KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   17 / 40

48K to 51K   out of 119.4K words

kai a hankali, yana kallonsu dukkansu. "Kusan shekara goma kenan da wasu abubuwa suka faru… kuma sai yanzu suke tambayata su kansu. Abin mamaki, ko ba haka ba?"

Hajiya Karama ta shiga girgiza kai. "To, me ya sa sai yanzu suka tuna? Ai da ace wani abu ne mai muhimmanci, da tuni sun yi magana da kai a baya."

Alhaji Uzairu ya dan saki murmushi mara dadi. "Hakan nake tunani. Amma kin san wani abu? Na fara jin kamar akwai wani abu da ba a gaya min ba. Kuma hakan yana bani mamaki sosai."

Hajiya karama ta dan yi dariya. "Me kake nufi da wani abu da ba a gaya maka ba? Me ya sa kake tunanin haka?"

Sai ya jingina da kujera, yana dubansu dukkansu da idon bincike...

"Hakane," ya ce yana kallonsu da ido mai zurfi, "amma abin da ya faru bai shuɗe haka kawai ba. Ko dai wani ne ya sa hannu, ko kuma akwai wani SIRRI da ake boyewa."

Hajiya da Hajiya Karama suka kalli juna a lokaci guda, tamkar suna kokarin jin wace za ta fara magana. Sai dai dukkansu sun kasa cewa komai nan take.

Alhaji Uzairu ya gyara zama, yana nazarinsu. "Kun san abinda ya fi bani mamaki?"

Hajiya Karama ta yi saurin girgiza kai. "A’a."

Ya sake dubansu duka, sannan ya furta a hankali: "Yadda duk sanda aka ambaci sunan Zaytunah, sai ku dinga kokarin gujewa maganar."

A take, Hajiya ta ɗan ja numfashi. "Ba haka bane, Alhaji. Ai ba wai muna gujewa bane, kawai dai... ba mu ga amfanin tada wannan batu ba."

"Ba ku ga amfaninsa ba?" Ya jinjina kansa, yana kallonsu da kyau. "Matar aure ce, Mahaifiya ga yayanta. Yara biyu. , baƙar rana daya ta ɓace, har yau ba a san inda take ba da iyalanta, ba a san ko tana raye ba ko kuma..." Ya dan dakata, yana son ganin yadda za su karɓi kalmomin nasa.

Hajiya Karama ta sake gyara zama, ta lumshe ido na ɗan lokaci, kamar tana tunanin wani abu. Da ta buɗe su, sai ta ce da ƙasa-ƙasa: "Ai Allah kadai yasan inda take, Alhaji."

Alhaji Uzairu ya haɗiye yawu. Yanzu ya fara jin wata irin hujja a cikin muryarta. "Kun tabbata?" Ya tambaya, yana jefa musu wani irin kallo da ya sa dukansu suka rasa yadda za su mayar masa da martani.

Hajiya ta ɗauke kanta gefe, yayin da Hajiya Karama ta sunkuyar da kai. Wannan ne karon farko da ya tabbatar da cewa akwai wani abu da suke ɓoyewa. SIRRI ne da suka daɗe suna rufewa, amma yanzu lokaci ya kusa da za a tona komai.

Alhaji Uzairu ya jima yana kallon matansa, zuciyarsa na harbawa da sauri. Sun kasa sake kallo da shi kai tsaye, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa akwai wani abu da suke ɓoyewa.

Ya numfasa a hankali, sannan ya ce da murya mai cike da tuhuma,

“Da alama akwai wani abu da ba a gaya min ba.”

Hajiya ta ɗan ɗago kai cikin gaggawa. “Me kake nufi da haka, Alhaji?”

Ya gyara zama, yana mai haɗa yatsun hannunsa. “Ina nufin, tun shekaru da yawa da suka wuce, na lura da yadda kuke kaucewa batun Zaytunah. Kullum idan na kawo maganarta, sai ku canza zancen. Kuma a yau ma, abin da kuka faɗa ya kara bani mamaki.”

Hajiya Karama ta yi saurin girgiza kai. “Ai ba haka bane, Alhaji. Muna tsoron kada wannan maganar ta dawo da maka damuwa ne. Ka san dai yadda rayuwa take…”

Alhaji Uzairu ya saki wani murmushin da bai kai idonsa ba. “Rayuwa ko kuwa wani abu daban?”

Hajiya Karama ta shiga ƙara haɗiye yawu, alamar damuwa. Ita kuwa Hajiya, sai ta cije leɓenta na ƙasa, kamar mai tunanin wani abu.

