Gwaggo Hafsatu ta dago tana duban Fawaaz.
"Subhan'Allah... Dawuda, Kaga Zaytunah an aske gashin ta. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Waɗannan mutane da sukai wannan abu Ubangiji Allah ya saka muku Allah ya bi muku hakkin ku.. Gwara mu tashi mu tafi asibiti kafin gabatar da komai...Har a tabbatar da lafiyar su. Ina so mu rankaya asibiti, ko da babu wata matsala, A dai tabbatar."
Fawaaz ya kada kai yana amincewa. "Tohm gwaggo . Hakan yayi" ya fada a takaice.
"Subhan'Allah. Ai a hakan ma gwaggo an auna arziki. Ubangiji Allah yasa karshen wahalar kenan ... Bayaga haka babu wani abun na daban ko?" Cewar major general dawud. Yana duban hajia zaytunah.
Hajiya Zaytunah tayi hanzarin girgiza kanta da sauri ta Kuma ce,
"Babu wani abu na daga labari marar dadi. Sai dai duka da sukayi mana sun azabtar da mu sosai.. Duk kuwa da umarni ne daga wadanda suka turo su acewar su. Don dayan umarnin nema Allah ya tsare bai faru ba. Kusan akansa nema wasu daga cikin yan fashin suka bijere maganar shugaban su. Suka ketare suka kubutar da mu"
"Subhan'Allah Subhan'Allah..ai idan Allah yarda duk masu hannu acikin wannan abu zamu kamasu red handed. Shin wani abu ne wannan da basu kaiga aikatawa ba Allah ya takaita ku ka kubata?"
Hajia Zaytunah ta dubi major general dawud tana tunanin yadda zata fada. Don maganar batasan fadar tama saboda tsananin muninta,
Falo ya ɗauki shiru bayan da Major General Dawud ya yi tambaya mai nauyi,
"Zaytunah, me ya faru da ku?"
Gwaggo Hafsatu ta gyara zama a kujerarta, zuciyarta tana tafasa da fargaba. Nabeeha da Hammad kuwa sun natsu a gefen mahaifiyarsu, suna jiran jin yadda zata bayyana abin da suka fuskanta. Fawaaz yana gefe, yana kallon fuskar Hajia Zaytunah da idanun da ke cike da zurfin nazari.
A farkon fara magana, Hajia Zaytunah ta runtse idonta na dan lokaci, kamar wadda take kokarin tattara karfin gwiwa. Zuciyarta tana bugawa da karfi, wani irin tsoro da ba ta san yana ciki ba yana neman turnuke ta.
Sai ta bude idanu, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta soma magana da muryar da ke sanyi, amma mai nauyi.
"Sun kama mu... sun yi mana azaba fiye da tunanin dan adam," ta fara, tana jin yadda muryarta ke rawar jiki.
"Sun daure hannuwanmu da kafafuwan mu da igiya mai karfi... kamar wata dabba da ba ta da iko da jikinta. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani."
Duk wanda ke cikin falon ya zura mata idanu, babu wanda ya motsa.
Ta ɗauki wani numfashi mai nauyi, hawaye na taruwa a idonta. "Sun... sun aske min gashi. Ba don......"
Sai Kuma tayi shiruh ta kalli Gwaggo Hafsatu da Major General Dawud, idanunta cike da hawaye. Kamar tana sake jin raɗaɗin abin da suka fuskanta a hannun miyagun mutanen da suka kama su. Ta ɗan tsaya na wani lokaci, kamar mai tattara ƙarfin gwiwa, sannan ta ci gaba da magana.
"Sun kama mu a dare, babu wanda ya san inda aka kai mu. Sun daure hannuwan mu da kafafuwan mu da igiya mai ƙarfi, kamar wasu dabbobi da ba su da iko da jikin su. Sun toshe mana baki da zani don kada mu iya kiran wani. Munyi ƙoƙarin tserewa, amma igiyar da suka ɗaure mu da ita tana matse ƙasusuwanmu har ba ma iya motsawa.
"A lokacin da suka kawo Nabeeha da Hammad a gabana, zuciyata ta karye. Na ga yadda suka dinga dukansu. Hammad yana ihu yana kiran sunana, yana kuka, amma babu wanda ya ji shi. Idanunsa sun kumbura saboda dukan da suka masa. Nabeeha kuwa, ba zan taɓa mantawa da yadda wani daga cikin su ba ya taka ruwan cikinta..Sun yi ƙoƙarin raba ta da mutuncinta! Amma Allah bai nufa hakan ya faru ba!
