KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   38 / 40

111K to 114K   out of 119.4K words

YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE:62_




Fawaaz ya ci gaba da rike hannunta a cikin nasa, yana shafa tafin hannunta da yatsunsa cikin kulawa. Idanunsa sun cika da soyayya, zuciyarsa na bugawa da nutsuwa mai dauke da farin ciki.

"Nabeeha…" ya kira sunanta a hankali, kamar yana jin dadin yadda yake fitowa daga bakinsa.

Ta lumshe ido, zuciyarta na jin nauyin irin kalaman da yake fada mata. Shi kuwa ya ci gaba, yana shafa bayan hannunta da murya mai cike da tsantsar soyayya,

"Kin zamo wata duniya a rayuwata, wadda ba zan iya rayuwa babu ke ba. Kin zamo hasken da ke jagorantar zuciyata a cikin duhu. Kin zamo farin ciki da nutsuwata."

Ya dan janye, yana kallon fuskarta, idonsa cike da tsafta da gaskiya.

"Nabeeha, wallahi, ba zan taba gajiya da godiya gare ki ba. Kin kare mutuncinki, kin kawo min shi cikin daraja da girmanki. Ba zan taba iya godewa Allah da ya bani mace kamarki ba."

Ya kamo kumatunta da hannunsa guda, yana shafa gefen fuskarta cikin kulawa.

"Ke ce wadda na dade ina nema. Ke ce burin zuciyata. Ke ce mafarkina da ya zama gaskiya. Soyayyarki ta shige ni har jini da tsoka."

Ya sumbaci goshinta a hankali, sannan ya sauke numfashi, yana jin yadda dumin jikinta ke ratsa nasa.

"Kin zamo zuciyata, Nabeeha. Kin zamo numfashina. Kin zamo komai a rayuwata."

Sai da ya sake jawo ta jikinsa sosai, sannan ya daga hannunsa sama, yana fadin,

"Ya Allah! Ka albarkaci rayuwarmu. Ka kare mana soyayyarmu daga dukkan sharri. Ka sanya soyayyarmu ta dore har karshen rayuwarmu. Ka bani ikon kareta, kulawa da ita, da girmamata har abada."

Ya sake kallonta, idonsa cike da natsuwa.

"Nabeeha, na yi alkawari… ba zan taba barin ki ba. Ba zan taba bari wani abu ya kawo miki damuwa ba. Zan so ki fiye da yadda nake son kaina. Zan kare ki fiye da yadda nake kare numfashina."

Ya daga hannunta zuwa kirjinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi.

"Kin jiyo?" Ya rada mata a kunne. "Wannan bugu ne da ke ambaton sunanki a duk daƙiƙa. Har karshen rayuwata, Nabeeha, ke ce zabina."

Zuciyarta ta harba da karfi, wata soyayya mai karfi ta lullube ta. Ta dora kanta a kirjinsa, tana jin bugun zuciyarsa yana gauraya da nata.

A haka suka kwanta, jikin juna, zuciyoyinsu na aiki da bugun soyayya daya, ba tare da wata shakka ko kokwanto ba....

Fawaaz ya ci gaba da shafa bayan kanta a hankali, yana jin yadda numfashinta ke gauraya da nasa. Hannunsa na dama ya shafi bayanta a natse, yana jin yanda jikinta ke laushi a jikin nasa.

"Nabeeha…" ya kira sunanta a kasalance, kamar wanda ke jin dadin furta shi.

"Na'am," ta amsa a hankali, muryarta cike da sanyin soyayya.

Ya lumshe ido, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin kaunarta. Sannan ya rada mata da murya mai laushi da shauƙi,

"Kin san cewa kin zamo rayuwa a gare ni? Kin zamo jini a jikina. Idan har babu ke, to babu ni. Kin sani?"

Ta kasa amsawa, kawai ta gyada kanta a hankali, tana jin yadda kalamansa ke ratsata.