Sai ya jingina da kujera, yana dubansu da kyau. “Ko da ace an manta da duk abin da ya faru, to me zai hana ku gaya min gaskiya yanzu? Ku faɗa min abin da kuka sani game da batan Hajiya Zaytunah.”

A take, fuskar Hajiya Karama ta ɗan chanza launi, sai dai ta yi kokarin boyewa. “Ai... ai bamu san komai ba, Alhaji.”

Alhaji Uzairu ya daka tsaki, yana jin zafin yadda suke ƙoƙarin ɓoye wani abu. Ya dafe goshinsa sannan ya dubi Hajiya da idanu masu ƙayatarwa. “Na faɗa muku gaskiya za ta bayyana, ko da ba daga gare ku ba. Amma idan har wani abu ya fito daga bakin wani, ba daga wurin ku ba, to wallahi ba zan taɓa yafewa ba.”

A take, Hajiya Karama ta yi saurin kallon Hajiya, fargaba na bayyana a fuskarta. Hajiya ta matse hannunta tare da jan numfashi. “Alhaji…” Ta kira sunansa da wata irin murya.

“Na ji,” ya katseta da kakkausar murya. “Sai dai in faɗi haka kawai, amma na san tabbas kuna da hannu a cikin batan Hajiya Zaytunah.”

Hajiya Karama ta shiga girgiza kai da sauri. “A’a, Alhaji, ba haka bane…”

Ya tashi tsaye da sauri, yana mai jefa musu wani kallo mai tsananin tuhuma. “Kada ku ƙara ƙoƙarin raina min hankali. Gaskiya tana nan kusa, kuma da izinin Allah, zan gano komai.”

Ya juya yana barin falon, zuciyarsa na tafasa. A yanzu, ya tabbatar da abu guda—matansa sun san wani SIRRI mai girma, kuma lokaci ya kusa da dukkan komai zai fito fili!






MX

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :27*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb



Nabeeha ta goge hawayen da suka wanke mata fuska. Har yanzu zuciyarta tana dukan da ba ta saba ba. Komai yana yawo a kwakwalwarta tamkar mafarki.

"Ammi, me kike nufi da cewa har yanzu ba kya so wasu su san kina raye?"

Hajiya Zaytunah ta dafe zuciya, tana jin yadda kalmar da Nabeeha ta furta ke da nauyi. Ta san cewa dole ne ta karasa bayyana komai, amma ba ta so ta daga hankalin ‘yarta fiye da haka.

"Nabeeha, akwai abubuwan da suka faru a baya da suka tilasta min boyewa," ta fara da murya mai rauni. "Ba wai kawai kishiyoyina suka yi min sharri ba, har da wasu daga cikin dangin mahaifinki sun hada baki."

Idanun Nabeeha suka kara girma. "Dangin Abba?"

Hajiya Zaytunah ta gyada kai. "Eh, Nabeeha. Ba kowa ne a dangin mahaifinki ke kaunata ba. Wasu sun yi kokarin ganin cewa na rasa komai, har da rayuwata."

Nabeeha ta hadiye wani yawu mai daci. "

Nabeeha ta ji wani irin nauyi a zuciyarta, kamar ana kokarin murkushe ta.

"Ammi, wa ke da alhakin rabamu da ke? Ban da kishiyoyin ki, wane daga cikin dangin Abba ke da hannu?"

Hajiya Zaytunah ta yi shiru na tsawon lokaci, tana tunanin yadda za ta fassara wa ‘yarta matsalar da ta jima tana gujewa.

"Akwai mutanen da ba za su so ki san gaskiya ba, Nabeeha," ta fada a hankali. "Ba wai kishiyoyina kadai suka so su hallaka ni ba, akwai wasu daga cikin ‘yan uwan mahaifinki da suka dauka cewa kasancewa ta a cikin gidan na zama barazana gare su."ta karasa fada tana boye lamarin game da ainihin babun rumanah yar uwarta Kuma matar wan mijin tah..

Nabeeha ta dafe kanta. "Ammi, menene hakan ke nufi?"

Hajiya Zaytunah ta gyara zama, tana mai tattara natsuwarta.

"Na kasance a matsayin matata biyu ga mahaifinki, kuma hakan ya sa na samu kulawa da girmamawa sosai daga bangaren danginsa," ta fara bayani. "Kishiyoyina ba su taba jin dadi da hakan ba. Sun san cewa idan zan zauna a gidan, ina da damar yin tasiri, kuma ina iya tabbatar da cewa yaran da na haifa su ne za su gaji mahaifinsu fiye da kowa."

