idanunsa suka hadu da nata. A karo na farko, bai iya boye damuwarsa ba.
"Da gaske za ki bar ni?"
Ta bude baki, amma bata san me za ta ce ba.
"Da gaske za ki auri wani?"
Zuciyarta ta buga da karfi. Bai taba tambayar ta haka ba. Bai taba fadin irin wadannan kalmomin da kansa ba.
Sai ta runtse idonta, zuciyarta tana neman bugawa da sauri. Soyayyar Fawaaz... ta fara bayyana!
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:42_
Zuciyarta tana bugawa da sauri. Tambayar da Fawaaz ya yi mata tana yawo a kunnenta,
"Da gaske za ki bar ni?"
"Da gaske za ki auri wani?"
Nabeeha ta kasa bude baki. Tana jin numfashinsa yana fita a hankali, amma yana da nauyi kamar yana shan wahala.
Tana kallonsa, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama. Ta san Fawaaz miskili ne, ba ya fada kai tsaye, ba ya taba bayyana soyayya ko damuwarsa. Amma wannan karon… ya kasa boyewa!
Ta hadiye yawun bakinta. “Yaa Fawaaz…”
Ya dago idanunsa, suka hadu da nata. Idanuwansa sun canza, akwai damuwa, akwai tsoro, akwai kishi… akwai abu da ba ta taba gani a tare da shi ba.
Bata taba ganin Fawaaz a haka ba. Bai da karfin yin kuka, amma idanunsa sun bayyana rashin kwanciyar hankali.
Ta dafa kan giyar mota a hankali. “Ka kwantar da hankalinka.”
Shiru. Bai ce komai ba. Sai dai ya lumshe idanunsa na wasu dakiku, sannan ya bude su a hankali.
Ya dago hannunta daga inda take dafe da shi, ya matse cikin nasa.
Jikinta ya dauki rawa. Duk da sanyin AC, amma tafin hannunsa yana da dumi.
"Me yasa zuciyata ke bugawa haka?" Ta raya a ranta.
A hankali, ya bude baki, muryarsa kamar mai radadi. “Nabeeha… ki fada min, da gaske ne?”
Ta runtse ido, ta bude. “Menene da gaske?”
Ya dan saki ajiyar zuciya. “Zaki aure shi?”
Ta dauke kanta gefe. Babu abin da ta tsana irin wannan tambayar, saboda itama ba ta san me zai faru da ita ba.
“Bana son ayi auren.” Muryarsa ta soma sauyawa.
Ta dago da sauri. “Me kake nufi?”
Fawaaz ya juyo, ya kalle ta sosai, ya bude baki, amma sai ya sake rufe shi. Bai san me zai fada ba.
"Ba zan iya fadin cewa ina son ki ba. Amma ba zan iya barin wani ya same ki ba."
Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. “Kiyi wani abu. Karki amince.”
Ta girgiza kai. “Ya Fawaaz, aure ba wasa ba ne.”
Ya dan rike kansa. “Ke kike tunanin wasa nake? Ke kike tunanin wannan abu wasa ne?”
Ta yi shiru.
Ya ci gaba da fadin, “Tun da kika san cewa aure ba wasa ba ne, me zai hana ki duba zuciyarki ki tabbatar ko kina son shi?”
Hankalinta ya tashi. Ta furta cikin kasa da murya, “Bana son shi…”
Ya dago da sauri, yana kallonta da mamaki. “Me kika ce?”
“Bana son shi,” ta maimaita.
Numfashinsa ya fara sauka a hankali. Ya kura mata ido.
“Ina so ace na samu hanyar kubuta daga wannan matsala,” ta fada a hankali.
Fawaaz ya jinjina kai. “To ki fada. Idan bakya so, ni zan fitar da ke.”
Ta dago ido, tana kallonsa. “Ta yaya?”
Ya shafa sumar kansa. “Ki bar wannan a kaina.”
Zuciyarta ta doka.
Fawaaz zai iya yin komai don ya hana ta barinsa? Don Allah, menene ma’anar hakan? Wannan ba kishi ba ne kawai… wannan soyayya ce!
Ta sake kallonsa, zuciyarta cike da mamaki da ruɗani. A karon farko, zuciyarta ta fara fahimtar Fawaaz.