Ta runtse idanu, hawayenta na sauka
"Nabeeha ta yi ta kokawa da karfinta, tana kuka tana ihu. A karshe, daya daga cikinsu ya daga hannu zai mare ta, amma wani daga cikinsu ya hana shi. Har yanzu, ban san dalilin da yasa ya hana ba, amma yana daya daga cikin dalilan da yasa bata fuskanci mafi munin abin da suka nufa ba."
Fawaaz ya matse hannayensa, jijiyoyin wuyansa sun fito. Idanunsa sun kada da tsananin fushi, amma bai ce uffan ba. Kawai yana saurara, zuciyarsa na tafasa.
Hajia Zaytunah ta ci gaba,
"Sun ci mutuncinmu da kalmomi, sun dinga zaginmu suna dariya. Sun ce babu mai kubutar pda mu, sun ce za su kashe mu a ranar da suke so. Amma Allah ya kawo mana agaji a hannun wasu da ba mu yi tsammani ba, wasu daga cikin su, wato su Gora da Bala."
Tana ambaton sunayen, sai Gwaggo Hafsatu ta ɗago kai da sauri. "Gora da Bala?"
"Eh, su ne suka taimaka mana. Duk da cewa suna cikin 'yan ta'adda, amma sun nuna jinƙai. Sun nemo mana abinci da ruwa. Suna boye mu daga sauran miyagun. A ƙarshe, su ne suka sassauta igiyoyin da suka ɗaure mu da su, har suka samar mana hanya muka tsere daga hannunsu."
Tana gama faɗin haka, sai ta sunkuyar da kai, tana jin kamar duk tsawon lokacin da suka shafe a hannun miyagun ya dawo da ita cikin wannan dakin.
Shiru ya biyo baya, amma shiru mai cike da nauyi. Kowa yana jin girman azabar da suka sha.
Fawaaz ne ya fara magana, cikin muryar da ke cike da ƙarar zuciya.
"Wadanda suka aikata wannan azaba ba za su tsira ba."
Major General Dawud bai ce komai ba, amma idanunsa sun nuna alamar hukunci. Ba zai bari su tsira ba.
Gwaggo Hafsatu kuwa ta rungume Hajia Zaytunah cikin kulawa da ƙauna.
"Alhamdullillah, Kun tsira da ran ku, Sannan baa yi Wa nabeeha wannan danyen aiki ba. kuma wannan shine abu mafi muhimmanci."
Haka dai suka cigaba da tattaunawa. Kafin daga bisani sukayiyyi wanka bayan sunci abinci suka dauro tsarki. Suka rama sallolin da basuyi ba .. sannan suka rankaya zuwa asibiti kamar yadda gwaggo tabada shawara.
A cikin motocin soja da ke rakiyarsu, suka isa asibitin cikin girmamawa. Likitoci da nas-nas sun riga sun shirya don karbar su, saboda Fawaaz da Major General Dawud sun tabbatar an sanar da su kafin isowarsu.
An fara da gwaje-gwaje na cikakken lafiya. An duba Hajia Zaytunah sosai, aka tabbatar babu wata matsala babba, sai dai radadin da ta ke ji a wurin da aka yanke mata gashin kanta. Don haka, likitocin suka yi mata karin ruwa don karfafa jikinta, sannan suka bata magungunan rage radadi.
Nabeeha da Hammad suma an yi musu gwaje-gwaje, aka tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya. Sai dai an musu allurori na kariya da magungunan antibiotics don hana kamuwa da wata cuta sakamakon wahalar da suka sha.
Gwaggo Hafsatu ta cigaba da nuna damuwarta har sai da likita ya tabbatar mata da cewa babu wata matsala.
Bayan an kammala komai, suka fito daga asibitin, kowa cikin kwanciyar hankali da godiya ga Allah. A cikin motocin da ke tafiya a nutsuwa, ana jin saukar zuciya a tare da kowa.
A zuciyar kowa, sun san cewa rayuwa za ta cigaba, kuma a wannan lokaci, sun san cewa akwai sabuwar fata da sabuwar soyayya da ke ci gaba da bayyana a zuciyoyinsu.
