INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:52_
Ta buɗe idanunta a hankali, suka haɗa ido da shi. Sai dai ta kasa cewa komai.
Shi kuwa Fawaaz, murmushinsa bai gushe ba. A hankali ya ɗaga hannunsa, ya ɗan taɓa gefen motar da yake jingina da ita, yana kallonta da zurfi.
"Ba sai kin ce komai ba, Nabeeha."
Ta ɗauke idonta, amma zuciyarta ta kasa yin shiru. Sai bugawa take kamar ana danna gangar zuciya.
Muryarsa ta sauka cikin sanyi, kamar iska mai sanyaya rai. "Amma ki sani... idan wata rana zuciyarki ta taɓa furta wani abu game da ni, ko da kuwa a cikin ruwan sanyi ne, zan ji shi."
Wani abu ya tsaya a KIRJIN ta.
Ya sake murmushi mai taushi. "Zan saurara… zan ji, har ma in amsa."
Zuciyarta ta yi nauyi da wani abu mai daɗi da ban tsoro a lokaci guda.
Shi kuwa ya gyara tsayuwa, yana kallonta cikin nutsuwa. "Ina so ki san cewa babu rana guda da zata wuce ba tare da na yi tunaninki ba."
Ta haɗiye yawu.
"Babu safiya da zata waye ba tare da zuciyata ta ambace ki ba."
Ta ƙura masa ido, zuciyarta na tafarfasa.
"Babu dare da zan kwanta ba tare da hotonki a cikin tunanina ba."
Ta numfasa, amma numfashin da bata san yana ɗauke da nauyi ba.
Shi kuwa, ya janye idonsa a hankali, yana duban sararin samaniya kamar yana magana da taurari.
"Idan har akwai soyayya da zata iya riƙe mutum gaba ɗaya, to ni na san cewa kin riga kin mallake ta a wajena."
Kallonta ya dawo kanta, cikin zurfin so da gaskiya.
"Nabeeha… ina son ki."
Hankalinta ya tsaya cak. Zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci, kafin ta cigaba da bugawa da wani irin yanayi da bata taɓa jin irinsa ba.
Fawaaz ya gyara tsayuwa, yana dubanta da kwanciyar hankali. "Kuma ba zan taɓa gajiya da faɗin hakan ba."
Ya numfasa a hankali, sannan ya ce, "Ko da baki ce komai ba… ko da kin ci gaba da ɓoye zuciyarki, zan tsaya har sai lokacin da kike da shirin bayyana min abinda take ji."
"Har abada, zan jira."
Shiru ya ratsa tsakaninsu. Amma shiru ne mai cike da nauyin soyayya da kalmomin da suka yi ƙaura a zuciya.
Nabeeha ta ji ƙafafunta sun gaza ɗaukar ta. Sai ta ɗauke idonta daga nasa, zuciyarta na tafasa da abu mai wuyar fassara.
Fawaaz kuwa, sai ya ja numfashi, sannan a hankali, ya matsa daga kusa da ita, yana kallonta da murmushi mai taushi.
"Zan wuce yanzu. Amma zan sake dawowa."
Ya juya a hankali, yana tafiya zuwa mota.
Daidai lokacin da ya shiga, sai ya sake kallonta, yana gyada kai. "Ki kula da kanki, Nabeeha."
Ya tada motarsa, ya fice a hankali, zuciyarsa na barin wani ɓangare a wajenta.
Ita kuwa, ta tsaya a wurin, har sai da sautin motarsa ya ɓace.
A hankali ta lumshe idonta, zuciyarta na tafasa da wani irin yanayi.
Bata san yaya zata yi da zuciyarta ba. Bata san wane mataki zata ɗauka ba.
Amma abu guda ta sani.
Soyayyar Fawaaz…
Tuni ta shiga jikinta, kuma bata san ko zata iya fita daga gare ta ba.
Nabeeha ta tsaya daram a wajen, zuciyarta na dokawa da wani irin sauti da bata taɓa ji ba. Hannunta ta ɗaura saman KIRJIN ta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri kamar zata tsinke.
Idanunta suka lumshe a hankali, kalmomin Fawaaz suna sake dawo mata a zuciya.
