KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   36 / 40

105K to 108K   out of 119.4K words

hankali, ya kamo tafin hannunta ya riketa da duka hannayensa. “Daga yau, zan kula da ke fiye da yadda na taba yi.”

Idanunta suka cika da ruwa, zuciyarta na bugawa da sauri. Kalaman Fawaaz sun ratsa ta, don ta san cewa idan ya yi alkawari, ba ya saba.

Ya kalleta ido cikin ido, sannan ya furta a hankali, “Kina da daraja a zuciyata, Nabeeha.”

Hakan ya tabbatar mata da cewa wannan soyayyar nasu ta fara shiga sabon mataki—matakin da ya fi ƙarfinsa da na ita, matakin da zai cika da kulawa da soyayya fiye da yadda suka taba tsammani.

Fawaaz ya ci gaba da kallon Nabeeha, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da wani irin shauki mai daɗi. Bai taɓa tsammanin cewa wata rana zai iya zama haka ba—mutum mai iya bayyana soyayyarsa da kulawa ba tare da wani shakku ba.

A hankali ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon yadda ta kaɗa idanu kamar mai jin kunya. Hannunsa har yanzu yana riƙe da nata, yana jin dumin tafin hannunta kamar wani abu mai daɗin gaske.

“Ina so ki ci abinci,” ya furta a hankali, murya mai laushi da cike da kulawa. “Ba zan bar ki da yunwa ba.”

Nabeeha ta lumshe ido, tana jin yadda wani sanyi ke ratsa ta. A da, ita ce ke kula da kowa, ba tare da tunanin cewa wani zai damu da ita haka ba. Amma Fawaaz, yana nuna mata wata soyayya mai cike da kulawa fiye da yadda ta taɓa tsammani.

"Me za ka kawo min?" ta tambaya a hankali, tana kallon shi ido cikin ido.

Fawaaz ya ɗan yi murmushi, sannan ya yi tunani na sakanni. “Me za ki so?”

Ta ɗan yi shiru, sai ta ce, “Ko tea kawai ma ya isa.”

Ya girgiza kai. “A'a, sai dai idan zan haɗa da biredi ko wani abu.”

Murmushinta ya ƙara faɗaɗa. “To shikenan, na yarda.”

Ba tare da ɓata lokaci ba, Fawaaz ya miƙe tsaye, yana ɗaukar wayarsa don kiran mai kawo abinci. Duk da cewa zai iya fita da kansa ya siya, amma a yanzu bai son barin Nabeeha ita kaɗai.

Bayan ya gama kiran, ya dawo ya zauna a gefenta, yana kallonta da wani irin nazari. "Nabeeha," ya kira sunanta a hankali.

Ta ɗago ta kalle shi. “Na’am?”

Ya dan lumshe ido kafin ya buɗe su a kanta. “Kin san cewa ina son ki?”

Zuciyarta ta buga da sauri, sai ta kasa cewa komai.

“Ban taɓa jin irin wannan soyayyar ba,” ya ci gaba da magana, murya mai sanyi. “Kuma ban san yadda zan bayyana shi ba. Amma na san cewa bana son na rasa ki.”

Nabeeha ta ji kamar zuciyarta zata fito saboda yadda take bugawa da ƙarfi. Wannan ba Fawaaz ɗin da ta saba gani ba ne. Wannan wani sabon Fawaaz ne, wanda yake bayyana zuciyarsa kai tsaye.

Ta sunkuyar da kai, tana jin yadda hawayen farin ciki ke taruwa a idonta.

Fawaaz ya miƙa hannu ya ɗaga fuskarta a hankali, yana kallonta da kulawa. “Ki daina boye min duk wani abu da ke cikin zuciyarki,” ya ce. “Ko da wani abu ke damunki, ko da kina cikin farin ciki. Ina so na kasance tare da ke a kowanne lokaci.”

Hawayen da take riƙe suka silalo. Ta yi murmushi, sannan ta ce a hankali, “Na san hakan, Yaa fawaaz.”

