KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   15 / 40

42K to 45K   out of 119.4K words

da zai fara da su. Ita kuwa Nabeeha, hankalinta ba kan wayar yake ba – tana can tana sake tunanin Fawaaz da sakonnin da ya turo mata.

Muhammad ya numfasa. "Nabeeha... I love and miss you soo much"

Ta dan runtse idanu. Ta san abin da zai fada.

"Nabeeha, ina kaunarki."

Zuciyarta ta buga, amma ba don maganar Muhammad ba – sai don tunanin yadda Fawaaz ya kasa furtawa haka.

"Kullum dada kewarki. Nake, tamkar na janyo ranar bikin mu haka nakeji, Ban san me yasa ba, amma tun farkon haduwarmu, na ji wani abu na daban a kanki. Ina son ki, Nabeeha, da gaske nake."

Shiru ta yi, ba ta ce komai ba. A zahiri, ta ji kalmomin Muhammad, amma ba su shiga zuciyarta ba. Tunani kawai take—da ace Fawaaz ne ke furta mata hakan a baki, ba kawai a rubuce ba…

Yar wahalaaaaa🤭😏

Muhammad ya dan yi murmushi. "Kin yi shiru?"

Ta numfasa. "Ba komai."

"Ba ki ce komai ba akan abin da na fada."

Ta dafa goshinta. "Muhammad… Kai na ke ciwo. Yi.hakuri"

Ya yi shiru na wani lokaci. "Babu matsala. Amma a kalla ki san cewa na fadi abin da zuciyata ke ji. Kuma ba zan yi nadamar fada ba...Allah yakara miki lafiya da nisan kwana mai albarka amin"

Ta dan yi murmushi kadan. "Nagode."

Sun dan kara hira kadan, sannan suka yi sallama. Ta mika wa Humayrah wayarta, sannan ta koma ta kwanta, zuciyarta na kara cike da tunanin Fawaaz.

"Me yasa ya kasa furtawa a baki?"

"Me yasa ya ke boye abin da yake ji?"

"Ko kuwa yana fargabar abinda zai biyo baya?"

Watan wata rana… wata rana zai iya furtawa?

Bayan tattaunawarta da Muhammad, Nabeeha ta ajiye mikawa humyrah wayarta,. Sai dai, ko da suka yi sallama, ba kalmomin Muhammad take tunani ba—sai Fawaaz.

"Me yasa ya kasa furtawa a baki?"

Tana kwance kan gadonta, hannayenta sun dunkule a kirjinta, zuciyarta tana gudu da sauri. Ta rufe idanuwanta da karfi, tana kokarin korar tunanin da ya mamaye ta. Amma hakan bai yiwu ba.

Tunanin Fawaaz ya ci gaba da dawowa. Idanunta na kulle, ta fara tuno lokacin da ta fara lura da sauyin da ya faru da shi—lokacin da ya fara kallonta da wata irin kallo mai nauyi, lokacin da ta fara samun sakonninsa masu dauke da kalmomin da suka fi yadda yake iya furtawa.

"Ba zan iya furtawa a baki ba… amma ki sani, zuciyata ta yarda da ke."

"Ke ce abin da nake bukata, ko da kuwa duniya ba ta fahimta."

Tana da tabbacin cewa Fawaaz yana da wata irin soyayya a gare ta, amma ya kasa furtawa a fili. Me yasa? Shin miskilancinsa ne ke hana shi? Ko kuwa wani abu ne da ba ta sani ba?

Ta bude idonta, tana duban rufin dakin. "Idan har yana sona da gaske, me zai hana ya fada?"

Tana cikin wannan tunani ne sai aka turo kofar dakin.

"Nabeeha!"

Ta dago da sauri. Humayrah ce ke kokarin shigowa, fuskarta cike da murmushi.

"Mene ne kuma?" Nabeeha ta tambaya, tana zuba mata harara.

Humayrah ta zauna a gefen gadon, tana yatsina fuska. "Haba dai, ke kam. Me yasa kika yi kamar ba kya son magana da Muhammad?"

"Ban ce ba na son magana da shi ba."

"Amma ba ki nuna sha'awar tattaunawar ba."

Nabeeha ta dube ta da murmushin gefen baki. "Ke dai bari kawai, ina cikin tunani ne."

Humayrah ta mike tana kallonta. "Tunanin wani kike ko?"

Nabeeha ta zabura. "Me yasa kika ce haka?"