Ya sauke numfashi a hankali, yana shafa gefen fuskarta da yatsunsa masu laushi.

"Nabeeha, ke ce mafarkina da ya zama gaskiya. Kin sani? A da, ina tunanin soyayya tamkar tatsuniya ce, amma tun da kika shigo rayuwata, na fahimci cewa soyayya tana da rai, kuma tana da zuciya—kamar yadda nake jin naki yana hadewa da nawa.You are not just my love, Nabeeha. You are my peace, my happiness, and my greatest blessing ."

Ya kai bakinsa kan goshinta, ya sauke wani sumba mai laushi.

"Bana jin zan iya rayuwa babu ke, Nabeeha. Kin cika wani gibi a zuciyata da ban san yana wanzuwa ba. Kin sani kuwa?"

Ta lumshe ido, zuciyarta cike da shauki. Ta dan motsa kadan, tana jin dumin jikin Fawaaz yana lullube ta..

A HANKALI tace,

"You are not just my husband, Ya Fawaaz. You are my best friend, my protector, and the love of my life."

"Duk ran da babu ke, Nabeeha, to tamkar ba ni da numfashi. Duk da nake jin numfashina na fita, amma a zahiri zuciyata tana mutuwa a hankali...Every beat of my heart whispers your name, because you are my everything"

Ya sauke wani ajiyar zuciya, sannan ya ci gaba da shafa gefen kumatunta.

"Godia nake Yaya fawaaz. Allahn daya sa kake so na kamar haka. Allah ya so ka fiye da haka Amin .. ya fawaz Every moment with you is a treasure, and every day I spend with you is a blessing"

"Ni gaskia adena cutata ane Kirana da wani Yaya. Ni ba yayan ki bane. Ni mijin ki ne. Gamu gado daya Muna sha'aninmu. Gaskia a temaka a canzan suna. Loving you is not a choice, Nabeeha. It is a part of my existence, just like breathing.. Nabeeha, the world may change, the stars may fade, but my love for you will never diminish. Bi'ixnillah! You are the only one who holds the key to my heart, and I pray that you never let it go...Nabeeha i don’t need paradise because I have you. And as long as you are with me, my world is complete. Ba karya ba every time I look into your eyes, I see my entire future—beautiful, peaceful, and filled with love...Nabeeha our love is the light that guides me, the warmth that comforts me, and the joy that completes me.ki sani, No matter how many years pass, I will always fall in love with you over and over again. Nabeeha, you are not just a part of my life—you are my whole life."

Nabeeha tayi murmushi tana jujjuya kalaman sa. Hadi da gyara kwanciyar ta tana kokarin mayar da martanin dake cikin zuciyar ta Wanda zasu wanzu a labbanta,

"Hayatim (my life in turkish)If love had a face, it would look exactly like you, your love is my strength, your presence is my comfort, and your arms are my home..no matter where life takes us, as long as I have you, I have everything I need. Ya Fawaaz, au hayatim.. you are my dream come true, my answered prayer, and my greatest gift....i fall in love with you every single day, and I will keep falling for you until my last breath...When I am in your arms, I know I am exactly where I am meant to be...hayatim you are my sun in the morning, my moon at night, and my heart every second of the day.. wallahi if love is a journey, then I want to walk every step of it with you, Yaa Fawaaz."

Tana kaiwa karshe fawaaz ya rarumeta ya rungumeta tsam a faffadan KIRJIn sa.. kalamanta sun ratsa shi sosai. Cike da farin ciki ya cigaba da cewa,

"Ya Allah, Ka sanya Nabeeha ta zamo rabin rayuwata har abada. Ka bani ikon kareta, girmamata, da sanyaya mata zuciya a duk lokacin da take bukata. Ka sanya zuciyata ta zamo mafakar farin cikinta, kamar yadda take mafakar tawa."

Ya sake rungumeta, yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa tare.

"Nabeeha, da ace akwai wata duniya bayan wannan, to wallahi har can zan ci gaba da son ki. Har abada, soyayyarki zata kasance a zuciyata."

