wani ‘dai-dai.’ Kin fi su daraja a gare ni."
Tayi murmushi. "To yanzu ka bani izini ko kuwa?"
Ya yi shiru na ƴan sakanni. "Bari in yi tunani."
Nabeeha ta dafe kanta. "Tunani? Akan fita ɗaurin aure?"
A ƙarshe, ya amince, amma da sharadi.
"Ki tsaya cikin mutuncinki. Kada ki yi wata mu'amala da wani namiji da ba dole ba. Ki kula da abinda kike yi. Ki turo min location."
"Na ji." Ta ce tana murmushi.
"Kiyi kyau sosai, amma kada ki burge kowa sai ni."
Nabeeha ta yi dariya. "To ai ko da na so ba zan iya burge kowa ba sai kai."
"Kin gane mana."
A cikin wurin taron, an tsara komai cikin tsari. Mata sun zauna a gefe guda, maza a gefe guda. Amma a wajen siyan baki, an haɗa matan amare da abokan ango.
Sajieedah ta ja hannun Nabeeha. "Mu je mu tsaya kusa da amarya. Daga baya sai a fara siyan bakin."
Nabeeha ta fara tafiya da ita, amma kafin su isa, sai taji ƙarar waya. Fawaaz ne!
Ta ɗaga da sauri. "Hello?"
"Ina kike?" Muryarsa ta sauya, kamar yana canza yanayi.
"Ina wajen bikin mana, kamar yadda na gaya maka."
"Dama kuna siyan baki da abokan ango ne?"
Nabeeha ta rufe ido. "Ya fawaaz… Ni ba ma cikin su fa."
"Ki fita daga wajen nan. Ba na son ki zauna kusa da su."
"To!"
Ba tare da wata gardama ba, ta ja hannun sajieedah suka koma gefe. Sajieedah ta kalleta cike da mamaki.
"Nabeeha! Wane irin saurayi me kishi ne haka?"
Nabeeha ta yi murmushi. "Wannan kishi ne mai daraja. Ki barshi kawai."
Bayan wani lokaci, sajieedah ta kalli gefe, sai ta hango wani mutum yana kallon Nabeeha.
"wani saurayi yana kallonki!" Ta ce tana dariya.
Nabeeha ta girgiza kai. "Wani kuma?"
Duk da ba ta kula shi ba, sai da taji ƙarar waya. Fawaaz ne!
Ta ɗaga da sauri. "Ina jin ka."
"Wani ne yana kallonki?" Muryarsa ta canza gaba ɗaya.
Ta haɗiye yawu. "Ban sani ba."
"To koma gida."
Ta zabura. "What?!"
"Nace ki koma gida! Ko sai nazo na same ki yanzu?"
Nabeeha ta sunkuyar da kai, ta ɗan murmusa. "Toh, zan koma."
A haka dai, ta bar bikin kafin kowa ya ankara!
Bayan ta koma gida, tana shiga ta tarar da Fawaaz yana zaune a falo.
"Kin fiye kyau da yawa." Ya ce yana kallonta da kulawa.
Ta zauna a gefensa, tana kallonsa da murmushi. "Na san dai baka barni na yi farin ciki a wajen bikin ba."
Ya ɗauki hannunta. "Ba zan so wani ya kalle ki da niyya ba."
Ta yi murmushi. "Kai fa akwai matsala!"
Ya yi dariya, ya zuba mata ido da tsananin kulawa. "Kiyi hakuri, my queen. Kishina ne kawai."
Nabeeha ta gyada kai. "Na san hakan. Kuma na yarda da kai."
A haka dai rayuwa da Fawaaz ke tafiya—cike da soyayya, kulawa, da kuma matsanancin kishi!
Bayan kwanaki, Nabeeha ta fara fahimtar cewa Fawaaz ba mutum ba ne mai sauƙin shawara idan har maganar kishinsa ce. A duk inda suke fita tare, yana da wani irin saurin lura da kallo ko motsi da wani namiji zai yi a kanta.
Ranar da Ta Fita Ba tare da Izinin Fawaaz ba
Wata rana, bayan Fawaaz ya fita zuwa aiki, Nabeeha ta kira saj don su fita zuwa boutique don yin siyayya. Tana tunanin cewa idan ta koma kafin Fawaaz ya dawo, ba zai sani ba.