Shiru ya biyo baya. Shiru mai nauyi.
Idanun Fawaaz na kan Nabeeha, idanunta na kansa. Ba wanda ya san me ke zuciyar dayan.
Da alama zuciyoyinsu na fassara abu guda, amma suna jin tsoron furtawa.
Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya, ya dauke kai gefe. Bai san me zai ce ba, kuma ba ya son cewa wani abu da zai sa ta ji kamar yana tilasta ta. Amma zuciyarsa… zuciyarsa tana barazanar fasa KIRJI ta fito.
A hankali, Nabeeha ta dan gyara zamanta. “yaa Fawaaz…”
Bai kalleta ba, amma ya amsa da muryar da bata saba da jin irin ta a tare da shi ba,
"Na'am?"
Ta dan hadiye yawu. “Me kake nufi da cewa zan bar komai a kanka?”
Ya lumshe ido na wasu dakiku. Daga bisani ya bude su. “Ba sai kin damu ba.”
Ta dan kalle shi da mamaki. “Ka ce haka bayan ka janyo ni daga wajen bachelorette party, ka mayar da ni kamar wata… wata—”
Ya juyo da sauri. “Kamar wata me?”
Ta girgiza kai. “Kamar wata wadda ba ta da ‘yancin kanta.”
Idanunsa suka hade da nata. “Ba haka bane.”
Tayi shiru tana kallonsa. Tana son fahimtar shi, tana son jin dalilin da yasa yake acting haka.
Ya ci gaba da kallonta, sannan a hankali ya furta, “Ban san yanda zan fada miki ba.”
Ta tsura masa ido. “Ka fada kawai.”
Ya dauke kai gefe. Fawaaz bai taba jin wannan nauyin kalmomi a bakinsa ba. Bai taba jin wannan tsoron fadin abu ba.
Bai san lokacin da ya furta ba,
“Ban san yanda zan rayu ba idan har na ganki da wani ba.”
Numfashinta ya tsaya cak!
Hannunta ya fara rawa. Ta bude baki, amma bata san me za ta ce ba.
Shi kansa yana jin kamar ya furta wani SIRRI da bai shirya bayyana ba. Amma da gaske ne!
“Nabeeha.” Ya kira sunanta a hankali.
Ta dago idonta da sauri.
Ya kura mata ido, yana jin zuciyarsa na tafarfasa. Kamar yana gab da furta abu mafi girman da ya taba fada a rayuwarsa.
Sai dai… wani bugun wayarsa ya katse shirin da zuciyarsa ta gama yanke hukunci a kai.
Ya sauke numfashi, ya dauki wayarsa.
"Captain Idris."
Ya yi shiru, yana duban sunan da ke yawo a fuskar wayar. A hankali, ya danna answering call, muryarsa a dake.
"Captain, kana ina?"
Muryar can daga daya bangaren ta fada.
"Muna da matsala a base"
Fawaaz ya sauya fuska bayan su. Gaysa. “Wace irin matsala?”
"Matsalar taron gaggawar nan da shugaban kasa zai zo."
"Roger that .. okay later" ya katse Kiran yana sake duban Nabeeha.
Zuciyarsa ta buga da karfi. Idan bai dauki mataki ba, Nabeeha za ta tafi!
Ya bude idonsa a hankali, yana kallonta. Tana kallonsa shima.
Hannunta yana cikin nata, amma ba ta san lokacin da ta rike nasa ba. Tana jin jikinta yana rawa.
"Menene dalilin wannan kishi da yake nuna min?" Ta tambayi zuciyarta.
"Shin hakan yana nufin Fawaaz yana sona?"
"Ko kawai yana jin kishi ne don ba ya son wani namiji ya same ni?"
Tayi shiru. Bai ce komai ba, ita ma bata ce komai ba. Sai dai zuciyoyinsu suna magana da juna.
Shiru na wasu dakiku…
Sai Fawaaz ya sauke ajiyar zuciya. Ya saki hannunta a hankali.
Ya juyo da kyau ya kalle ta. “Da gaske zaki tafi?”
Ta lumshe ido, ta bude. “Yaw Fawaaz… ban san me zan ce ba.”
