ya kalleta da ido mai zurfi. “Nabeeha.”
Ta juyo tana kallonsa.
Ya dauke idanunsa daga hanya ya sauke a kanta. “Jiya na kwana ina tunani.”
Ta hadiye yawu, ba tare da ta iya cewa komai ba.
Ya sauke numfashi. “Kin ce ba za ki bar zuciyata ita kadai ba.”
Ta gyada kai.
Ya dan yi murmushi, sannan ya jefa tambaya wacce ta tsaya mata a zuciya kamar an rubuta da zinariya.
“Amma kin san dalili?”
Zuciyarta ta buga, amma ba ta da amsar da zata bashi.
Shiru ya biyo baya.
Shi kuwa Fawaaz, sai ya mayar da hankalinsa ga hanya, amma da alama zuciyarsa da tunaninsa duk suna kan ita Nabeeha.
A ransa, yana jira ta gane kanta. Amma zai iya jira? Hakan ne tambayar da bai da amsar sa.
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:54_
Nabeeha ta dan lumshe ido, zuciyarta na bugawa da sauri. Tambayar Fawaaz ta tsaya mata a zuciya, kamar sautin da ya tsaya a kunne ba tare da ya fita ba.
“Amma kin san dalili?”
Tayi shiru, ta kasa amsawa. Ba don bata da amsar ba, sai don bata san wacce ta dace da furta ba. Shin yana nufin yana son jin idan soyayyarsa tana da amsa daga zuciyarta? Ko kuwa tambayarsa wata hanya ce ta tabbatarwa kansa cewa ba shi kadai yake tafiya a cikin wannan yanayi ba?
Shi kuwa, yana kallonta daga gefen ido, yana jiran ta ce wani abu. Amma babu komai.
Daga karshe, sai ya sauke numfashi a hankali. “Ba sai kin amsa yanzu ba.”
Ya mayar da kallonsa ga hanya, yana ci gaba da tukinsa da nutsuwa. Amma zuciyarsa bata da kwanciyar HANKALI. Ita kuwa Nabeeha, sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi na dogon tunani.
..
Bayan sun isa kofar gidan Humyrah, saboda shirye shiryen presentation na term paper da zasuyi na makaranta, Fawaaz ya tsaya yana kallon agogon hannunsa.
“Kar ki daɗe,” ya fada a hankali.
Nabeeha ta juya, tana kallonsa da fuskarta a dan kame. “Me zai hana ka shiga?”
Ya girgiza kai. “Ba zan tsaya ba. Amma zan jiraki anan.”
Ta kalli yadda ya jingina bayansa da kujerar mota, hannayensa rike da sitiyari, yana kallon hanyar gaba. Yadda yake kokarin gujewa ido da ita, ya sa ta fahimci cewa lallai yana cikin tunani mai zurfi.
Da wannan tunanin a ranta, ta sauka daga motar, ta shige gidan.
Humyrah na ganin Nabeeha ta shigo sai ta kama hannunta, ta ja ta cikin falon. Wani murmushi ne a fuskarta wanda ke nuna cewa tana jin daɗin abinda ke faruwa.
“Ina yayana?” Ta tambaya da tsokana.
Nabeeha ta daure fuska. “Yana waje, yana jirana.”
Humyrah ta ja tsaki. “To shi kenan. Amma kin san me?”
Nabeeha ta dan kalleta. “Meye?”
Humyrah ta saki murmushi. “Tun shekaru da yawa nake da wannan zaton. Sai dai yaw Fawaaz ba mutum bane mai son bayyana zuciyarsa. Amma yadda yake kula da ke, yadda yake tsare ki fiye da kowa… hakan bai taba barin shakku a zuciyata ba.”
Ta dan tsagaita, sannan ta dan matsa kusa da ita.
“Kin san mene ne?”
Nabeeha ta girgiza kai.
“Soyayya ba wai sai an faɗa take bayyana ba. Wani lokaci, ana iya gani a cikin ayyukan mutum.”
Nabeeha tayi shiru, tana jin yadda maganganun Humyrah ke ratsata.
Daga nan suka dan taba hira na ‘yan lokuta, sannan Nabeeha ta mike tsaye.
“Zan tafi.”