Ta shirya cikin doguwar riga mai kyau da hijabi. Ba ta yi wata kwalliya mai nauyi ba, amma duk da haka ta kasance cikin wani irin kyau na halitta.
Suna tafiya a cikin boutique suna duba kaya, sai wani mai siyar da kaya ya kalleta da murmushi.
"Madam, wannan kayan ya yi miki kyau sosai. Ya kamata ki ɗauka."
Humairah ta kalle ta tana murmushi. "Lallai kuwa! Nabeeha, ki sayi wannan kayan."
Nabeeha ta ɗauki rigar tana nazari, amma kafin ta ce komai, sai taji wata murya daga bayansu.
"Ki ajiye kayan, ki zo mu tafi."
Gabanta ya faɗi. Tana juyowa, sai ta ga Fawaaz yana tsaye a ƙofar boutique ɗin, hannuwansa a haɗe, idonsa cike da tsawa.
Tayi shiru na ƴan dakiku kafin ta ce cikin sanyin murya. "Fawaaz… ka dawo kenan?"
Ya ɗan tsuke fuska. "Ba ma haka ba. Me kike yi a nan?"
Ta kalli saj da ke kallonsu da mamaki. Sai kuma ta ce cikin damuwa. "Na fita ne kawai don yin siyayya."
Fawaaz ya kalli mai siyar da kaya, yana hura hanci kamar zai ƙone da wuta. Sannan ya dawo da kallonsa kanta.
"Wato kin fita ba tare da izini na ba? Kuma wani yana yi miki murmushi yana cewa wannan kayan ya miki kyau?!"
Nabeeha ta buɗe baki zata yi magana, amma sai ya ce: "Mu tafi, yanzu!"
Tayi shiru, ta sauke rigar hannunta sannan ta bi shi da sauri. Saj ta bita da kallo cike da mamaki da sha’awa.
A cikin mota, babu wanda ya yi magana. Sai dai Fawaaz yana tuka motar da wani irin ƙarfin hali, yana riƙe sitiyari tamkar zai balla shi.
Bayan sun isa gida, sai ya tsaya yana kallonta da ido mai cike da kishi.
"Wani ne ya taɓa ki?"
Ta zaro ido. "A’uzu billah! Ya Fawaaz! Me kake nufi?"
"Wani ne ya ce yana son ki?"
Ta saki baki da mamaki. "Kai fa akwai matsala! Ba wanda ya ce haka!"
Ya harare ta. "To me ya sa ya ce miki wannan kayan ya miki kyau?"
Ta taɓe baki. "Ai hakan ba laifi bane. Yana siyar da kaya ne, ya kamata ya faɗi hakan."
Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallonta da tsantsar kulawa. "Ki kula, Nabeeha. Ba zan yarda wani namiji ya kalli matata da wata manufa ba." Kai kace an shafa fatiha yadda yake nuna ikonsa akanta 🤣
Ta yi murmushi. "Fawaaz, kana da matsanancin kishi."
Ya yi murmushi shima. "Ba matsananci ba, sai dai na gaskiya."
🎀🎀
A nutsuwar dare mai annuri, tsit ya lullube anguwar da ake kyalli da fitilu, iska mai laushi na kadawa kamar tana busa saƙon wata soyayya da ke ɓoye. A gaban wani babban gida, wata bakar Jeep mai kyan gaske ta faka a gefen hanya. Wani saurayi tsaye a cikin motar, hannunsa na dama na bisa steering, na hagu kuma yana jan wayarsa don kiran wata ‘yar baiwa.
Captain fawaaz.
Cikakken mutum ne, dogo, mai murɗaɗɗen jiki irin na sojoji. Fuskar tasa cike take da kwarjini da miskilanci, amma yau idanunsa sun zubo da wani yanayi mai cike da salo. Yana sanye da bakar riga mai nauyin gaske, wadda ta kwanta ajikinsa, sai wando jeans mai tsari da sneakers na designers. Lallausan gashinsa yana kwance a saman goshinsa, idonsa masu kauri da tsantsar baƙi suna haskawa da natsuwa, lebensa yana ɗauke da ƙanƙantar murmushi.
Ya danna kiran.
Daga can cikin gida, Nabeeha na zaune akan gadonta, cikin farin riga ta shadda mai tsabta, wadda ta zauna luf akan ta. Gashinta a daure cikin style mai kyau, sai ta lulluba da mayafi irin na ladabi. Idonta suka sauka kan sunan da ya bayyana akan wayarta. "Captain Fawaaz Dawud." Kamar an danna mata wutar lantarki haka ta ji, zuciyarta ta buga, amma ta ɗauki wayar cikin sanyin jiki.