Humayrah ta harare ta. "Ai a yanzu haka, koda ace wani zai baka labari mai dadi, amma kana da wani abu a zuciyarka, ba za ka ji dadin labarin ba."

Ta yi shiru, tana nazarin maganar Humayrah. Ko da yake ba ta son yarda da hakan, amma akwai gaskiya a ciki.

"Ke dai bari kawai," ta ce, tana kokarin kawar da batun.

Humayrah ta yi dariya. "To Allah ya kyauta. Amma dai Muhammad na nan, yana jiranki ki yanke hukunci."

____

A gefe guda, Fawaaz yana zaune a kofar falonsa, cikin duhun dare. Ya jingina da kujerar da yake zaune a kai, hannunsa rike da wayarsa. Ya kafe screen din wayar da idanu, yana nazarin sakonnin da ya tura wa Nabeeha.

Ya sani. Ya sani cewa bai dace ya ci gaba da boye soyayyarsa ba. Ya sani cewa ba zai iya ci gaba da kamewa ba, amma me zai yi?

Zuciyarsa na cike da tsoro. Ba tsoron soyayya ba—tsoron abin da zai biyo baya.

Yana jin zuciyarsa na dukan abu guda. Idanunsa sun kada kadan saboda tunani da damuwa.

A can can, zuciyarsa na tambayarsa,

"Za ka ci gaba da ɓoye gaskiyar zuciyarka?"

"Ko kuwa lokaci ya yi da za ka bayyana?"

Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin daren yana yi masa nauyi.

Numfashin Nabeeha ya tsaya cak. "Yaa Fawaaz?"

Muryarta ta fita da sanyi, tamkar ba ita ta yi magana ba.

A daya bangaren, shiru ne. Sai daga baya ta ji numfashinsa ya sauka kadan. "Eh, .. Zan iya ganinki?"

Wata irin kasala ta shige ta. Hannunta ya yi sanyi, zuciyarta na bugawa kamar zata fado daga kirjinta.

Me zai fada mata?

Meyasa yake neman ganinta a wannan dare ta intercom din dakin ta?

Tayi shiru, zuciyarta na kokarin tattaro amsar da zata bashi.

"Ina kusa da balcony. Idan har ba damuwa, ki fito."

Zuciyarta ta tsananta bugawa.

Shin ta fita?

Shin da gaske zai iya furtawa a yau?

Tana cikin wannan tunani ne sai aka turo kofar dakin. Humayrah ce.

"Ke! Waye haka yake magana da ke da daddare?" Ta tambaya, tana kokarin karbar wayar.

Da sauri Nabeeha ta kashe kiran, zuciyarta na harbawa. "Ba kowa."

Humayrah ta kalle ta da mamaki. "Ba kowa kuma? To me yasa kika kashe wayar da sauri?"

Nabeeha ta girgiza kai, tana kokarin boye rikicin zuciyarta. "Ki daina bincike mana."

Humayrah ta tabe baki. "To ai da gani akwai abu. Ko dai Muhammad ne ya kira?"

"A'a kuma ta intercom? ." Nabeeha ta fada da sauri, tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da dukan abu guda.

Humayrah ta yi shiru, sannan ta kalli gefenta. "Da gaske dai babu matsala?"

Nabeeha ta yi kokarin murmushi. "Eh, ki kwantar da hankalinki."

Amma ita kanta ta san cewa hankalinta ya tashi.

Ta mike daga gadon, zuciyarta na tafasa. Shin ta fita ta hadu da Fawaaz?

Ko kuwa ta share shi kamar yadda yake son boye soyayyarsa?

Fawaaz yana tsaye a jikin motarsa, hannayensa a cikin aljihu. Zuciyarsa na tafasa, yana jiran amsar Nabeeha.

Me zai ce idan ta fito?

Meyasa bai iya furtawa a da ba?

Ya sauke numfashi. "Yau, dole zan fada."

Idan har ba zai iya furtawa a yau ba, to zai iya rasa ta har abada.





_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
**KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :23*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb


__

A tsakar dare, Fawaaz yana zaune a kan kujerar barandar gidan, hannunsa na jingine da gefen kujera, yana kallon sararin samaniya. Hasken wata yana haska filin gidan, yana ba da nutsuwa, amma zuciyarsa ba ta da nutsuwa ko kadan.

Me yake yi da zuciyarsa haka?

Ya rike goshinsa a hankali. Duk yadda ya so ya boye abin da ke ransa, ya kasa.

Yana son Nabeeha.

Bai san yadda zai iya rayuwa ba tare da ita ba.

Yana shakar numfashinta idan tana kusa.