Nabeeha ta lumshe ido. Ta san irin takun saka da ke tsakanin mata da kishiyoyinsu, amma ba ta taba tunanin cewa hakan zai kai ga irin wannan makircin ba.

"Kishiyoyina sun hada baki da wasu daga cikin mutanen su suka yanke shawarar kawar da ni," Hajiya Zaytunah ta cigaba. "Sun fara da haddasa matsala a tsakanina da mahaifinki, ta yadda zai fara jin cewa ni ce matsalar gidan. A lokaci guda kuma, suna aiki a bayan fage domin ganin na fada cikin wani hali da ba zan iya dawowa daga ciki ba."

Nabeeha ta kasa hakuri. "Shin mahaifin mu ya san da wannan makirci?"

Hajiya Zaytunah ta numfasa. "Ba zan iya cewa ya sani gaba daya ba, amma yana da laifin kasa gane gaskiya. Sun rufe masa ido da makirci, suka sa shi ya fara kallona a matsayin matsala maimakon matar da yake so. Hakan ya sa na shiga wani hali da ba zan iya fita daga cikinsa ba."

Shiru ya ratsa dakin. Nabeeha ta ji wani irin zafi a zuciyarta. Kamar zuciyarta tana tafasa da wani abu mai radadi.

"Ammi, don Allah ki gaya min gaskiya, shin mahaifin mu yana da hannu a abin da ya faru da ke?"

Hajiya Zaytunah ta kalli ‘yarta a hankali. "Ba zan ce yana da hannu kai tsaye ba, amma laifinsa shi ne kasa fahimtar gaskiya. Idan da ya tsaya ya bincika, da ba zan shiga wannan hali ba. Idan da ya tsaya ya kare ni kamar yadda ya kamata, da ba zan shiga cikin wahalar da na shiga ba."

Hawayen Nabeeha suka cika idonta. Tana jin wani irin takaici a zuciyarta. Ashe mahaifinta ya bar mahaifiyarta cikin hali mara dadi? Ashe ya bari wasu suka yi mata sharrin da ya raba su?

"Ammi, menene ya faru da ke bayan kin bar gidan?"

Hajiya Zaytunah ta lumshe ido. "Bayan an yi min asiri, na yanke shawarar barin gidan, amma ba da sanin mahaifinki ba. Na san cewa idan har ya san inda nake, zai iya sa a dawo da ni, kuma hakan na iya jawo wani mummunan abu. Gwaggo Hafsatu ce kadai ta san gaskiyar lamarin. Ita ce ta dauke ni ta kawo ni gidan nan, ta rufa min asiri....duk da lokacin Dana bar cikin gidan mahaifin ki. Gaskia magana bansan inda Kai na yake ba a lokacin. Na ji dai tamkar ana ingiza wutar kiyayyar san barin cikin gidan a zuciyata. Na kasa nutsuwa da sukuni har sai Dana bar cikin gidan. Kai tsaye bansan inda Kai na yake ba. Har na bar garin. Da temakon Allah da dattijuwar arzikin da muka hadu da ita. Allah ya sanya albarka a yadda na kawo a yanzu . Ciki harda ku. Ke da Hammad"

Nabeeha ta goge hawayenta. "To, me ya sa har yanzu ba ki yi kokarin sanar wa mahaifin mu gaskiya ba? Ba kya so ya san cewa kina raye?"

Hajiya Zaytunah ta girgiza kai. "Ba haka kawai zan iya komawa rayuwarsa ba, Nabeeha. Abubuwa da yawa sun faru. Ba zan so komawa rayuwarsa ba tare da tabbacin cewa zan iya kare kaina daga masu son ganin bayana ba."

Nabeeha ta gyada kai, tana jin yadda zuciyarta ke cike da damuwa. "Ammi, me zai faru idan Abba ya gano gaskiya? Idan ya san cewa kina raye?"

Hajiya Zaytunah ta dafa hannun ‘yarta. "Zan fuskance shi idan lokaci ya yi. Amma har yanzu, ba na son hakan ta faru ba tare da nayi shiri ba."

Shiru ya ratsa dakin. Nabeeha ta ji wani irin nauyi a zuciyarta. A yau, ta gano cewa rayuwarta ba kamar yadda take tunani ba ce. Ashe ita ‘yar wata halitta ce da aka ci da sharri? Ashe ita ce ‘yar matar da aka aikata mugunta a kanta?

Daga karshe, ta kalli Ammi da idanu masu cike da alamar tambaya.

"Ammi, yanzu me kike so in yi da wannan gaskiya?"

