rufin asiri.”

Ya ɗaga kai cikin girmamawa, yana amsawa,

“Amin, Hajiya. Mun gode da addu’a. Allah Ya bar mana ke.”

Bayan ya gama gaisheta da mutuntaka, sai ya juya zuwa sauran da suka zo. Ya miƙa wa Alhaji Amiru hannu, yana kallonsa ido cikin ido da cikakken mutuntaka.

“Sannu da zuwa, Alhaji Amiru. Da fatan an zo kuma hanya lafiya?”

Alhaji Amiru ya kama hannun nasa da ɗan murmushi, yana gyada kai.

“Lafiya kalau, Major General. Mun gode da kulawa.”

Bayan haka, ya miƙa wa Alhaji Uzairu hannu, suma suka gaisa cikin mutuntaka da ladabi.

A ƙarshe, idonsa ya sauka kan Muhammad, matashin saurayin da ke zaune kusa da mahaifinsa.

Muhammad Hammad, da zarar idonsa ya haɗu da Major General Dawud, sai ya ji wata irin kunya da girmamawa sun mamaye shi. A matsayinsa na mutum mai natsuwa da kamun kai, Muhammad ya san yadda ake mutunta manya, musamman irin su Major General Dawud, wanda shahararsa da mutuncinsa sun bazu a ko’ina. Uwa uba kuma mai babban matsayi ga zuciyar da yake kaunar kasancewa da ita wato Nabeeha..

A hankali, ya miƙa masa hannu cikin girmamawa, yana faɗin da wata murya mai cike da girmamawa,

“Ina wuni, Baba barka da war haka.”

Major General Dawud ya karɓi hannunsa da kulawa, yana kallonsa da idanu masu zurfi, amma ba tare da ya nuna wani abu a fili ba. Ya fahimci yadda Muhammad ke ji a lokacin, kuma bai da niyyar tsorata shi ko sanyaya masa guiwa.

“Lafiya lau, Muhammad. Ya wajen su mama?”

Muhammad ya gyada kai cikin girmamawa, yana cewa,

“Alhamdulillah, suna lafiya.”

Bayan haka, Major General ya matsa kaɗan ya zauna cikin kwanciyar hankali, fuskarsa na bayyana cikakken nutsuwa da sanin ya kamata.

Duk da cewa kasancewarsa mutum mai ƙwarewa a lamurran tsaro ya sa yana da natsuwa da ƙarfin zuciya, yana da kyakkyawar dabi’ar girmama mutane, musamman waɗanda suka girme shi da shekaru ko matsayi.

A cikin falon, an ɗan yi shiru na wasu ‘yan dakiku, kowa yana duba yadda yanayin zaman zai kasance. Kafin a soma tattaunawa kan batun da ya kawo su, Major General Dawud ya ɗauki lokaci yana duban fuskokinsu, yana nazarin yadda kowannensu ke kallon sa.

Wannan shiru da nutsuwa da ya nuna, ya ƙara tabbatar wa da su cewa mutumin da ke gabansu ba mai sake-sake bane. Sai dai duk da haka, yana da halin yin biyayya da girmama waɗanda suka cancanta. Tuni maaikatan suka cika gaban su da abinci da sauran abubuwan motsa baki..

Bayan ɗan lokaci, Ya ɗan gyara zamansa, yana kallon Gwaggo Zainabu da sauran bakin da ke falon, yana jiran jin dalilin zuwansu da abinda suke da bukatar tattaunawa a kai.

"Ranka ya dade... Nasan wata kila chief judge ya sanar maka da zuwan mu ko?"

"Eh anyi haka. Yace zaku zo da yardar Allah..Dazu ma ya kirawo ni yake duba jikin mahaifiyata yake kuma sheda mun cewar shugaban kasa yana neman su kan wata shariah da.. yace idan ya dawo daga tafiyar zai shigo inshaa Allah"

"Allah sarki. Shi yasa nayita kiran wayar sa bata shiga?" Cewar Alhaji Amiru

"Zai iya yiwuwa kam. Kila suna cikin meeting. Allah yasa adace"

"Aameen Yaa Rabbi. Ya jikin Hajian? "
Suka shiga tanbayar jikin Gwaggo Hafsatu

"Da sauki Alhamdulillah.... Zata karaso nan din yanzu Inshaa Allah.." major general ya fada yana murmushi.

Bai rufe baki ba kuwa... Gwaggo Hafsatu ta shiga parlorn. Hajia Hauwa tana biye da ita a baya. Bakunan su dauke da sallama suka karasa shiga

Suka amsa sallamar ta su... Gwaggo Hafsatu ta zauna akan kujera yayinda hajia Hauwa take daga kasanta.

Gaisuwa suka farayi. Gwaggo Hafsatu da gwaggo zainabu sun gaysa sosai. Har suna tuno abubuwan da suka faru a baya lokacin da suka fara haduwa a asibitin dake birnin mawii.