Humyrah ta harare ta. “Ai nasan bazaki jima ba. Idan naji ance kin daɗe, lallai zan zo na ja kunnenki.”ta karasa tana gwada muryar fawaaz.
Suka yi dariya tare, sannan Nabeeha ta fita daga gidan.
Bayan ta fita, ta hango Fawaaz yana tsaye a gefen motarsa. Hannayensa sanye cikin aljihunsa, yana kallon sama kamar mai nazarin taurari.
Tana isowa, ya juyo ya kalleta. Babu tambaya a idanunsa, amma akwai abu mai yawa a cikinsu.
Ya bude mata kofa, ta shiga. Shima ya shiga, sannan ya tayar da motar.
Sai da suka fara tafiya na wasu mintuna kafin yayi magana. “Kin yi sauri.”
Nabeeha ta dan juyo tana kallonsa. “Ka ce kada in daɗe.”
Ya saki murmushi, yana mayar da hankalinsa kan hanya. “Haka ne.”
Shiru ya biyo baya. Amma shiru ne mai dadi—mai dauke da wata irin nutsuwa.
Can cikin tafiya, sai ya dan rage gudun motar.
“Nabeeha.”
Ta juyo tana kallonsa.
Ya dan sauke numfashi, sannan ya jefa tambaya wacce ta kara sa bugun zuciyarta ya tsananta.
“Idan har ba za ki bar zuciyata ita kadai ba, shin hakan yana nufin zuciyarki tana tare da tawa?”
Wannan karon, babu inda za ta buya. Wajibi ne ta fadi abin da zuciyarta ke ji.
Tayi shiru na wani lokaci, kafin ta dan bude baki.
“Yaa fawaaz…”
Ya juyo yana kallonta, yana jiran amsar da zai adana a cikin Kirjin sa—Akwatin Sirrin Sa.
Fawaaz ya tsaya da numfashinsa yana jiran amsar da Nabeeha za ta bayar. A karon farko, zuciyarsa ta kasance cikin yanayin da bai saba da shi ba—zuciyarsa a hannunta take.
Shi da ya saba riƙe komai a ransa, shi da bai taba bari wani ya fahimci abin da ke zuciyarsa ba, yau shine ke jiran wata ta yanke hukunci a kansa.
"Idan har ba za ki bar zuciyata ita kadai ba, shin hakan yana nufin zuciyarki tana tare da tawa?"
Wannan tambaya ce mai nauyi. Tambayar da ko da yaushe yake gujewa. Amma yau, babu gudu babu ja da baya.
Nabeeha tayi shiru. Ba wai don bata da amsar da zata bashi ba, sai don tana jin cewa idan ta furta hakan, abubuwa ba za su taba dawowa yadda suke ba.
Ta sauke numfashi a hankali. “Yaa Fawaaz...”
Ta kalli yadda idanunsa suka cika da zurfin tambaya.
Sai ta dan sunkuyar da kanta, kafin ta dube shi a karo na biyu.
“Ina tsoron cewa idan na fada, abubuwa ba za su taba zama kamar da ba.”
Fawaaz ya gyara zamansa a kujerar motar, zuciyarsa tana bugawa. Amma bai kalli gefe ba, ya tsaya yana kallonta, yana jiran ta ci gaba.
“Me kike nufi?”
Nabeeha tayi shiru na wani lokaci, sannan tace, “Ka taba tunanin cewa akwai abubuwan da idan an furta su, sai zuciya ta rasa inda zata tsaya? Na tabbata kana fahimta, domin kai da kanka ka shafe shekaru da yawa ba tare da ka bayyana abin da kake ji ba.”
Fawaaz ya lumshe ido, sannan ya bude su a hankali. “Idan so ne, Nabeeha, to a duk inda zuciya zata tsaya, ni zan kasance anan, tare da ke.”
Kalmarsa tayi nauyi fiye da duk wata magana da ya taba yi a rayuwarsa.
Nabeeha ta juyo ta kalle shi. Zuciyarta cike da wani irin dadi da tsoro a lokaci guda.
Fawaaz ya gyada kai, yana murmushi kadan. “Ba zan matsa miki ba. Amma ki sani, tun kafin ki furta, zuciyata ta rigada ta gane amsar da take so.”