Ya girgiza kai, yana share mata hawayen da yatsunsa. “Ba wai kawai ki sani ba,” ya ce, yana murmushi, “ina so ki yarda da shi.”

Nabeeha ta lumshe ido, zuciyarta cike da soyayya. Tabbas, ta yarda da Fawaaz. Kuma yanzu, ta san cewa rayuwarsu za ta shiga sabon mataki—matakin da zai cika da soyayya, kulawa, da amana fiye da duk abin da suka taɓa fuskanta a baya.


ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:59_

Fawaaz ya ci gaba da kallonta, yana jin yadda zuciyarsa ta cika da wani irin nutsuwa. Ganin hawayenta ba ya masa daɗi, amma ya san waɗannan hawaye na farin ciki ne. Wannan ita ce Nabeeharsa, wacce ya daɗe yana ɓoye soyayyarsa gare ta. A yau, babu wani shakku ko jin tsoro. Ya bayyana komai.

A hankali, ya kamo hannunta cikin nasa, yana murza tafin hannunta da yatsunsa. “Kin yarda da ni?” ya tambaya cikin wata murya mai laushi da cike da kulawa.

Ta ɗago idonta da suka cika da ƙwalla, sannan ta gyada kai. “Na yarda da kai, Ya fawaaz.”

Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin kamar ya sauke wata babbar nauyi daga kirjinsa. “Wannan ita ce kawai maganar da take da mahimmanci a yanzu.”

Suka yi shiru na wasu sakanni, zuciyoyinsu suna sadar da sakonnin soyayya ba tare da furuci ba. A wannan lokacin, babu wani abu da ya fi masa muhimmanci sama da kasancewa tare da ita.

A can nesa, karar ƙararrawa ta katse shurun da ke tsakaninsu. Abincin da ya kawo mata ya iso. Fawaaz ya miƙe, yana murmushi. “Za mu ci tare.”

Nabeeha ta murmusa, zuciyarta cike da farin ciki. A yau, soyayyar su ta wuce tunani. Sun isa matakin yarda—matakin da babu wani abu da zai iya karya shi...

Fawaaz ya dubi Nabeeha da murmushi a fuskarsa. Ya ɗauki cokali, ya ɗiba mata abinci a hankali, sannan ya miƙa mata. “Ki buɗe baki.”

Nabeeha ta kalle shi da mamaki, zuciyarta na bugawa da sauri. Bai taba nuna mata irin wannan kulawar kai tsaye ba. Amma yadda yake kallonta da yadda fuskarsa ke cike da kwanciyar HANKALI, sai ta ji wani irin yanayi da ta kasa bayyanawa.

A hankali, ta buɗe baki. Ya saka mata abincin cikin taushin hali, yana kallon ta yadda take ci. Sai da ta haɗiye sannan ya ce, “Daga yau, zan kula da ke fiye da yadda kike zato.”

Hannunsa ya ɗora saman nata, yana dan matsawa. “Nabeeha, kin san me yasa nake son ki haka?”

Ta girgiza kai a hankali, idonta yana cikin nasa.

“Saboda ke ce wacce zuciyata ta amince da ita tun kafin ki san hakan. Ke ce nutsuwa ta, ke ce addu’ata. Kin san yaushe na fara son ki?”

Nabeeha ta ɗan lumshe idanu, tana jin wani irin sanyi na ratsata.

Fawaaz ya ɗan yi murmushi, yana ci gaba, “Tunda na gane cewa ba za ki iya rayuwa da ciwon kewa ba, na rantse a raina cewa zan dinga kasancewa kusa da ke. Amma sai na lura cewa soyayyar da nake ɓoyewa ta fi ƙarfi fiye da abin da na zata.”

Nabeeha ta kafe shi da idanu, tana jin yadda kalamansa ke ratsa zuciyarta. Dama ya iya kalaman magana haka? Haka ya iya tsara zance? Haka ya iya zuba soyayya tamkar a film? Ta murmusa kawai, kalaman sa na ratsa magudanar jini da tsokar jikin ta.

Fawaaz ya ɗauki wani cokali na abinci, ya sake miƙa mata. “Ki ci, domin na san dole ne ki sami ƙarfi. Ba na so ki rame saboda tunani ko damuwa.”