Ya kura mata ido, sannan ya furta kalmomin da suka gigita ta,
“Idan har baki son tafiya, zan iya hana ki.”
Idanunta suka bude da mamaki. “Me kake nufi?”
Ya dago hannunsa ya dafa saitin zuciyarsa. “Zan dauki matakin da zai hana ki auren Muhammad.”
Jikinta ya dauki rawa. Shin me yake nufi?
"Yanzu zan je wajen su baba"
Idonta ya karu. "Me zai hana?"
Ya tsura mata ido. "Zan fada masa cewa ni nake son ki."
Ta saki baki da mamaki!
Shin Fawaaz ya fadi hakan da gaske?
Numfashinta ya dauki sama. Ta ji kamar an zuba mata ruwan sanyi a zuciya. Ta kasa furta komai.
Idanunsa sun kada. “Nabeeha, bana wasa. Zan je in fada masa a yau.”
Tayi shiru. Tana jin kamar mafarki take yi.
Kafin ta iya cewa wani abu, Fawaaz ya bude kofar motar, ya fito da sauri.
Tana jin numfashinsa yana fita da nauyi. Gaskiya ne!
Zai fada wa Major General cewa yana sonta.
Shiru ya kara mamaye falon. Kowannensu ya tsaya da tunani, yana kokarin fahimtar abin da ke faruwa. A yau dai gaskiya ta fito fili!
Major General Dawud ya jingina bayansa da kujerarsa, yana kallon Fawaaz da wani irin kallo mai zurfi.
"Ka san me kake fada?" Ya sake tambaya.
Fawaaz ya dan runtse ido, sannan ya bude su cikin girmamawa. A karo na farko, ba shi da niyyar boye komai!
"Eh, Baba," ya fada a hankali.
Gwaggo Hafsatu ta dafe KIRJIN ta. "Kai Fawaaz! Ai wannan maganar ka bata da sauki! Kasan me kake bukata daga gare mu ne kuwa?"
"Dan Allah ina so ku dakata da shirin aurenta da Air Captain Muhammad."
Dakin ya dauki shiru!
Hajiya Zaytunah ta dubi Major General da sauri, kamar tana neman jin ra’ayinsa.
"Fawaaz," inji Major General, "kai ɗana ne. Amma kayi sake mai girma."
Fawaaz ya gyara tsayuwarsa, yana jin bugun zuciyarsa na karuwa. Amma ya kudurta cewa ba zai janye ba!
"Baba" ya kira cikin nutsuwa, "bani da mafita da ta wuce wannan. Na san nayi sake, amma ita ce zabina."
"Kai baka da hankali ne?!" Cewar Gwaggo Hafsatu, tana dubansa da mamaki. "Tun yaushe kake son ta, amma baka fada ba?"
Fawaaz ya ji kunya ya lullube shi, amma hakan bai hana shi ci gaba da magana ba.
"Na tsorata, Gwaggo," ya fada da gaskiya. "Na tsorata da yadda za a fahimce ni. Na tsorata da abin da Nabeeha za ta fada. Na tsorata da cewa ba za ta karbeni ba! Na fara kaunar nabeeha tun ranar dana fara dora idanuna akanta sanda suka dawo gidan nan tun muna kanana. Tun bansan meye so ba gwaggo...kaunar da nake mata batada iyaka. Bama zan iya fasaltata ba ko na bayyana adadinta"
Major General ya gyada kai a HANKALI. Kamar yana jin tausayin dan sa..
"Baka da tabbacin cewa ita ma tana sonka?"
Shiru ya ratsa dakin. Fawaaz ya ji zuciyarsa ta buga. Hakika bai da tabbas!
Ko Nabeeha za ta amince da shi?
Ko kuwa zata dauke shi a matsayin wani mai bata lokaci?
Hajiya Zaytunah ta numfasa. "Fawaaz," ta kira shi a hankali.
"Na’am, Aunty ." Ya amsa cike da kunyar ta mai girma...
Ta kalli Major General, sannan ta kalli Gwaggo Hafsatu. "Idan har Nabeeha zata amince da shi, to ni ba ni da matsala."
Gwaggo Hafsatu ta kada kai. "Ai maganar ita ce, yaushe zai fada mata?"