Hajiya Zaytunah ta sauke numfashi. "Ina so ki yi hakuri, Nabeeha. Kuma ina so ki ci gaba da rayuwarki da tsantsar HANKALI. Kada ki bari wannan gaskiya ta rude ki har ki dauki matakin da ba a shirya ba."

Nabeeha ta runtse ido. Ta san cewa daga yau, babu komai da zai kara zama kamar da..

Duk da fadin hajia zaytunah cewa kada ta bari wannan gaskiya ta rudeta, zuciyar Nabeeha ta kasa daukar hakan. Ta kwana tana juyi akan gado, zuciyarta tana yawo daga abu zuwa abu. Tunani daban-daban suka cunkushe mata kwakwalwa—abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya shine mahaifinta, Alhaji Uzairu.

Idan har Ammi ba ta so ya sani, to me ya kamata ta yi? Ta ci gaba da rayuwa tamkar babu komai? Ta rike wannan sirrin a ranta har abada?

Da safe, har ta gama shiri ba ta ga Ammi ba. Wannan ya dada dagula mata lissafi, don haka sai ta nemi Hammad a waya.

“hammad, kana ina?”

Muryar Hammad ta amsa da kasala. “Ina gida. Kina bukatata?”

“Kana da lokacin magana?”

“Eh, menene?”

Nabeeha ta hadiye yawu. Duk da cewa Hammad yana cikin wannan al’amari, har yanzu bai fahimci nauyinsa ba kamar yadda take ji

Shiru daga dayan bangaren na dan lokaci, sannan Hammad ya ce, “Tun kafin na zo nan.”

Nabeeha ta runtse idom

A bangaren Ammi kuwa, tana cikin falonta tana tunanin irin kallon da Nabeeha ke yi mata tun jiya. Duk da cewa ta gama shari’ar da kanta cewa Nabeeha za ta dauki lokaci kafin ta gama karbar gaskiya, ta san cewa yarinyar nan tana da son sanin hakikanin gaskiya.

A ranar, tana zaune tare da Gwaggo Hafsatu a dakin. Bayan dogon shiru, sai Gwaggo Hafsatu ta kalle ta.

“Zaytunah, ya kamata ki shirya kanki.”

Hajiya Zaytunah ta dago ido. “Meye hakan ke nufi, Gwaggo?”

Gwaggo Hafsatu ta dan ja dogon numfashi. “Nabeeha za ta iya tunkarar mahaifinta da kanta. Idan har hakan ta faru, ba zai kasance da sauki ba.”

Hajiya Zaytunah ta dafe kanta. “Gwaggo, har yanzu ban shirya fuskantar sa ba. Ban shirya fuskantar dukkan su ba.”

Gwaggo Hafsatu ta kalli Zaytunah da kulawa. “Dole ne ki shirya. Idan har Nabeeha ta tunkare shi da kanta, ba zai kasance da sauki gare ki ba. Idan har gaskiya ta fito, ba za ki so a same ki cikin rashin shiri ba.”

Shiru ya ratsa dakin. Hajiya Zaytunah ta san cewa Gwaggo Hafsatu na da gaskiya, amma har yanzu zuciyarta tana tafasa da fargaba.


---

A ranar, da yamma, Nabeeha ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta. Idanunta sun cike da damuwa, zuciyarta tana bugawa da sauri. .



MX

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :28*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb


×××Alhaji Uzairu ya ja dogon numfashi a daya bangaren wayar, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri.

"Nabeeha, menene wannan magana?"

Nabeeha ta rufe idonta da karfi, zuciyarta tana tsananta bugawa. Wannan shi ne lokaci mafi wahala da ta taba fuskanta.

"Abba na,Ashe inada rabon ganawa da ku a doron duniyar nan? Ashe muma munada mahaifi da yake a raye kamar su Humayrah? zan zo wajenka in gaya maka da kaina abba," ta fada a hankali.

Shiru ya ratsa tsakanin su na tsawon dakika goma. Sannan sai Alhaji Uzairu ya furta,

"Eh mana diyar albarka, wannan batu haka yake. To shikenan, ina jiranki."

Nabeeha ta kashe wayar, sannan ta dafe KIRJIN ta. Har yanzu, zuciyarta ba ta dai-daita ba. Shin ta yanke shawarar da ta dace? Shin hakan ba zai jefa Ammi cikin matsala ba?

Firgigit tajiyo karar sautin maganar Hammad ya shigo dakin yana kallonta.

"Me kike yi haka?"

Na beeha ta dago ido, tana jin yadda jikinta ya yi sanyi.ashe mafarki take yi?

"Na kira Abba. Zan je in gaya masa komai."

Hammad ya runtse ido yana girgiza kai.