Bayan sun gama cin abinci, Fawaaz ya jasu sallah tare. Ya tsaya yana kallon yadda take yin addu’a da nutsuwa. Idanunsa sun cika da ƙauna da girmamawa.

Bayan sallar, ya matsa kusa da ita, yana ɗora hannunsa saman nata. “Allah ya bar min ke, Nabeeha. Ina addu’ar alheri a gare ki, kuma ba zan daina ba.”

Sai dare ya ja, suna tare cikin kwanciyar hankali, zuciyoyinsu sun haɗu da juna ba tare da wata shakka ba. Wannan shi ne matakin yarda—matakin da babu komai face soyayya da kulawa ta gaske.

Daren ya tsawaita, amma Fawaaz bai damu ba. Yana kallon Nabeeha da wata irin nutsuwa da bai taɓa jin irinta ba a rayuwarsa. Idanunsa sun cika da so da kulawa, zuciyarsa tana bugawa da wani irin shauƙi da yake wahalar bayyana.

Ya sake kamo hannunta cikin nasa, yana jin yadda tafin hannunta ke da ɗumi mai daɗi. "Nabeeha," ya ambaci sunanta a hankali, kamar yana jin daɗin furta shi.

Ta ɗago idanuwanta da suka cika da kwanciyar hankali, tana kallonsa.

"Kin san cewa zuciyata ta dade tana son ki?" Ya tambaya da muryarsa mai laushi.

Ta lumshe idanuwa a hankali, tana jin wani sanyi yana ratsata. "Na sani, Ya fawaaz."

Ya ɗan yi murmushi, yana jin yadda furucinta ke ƙara ƙarfafa shi. "Amma ba wai kawai son ki nake ba, Nabeeha. Ina ƙaunarki da zuciyata gaba ɗaya. Ina kallon ki, ina jin kamar kin mallake ni tun kafin ma ki sani. A yau, babu wata shakka, babu wata shinge. Na baki zuciyata gaba ɗaya."

Nabeeha ta lumshe idanu, ta ɗan saki numfashi mai nauyi. "Ni ma na yarda da kai, Yaa Fawaaz. Na amince da kai fiye da kowa. Ka daɗe kana ɓoye komai, amma zuciyata tana karanta ta taka, ko da baka furta ba."

Fawaaz ya murmusa, yana jin yadda furucinta suka saukar masa da natsuwa. "Kin san me yasa na daɗe ina ɓoye soyayyata?"

Ta girgiza kai, tana jiran jin amsar sa.

"Saboda bana son zuciyata ta takura ki. Bana son na ɗora miki damuwar da ba ki shirya da ita ba. Amma yau, ba zan iya ɓoye komai ba. Nabeeha, kin mallake ni gaba ɗaya."

Hannunsa ya ɗaga ya shafi fuskarta a hankali, yana kallon yadda idanuwanta ke cike da ƙyau da kwanciyar hankali. "Duk da haka, ina son ki fiye da abin da zan iya furtawa. Ina addu'ar Allah ya tabbatar min da ke."

Hannunta ya sake rikewa, yana matse shi a hankali. "Kuma daga yau, ina son na dinga kula da ke. Ba zan bar ki da yunwa ba, ba zan bar ki da damuwa ba. Ba zan bari wani abu ya taɓa ki ba, har abada."

Nabeeha ta sunkuyar da kanta, zuciyarta tana bugawa da nauyin farin ciki.

Fawaaz ya kalli fuskarta, sannan ya kai hannunta zuwa KIRJIN sa. "Ji yadda zuciyata take bugawa saboda ke, Nabeeha."

Hannunta ya ji yadda bugun zuciyarsa ke da ƙarfi, yana tafiya da daɗin ƙauna mai tsafta.

Daren yana ƙara ja, amma babu wanda ya damu da lokaci. Sun shagala cikin soyayyar da take tafiya a hankali, cikin tsafta da aminci.