Major General Dawud ya kura wa Fawaaz ido.
"Fawaaz," ya furta, "ka shirya don fuskantar ita kanta?"
Fawaaz ya hadiye yawu.
Wannan ce babbar matsalarsa!
Yana so ya fada wa Nabeeha. Amma yana tsoron amsar da zai samu. Ko zata amince da shi ko zata ki karbar kokon barar sa.... Don gudun kada ta badawa su gwaggo Hafsatu kasa a idanu....
Fawaaz yayi shiru kansa a kasa. Gwaggo Hafsatu da dama tasan haka zata faru don ta lura da yanayinsa ta tabbatar yana kaunar nabeeha sosai. Amman saboda tsananin fadin ransa da miskilancinsa bata taba zaton zai iya bayyanawa ba. Lalle ba karamar kauna yakewa Nabeeha ba. Don haka ta nisa kafin tache,
"Wannan batu sai da amincewar kowanne bangare. Ba a neman aure akan wani neman. Ma'ana tunda Muhammad ya rigaka to fa sai da amincewar sa idan zai hakura yabar maka. Haka zalika sai idan nabeehan ta amince da karbar kaunar ka. Fata dai Allah Ubangiji yayi zabinsa na gari. Allah ya zaba mata mafificin alkhairin sa acikin ku Amin. Wannan batu sai manya sun shiga cikin sunga yiwuwar sa. Inn shaa' Allah."
"Toh granny" fawaaz ya amsa a takaice ya dan dunkufa yana musu sallama.
"A huta lafiya" ya Mike ya fice da sauri.
Yayinda su Kuma suka cigaba da maimaita lamarin..
🎀🎀🎀
Zaune air captain, pilot Muhammad Amiru yake akan makeken gadonsa. Kansa a saman pop.
Na'urar dake tache abun kallo tana haskawa da faifon bidiyon komai da maganganun su na ranakun gaba daya.
Kunya, takaici da nadama suka taru suka gauraye shi. Duk karfin halin sa sai da hawaye suka zurara daga idanuwan sa...
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:43_
Faifon bidiyon ya fara tariyo masa tun daga, Zauren babban falo ne su Gwaggo Zainabu, Alhaji Uzairu, da Alhaji Amiru suka zauna, kowanne cikin shigar mutunci, amma zuciyoyi na ruf da ciki. A gefen su kuma, a durkushe kan kafet, su Hajiya Ladi, Hajiya Karama, da Hajiya Rumanah suna zaman nasu, tamkar basu da damuwa.
Muhammad, ɗan Hajiya Rumanah, yana zaune a gefen kujera, yana kallo da al'ajabi, zuciyarsa cike da shakku da mamaki. Bai taɓa tunanin mahaifiyarsa da matan kanin mahaifinsa suna da wata boyayyar magana ba, amma yau abin ya bayyana.
Alhaji Amiru ne ya fara magana da muryar nutsuwa, amma a ciki akwai wata alama ta tuhuma.
"Ina Zaytunah?"
Gaba ɗaya suka dubi juna, sannan suka girgiza kai da ƙarfin gwiwa.
"Mun ce ba mu da masaniya," cewar rumanah, tana kallon Alhaji Amiru da kyar.
"Tun batan da tayi shekaru da suka wuce, ba mu sake jin labarinta ba," in ji Hajiya Rumanah.
Alhaji Amiru ya kalli kowannensu ido cikin ido, sai ya sake tambaya, "Ina Zaytunah?"
Gaba ɗaya suka mayar da amsa iri ɗaya, ba tare da wata alamar shakku ba,
"Ba mu sani ba."
Sai da ya sake tambaya karo na uku.
A wannan karon ma, babu wanda ya canza furuci, "Ba mu sani ba."
Sai kawai ya murmusa, yana daga kansa sama da jinjina labban sa. A take ya mike tsaye, yana mai daga dogon gyale yana gyara hularsa. Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya ya fita daga falon.
Ba a jima ba, sai gashi ya dawo. Amma ba shi kaɗai ba, yana shigowa tare da wasu sojoji biyu, hannunsu rike da wani mutum da aka daure da ankwa.
Bokan ne!