"Wane Abba kuma dear sis? Me zaki fada masa? Mafarki kike ne?"

Nabeeha ta numfasa tana sauke katuwar ajiyar zuciya tace,

"Ina jin tsoron ci gaba da rayuwa cikin wannan duhun, Hammad" ta fada da shesshekar kuka.

"Ya kamata mu waiwaya dangin mahaifin mu. Tabbas ammi taga rayuwa tana kuma cikin jarabawar wannan kaddarori da taketa fuskanta..!"

Hammad ya dafe kansa, yana jin tsantsar tashin hankali. Bai san me zai ce ba, domin yasan cewa komai ya kusa fashewa.

"Inshaa Allah khair... Dear sis.... Kowani tsanani yanatare da sauki. Da yardar Allah lokacin warwarar komai ne yazo gangara..."

"Allah ya amince"

"Aameen"

🎀🎀🎀🎀

Cikin sanyin jiki da girmamawa, Gwaggo Hafsatu ta dubi fuskokin dake gabanta. Babban parlorn nata ya cika da nutsuwa, sai murmushin hikima dake kwance a gefen lebenta. Kowa ya zauna bisa kujera, duk da a kasa suka fara zama dukansu gwaggon taki kememe kan kowa ya koma kan kujera saboda sanyin ac dake busawa ko'ina na marbles din ya dauka da sanyi...

amma babu wanda ya iya fadin uffan. Fuskokin su Nabeeha da Hammad cike suke da tambayoyi, yayin da Hajiya Zaytunah ke daure fuska, tana kokarin kwantar da hankali.

A gefen dama Major General Dawud ne, yana zaune da kamewa. Kamar kullum, dattako ya rufe fuskarsa, sai idanunsa da ke bin komai a parlorn da kulawa. Hajiya Zaytunah na kusa da Gwaggo Hafsatu, tana dafe da mayafinta kamar mai jin sanyi. Nabeeha da Hammad kuwa, suna gefenta suna jiran jin abin da zai fito daga bakin Gwaggo Hafsatu.

Gwaggo Hafsatu ta numfasa a hankali, sannan ta dube su duka.

"Nasan kun dade kuna tunanin wanene ku, daga inda kuka fito. Lokaci yayi da ya kamata ku san asalin usulin ku," ta fara magana cikin muryarta mai nutsuwa.

Ta kalli Nabeeha da Hammad kai tsaye.

"Mahafiyarku, Hajiya Zaytunah, 'yar gidan kirki ce. Ta taso cikin jin dadi da kulawa, amma hakan bai hana rayuwa tura mata jarabawarta ba. Kafin a haife ku, ta yi aure da mutum mai tarin nutsuwa da hikima, sunansa Alhaji Uzairu Muhammad, mijin ta na sunnah. Shi da yayansa, Alhaji Amiru Muhammad, su ne suka gaji dukiyar gidan su. Sai dai fa wannan aure bai kasance cikin kwanciyar hankali ba, domin kishiyoyinta biyu, Hajiya Ladi da Hajiya Karama, sun mayar da ita kamar baiwar da ta shigo gidan da kafafunta."

Gwaggo Hafsatu ta dan ja numfashi. "Hajiya Ladi da Hajiya Karama sun yi iyakar bakin kokarinsu wajen ganin cewa mahaifiyarku ba ta sami kwanciyar hankali a gidan ba. Sun hada baki da wata uwa 'yar uwarta, Hajiya Rumanah, wadda ke da tsantsar tsana da kyashi gare ta tun suna yara. Hajiya Rumanah ba wai kishiyar mahaifiyarku bace da dai da ita zaa daura auren ta da Alhaji uzairu sai Allah yayi ikon sa aka daura aurenta da Alhaji Amiru.Wato yayan mahaifinku."

Gwaggo Hafsatu ta girgiza kai, sannan ta cigaba,

"Bayan mahaifiyarku ta haifi Nabeeha, ke kenan .. sannan ta dauki ciki na biyu,wanda ke cikinta shine kai, Hammad, aka shirya wata mummunar makarkashiya. Asiri aka mata! An hada baki da bokaye, aka tsara makircin da zai sa mahaifiyarku ta bar gidan ba tare da tunanin dawowa ba. Kuma hakan ya faru."

Nabeeha ta saki numfashi, tana kallon mahaifiyarta da idanun da suka cicciko da kwalla.

"Ammi, me yasa kika bar gidanmu? Me yasa baki koma ba?"

Hajiya Zaytunah ta rintse ido, ta dafa hannun Nabeeha.

"Ba zan iya komawa ba, Nabeeha. Na

17 / 40