Fawaaz ya dubi kyawun fuskarta, sannan ya lumshe idanu. "Ina addu’a Allah ya albarkaci rayuwarki, Nabeeha. Ina addu’a ki kasance cikin farin ciki har abada."

Sai ya sake kallonta da murmushi. "Kin yarda da ni?"

Ta gyada kai, murmushi yana bayyana a fuskarta. "Na yarda da kai, Ya fawaaz."

Daga nan, shiru ya ratsa tsakanin su, amma zuciyoyinsu suna magana fiye da furuci. Wannan matakin da suka kai ba wai kawai soyayya ba ce, aminci ne, kulawa ne, addu’a ce da ba ta yankewa.

Soyayyarsu ta kai matakin da babu komai face tsarkin zuciya da yarda. Wannan matakin ne da ba zai taɓu ba, har abada.

,,,,,,

A hankali Hammad ya turo kofar falon yana rike da basket dauke da warmers na abinci. Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya shiga, yana murmushi.

"Assalamu Alaikum."

Nabeeha ta dago daga inda take zaune tana duba wayarta. "Wa’alaikumus Salam, Hammad! Dear bro..iyye me muka samu? "

Ya ajiye ledojin a kan teburi yana fadin, "Abinci daga gidan Granny. Tace a gaishe ku."

Fawaaz, wanda yake zaune gefen kujera yana kallon wasan kwallon kafa a TV, ya dan kalle su, sannan ya mayar da hankalinsa ga wasan.

"Nagode sosai," Nabeeha ta fada tana bude ledar don ganin me aka kawo. "Sannu da kokari ."

Hammad ya yi murmushi yana zama. "Babu komai. Yanzu dai ku ci kafin yayi sanyi."

A lokacin Fawaaz ya dan juya kansa ya kalli Hammad. "Ya fawaaz barka da rana"

Hammad ya gyara zama, yana murmushi. "Lafiya kalau, bro"

Fawaaz ya dan kada kai, ya maida kallonsa kan wasan da ake yi a TV. "Daga gani Barcelona ce take wasa da Real Madrid."

Hammad ya yi dariya. "Eh mana! Kuma kaga yadda suka rike ball, ai dole su yi nasara."

Fawaaz ya dan gyara zama yana kallon yadda ake buga wasan. "A ganina Real Madrid suna da damar cin kofin wannan shekarar."

"Wallahi kuwa," Hammad ya amsa, yana kallon TV. "Messi dai ba wasa ba ne, amma kalli yadda Benzema ke kokari."

Suka dan ci gaba da hirar kwallon kafa na tsawon mintuna kadan, kowannensu yana fadin ra’ayinsa kan wasan. Sai da suka ji sun dan gamsu, sannan Hammad ya sauke numfashi yana gyara zamansa.

"Yaa Nabeeha, Yaa Fawaaz... zan koma makaranta gobe in sha Allah."

Nabeeha ta dago da sauri, tana kallonsa da mamaki. “Hammad? Haka kawai? Da wuri haka?”

Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dan kalli Hammad.

Hammad ya gyada kai. "Eh, hutuna ya kare, dole na koma."

Nabeeha ta dan lumshe ido. "Allah ya kiyaye hanya."

Fawaaz ya gyada kai. "Allah ya tsare."

Hammad ya mike yana murmushi. "Nagode. Zan tafi yanzu, sai mun yi waya."

Nabeeha ta raka shi da kallo, zuciyarta cike da kewar tafiyarsa. Fawaaz ya ci gaba da kallon wasan, amma yana sauraron yadda Hammad ke ficewa daga falon.

Bayan dan lokaci, Nabeeha ta numfasa a hankali. "Zan rasa yawan damun Hammad kenan."

Fawaaz bai ce komai ba, sai dai ya dauki remote ya kara volume din TV kadan, yana mai mayar da hankalinsa ga wasan da ake yi.

Tuwon shinkafa da motar ganye dataji tantakwashi. Sai peppersoup na kaji da gasasshen cat fish. Sai doya da kwai da kunun gyada. Sai fruits da meat pie da samosa. Lamarin sai Wanda yagani kawai....