Idan ta wuce ta gefensa, wani kamshi na musamman ke ratsa shi. Bai san ko menene ba, amma yana tabbatar da cewa ko a cikin taron mutane dari, zai iya gane Nabeeha.

Komai nata daban ne.

Tana da nutsuwa, tana da sanin ya kamata, tana da ilimi, tana da hankali fiye da yadda yawancin mata ke da shi.

Ba kawai kyawunta ba ne ya ke ja shi gare ta, dabi'arta ce, hankalinta, tausasawarta.

Ya yi murmushi a hankali. Ta na da tausayi.

Yana iya tuna yadda take tausaya wa kowa, har da wadanda ba su san tausayin wasu ba.

Ya kan ga yadda take rike da addininta, yadda take nisantar abin da bai dace ba. Ba wai tana takura wa kanta ba, amma tana da tsoron Allah.

Wacce mace ce kamar haka?

Duk da cewa tana da karancin shekaru, ta fi kowace mace da ya sani.

Yana sonta. Yana son ta fiye da yadda ya taba son wani abu a rayuwarsa.🥹

Amma yana tsoron furtawa.

Ya jima yana tunanin hakan. Idan ya fada mata, me zai faru?

Shin zata karba?

Shin zata fahimce shi?

Shin zata yi dariya kawai ta bar shi yana jin zuciyarsa na kuncewa?

Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin bugun zuciyarsa na tsananta.

Nabeeha tana zaune a gefen gadonta, tana rike da wayar Humayrah da ta ajiye a gefenta. Hannunta da sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri.

"Ya fawaaz..."

Shin da gaske yana son ganinta?

Me zai ce?

Meyasa yake ta ɓoye abu a zuciyarsa?

Tun da ya fara turo mata sakonni a rubuce, zuciyarta ta daina samun sukuni.

Tana son sanin dalilin da yasa yake haka.

Idan har yana da abin da yake ji a zuciyarsa, me zai hana ya fada?

Tayi shiru, tana jin zuciyarta na kokarin bata amsa,

"Ko kuwa miskilancinsa ne ke hana shi furtawa?"

Ta rike hannunta da hannu guda, tana jin yadda jikinta ke daukar zafi. Tana jin dadin yadda Fawaaz yake kula da ita, duk da cewa bai taba cewa tana da muhimmanci a gare shi ba.

Sai dai zuciyarta tana jin hakan.

Tana jin yadda idanunsa ke magana idan suka hada ido.

Tana jin yadda shiru yake da ma'ana idan suna tare.

Tana jin yadda kalmominsa ke bayyana da sauri a rubuce, amma ba zai iya fada da baki ba.

Tana jin yadda yake tsoron furta abu a bakinsa.

Tana jin yadda ya rasa yadda zai fada mata abin da zuciyarsa ke rayawa..

Ta lumshe idonta a hankali. Ta fahimci abu daya.

Fawaaz yana sonta.

Amma ya kasa furtawa.


Fawaaz ya tsaya yana kallon wayar da ke hannunsa. Sabuwar waya ce mai kyau da tsada, kirar zamani, wadda ya siya da sabon SIM a ciki. Tun kafin ya karɓi wannan matsaya, ya sha gwagwarmaya da zuciyarsa. Ya dade yana tunani, yana shan shakkar ko hakan daidai ne. Amma a ƙarshe, ya yanke shawara, yanzu lokaci ne na aikatawa, ba tunani ba.

Ya ɗan gyara zaman rigarsa, ya kalli agogo. Wajibi ne ya kammala wannan lamari cikin nutsuwa, batare da wani yayi tunanin akwai wani abu daban ba.

A hankali ya kira Nabeeha, murya a daidai misali.

"Ina son ganinki a waje," kawai ya ce mata, ba tare da wata sharhi ba.

**A lokacin da ta fito, ya jingina da motarsa, hannayensa a cikin aljihu, idanunsa na kallon gefe tamkar ba shi ya kira ta ba. Nabeeha ta dan yi jinkiri tana nazarinsa, sannan ta karasa kusa da shi. Tana gayshe da shi..

"Ga wannan."

Bai iya kallonta ba yayin da ya miƙa mata wayar. Murya a dakile, kamar yana bayar da wani abu mara muhimmanci.😂

Nabeeha ta kalli wayar da mamaki. Idanunta sun cika da alamar tambaya.

"Wannan fa?"

Fawaaz bai amsa ba. Ya ɗan juya gefen fuskarsa, yana kallon wata hanya kamar wanda ba ruwansa da abin da ke faruwa.