"Nabeeha… ina son ki."
Numfashinta ya ɗauke na wasu dakiku. Sai ta buɗe idanunta da sauri, ta ɗauke idonta daga inda motarsa ta ɓace.
Soyayya ce?
Zuciyarta ta ambace shi?
A hankali ta ɗaga hannunta, ta taɓa saitin zuciyarta da laushi. Ta girgiza kai da ƙyar, tana ƙoƙarin kawar da wannan tunanin.
Sai dai wani murya mai taushi ya faɗo mata a cikin zuciya.
"Har abada, zan jira."
Ta haɗiye yawu, zuciyarta na ƙoƙarin amincewa da wani abu da ita kanta bata gama fahimta ba.
Wani ganyen bishiya ya fado ya ratsa kusa da ita yana busa iska, sai ta dawo daga duniyar tunaninta. Ta sauke numfashi a hankali, sannan ta ɗaga ƙafafunta da ƙyar, ta juya zuwa cikin gida.
Tana jin kamar tana tafiya cikin wani sabon yanayi da bata taɓa sanin tana da shi ba.
Kuma a karo na farko…
Ta ji zuciyarta na yarda da abu guda.
Soyayyar Fawaaz…
Tuni ta fara ratsa tsokar zuciyarta, kuma bata da ikon tsayar da ita...
🎀🎀🎀
Gwaggo Hafsatu na zaune a kan gadonta, hannunta rike da carjib, tana jan karatu cikin nutsuwa. Hajiya Zaytunah ta shigo dakin a hankali, jikinta cike da lumana. Idanunta na bayyana natsuwa da shawara, duk da cewa zuciyarta tana bugawa da karfin gaske.
“Gwaggo…” Ta kira da murya kasa, tana durkusawa gabanta.
Gwaggo Hafsatu ta janye kallonta daga abunda take, ta kalli Zaytunah da idanu masu cike da hikima. “Na’am, Zaytunah.”
Ta dan numfasa, sannan ta lumshe ido na wasu dakiku kafin ta bude. “Na gama istikhara, Gwaggo. Na ji kwanciyar HANKALI a raina. Na yanke shawarar komawa gidan mijina.”
Shiru ya ratsa dakin na ‘yan dakiku. Gwaggo Hafsatu ta ajiye misbah dinta a hankali, tana nazarin fuskarta. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi murmushi mai cike da farin ciki.
“Alhamdulillah,” ta fada da sigar godiya. “Allah Ya tabbatar da alheri.”
Zaytunah ta gyada kai da girmamawa, zuciyarta tana karbar kalmomin da natsuwa.
Gwaggo Hafsatu ta kai hannu ta rike nata. “Zaytunah, komawar ki gidan Alhaji Uzairu ba matsala ba ce, amma ki tabbatar kin shiga da addu’a. Duk wanda ya dogara ga Allah, ba zai tozarta ba.”
Cikin sanyin murya, Zaytunah ta amsa, “Na yarda, Gwaggo. Da addu’a zan shiga.”
Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kulawa. “Allah Ya albarkaci zaman ki.”
....
Motar Fawaaz ta tsaya a gefen titi a gaban wani gida mai tsari. A cikin motar, shi da Nabeeha suna zaune, amma babu wanda ke magana. Sai shiru mai cike da nauyi.
A hankali ya juyo ya kalleta, idanunsa masu zurfi da kwarjini sun ratsa ta.
“Ki shigo ki gaisa da Humyrah, amma...” Ya dakata kadan, yana dauke kansa kamar ba ya so ya fadi abin da ke ransa. “Kada ki dade.” ya karasa fada ahankali..
Nabeeha ta dan saki murmushi, sai dai ba ta kalle shi ba. “Toh.”
Ta bude kofar motar ta fito. Duk da sanyin dare da ke tashi, tana jin zafin bugun zuciyarta. Fawaaz ya kara gyara zaman sa, amma bai dauke idanunsa daga kanta ba har sai da ta bace cikin gidan.
Humyrah ta karbi Nabeeha da murmushi mai cike da tsokana. Kafin ma su zauna da kyau, ta riga ta fara dariya.
“Nabeeha, kin san me?”