Fawaaz ya Mike ya dakko tray ya zuzzuba musu komai. Ya karasa wajen nabeeha batayi aune ba tajita a sama. Fawaaz ya daga chak ya dora ta akan cinyarsa..

Ya samu kansa da juyar da fuskar ta ya kamo labbanta da nasa yana tsotsar bakinta...

Hannunsa daya Kuma ya zura shi rigar ta yana wasa da abubuwa Mafi soyuwa daga jikinta a zuciyar sa..

"Na...k...ko... Shi" ta fada a rarrabe tamkar zata shide saboda sabon lamarin da hannun fawaaz keyi acikin rigarta.

"Sai da ruwan ciki akejan na rijiya... Beautiful Nabeeha" fawaaz ya radamata a kunne yana lasar gefen kunnen ta.

Ta sauke ajiyar zuciya da kyar tana ajiye sautin numfarfashi...

Ta shiga zame hannun fawaaz amma ya riketa kam. Sai dayaga ma jagulata sannan ya kyaleta yana bata abincin a baki. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta...


ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE:60_


Fawaaz ya Mike tsaye yana mikawa Nabeeha hannunsa. Dakyar ta iya kama nashi ya mikar da ita yana rarumar ta. Ya rungumeta tsam wanda zaa kwace masa ita..

"Muyi wanka mu raya daren yau ko love?"

Nabeeha tayi shiru batace dashi komai ba. Gabanta ya tsananta bugawa fat fat fat.

"Mu raya daren yau?" Tanbayar da yayi da muryarsa ta tariyo a dodon kunnenta.

Jikinta ya dauki rawa. Inde raya dare ne. Irin Wanda humyrah ta sanar mata. To tabbas bata shirya masa ba. Don haka tayi kokarin zame jikinta.

Ya sanya hannunsa yana tallabo fuskar ta.

"Menene... Uhm? "

"Ba.... Bakomai"

"Ko zaki shiga kiyi wankan ki dauro alwala?" Ya fada mata ganin kamar kunya takeji. Kada ya takurata.

Daman abunda take jira kenan. Don haka tayi hanzarin daga kai kafin da sauri tache,

"Eh"

"Tohm bari Nima naje"

Da sauri tabar wajen ta shige cikin dakin. Fawaaz ma ya shiga dakinsa. Tayi saurin Saka mukulli ta rufe dakin. Gabanta ya tsananta bugawa.

Bandaki ta fada tayi wanka, da bathe khumrah na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE. Bayan ta gama wankan ta dauraye jikinta da after bathe khumrah. Wani kamshi ya gama gauraye ta ... Kulaccam din kamfanin turaren ta dauka ta shafe jikinta dashi. Ta sanya riga da wando masu nauyi ta zura hula akanta

Ita kanta yadda jikinta ke tashin kamshi yasa ta Kai hancinta tana sunsunar kamshin da fatarta ke bayarwa da kayanta da suke kamshin turaren kayan YERWA INCENSE AND MORE. Dake gab da zata tare aka Kai kayan kamfanin turaren na YERWA INCENSE AND MORE ta turara mata su... Sai kamshi ne ke tashi sai kace a kamfanin surrati..

Bayan ta kammala komai ne ta koma bakin gado ta zauna tana murza yatsunta..

Fawaaz yanata zaune a parlor shiru shiru yana juranta. Tuni har yayi wanka ya dauro alwala shima tun dazu. Ita yaketa jira shiru.

Ya tashi ya nufi kofar dakin zai bude ya jita a rufe. Ganin ko bata karasa bane yasa ya koma ya zauna. Can bayan wani lokaci ya Kara komawa. Nanma dakin a rufe gam. Ya danyi murmushi yana sosa keyarsa cikin muryar lallashi yache,

Fawaaz ba zai yi saurin nuna damuwarsa da son kwadaituwa da kasancewar sa da Nabeeha kai tsaye ba, amma yayi kokarin amfani da salo mai nutsuwa da kalmomi masu taushi domin ya janyo hankalinta ta fito daga dakin da ta buya. Sai aunawa yake kalaman da

36 / 40