"Ina kika shiga?" Muryarsa mai daɗi da ƙara wa zuciya sauti ya fita daga wayar.
"Uhmm… ina daki." Ta amsa a hankali.
"Fito ki zo."
Shiru ta ɗan yi, kafin ta tashi da natsuwa, zuciyarta na harbawa da nau’in wata soyayya da ta kasa fassara. Har ta ƙarasa bakin kofa, tana jin yadda numfashinta ke sauyawa.
A hankali ta ƙarasa inda motarsa take, tana taku cikin cika alkawarin mace mai haiba da kamun kai. Fawaaz yana kallonta ta cikin madubin motarsa, yadda take tafiya da nutsuwa, yadda hasken fitilu ke bayyana kyanta, har sai da ya ɗan ja numfashi.
Da isarta kusa da motar, ya buɗe ƙofar gaba, ya watsa mata wani kallo na ƙwarjini. "Shigo."
Ba tare da wata gardama ba, ta shigo, numfashinta na luguden wata dabara da zuciyarta ke kokarin ɓoyewa.
Ya juyo gareta, ya sauke idanunsa cikin nata, sannan ya ɗan lumshe su kafin ya ce, "Kin san ba zan kira ki na ce ki fito haka kawai ba, ko?"
Ta ɗan haɗiye yawu, tana jinsa da kasala.
Ya ɗan ɗaga gira, yana kallonta kamar yana nazarinta. "Nabeeha… kin taɓa jin ana soyayya da zuciya amma baka san ta ina za ka fara furta kalmomin ba?"
Numfashinta ya tsinke. Ta kalli gefe. "Ba…" Muryarta ta makale.
Ya saki murmushi, mai ɗan ƙanƙantar gaske, sannan ya ce, "Ina fargabar gaya miki abubuwa da yawa, domin zuciyata tana da SIRRI ka da yawa. Amma daya daga ciki shine…"
Ya ɗan yi shiru, yana kallonta. "Kullum ina tunanin ki."
Nabeeha ta runtse idonta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke, amma bata iya cewa komai ba.
Fawaaz ya ci gaba. "Kina yi min yawa, Nabeeha. Idan kina kusa da ni, zuciyata na yin wani iri. Idan ba ki kusa, zuciyata na jin wani iri. Me kike so inyi da kaina?"
Tayi shiru, tana jin yadda kalmominsa suka daki zuciyarta.
Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon fuskarta da ido mai cike da wani sirrin soyayya. "Kin san tun farko bana tunanin zan iya cewa haka? Amma yanzu ba zan iya ɓoyewa ba."
Ya sauke wani numfashi, ya ɗan yi ƙasa da murya. "I love you, Nabeeha."
Wani irin abu ya tsarga a zuciyarta, idanunta suka lumshe, zuciyarta na dokawa kamar ana bugun ganga.
Ya juyo sosai gareta, yana jira ta ce wani abu. Amma ta yi shiru.
Fawaaz ya ɗan yi murmushi mai taushi. "Ba sai kin ce komai ba. Amma ki sani… zuciyata ta faɗa cikin wani launi da bai taɓa sanin sa ba saboda ke."
Shiru ne ya mamaye motar, sai kukan zuciyoyi biyu da ke tafiyar da soyayya cikin shauki.
MX 🧕
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:49_
Shiru ne ya wanzu a cikin motar, amma zuciyoyi biyu na bugawa da wani irin kida mai nauyi. Idon Nabeeha har yanzu yana lumshe, tana jin kamar a mafarki ake furta mata kalmomin da suka gama ratsa tsokar zuciyarta. Ita ce? Ita ce wadda Fawaaz ke furtawa irin wannan zance? Ita ce zuciyarsa ke kira da son a kusa?
Tayi shiru, ba don bata da amsa ba, sai don bata san da wanne zance za ta fara ba.
Fawaaz ya jinjina kai kadan, yana kare mata kallo. Wani murmushi mara sauti ya sake, sannan ya ce, “Kin san me yasa na kira ki ki fito?”
Ta yi saurin ɗago ido, ta kalle shi. Kallon da ya cika da tambayoyi.