Zuciyarta ta harba da karfi, wani irin shauki ya lullube ta. Ta kasa cewa komai, sai kawai ta kara shigewa jikinsa, tana jin dumin soyayyarsa na ratsata.

Shi kuwa Fawaaz, ya lumshe ido, yana jin yadda bugun zuciyarta ke gauraya da nasa. Ya san cewa daga yau, babu abin da zai rabasu. Soyayyarsu ta kasance, kuma za ta ci gaba da wanzuwa har abada.

🎀🎀

Yau Fawaaz da Nabeeha sun shirya zuwa ziyarar Humayrah da Raudah, kannen Fawaaz kuma ‘yan uwan Nabeeha. Tun da safe Nabeeha ke cikin shiri, tana cike da farin ciki. Fawaaz kuwa yana kallonta yana murmushi, yana jin yadda farin cikinta ke ratsashi.

A cikin mota suna tafiya a hankali, hannunta cikin nasa. Ya kalleta da dariya a fuskarsa.

"Kin ga yadda kike murna kuwa? Kamar wata yarinya da za a kaiwa sabuwar shakatawa."

Ta yi dariya, ta dan rankwafa a kafadarsa. "Kai dai bari. Ai na dade ban ga Humayrah da Raudah ba. Kuma na san sun jima suna jiranmu."

Ya dan girgiza kai yana murmushi, ya cigaba da tukinsa har suka iso kofar gidan.

Da jin karar horn din motarsu, sai ga Humayrah da Raudah sun fito da sauri, fuskokinsu cike da farin ciki.

"Ah! Lallai yau mun sha mamaki!" Humayrah ta fada tana dariya.

Raudah ta ruga ta rungume Nabeeha. "Aunty Nabeeha! Kin tuna da mu yau?"

Nabeeha ta rungume ta itama tana dariya. "Ai ba zan iya mantawa da ku ba, kun fi kowa."

Fawaaz ya kalli kannensa yana murmushi. "Ku dai kun fi son Nabeeha a kaina, ko?"

Humayrah ta gyada kai da wasa. "Eh mana, ai ita ce ta fi sanin yanda za ta yi mana lallashi."

Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga gidan cikin nishadi da farin ciki....

Dake gidan Raudah Dana humyrah ba nisa sosai. A estate daya suke. Shi ya sanya humyrah taje gidan Raudah suka hadu gaba daya...

_____

Tunda safe Gwaggo Hafsatu ke zaune a falonta, tana lazimi cikin nutsuwa. Koda aka sanar da ita cewa Fawaaz da Nabeeha za su kawo mata ziyara tare da Humayrah da Raudah, sai ta ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarta.

Bata jima da idar da azkar ba, sai ga su sun iso. Mai gadi ya bude musu ƙofar, suka shigo cikin harabar gidan cikin natsuwa. A lokacin da suka sauka daga mota, suna kokarin shiga cikin gidan, sai ga Gwaggo Hafsatu ta fito zuwa zaure da fara’a a fuskarta.

"Ah! Lallai yau na samu dama. Jikokina sun zo ne gaba ɗaya?!"

Dariya suka yi gaba ɗaya, sannan suka karasa kusa da ita.

Nabeeha ta durƙusa cikin girmamawa, tana fadin, "Granny, ina wuni?"

Ta amsa da fara’a, tana shafa kanta. "Lafiya lau, Nabeeha tah. Yau nasan zan ji daɗi sosai."

Humayrah da Raudah ma suka gaishe ta, sannan suka zauna kusa da ita, suna jin ɗumin soyayyarta.

Daga nan sai ga Major General Dawud ya fito daga sashensa, yana kallon su da murmushi a fuskarsa. "Ah, yau an yi baƙi na musamman."

Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai su suka ce sai na zo tare da su, idan ba haka ba, da an bar ni a gida."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da wasa. "Na san dai ke ce kika sa shi ya zo."