Duk da SIRRIN da ke tsakaninsu, akwai haske a gaban su.
Da zarar da motocinsu suka iso gida daga asibiti, sabuwar rayuwa ta soma fantsama cikin zuciyar kowa. Daga yanayin yadda Gwaggo Hafsatu ta sake rungume Hajia Zaytunah a lokacin da suka fito daga mota, har zuwa murmushin da ke fuskarta, ya nuna yadda take jin daɗin dawowarta gida cikin kwanciyar hankali.
"A yanzu, sai dai mu gode wa Allah," Gwaggo Hafsatu ta furta, tana kallon su Nabeeha da ke gefenta. "Kun ga, kowa ya dawo gida lafiya."
Wannan kalma ta sa Hammad ya saki murmushi yana jin wani irin nutsuwa yana ratsa shi. Duk wahalar da suka sha, sun samu nasarar komawa cikin iyalansu.
Nabeeha kuwa tana gefen mahaifiyarta, tana ta duba ta da kulawa. Tun daga asibiti har zuwa gida, ba ta dena tambayarta yadda take ji ba.
Fawaaz kuwa daga gefe yake, kamar kullum, yana kallon komai cikin nutsuwa da kamun kai. Bai ce komai ba, amma idanunsa sun nuna yadda zuciyarsa ke jin daɗin ganin kowa cikin farin ciki.
Da suka shiga falon, an sake jin daɗi a zuciyar kowa. Wurin ya cika da haske da kamshin turaren gida na kamfanin YERWA INCENSE AND MORE.. A gefen babban falon, manyan kujeru ne masu taushi da sanyin fata, suna ba da kwanciyar hankali ga wanda ya zauna a kansu.
Masu aiki sun taru suna murna, kowannensu na nuna farin ciki. Sun shirya kayan marmari da shayi mai zafi, don su samu nutsuwa bayan dawowarsu daga tafiya.
Daga nesa, motsin shigowar Major General Dawud. Da alama ya dade yana jiransu su dawo, saboda yana sanye da kaya masu sauki fiye da na jikinsa dazu, yana nuna cewa ya fi mayar da hankali ga tarbarsu a yau fiye da komai.
Da ya karaso, idanunsa suka fara sauka kan mahaifiyarsa. Daga nan sai ya dubi Hajia Zaytunah, wadda ke zaune kusa da 'ya'yanta. Kallon da ya yi mata ya nuna cewa yana jin tausayinta, amma ya fi jin daɗin ganin ta cikin koshin lafiya.
Ya numfasa kadan, sannan ya kalli su gaba ɗaya. "Mun gode wa Allah. Dukkanin ku kun sha wahala, amma Allah ya kawo mana sauki."
Hajia Zaytunah ta gyaɗa kai cikin jin daɗi. "Allah ya bar zumunci."
Gwaggo Hafsatu ta yi murmushi tana duban ɗanta. "Dawuda, zan sake cewa, mun gode maka. Kai da Fawaaz, da dukkan sojojin da suka bada gudunmawa wajen kubutar da yaran nan da mahaifiyarsu."
Ya girgiza kai cikin girmamawa. "Gwaggo na.., wannan aikina ne. Kuma na san duk wanda ke cikin wannan gida zai yi hakan idan da dama ta samu... Sannan sauran yan fashin da aka kama su da yardar Allah zamubi diddigin gano Wanda yasa suka aikata wannan abu. Sannan zamu hora su sosai zasu sha dukan sojoji sannan zamu dauki tsattsauran mataki akan su inn shaa' Allah"
Fawaaz ya gyada kai kadan. Duk da cewa bai fiye magana ba, yana jin irin godiyar da kowa ke yi a ransa.
🎀🎀
Bayan wannan rana, gidansu ya cika da kwanciyar hankali da farin ciki. Duk da cewa akwai abubuwan da ba a gama fahimtarsu ba, amma babu shakka, sun shiga wani sabon mataki na rayuwa. Daga bangaren Fawaaz kuwa, da sauran sojoji karkashin Dawud Mafia suna ci gaba da aiki don tabbatar da cewa babu wata barazana da ka iya sake samun su.
A gefe guda kuwa, akwai sabbin soyayyar da ke tasowa a hankali. Duk da cewa Fawaaz bai taɓa furta wani abu ba, amma yadda yake kulawa da Nabeeha ba boyayyen abu ba ne. A wasu lokuta, idan Nabeeha ta tashi daga zaune, idanunsa kan bita har ta fita daga falo. Idan kuma tana kusa da mahaifiyarta, yana lura da yadda take yi mata kulawa da so.