Alhaji Uzairu ya zauna cikin kamewa da dattako, ya gyara zamansa sannan ya fara magana da ladabi,

"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Yan uwa da iyayena mun zo gare ku ne a yau da farin ciki da girmamawa, domin mu gabatar da bukatar mu ta musamman. Da farko, muna mika gaisuwa da fatan alheri gare ku baki daya. Mun zo ne domin neman izinin ku da yardar ku, wajen neman auren 'yar ku, Nabeeha, ga ɗan mu, Muhammad. Mun yi imani cewa wannan haɗin zai kawo farin ciki da ɗorewar zumunci tsakanin iyalanmu.

"Muhammad, ɗanmu, matashi ne mai tarbiyya da kyawawan halaye. Ya kammala karatunsa tare da samun nasarori masu yawa, kuma yana da kyakkyawan aiki da ke ba shi damar kula da iyali yadda ya kamata. Wato matukin jirgin sama ne, Air captain Muhammad, Har ila yau, yana da kyakkyawar mu'amala da mutane, kuma yana da kishi da kishin al'umma. Mun yi imani cewa zai zama miji nagari ga 'yar ku, Kuma yar mu, Nabeeha.

"Mun kuma ji labarin kyawawan halayen Nabeeha, Mun yaba kwarai matuka, Yadda take da ilimi, Tana karatun likita, Ga tarbiyya, da kuma kwarewa a fannoni daban-daban. Mun yi imani cewa tare da Muhammad, za su kafa gida nagari mai cike da soyayya, fahimta, da kuma goyon bayan juna.

"Muna fatan Allah ya sa wannan haɗin ya zama alheri ga dukkanmu, ya kuma ba mu ikon cika dukkan hakkokin da ke kanmu wajen wannan aure. Muna kuma fatan za mu ci gaba da ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin iyalanmu, domin amfaninmu da kuma al'ummar da muke ciki.

"Aameen" suka amsa baki daya...

Bayan Alhaji Uzairu ya kammala bayani, Gwaggo Zainabu ta gyara zamanta cikin nutsuwa, ta kalli iyayen Nabeeha da murmushi, sannan ta fara magana,

"Assalamu alaikum.... Masha Allah, Ya gama fadan kusan daya daga cikin abunda ya kawo mu...Na zo tare da su ne domin nuna goyon baya ga wannan kyakkyawar manufa. Ina fatan wannan ziyara za ta taimaka wajen ƙara sanin juna, ƙarfafa zumunci, da gina kyakkyawar alaƙa tsakanin iyalanmu. Har ila yau, ina son in ga yarinyar da jikata, Muhammad, yake so ya aura. Wato kishiyata Nabeeha, don in fara Shirin damarar zama da wadda zaa kawo"

Suka Saka dariya baki daya... na Jin gwaggo zainabu tana wasan kaka da jika.. Gwaggo zainabu ta dan murmusa sannan ta cigaba da cewa,

"Ina fatan Allah ya sa wannan haɗin ya zama sanadin samun zaman lafiya, farin ciki, da ci gaba ga iyalanmu baki ɗaya.muna fatan za mu yi aiki tare wajen shirye-shiryen wannan aure, idan har an amince mana, tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin an gudanar da komai cikin nasara da yardar Allah. Allah ya sa a yi aure lafiya, ya ba su zuri'a dayyiba, ya kuma sa zaman aurensu ya kasance cike da farin ciki da albarka.

"Da fatan za mu ci gaba da haɗin kai da fahimtar juna a duk matakan da za a bi domin cimma wannan manufa ta alheri. Muna godiya da lokacinku da kuma karɓar mu da kuka yi da hannu biyu. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu."

"Wa'alaykumm Salam Wa rahamatullahi Wa barakatuh. Sannu ku da kokari Gwaggo. Muna godia kwarai da gaske. Hadi da kambamawa da wannan dattako irin naku. Harda wahala. Ga kayanan fal? Mungode Allah ya Saka da alkhairi " major general ya fada yana nuni da kayayyakin da suka kawo..

"Sai yanzu na lura da su... Aa harda kokari haka? Toh Allah ya Saka da alkhairi ya bar zumunci har gaban abadan. Sai dai ban sheda ka sosai ba" gwaggo Hafsatu ta karasa magana tana duban Alhaji Uzairu.

Alhaji Uzairu ya dubi Gwaggo Hafsatu da murmushi a kwance a fuskar sa yace,

"Laa Gwaggo kin manta uzairu? Ni ne ke zama da gwaggo a asibiti da safe zuwa da yamma kafin a kawo abinci."

"Oh haka haka. Allah sarki ai dake shekarun da yawa. Jikin tsufa. Toh Allah yayi muku albarka"

"Aameen gwaggo Aameen"

"Alhaji Uzairu ne. Kani ga Alhaji Amiru " major general ya dubi gwaggo

3 / 40