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Shiru mai cike da kauna da fahimta.
Motar ta tsaya a kofar gidan su Nabeeha. Amma babu wanda yayi yunƙurin motsawa.
Fawaaz ya juyo a hankali, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da basira.
“Ina son ki, Nabeeha.”🤭😍
Ya fada a hankali, ba tare da wata shakka ba.
Kamar numfashinta zai tsaya, ta dan lumshe ido. Wannan kalma da ta ke tsammanin ba zata taba ji daga bakinsa ba.
Ta bude ido a hankali, sannan ta ce da muryarta mai laushi, “Kirjin Mai Hankali—Akwatin Sirrin Sa.”
Fawaaz ya lumshe ido, yana jin yadda kalmarta ta sauka cikin zuciyarsa kamar ruwa a kan ƙasa mai ƙishirwa.
Ya bude idanunsa, yana murmushi.
“Kin san abin mamaki?”
Ta girgiza kai.
“Ke ce SIRRIN zuciyata, amma kema kina cikin AKWATIn SIRRIN ki.”
Sai ya jingina kansa da kujera, yana kallonta da murmushi. “Zan jira har sai ranar da za ki bude wannan akwatin.”
Nabeeha tayi murmushi, zuciyarta na tafasa da soyayyar da ta fara fahimta, soyayyar da bata san yaushe ta shige ta ba.
Ko da Nabeeha ta fito daga motar, bata iya tafiya kai tsaye ba. Ta tsaya tana kallonsa.
Fawaaz ya dan sunkuya kadan yana kallon ta, kamar yana jin cewa akwai wani abu da take son furtawa.
Sai ta saki murmushi, ta furta cikin wata irin murya mai sanyaya zuciya:
“Yaa Fawaaz... ni ma.”
Bai bukaci ta kammala maganarta ba. Domin ya rigada ya gane abinda take nufi.
Ya lumshe ido yana murmushi. A wannan lokaci, babu bukatar karin kalmomi.
Soyayya ta riga ta tabbatar kanta.
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:55_
Tun daga wannan dare, komai ya canza a tsakanin su Nabeeha da Fawaaz. Ba wai don sun fito fili sun bayyana soyayyarsu ba, sai don zuciyoyinsu sun riga sun fahimci juna, ko da ba su daɗe suna furta kalmomin soyayya ba.
Fawaaz ya sake zage damtsen kaimi wajen yawaitar kiranta a waya, yana tambayarta halin da take ciki, yana sauraronta fiye da da. Idan ta ce tana bukatar wani abu, ko kafin ta ƙarasa magana, zai yi kokari ya sameta da shi. Idan kuma suka hadu da juna, zai tsaya yana kallonta, kamar yana kokarin fahimtar SIRRIN da take ɓoyewa a cikin AKWATIn SIRRIN ta.
Hakan kuwa ya sa zuciyar Nabeeha ta fara jin sabuwar soyayya. Soyayya wacce ba ta cikin surutu da nuna isa, amma tana cikin ayyuka da kulawa.
🎀
Rana ce mai kyau, babu iska mai ƙarfi, babu rana mai zafi. Nabeeha ta fito daga gidan su, tana sauri saboda tana da wani aiki da zata yi a makaranta.
A lokacin da ta fito, ba ta yi tsammanin samun Fawaaz tsaye a bakin motarsa ba, yana jiranta.
Ta tsaya cak, tana kallonsa.
Shi kuwa, kamar bai ga mamakinta ba, sai ya bude mata kofa yana fadin, "Shiga."
Nabeeha ta ɗan taɓe baki, amma ba tare da ta ce komai ba, ta shiga.
Ya rufe mata kofa sannan ya zagaya, ya shiga driver's seat, ya tayar da mota. Ta gayshe shi cike da ladabi ya amsa tamkar zai hadiyeta saboda wani kallo da yake binta dashi. Ta masa kyau kwarai matuka tamkar wata baby doll..
Suna cikin tafiya, babu wanda yayi magana. Sai da suka yi tafiya mai nisa, sannan Nabeeha ta dan juyo tana kallonsa.
"Ya fawaaz."
Ya juyo a hankali, yana kallonta.
“Me yasa wani lokaci kamar kana tsoron soyayya?” Ta tambaya, kai tsaye.