"Ta waye.. ko tawa ce?" Ta tambaya a hankali, tana jin kamar mafarki take yi.

Ya numfasa kadan, yana cigaba da kallon gefe. "Ee."

Shiru ya biyo baya na ƴan dakiku. Sai da zuciyarta ta harba da wani yanayi mai rikitarwa.

"Nagode Allah ya Saka maka da alkhairi amin," ta ce cikin sanyin murya.

Bai amsa ba. Bai ce komai ba. Kawai ya jinjina kai kaɗan, sannan ya juya ya buɗe motarsa ya shiga fice daga gidan.

Yana barin wajen, zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai ce mata komai ba. Bai iya furtawa ba. Amma ya san, daga yanzu, zai iya jin ta kusa da shi... ko da kuwa ta hanyar sakonni ne kawai.

Nabeeha ta tsaya a wajen, hannunta rike da wayar da ya bata. Kamar mafarki ne, kamar ba gaske ba. Idanunta sun cika da tambayoyi, amma wanda ya dace ya amsa su, tuni ya tafi.

Ta lumshe idanu, zuciyarta na harbawa. Ba wai sayen wayar bane matsalar amma yadda ya bayar. Yadda bai ce komai ba, yadda ko murmushi bai yi ba, yadda ya maze kamar ba wani abu mai muhimmanci ya aikata ba.

Wayar ta rike a tafin hannunta, tana jin nauyinta fiye da yadda ta kamata. A hankali ta shaka iska, sannan ta juya zuwa cikin gida, zuciyarta na ji kamar tana tafiya da wani SIRRI.

***

Fawaaz yana tuƙi, amma hankalinsa ba a kan titi yake ba. Bai masan dalilin futar sa daga gida ba, Ba don yana da horo ba, da tuni ya samu matsala. Yana ta kici-kicin tunanin abinda ya aikata.

Me yasa bai iya cewa komai ba?

Me yasa ba zai iya cewa "na siya miki ne domin dubun kaunar ki danake da tsananin kwadaituwa da son jin muryar ki.." ba?

Bai gama amsa wa kansa wadannan tambayoyin ba, sai wayarsa ta fara ƙara. Ya duba—Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad.

Zuciyarsa ta harba. Sai dai ko da haka, ya tsare fuska kamar ba komai.

A hankali ya ɗaga, yana kokarin tabbatar da cewa muryarsa ba zata nuna wani motsin rai ba.

"Hello," ya ce a dakile.

Shiru daga dayan bangaren.

"Yaa Fawaaz..." Ta ambaci sunansa a hankali, kamar mai jin nauyin magana.

"Na'am," ya amsa, har yanzu ba tare da ya nuna wata alama ba.

"Ba ka gaya min me yasa ka siya min waya ba."

Sai da ya lumshe idanu kafin ya bude su a hankali. Bai san me zai ce ba.

"Saboda ina so ki dinga samun damar magana da kowa cikin sauki," ya ce, ba tare da ya yi tunani sosai ba.

Shiru.

"Yaa Fawaaz," ta sake kiran sunansa, murya a kasalance.

Ya ji kamar tana son tace wani abu. Kawai sai ya danyi ajiyar zuciya. "Nabeeha, ki yi amfani da ita. Hakanan."

Daga nan ya katse kiran.

Ya ajiye wayarsa a gefen kujera, ya dan tsare numfashinsa na ƴan dakiku. Bai san dalili ba, amma zuciyarsa na bugawa da wani iri.

Ya riga ya aikata. Kuma ko da kuwa bai fadi ba, ya san zata fahimta... ko ba yanzu ba, wata rana.



_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :24*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb


__

Nabeeha ta kalli wayar a hannunta, zuciyarta cike da tunani. Kalaman Fawaaz sun sake dawo mata da karfi,

"Nabeeha, ki yi amfani da ita. Hakanan."

Hakanan? Ta girgiza kai a hankali. Duk da miskilancinsa da kamun kansa, Fawaaz ba mutum bane da zai bada kyauta haka kawai. Wani abu ya sa shi yin haka, amma bai iya furtawa ba.

Ta lumshe ido, zuciyarta na bugawa da wani iri. Me yasa Fawaaz yake haka? Me yasa bai iya cewa komai kai tsaye ba? Me yasa yake boye komai a karkashin miskilancinsa?

***

Bayan kwana biyu, Nabeeha ta saba da sabuwar wayarta. Sai dai har yanzu, bata daina mamakin Fawaaz ba.