A ranar da Gwaggo Hafsatu ta lura da hakan, sai ta saki murmushi tana gyara zaninta. Ta kalli Nabeeha da ke gefen mahaifiyarta sannan ta kalli Fawaaz.
"Allah ya shiga cikin lamuran mu. Ya zaba mana abunda yafi alkhairi ," ta furta a hankali, tana jin cewa lokaci ne kawai zai nuna yadda za a shirya kaddarar da ke tafe.
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
**
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 18_
Koda suka koma gidan su bayan sun bar gidan alhaji Uzairu , Hajiya Rumanah ta ajiye hijabinta sannan ta nufi sashen Alhaji Amiru. A tsaye ta tarar da shi a kan sallaya, yana karanta azkar cikin nutsuwa. Ta dan tsaya daga nesa tana kallonsa, sannan ta nisa da kyau kafin ta karasa kusa da shi.
"Alhaji," ta kira shi da wata murya mai rauni.
Ya dago ya dubeta, ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta sunkuya ta zauna a gefen kujerar dake sashen nasa, sannan ta ci gaba da magana cikin kissa da kisisina.
"Gabana yana ta tsananta bugawa. Har yanzu ba mu da wani bayani a kan Hajiya Zaytunah da yaranta?"
Ta dan yi shiru kadan, tana nazarin fuskarsa. Alhaji Amiru ya ajiye tesbihinsa, yana me gyara zamansa. Fuskar nan tasa da ba a cika fassara ainihin abinda ke cikinta ba, ya dauki lokaci kafin ya dago ya kalleta.
"Me ya sa kike tambayar hakan a yanzu, eh rumanah?" Ya tambaya cikin yanayi mai cike da taka tsantsan.
Hajiya Rumanah ta dan gyara zama, tana wasa da zoben hannunta.
"Alhaji, shekara da shekaru muka dauka ba tare da sanin inda suka shiga ba. Kuma kai da kanka ka ce a lokacin ba sai mun ci gaba da bincike ba. Amma yanzu... yanzu abubuwa sun fara daure min kai. Ba ka ganin lokaci yayi da ya kamata mu san halin da suke ciki?"
Alhaji Amiru ya zuba mata ido, yana nazarin ta da kyau. A fili yana jin tsananin nauyin wannan tambaya, domin kuwa akwai SIRRIN da bai son ya bude.
Ya daure fuska, sannan ya ce cikin kakkausar murya,
"Rumanah, ki daina yawo da tunani mara amfani. Idan lokaci yayi, Allah zai bayyana komai."
Hajiya Rumanah ta runtse idanu, tana jin wani yanayi na takaici yana ratsa zuciyarta. A ranta, ta san akwai wani abu da Alhaji Amiru bai fada mata ba, amma ba ta da ikon matsa masa don jin ainihin gaskiyar lamarin.
Bayan Hajiya Rumanah ta tashi ta bar sashen nasa, Alhaji Amiru ya jingina da kujerarsa, yana kallon sararin dakin kamar mai neman amsar wata tambaya. Ya lumshe idanu, yana jin nauyin tunanin da maganganunta suka jefa shi ciki.
"Har yanzu ba mu da labarin Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta?"
Wannan tambaya tana da nauyi a zuciyarsa. Tun kafin ta tambaye shi, wannan batu yana damunsa, amma yana kokarin rufe shi da tunanin cewa lokaci ne kawai bai kai ba. Amma me yasa Hajiya Rumanah ta kawo maganar yanzu? Shin tana jin wani abu ne?
Ya sauke ajiyar zuciya. Idan har za a waiwaya baya, babu shakka, Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta sun bace a duniya kamar ba su taɓa wanzuwa ba. Bai taba ganin wata alama da ke nuna inda suka shiga ba, kuma babu wanda ya taba kawo musu wata kwakkwarar magana a kansu. Amma zuciyarsa tana tsananta bugawa a duk lokacin da aka ambaci sunanta.