Ta dan dago ido tana kallonta. “Mene?”
Humyrah ta dan rankwafa kadan, tana kallonta da wani kallo na tsokana. “Tun shekarun baya nake tunanin cewa Yaya Fawaaz yana kaunarki.”
Nabeeha ta dan zaro ido da mamaki, sannan ta kada kai da sauri. “Ke dai Humyrah, me ya sa kike tunani haka?”
Humyrah ta tabe baki. “Ai yana bayyane! Yanda yake kula da ke, tsananin tsaro da yake bamu, yadda baya barin kowa ya shiga tsakaninku…” Ta ja numfashi, sannan ta dan yamutsa fuska. “Ko da yake, miskili ne, sai da wuya ya nuna abin da ke zuciyarsa.”
Nabeeha ta dan saki murmushi, zuciyarta na bugawa da sauri.
Suka zauna. Ta cika gaban Nabeeha da kayan kwalam. Kafin daga bisani ta fita da kanta da drinks da snacks ta kaiwa yayan nata suka gaysa. Sannan ta dawo wajen nabeeha suka cigaba da hirar su..
Fawaaz na tsaye a gefen motarsa, hannayensa a kugu. Fuskar sa kamar yadda aka saba—ba yabo ba fallasa. Amma idanunsa sun nuna yana cikin tunani mai zurfi.
A hankali, yaga Nabeeha ta fito daga gidan, tana tafiya cikin nutsuwa kamar yadda ya saba hangota.
Bai ce komai ba har sai da ta karasa kusa da shi. Ta tsaya, tana kallonsa da ido masu cike da tambayoyi.
Ya dan numfasa, sannan ya furta da murya mai kwarjini amma cike da saukin gaske.
“Nabeeha…”
Ta dago kai tana kallonsa, zuciyarta na bugawa da sauri.
Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai sanyin iska da ke kadawa a hankali.
Daga nan sai ya matsa kusa da ita, yana kallon cikin idanunta kai tsaye.
“Kin san abin da ke cikin KIRJIN duk wani MAI HANKALI?”
Ta dan girgiza kai a hankali, idanunta na bayyana sha’awar jin amsar.
Ya lumshe ido na wasu dakiku, yana dauke numfashi, kafin ya bude su da wani yanayi na soyayya mai cike da natsuwa.
“AKWATIN SIRRIN SA ne,” ya furta da murya kasa kasa.
Hannunta ya dan motsa, kamar tana son rikewa da gaske. Amma sai ta tsaya, tana kallonsa da wata shaukin fuska.
Shi kuma ya ci gaba, “Kuma kinsan mene ne SIRRI na?”
Ta sake girgiza kai, zuciyarta na neman dukan kirjin ta.
Ya yi murmushin da ba kasafai ake ganinsa da shi ba. A hankali, ya rike hannunta, yana kallonta da wani yanayi na dabara.
“Ke ce, Nabeeha.”
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:53_
Nabeeha ta tsaya cak, idanunta sun kasa dauke wa daga nasa. Zuciyarta na bugawa da sauri fiye da kowane lokaci. Kalmar da ya fada ta ratsa ta, ta tsaya a zuciyarta kamar an rubuta da bakin zinariya.
"Ke ce, Nabeeha."
Ba ta san lokacin da ta dan saki numfashi ba. A karo na farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba kawai mai kareta ba ne, zuciyarsa na tare da ita.
Fawaaz ya dan kalleta, sai kuma ya dauke kansa kamar ba shi da abin cewa. Amma hannunsa da ke rike da nata bai motsa ba. Sai ma ya kara matse shi a hankali, yana jin yadda tafin hannunta ke sanyi kamar yana jin bugun zuciyarta ta ratsa nashi.
“Nabeeha…” Ya kira sunanta cikin nutsuwa.
Ta amsa da ido kawai.
Ya lumshe ido kadan, sannan ya bude su da wani yanayi na SIRRIN ta ne kawai zai iya fassara. “Kin taba jin yadda zuciya ke ji idan tana son abu da gaske?”
Ta dan girgiza kai. “Ban sani ba.”