Tun daga lokacin da ya bata wayar, bai sake magana da ita ba. Kamar yadda ya saba, sai dai idanunshi da take ji kamar suna bin ta a duk lokacin da suke tare da kowa.

Wannan dare, tana dakin ta tana duba wayar. Bata san dalili ba, amma sai da ta shiga sakon ta na WhatsApp ta fara neman lambarsa. Sai ta tsinci kanta da kallon chat dinsu.

Kusan duk sakon da ya taba turawa yana da kamewa. "OK."
"Na gani."
"Zan duba."

Ko da wasa bai taba cewa wani abu mai yawa ba. Sai dai a tsakanin wadannan sakonnin masu takaitaccen lafazi, tana jin akwai abu da yake boyewa.

A hankali ta zura yatsarta ta rubuta,

"Yaa Fawaaz, nagode."

Ta aika, tana jin bugun zuciyarta yana karuwa.

Tana shirin kashe wayar, sai ta ga alamar typing. Zuciyarta ta tsaya cak.

Daga nan, sai sakonsa ya shigo.

"Ba komai."

Saukakken kalma ce. Amma tana jin kamar akwai wani nauyi tattare da ita.

Ta cije leɓe. Hannunta na rawa kaɗan, ta sake rubuta wani sako.

"Me yasa ka siya min ita?"

Sai shiru. Babu alamar typing. Babu komai.

Duk da haka, ta tabbata ya gani. Kuma ta tabbata yana ji kamar yadda take ji.

Tana ajiye wayar a kan filo, zuciyarta cike da tambayoyi da ba ta da amsarsu.

Fawaaz yana son boye kansa. Amma ita, tana jin kamar lokaci na zuwa da zai fuskanci zuciyarsa, ko da kuwa da kalmomi masu sauki ne.

Zuciyar da Ba Ta Magana

Fawaaz yana kwance a gadonsa, wayarsa a hannu, yana kallon sakon Nabeeha.

"Me yasa ka siya min ita?"

Zuciyarsa ta harba, amma bai motsa ba. Bai rubuta komai ba. Bai san me zai ce ba.

Me zai ce? "Saboda ina son ki"?
Hakan ba zai taba fita daga bakinsa ba.

Ko "Saboda ina kaunarki"?
Ai ma ya kasa furtawa ga kansa, balle kuma gareta.

Hannunsa ya kara matse wayar. Bai taba jin kansa haka ba. Bai taba jin tsoron furta abu ba kamar haka. Amma ita, ta sanya shi jin wani yanayi da bai saba da shi ba.

Sai ya kashe wayar, ya ajiye a gefensa, yana jin nauyin zuciyarsa.

***

A rana ta gaba, sun hadu a farfajiyar gidan. Kamar yadda aka saba, Fawaaz yana zaune ne yana duba laptop dinsa, yana duba wasu bayanai na aikin sa.

Nabeeha ta karaso, hannunta rike da wayar da ya bata.

A hankali ta tsaya a gabansa, tana kallonsa.

"Fawaaz."

Ya dago ido, fuskarsa kamar ba shi ya jiya sakonta ba jiya.

"Me yasa ka siya min ita?" Ta sake tambaya, kamar yadda ta rubuta a sakon WhatsApp.

Shiru. Ya kalleta, amma ba tare da ya furta komai ba.

Ta sauke ajiyar zuciya. "Idan ba ka son fada, ba komai. Amma na gode."

Ta juya da niyyar barin wajen.

Amma kafin ta taka mataki na biyu, sai ta ji muryarsa—mai sanyi, mai nauyi, wadda ta sa numfashinta tsayawa.

"Saboda na san wata rana, zan so jin muryarki... ko da kuwa ba za ki taba ji na na magana ba."

Ta tsaya cak, ta juyo da sauri. Idanunta suka sauka a kansa, amma har ya riga ya sunkuyar da kai, yana sake maida hankalinsa kan laptop dinsa, kamar ba shi ya furta kalmomin ba.

Zuciyarta ta harba. Ta bude baki da niyyar cewa wani abu, amma ba ta san me zata ce ba.

A karo na farko, Fawaaz ya bar zuciyarsa ta yi magana. Ko da kuwa a takaice ne.

Kuma ita ta fahimta. Ta fahimci komai.

______

Dakin shiru ne. Babu komai sai kiran iskar dare daga waje da kukan agogon bango yana tafiya a hankali.

Fawaaz yana kwance a gadonsa, hannunsa daya a dunkule,

15 / 40