Nabeeha ta yi murmushi tana kallon ƙasa. "Ai ya dace ya zo Gwaggo, ba zai tsira ba."

Suka fashe da dariya gaba ɗaya.

Major General Dawud ya zauna, yana kallon su da kulawa. "Yau na samu ikon zama tare da ku, ya kamata ku kawo min labarai."

Humayrah ta yi dariya, tana cewa, "Ai Baba, tunda ba ka fiye zama a gida ba, yau sai mun dame ka da hira."

Raudah ta gyara zama tana cewa, "Ko da yake, Aunty Nabeeha ita ce zata fi ba da labarai, tunda ita ce ta fi shiru kullum."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da murmushi. "Yau zan zauna na ji yanda kike jituwa da Fawaaz."

Fawaaz ya yi gyaran murya, yana kallon Nabeeha da wasa. "Ai nasan za ta ce kina son jin SIRRIN mu ne."

Dariya suka yi gaba ɗaya.

Bayan dan lokaci, an kawo musu kayan ciye-ciye da ruwan zafi. Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da kulawa, tana cewa, "Yaya kike ji a gidan Fawaaz? Yana kula da ke sosai kuwa?"

Nabeeha ta kalli Fawaaz, sai kuma ta yi murmushi tana cewa, "Eh Gwaggo, yana kula da ni. Kullum yana kokarin faranta min rai."

Gwaggo Hafsatu ta kalli Fawaaz da murmushi. "Ka ga kuwa? Wannan shi ne abin da nake so."

Major General Dawud ya yi murmushi yana gyara zama. "Ai Fawaaz ya gaji da jin kunya, tunda har Nabeeha ke yaba shi a fili."

Suka fashe da dariya gaba ɗaya.

A haka suka ci gaba da hirarsu cikin annashuwa, suna jin daɗin kasancewa tare da juna. Gwaggo Hafsatu ta yi wa Fawaaz da Nabeeha addu’a, tana rokon Allah ya kara musu soyayya da fahimta, sannan ta shafa musu albarka.

Bayan sun jima, suka tafi da alkawarin cewa ba za su jima ba sosae zasu sake dawowa wata ziyarar bi'iznillah.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE:63_



Tunda asuba Nabeeha ta farka tana shirin tafiya gidan iyayenta. Tun a kwanakin baya take shirin wannan ziyara, saboda ta dade ba ta ziyarce su ba. Tun kafin auren ta, Fawaaz ne ya lallaɓa ta suka ɗauki lokaci suna jira har zuwa lokacin da zai dace, don su tafi tare.

A yau kuwa, babu wani uzuri. Sun shirya, suka fita da safe domin yin ziyarar gaisuwa ga mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah, da mahaifinta, Alhaji Uzairu.

A cikin mota, Nabeeha ta naɗe kanta da mayafi, tana kallon tituna cikin farin ciki. Fawaaz ya dan juyo ya kalleta yana murmushi.

"Kin yi shiru, ko kina tunanin yanda za a tarbe mu?"

Ta juyo tana murmushi. "A’a, kawai ina tunanin dadin ganin su ne. Na dade ba na tare da su."

Ya girgiza kai yana cewa, "To yau sai an yi zaman hira mai kyau, tunda ke ma kin zo da shirin dadewa."

Tafiyar ba ta dauki lokaci mai tsawo ba, suka iso kofar gidan. Mai gadi ya gansu, da sauri ya bude musu kofa da murmushi.

"Sannu da zuwa, oga Fawaaz da Hajiya Nabeeha!"

"Yawwa Baba Lawal, ya gida?" Fawaaz ya tambaya, yana ajiyar motarsa.

"Alhamdulillah."

Suna fitowa daga mota, sai ga Hajiya Zaytunah ta fito daga cikin gida da fara’a, har tana dan tafiya da sauri saboda farin ciki.

"Ah! Lallai yau na sha mamaki! Nabeeha da Fawaaz a tare?"