Ya yi murmushi kadan, sai dai murmushinsa mai nauyi ne. “Zuciya ba ta da hayaniya, amma tana da karfi. Idan ta kamu da so, ko da baka fadi ba, sai duniya ta fahimta.”
Tayi shiru, zuciyarta na harbawa da sauri.
Ya dan matsa kusa da ita, murya a hankali. “Kin san nawa lokacin da zuciyata ta dauka tana son ki?”
Ta girgiza kai. “ Yaa Fawaaz…”
Ya kara matsowa kadan, idanunsa cike da gaskiya. “Tun kafin kisan meye soyayya.”
Nabeeha ta kasa cewa komai.
Ya sauke numfashi a hankali, yana kallonta da idanu masu cike da soyayya. “Ke ce SIRRI na, Nabeeha. AKWATIN SIRRIN da zuciyata ta rufe tsawon lokaci.”
Ta lumshe idanu, zuciyarta na bugawa da sauri. Wannan kalaman da yake fada, ba yau suka taso ba. Ya dade yana ajiyesu a zuciya. Kuma yanzu, sun fito fili kamar yadda haske ke bayyanar da komai a dare mai duhu.
A hankali, ta bude ido, tana kallon shi da fassara mai zurfi. “ Yaa Fawaaz…”
Ya dan matse hannunta, yana jin yadda jikinta ya dauki dumi. “Ba zan bukaci komai daga gare ki ba, Nabeeha. Sai dai abu guda…”
Ta kara kasa da murya. “Mene ne?”
Ya yi murmushi, yana juyar da kallonsa gefe kadan. “Kada ki bar zuciyata ita kadai a cikin wannan tafiyar.”
Idanunta suka kada, zuciyarta ta dauki zafi. Shin yana nufin... tana da wani matsayi da ya wuce abokiyar rayuwa a cikin zuciyarsa?
Fawaaz ya dago yana kallonta da ido masu cike da soyayya, amma ba tare da ya ce wani abu ba. Sai numfashinsa da ke bayyana nauyin abin da ke zuciyarsa.
Shiru ya ratsa tsakanin su. Sai dai ba irin shiru na rashin magana ba—shiru ne mai cike da fassara, mai cike da abinda kalmomi ba za su iya bayyana ba.
Fawaaz ya fadi soyayyarsa. Kuma yanzu… Nabeeha ce ke da hakkin yanke hukunci.
Nabeeha ta dauke numfashi a hankali, zuciyarta na harbawa da sauri. Ta kasa dauke idanunta daga nashi, kamar tana neman wani abu a ciki. Fawaaz kuwa, sai ya dan ja da baya kadan, yana kallonta da kwanciyar HANKALI, amma a ciki, akwai abu da yake kokarin boyewa.
Ya san kalmomin da ya fada suna da nauyi. Ya san ya bude AKWATIN SIRRIN da ya daɗe yana adanawa a zuciyarsa. Amma ba ya da nadama.
Shi kam, ba shi da wata bukata sai dai jin abin da Nabeeha ke ji.
“Ina jiranki a mota,” ya fada a hankali, yana dauke kansa.
Nabeeha ta yi shiru, har sai da ya juya zai bar wurin. Da sauri ta kira sunansa.
“Yaa Fawaaz.”
Ya tsaya cak, amma bai juyo ba.
Tayi shiru na wani lokaci, sai kuma ta dan gyada kai. “Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba.”
Fawaaz ya runtse ido na wani dan lokaci. Wannan kalma ta shiga cikin zuciyarsa fiye da duk wani abu da zai ji a yau. Sai kuma ya yi murmushi—murmushin da ya saba ɓoyewa.
Ya juyo a hankali, yana kallonta da ido masu cike da jin dadi. “Nagode.”
Ya fadi haka kawai. Amma cikin wannan "nagode", akwai soyayya, akwai nutsuwa, akwai alƙawari.
Tafiyar su gida tayi shiru. Amma ba irin shiru na damuwa ba—shiru ne na zuciyoyin da suka soma fahimtar juna ba tare da kalmomi ba.
A lokacin da suka isa kofar gidan su, Nabeeha, Fawaaz bai yi kokarin bude mata kofa ba kamar yadda ya saba. Sai dai ya tsaya, yana kallonta da nutsuwa.