Ya ɗan ja numfashi, yana kallon ta kai tsaye. “Saboda bana iya kwana yau idan ban ji muryarki ba. Idan kika yi shiru kamar haka, zuciyata na jin wani iri.”
Nabeeha ta sauke idanunta kasa, wani abu na tsarga a cikin zuciyarta.
Fawaaz ya matsa kadan, ya jingina hannunsa kan kujera, yana fuskantar ta sosai. “Nabeeha, kin san lokacin da na fara son ki?”
Ta girgiza kai a hankali.
Ya saki murmushi. “Tun farko, tun lokacin da kika fara zama a cikin gidanmu. Tun lokacin da nake yi miki kallon wata yarinya da bata ma san yadda take a zuciyar wani ba.”
Zuciyarta ta buga.
Fawaaz ya ci gaba, murya a hankali, amma da zurfi. “Duk sanda na ganki da murmushinki na nutsuwa, zuciyata na bugawa. Duk lokacin da kika shigo inda nake, sai na tsinci kaina da jin wani abu da bana iya fassara wa.”
Ta lumshe ido, tana jin yadda muryarsa ke saukar mata kamar iska mai daɗin gaske.
“Kin taba ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?” Ya yi murmushi, yana kallonta. “Ina jin tsoro, Nabeeha. Amma na gaji da tsoro.”
Ta ɗago idonta, suka haɗa ido.
Muryarsa ta yi ƙasa, “Idan zan zama maras gaskiya, to zan ci gaba da ɓoyewa. Amma idan ina so na kasance mai gaskiya… to na san cewa son ki ba abin ɓoyewa ba ne.”
Numfashin Nabeeha ya ɗauke na wuni. Duk da yadda take jin zuciyarta na tafasa da wani iri, sai ta samu kanta da cewa, “ya fawaaz… baka tsoron cewa… idan muka biye wa zuciya, wata rana za ta cutar da mu?”
Fawaaz ya ɗan saki murmushi mai cike da kauna. “Nabeeha… idan zuciyata zata cutar da ni saboda ke, to na amince.”
HANKALIn ta ya tsaya. Idanunta suka cika da wani irin yanayi mai wuyar fassara.
Shi kuwa Fawaaz, ya matsa kadan, yana kallonta kamar yana son karanta zuciyarta. “Amma kafin wannan, ki gaya min abu guda daya.”
Tayi shiru.
Ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su cikin wata murya mai taushi. “Kin taɓa jin kamar zuciyarki tana da wani abu da take so ta faɗa min?”
Hannunta ya matse a cikin rigarta. Sai dai bata san me za ta ce ba.
Fawaaz ya ɗan matsa kaɗan, ya ɗaga hannunsa ya shafi steering, yana kallonta. “Ba sai yanzu ba. Ba sai yau ba. Amma zan jira.”
Ya kai hannunsa ya danna makullin motar, sannan ya ce, “Amma kafin nan, ina so ki sani…”
Ta juyo tana kallonsa, tana jiran jin abinda zai ce.
Ya saki murmushi. “Zuciyata ta riga ta yanke shawarar inda take so ta tsaya. Kuma wannan wuri… shine ke, Nabeeha.”
Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta yi wani irin harbi.
Shiru ne ya sake cika motar. Amma shiru mai cike da launin soyayya da murmushin zuciya...
Shiru mai nauyi ya wanzu a cikin motar. Idanun Nabeeha suna ƙasa, zuciyarta na dokawa da ƙarfi, hannunta na lafe a kan cinyoyinta. A karon farko a rayuwarta, ta ji kalmomin da suka ɗaga mata hankali fiye da tunaninta. Kalaman soyayya ne, amma ba irin na wasanni ba. Na gaske ne. Na zuciya ce da ta tsinci kanta a cikin wani soyayyen wuri da bata taɓa sanin tana bukatar sa ba.
Shi kuwa Fawaaz, bai sake cewa komai ba. Ya jingina bayansa a kujerar motar, yana kallonta a hankali. Yana nazarin yadda fuskarta ta canza, yadda idanunta ke ƙoƙarin ɓoye tsoro, da ruɗani, da kuma wani abu mai kama da yarda.
A hankali, ta sauke numfashi. “ya fawaaz…” Ta kira sunansa da wata murya mai laushi.
Ya amsa da kallonta da kyau, sannan ya ce, “Na’am, Nabeeha?”