Ya ɗan yi murmushi, sannan ya mayar da kallonsa ga hanyar gaba.
"Ba tsoro ba ne, Nabeeha. Ina kallon soyayya ne a matsayin abu mai tsarki. Abu wanda ba a wasa da shi."😂
Shiru ya biyo baya.
Ya sake cewa a hankali, kamar yana magana da kansa,
“Soyayya ta gaske, ba a iya furtawa. Ana iya jin ta ne a zuciya.”
Nabeeha ta kalli fuskarsa. A karon farko, ta fahimci cewa Fawaaz ba kawai mutum ne mai miskilanci ba, yana da zurfin tunani akan komai da yake yi.
A ranta, sai ta furta: “KIRJIN MAI HANKALI... AKWATIN SIRRIN SA.”
Babu shakka, Fawaaz yana da SIRRI. Amma ita ma tana da SIRRI a cikin zuciyarta.
Sirrin da ya fara bayyana....
Tafiyar da suke yi a motar na da shiru, shiru mai cike da magana. Kowane daga cikinsu yana nazarin wanda ke gefensa. Duk da cewa babu abin da ya bambanta halayyar Fawaaz a zahiri, amma Nabeeha tana iya fahimtar cewa akwai wani abu da ya canza a tsakaninsu.
Fawaaz bai sake cewa uffan ba, amma hannunsa da ke kan sitiyari yana dan motsi kamar yana tunanin wani abu mai muhimmanci.
Nabeeha ta gyara zamanta. Ta sauke ajiyar zuciya. “Ya Fawaaz.”
Ya juyo a HANKALI, yana kallonta, idanunsa na bayyanar da zurfin tunani.
"Na’am."
“Wata rana… za ka iya bude AKWATIN SIRRIN ka?” Ta fada a HANKALI, kamar tana tsoron jin amsar da zai bata.
Fawaaz ya dan lumshe ido, sannan ya bude su da natsuwa. Bai amsa da sauri ba, sai da ya dauki lokaci yana kallonta, kamar yana kokarin sanin irin amsar da take bukata.
A karshe, sai ya murmusa kadan. "Idan kin shirya jin gaskiyar da ke cikinsa."
Nabeeha ta ji zuciyarta ta buga da sauri. Gaskiya? Shin menene gaskiyar da Fawaaz yake ɓoyewa a zuciyarsa?
Da suka iso gidan Humyrah, Fawaaz bai bar Nabeeha ta fito ita kadai ba. Sai da ya fita ya zagaya ya bude mata kofa.
"Kada ki dade," ya fada a hankali. "Ina nan a waje."
Nabeeha ta dan zaro ido. “Kana nufin za ka jirani yau ma?”
Fawaaz bai amsa ba, sai ya jingina da motarsa, yana kallonta da wani irin kallo mai nauyi.
"Ki fito da wuri."
Ta dan saki murmushi. “Ba zan jima ba.”
Tana shiga cikin gidan, sai ta tarar da Humyrah tsaye tana jiranta da fara'arta.
“Lallai kuwa! Daga ina kike da soja?” Humyrah ta fada tana dariya.
Nabeeha ta dan hade rai. “Me kike nufi?”
Humyrah ta matso kusa da ita tana tsokanarta. "Ai duk duniya babu wanda yake tsananta tsaro akanki kamar yayanmu Fawaaz."
Ta dan kalle ta da murmushi mai ma'ana, sannan ta gyada kai.
"Nima tun shekaru da yawa na fahimci cewa yana kaunarki, sai dai kawai miskilancinsa bai bari ya fada miki ba."
Nabeeha ta yi shiru, zuciyarta tana bugawa.
“Yana kaunata?”
Humyrah ta yi dariya. "Idan har baki gane ba, to ke ce matsalar!"
Fawaaz yana tsaye a gefen motarsa, yana jiran fitowar Nabeeha. Idanunsa suna kan kofar gidan, amma a zuciyarsa, yana tunanin abubuwa da dama.
"Shin, Nabeeha za ta fahimci cewa zuciyata ta dade tana ajiyarta a cikin Akwatin Sirrinta?"
Ya sauke ajiyar zuciya. Idan har akwai ranar da zai bude wannan akwati, to watakila, yau yana gab da hakan.