“Ina so ki huta da kyau,” ya fada a hankali.
Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta cike da wani irin yanayi mai daɗi. “Kai ma.”
Ta sauka daga motar, amma kafin ta rufe kofar, sai ta juyo.
“Ya fawaaz.”
Ya kalleta, yana jiran abin da za ta fada.
Sai tayi murmushi. “KIRJIN MAI HANKALI—AKWATIN SIRRIN SA.”
Zuciyarsa ta buga. Bati taba Jin kalamen sun masa dadi, cikin sanyin fuska mai daɗi irin haka ba.
Ta rufe kofar a hankali, sannan ta juya ta shige gidan, zuciyarta tana harbawa da sauri.
Fawaaz kuwa, ya jima a zaune a wurin, yana murmushin da shi kadai ya fahimta.
A wannan dare, zuciyoyin su biyu sun cika da sabbin tunani. Fawaaz bai koma gida kai tsaye ba. Sai da ya dan tsaya a gefen titi, ya sauke numfashi a hankali, yana kallon dare. Bai taba tunanin cewa rana irin ta yau za ta zo ba—rana da zai furta SIRRIN da ya adana tun kafin ya fahimci cikakken ma’anarsa.
A gefe guda kuwa, Nabeeha ta shige dakinta tana jin kamar kanta yana shawagi. Zuciyarta tana bugawa da wani yanayi da ba ta taba jin irinsa ba. "Ba zan bar zuciyarka ita kadai ba." Ta fada masa. Wannan kalma tana maimaita kanta a cikin kwakwalwarta.
Shin menene ma’anarta a gare ta? Ta san cewa tun tuni Fawaaz ya ke kulawa da ita fiye da kowa. Ya riga da ya kafa bango mai karfi tsakanin ta da duk wani hadari. Amma yaushe ya fara ganin hakan a matsayin soyayya? Kuma ita fa? Shin ta riga ta san abin da ke zuciyarta?
Tana cikin dogon tunani, sai wayarta ta dauki ringing. Humyrah.
Ta dauka a hankali. “Hello.”
Muryar Humyrah cike da tsokana ta doki dodon kunnenta. “Kin iso gida lafiya?”
“Eh,” ta amsa a kasalance.
Humyrah ta ja tsaki. “Karki min haka, Nabeeha. Na san kin shige a duniyar tunani. Amma ai babu wanda ya fi ni jin dadin abin da ya faru a yau.”
Nabeeha ta dan runtse idanu. “Meye hakan?”
Humyrah ta yi dariya. “Ke dai bari. Ina ganin yadda Ya fawaaz ya dade a waje bayan na fito. Wallahi idan so yana da fuska, to fuskar Ya fawaaz ce yau.”
Nabeeha ta daure fuska. “Humyrah, ki bar wannan.”
Humyrah ta yi dariya. “Ai ba za ki iya musantawa ba, domin yanzu kowa ya san gaskiya. Yaya Fawaaz yana son ki, Nabeeha! Kuma ba yau ya fara ba. Abin da kawai ya rage shine—ke fa?”
Wannan tambaya ta tsaya a zuciyar Nabeeha, ta kasa amsawa.
Da safe, Fawaaz ya fita da wuri, ba tare da ya jira kowa ya tambaye shi ba. A lokacin da ya dawo daga aiki, yana cikin mota yana kokarin shiga gidan su, sai ya hangi Nabeeha a bakin kofar gida tana jiran abu kamar mai son fita.
Ya dan tsaya a gefe, yana kallonta kafin ya sauke glass na motarsa.
“wani wajen zaki?”
Nabeeha ta juya, ta gan shi, sai zuciyarta ta buga. Duk da jiya sun raba dare da tunani, yau kuma ganin shi a fili ya kara tayar da HANKALIn ta.
“Eh,” ta amsa a hankali.
Ba tare da ya yi wata-wata ba, ya bude mata kofar mota. Ta shiga, zuciyarta na bugawa da sauri.
Lokacin da ya fara tafiya, babu wanda ya fara magana. Sai shiru mai cike da fassara.
Daga bisani, sai Fawaaz