Ta ɗan haɗiye yawu, tana ƙoƙarin tattaro kalmomin da zuciyarta ke ƙoƙarin gaya mata. “Ba ka jin tsoro? Ka ce kana son zuciyata, amma… ba ka jin tsoron cewa wata rana soyayyar nan za ta cutar da kai?”
Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa. “Me yasa zan ji tsoro?”
Ta ɗan daga ido ta kalle shi. “Domin…” Ta yi shiru.
Fawaaz ya ɗan girgiza kai. “Nabeeha, soyayya ba tsoro bace. So zuciya ce, kuma zuciya bata faɗawa inda za ta faɗa ba. Idan na tsorata da soyayyarki, na fi jin tsoron rayuwa babu ke a cikinta.”
Wani abu ya tsaya a makogwaronta. Ta runtse idonta na wasu ‘yan dakiku.
Shi kuwa Fawaaz, ya ɗan matsa kadan, yana kallonta da kwarewa irin ta namiji da ya yanke hukunci. “Nabeeha, ban kira ki yau don in buƙaci amsar ki ba. Na kira ki ne domin na gaya miki cewa zuciyata ta riga ta faɗa, kuma ba zan taɓa cire ki daga cikinta ba. Kuma ki shirya kullum zanzo tadin zance wurin ki. Tamkar yadda ko wani saurayi yake zuwa wajen budurwar sa kafin aure.."
Ta buɗe idonta, tana kallonsa. “Kana nufin… ba zaka daina ba?”
Ya yi murmushi, amma murmushi mai cike da natsuwa. “Ba zan daina ba.”
Ta sake numfashi, zuciyarta na tafarfasa da abubuwa da dama.
Fawaaz ya duba agogon hannunsa, sannan ya ce, “Ya kamata ki koma ciki.”
Duk da cewa zuciyarta na ɗauke da nauyi, sai da ta jinjina kai. Ta bude ƙofar motar a hankali, ta fito.
Daidai lokacin da ta kai ga rufe ƙofar, muryarsa ta sake fitowa cikin nutsuwa. “Nabeeha?”
Ta juyo, tana kallonsa.
Fuskarsa cike da kwanciyar hankali. “Ko ba yau ba, wata rana zan ji muryarki na amsa.”
Fawaaz ya bita da kallo, murmushi na sauka saman fuskarsa.
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:50_
Shiru ne ya sake cika motar. Amma shiru mai cike da launin soyayya da murmushin zuciya.
Idanun Nabeeha suna ƙasa, zuciyarta na dokawa da ƙarfi, hannunta na lafe a kan cinyoyinta. A karon farko a rayuwarta, ta ji kalmomin da suka ɗaga mata hankali fiye da tunaninta. Kalaman soyayya ne, amma ba irin na wasanni ba. Na gaske ne. Na zuciya ce da ta tsinci kanta a cikin wani soyayyen wuri da bata taɓa sanin tana bukatar sa ba.
Shi kuwa Fawaaz, bai sake cewa komai ba. Ya jingina bayansa a kujerar motar, yana kallonta a hankali. Yana nazarin yadda fuskarta ta canza, yadda idanunta ke ƙoƙarin ɓoye tsoro, da ruɗani, da kuma wani abu mai kama da yarda.
A hankali, ta sauke numfashi. “Ya Fawaaz…” Ta kira sunansa da wata murya mai laushi.
Ya amsa da kallonta da kyau, sannan ya ce, “Na’am, Nabeeha?”
Ta ɗan haɗiye yawu, tana ƙoƙarin tattaro kalmomin da zuciyarta ke ƙoƙarin gaya mata. “Ba ka jin tsoro? Ka ce kana son zuciyata, amma… ba ka jin tsoron cewa wata rana soyayyar nan za ta cutar da kai?”
Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa. “Me yasa zan ji tsoro?”
Ta ɗan daga ido ta kalle shi. “Domin…” Ta yi shiru.
Fawaaz ya ɗan girgiza kai. “Nabeeha, soyayya ba tsoro bace. So zuciya ce, kuma zuciya bata faɗawa inda za ta faɗa ba. Idan na tsorata da soyayyarki, na fi jin tsoron rayuwa babu ke a cikinta.”
Wani abu ya tsaya a makogwaronta. Ta runtse idonta na wasu ‘yan dakiku.
Shi kuwa Fawaaz, ya ɗan matsa kadan, yana kallonta da kwarewa irin ta