Ko da Nabeeha ta fito daga gidan, ta tsaya tana kallonsa na wani lokaci.
Shi ma yana kallonta, fuskar sa da natsuwa.
Sai ta taka a hankali, ta tsaya a gabansa.
“Yaa Fawaaz… Ni ma.”
Bai bukaci ta kammala maganarta ba. Domin ya rigada ya gane abin da take nufi.
Ya lumshe ido yana murmushi. A wannan lokaci, babu bukatar karin kalmomi.
Soyayya ta riga ta tabbatar kanta.
....
Falon gidan Gwaggo Zainabu cike yake da manyan mutane, kuma hirar da ake yi tana tafiya cikin annashuwa. Ana zaune cikin natsuwa, kowanne fuska cike da farin ciki da kwanciyar hankali.
A gefe guda, manyan mazajen suna tattauna al’amura. Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Major General Dawud, Muhammad, da Fawaaz, tare da Chief Judge Abdulfatah da wasu dattawa biyu suna zaune, suna tattaunawa kan rayuwa da zaman duniya.
A dayan gefen kuwa, Gwaggo Hafsatu da Gwaggo Zainabu suna zaune cikin jin daɗi, suna sauraron hirar da ke gudana. Sai kuma Hajiya Zaytunah, wacce ke zaune cikin farin ciki, tana kallon sabuwar rayuwar da aka shimfiɗa mata.
Gidan da aka gyara mata ba ƙaramin kyawu yake da shi ba. Komai sabo ne, kayan cikin gidan na ƙasashen waje, tamkar wata sabuwar amarya. Abin da aka yi mata ya wuce tunaninta, ya nuna karramawa da daraja.
An ci, an sha, an yi nishadi. An yi hira mai cike da barkwanci da dariya. Sai dai daga bisani, hira ta sauya salo.
Dattawan suka fara maganar rayuwa da al’amuran iyali, har suka shigo batun matasa da aure.
Chief Judge Abdulfatah ya kalli Major General Dawud da murmushi. “Yallabai, har yanzu wannan ƙaton yaron naka yana da aure a gaba?” Ya nuna Fawaaz da sigar zolaya.
Dariya ta biyo baya. Major General Dawud ya yi murmushi. “Shi ya sani. Idan ya shirya, to muna nan.”
Alhaji Uzairu ya jinjina kai yana murmushi. “Mu ma muna da tamu ‘yar gidan. Idan tana da miji a gaba, to muna jiransa ya bayyana.”
Ana cikin haka, Alhaji Amiru ya dubi sauran dattawan da ke zaune, yana mai dariya. “Ni dai ina ganin, tun da duk bangarorin suna da amincewa da juna, me zai hana a daura auren nan take, a nan cikin wannan falon?”
Wani shiru ya biyo baya, kowa yana nazari. Sai kuma gaba ɗaya suka amince!
Daurin Auren Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad da Captain Fawaaz Dawud
A lokacin da aka tsara don daurin aure, yan uwan duk sun hallara a babban parlorn...Captain Fawaaz Dawud, ya kasance cikin kayan mutunci, tare da iyayensa da abokan arziki. Amarya, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad, tana gida batasan wainar da ake toyawa ba ..
bayan sun gama tanadar komai an sayo su huhun goro da alawa, limamin masallacin gidan ne ya jagoranci daurin aure. An fara ne da ambaton sunayen ma’auratan da waliyyansu.
Amarya: Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad
Waliyyin amarya: Alhaji Amiru (wanda ya tsaya a matsayin waliyyi)
Ango: Captain Fawaaz Dawud
Waliyyin ango: Major General Dawud..
Limamin ya nemi waliyyin amarya, Alhaji Amiru, ya amince da bayar da auren Nabeeha ga Fawaaz. Sai Alhaji Amiru ya ce:
"Na aurar da Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad ga Captain Fawaaz Dawud bisa sadakin da aka yarda da shi."
Sai limamin ya tambayi ango, Captain Fawaaz Dawud, ko ya karɓa. Fawaaz, cikin kamun kai da nutsuwa, ya ce:
"Na karɓa."
Daga nan sai limamin ya yi addu’a, tare da albarka ga ma’auratan. Jama’a suka