Bokan da suka taɓa kaiwa don a mata asiri!
Cikin tsananin firgici, suka miƙe gaba ɗaya, fuska ɗauke da fargaba. Hajiya Ladi ta dafe KIRJIN ta, tana duban bokan da tsananin tsoro.
Hajiya Karama ta shiga rawa a tsaye, muryarta na kerma. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!"
Hajiya Rumanah kuwa, sai ta sunkuyar da kai, jikinta na rawa. Muhammad ya daskare a kan kujerarsa, idonsa waje yana kallon mahaifiyarsa da kuma sauran matan. Bai iya cewa uffan ba.
Alhaji Uzairu ya cilla musu wani kallo mai cike da takaici. Kamar wanda ya daɗe yana shakkunsu, amma yau shaidar ta bayyana.
"Kun janyo wa kanku," Alhaji Amiru ya furta da kakkausar murya. "Kun janyo wa kanku!"
Alhaji Uzairu ya sake kallonsu, zuciyarsa na cunkushe da ɓacin rai.
"Na gama zama da ke! Na gama!!" Ya faɗa da ƙarfi, yana daga murya.
A take a wajen, cikin shaidun da ke zaune da tsaye, ya dankarawa hajia rumanah saki uku..
Shiru ya ratsa falon. Kamar an ajiye dutse a cikin iska. Kowacce cikinsu ta ji tamkar an caka mata wuka a zuciya.
"Allah! Uzairu, ka duba da kyau!" Hajiya Ladi ta kurma ihu, tana dafa hannunsa.
"Wallahi ba laifinmu bane! Hajiya Rumanah ce ta ɗora mu a hanya!" Ta ƙara faɗi, hawaye na zubo mata.
Hajiya Karama ma ta durƙusa da sauri, tana roƙo: "Wallahi ita ce ta sa mu! Ba mu da hannu cikin hakan!"
Amma sai Hajiya Rumanah ta yi saurin miƙewa. Idanunta sun cika da hawaye, amma har yanzu tana da ɗan ƙarfin hali.
"Karya su ke yi! Su ne suka sa ni ciki! Ni ba ruwana!"
Muhammad ya cije lebensa. Wannan wane irin abu ne yake faruwa? Mahaifiyarsa ce da ta shuka irin wannan mugunta..
Da zarar suka hango shi, gaba ɗayansu suka miƙe tsaye cikin razana.
"Boka?!?!" Hajiya Ladi ta furta da wata muryar da ba ta saba da ita ba.
Muhammad, ɗan Hajiya Rumanah, wanda tun farko ya kasa fahimtar me ke faruwa, ya ji gabansa ya faɗi. Ya tsure da ganin mahaifiyarsa cikin wannan tashin hankali.
Idanunsu sun ciko da tsantsar tsoro, yayin da boka ya kada baki cikin wata murya mai cike da mugunta,
"Gaskiya ta fito! Dukan ku ne kuka haɗa baki kuka raba Zaytunah da mijinta! Ku ka raba ta da 'ya'yanta! Ku ka hana ta dawowa cikin danginta! To yau kun ƙare!"
Gaba ɗayansu suka daskare, jikinsu na rawa. Kamar su yi magana, amma harsunansu sun makale.
Alhaji Uzairu ya yi ajiyar zuciya mai nauyi. Babu shakka, idanun shi sun cika da takaici, kuma lokaci ne ya nuna masa gaskiya. Bai tsaya wata-wata ba, a take ya dubi su uku, da murya mai ƙarfi da ba ta buƙatar maimaitawa,
"Na sake ki saki uku, saki uku... Uku! Babu sauran zaman aure tsakanina da ke"
Wani irin shock ya kama su. Gaba ɗayansu suka girgiza kai, suka durƙusa suna roƙon sa, amma kamar ya gama yanke hukunci.
Hajiya Karama da Hajiya Ladi sun zabura suna kuka, suna cewa ba su da laifi, wai Hajiya Rumanah ce ta jefa su cikin wannan hali.
Ita kuwa Rumanah ta zabura cikin ɓacin rai, ta nunasu da yatsa tana cewa,
"Karya suke yi! Sune suka ɗaura ni a ciki! Ni ba