Nabeeha ta durƙusa tana gaida mahaifiyarta, tana murmushi. "Ammi, ina wuni?"

Hajiya Zaytunah ta kama hannunta cikin kulawa. "Lafiya lau."

Fawaaz ya gaishe ta da ladabi. "Ina kwana Hajiya?"

Ta amsa da fara’a. "Lafiya, Fawaaaz. Ya aikin soja. Da na bindiga"

Suka yi dariya gaba daya, sannan suka shiga cikin gida.

Da suka shiga falo, Alhaji Uzairu yana zaune yana karanta jarida. Da ganin su, ya ajiye takardun yana kallonsu da kulawa.

"Ah! Nabeeha da Fawaaz kenan?"

Nabeeha ta durƙusa tana gaida shi cikin ladabi. "Baba, ina wuni?"

Ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, ‘yata. Ya hanya kunzo kalau"

"Eh Baba, Alhamdulillah."

Fawaaz ya gaishe shi da ladabi, yana zama kusa da shi. "Ina wuni, Alhaji?"

Alhaji Uzairu ya amsa da murmushi. "Lafiya lau, Fawaaz. Yau kun kawo mana ziyara ko?"

"Eh, baba"

Nabeeha ta juyo tana kallon mahaifiyarta da murmushi. "Ammi, ya gida? Ya su Hammad?"

"Lafiya lau, Hammad yana can kasar karatun sa"

Suka zauna cikin natsuwa, ana tattaunawa kan abubuwan da suka faru tun daga lokacin da aka yi aure zuwa yanzu. Hajiya Zaytunah na kallon Nabeeha da kulawa, tana jin farin cikin ganin yarinyarta cikin koshin lafiya.

Bayan an yi dan lokaci ana hira, Hisham dan hajia karama ya shigo parlorn. Dake duk yaran suna hannun hajiya Zaytunah itake rike da su a yanzu..

"Kai! Yau dai Aunty Nabeeha ta zo mana?"

Nabeeha ta kalle shi tana murmushi. "Ai kuwa na zo. Kai ma ka dade ba ka ganni ba."

Ya zauna kusa da ita, yana fadin, "Ai dama kullum muna magana da Ammi, tace za ki zo."

Fawaaz ya kalle shi yana dariya. "Kana nufin ba ka yi missing dinta sosai ba kenan?"

Suka yi dariya gaba daya.

Bayan an sha hira, an ci abinci, sannan suka ce za su wuce gidan Alhaji Amiru da bangaren Gwaggo Zainabu.
..

Da suka iso gidan Alhaji Amiru, mai gadi ya bude musu kofa, suka shigo cikin mutunci. Da zarar sun shiga falon, Gwaggo Zainabu ta fito da fara’a tana kallonsu.

"Ah! Nabeeha da Fawaaz! Wannan ziyara ta musamman ce."

Nabeeha ta durƙusa tana gaishe ta. "Gwaggo, ina wuni?"

Ta shafa kanta da kulawa. "Lafiya lau, ‘yata. Yau kun tuno da mu kenan?"

Fawaaz ya gaishe ta da girmamawa. "Mukace bara mu zo mu gaishe ku."

Alhaji Amiru ya fito yana kallonsu da murmushi. "Kun kyauta. Sannun ku da kokari"

Suka zauna cikin falo, ana hira mai dadi. Gwaggo Zainabu na jin daɗin ganin Nabeeha, tana tambayarta game da zamanta a gidan Fawaaz.

"Kin more zaman aurenki ko?" Ta tambaya tana kallonta.

Nabeeha ta yi murmushi, ta kalli Fawaaz sannan ta juyo tana cewa, "Eh Gwaggo, Alhamdulillah."

Fawaaz ya sosa ƙeya yana murmushi. "Ai ko da ba ta fada ba, nasan cewa tana jin daɗi." Sukayi wasan kaka da jika da Gwaggon.

Suka yi dariya gaba daya.

Bayan sun jima suna tattaunawa, suka sha fura, sannan suka ce za

38 / 40