A wani bangaren zuciyarsa, yana jin wani mugun nauyi. Yana sane da irin matsin da Zaytunah ta shiga kafin tafiyarta. Yana sane da halin da ta bar gidan kanin nasa a ciki, da irin yadda abubuwa suka rikice mata. Amma ko da yake, hakan ba ya nufin yana son ci gaba da wannan bincike da Hajiya Rumanah ke kokarin tunzura shi akai.
Ya dafe goshinsa, yana jin wani iri. Idan har Zaytunah tana raye, ina take? Shin tana can tana rayuwa cikin kunci da wahala, ko kuwa lokaci ne kawai ya jefa ta cikin duhun da babu mai iya ganinta? Kuma idan har tana raye, shin za ta taba yafe musu abin da ya faru?
Ya gyara zamansa, zuciyarsa na sake nauyaya. Idan da akwai wani abu daya ke tsoro a rayuwarsa, to yana tsoron wani lokaci ya zo da ahalin zasu fuskanci Zaytunah. Ya san idan hakan ta faru, ba zai iya boye duk wata damuwarsa ba.
🎀🎀🎀🎀
A tsakar dare, dakin Hajiya Rumanah ya dauki shiru, sai karan AC da ke busa iska a hankali. Ta juyi a kan gadonta, zuciyarta cike da damuwa, amma har yanzu barci ya gagara daukarta.
Wayarta ta fara vibration, sai karar shigowar kira ta ratsa cikin dakin. A firgice ta bude idanu, zuciyarta na harbawa da sauri kamar mai shirin tsallake KIRJIN ta. Ta kai hannu ta dauki wayar daga gefen filo, ba tare da ta duba sunan mai kiran ba, ta amsa cikin murya mai sanyi, kamar wadda aka taso daga mafarki.
"Waye?" Ta tambaya, muryarta na nuna alamun rashin kwanciyar hankali.
A dayan bangaren, an dan yi shiru na ‘yan dakiku kafin wata murya mai cike da tsoro da gaggawa ta karanto mata,
"Hajiya... Nine! Na tsere! Su duka sun shiga hannu! Tawagar fashi an tarwatsa su, kuma wadanda kika saka a sace, sojoji sun kubutar da su!"
Zuciyarta ta harba da karfi, hannunta na tsananta zufa. Ta dan daka tsalle daga kwanciyarta, tana jin wani irin jiri na neman dibarta.
"Me kake nufi? Su waye suka shiga hannu?" Ta tambaya, cikin wata irin murya da ta kasa boye gigicewarta.
"Yan uwana, duka an kama su! Ni kadai ne na tsira, kuma na bar garin gaba daya. Hajiya, na yanke shawarar sanar da ke, don ki san cewa shirin ya rushe. Mutanen da kika saka a sace, sun kubuta!"
Wayar ta kubce daga hannunta, ta fado a kan gadon. Idanunta suka firfito waje, zuciyarta na bugawa kamar za ta tsage KIRJIN ta ta fito. Ji take tamkar iska ta daina ratsawa cikin huhunta.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un...!" Ta furta a hankali, hannunta na kerma.
Ta kama kanta da duka hannayenta, tana jin yadda gumi ke keto mata kamar wadda aka tsoma cikin ruwa. Asirinta yana kokarin tonuwa! Idan har sojoji sun kama su, babu shakka za su tona mata asiri!
Ta dauki wayarta da sauri, tana kokarin sake jin cikakken bayani, amma sai ta fahimci cewa mutumin ya kashe wayarsa. Ta danna lambar a gaggauce, amma ba ta shiga.
Cikin tashin hankali, ta mike daga gadon, zuciyarta na lugude kamar ana dukan ganga a cikinta. Ta fara tafiya a rude a cikin dakin, tana rikita kanta da tunani.
"Me zan yi? Ya Allah, me zan yi?"
Hannu ta daura a kanta, tana jin tamkar duniyar ta ruguzo mata. Idan aka kama ta, menene makomarta? Me Alhaji Amiru zai ce? Ya za a yi idan wannan magana ta fito fili?
Ta durkushe a kan kafafunta, jikinta na kerma tamkar wadda zazzabi ya rufe. Idan wani ya ganta a wannan lokaci, babu shakka zai dauka cewa ta haukace!
Tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi, yana kokarin tarwatsewa. Ashe, yau ce ranar da asirinta zai tonu?
Wayar ta ta Kara dubawa tana Kiran ainihin number mutumin daya hadasu da yan fashin... Ta sanar masa komai tamkar suna ganin juna yadda take