labarta masa. Shiru ya ratsa tsakanin su. Duk da cewa ba ta ganin fuskar wanda take magana da shi, amma ta san cewa wannan labari ya razana shi. Hannunta na kerma, zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi.
"Me kike nufi, Hajiya?" Muryar namijin ta sauya, akwai tsoro da damuwa a cikinta.
"Na ce sojoji sun kama su! Mutumin da ya kira ni yanzu ya ce tawagar fashi an tarwatsa su! Idan har sojoji sun kama su, ba shakka za su tona asirina! Dole ne mu dauki mataki kafin lokaci ya kure!"
Wani guntun shiru ya sake shiga tsakaninsu, sannan murya mai cike da taka tsantsan ta ce:
"Hajiya Rumanah, kina nufin ba a samu wanda ya kubuta ba?"
"Mutum daya ne ya tsira! Kuma ya ce ya bar garin gaba daya. Amma ka san me hakan ke nufi? Idan sojoji suka matsa wa wadanda aka kama, ba shakka za su fadi komai!"
Ta sake matsa wayar a kunnenta, zuciyarta na ci gaba da harbawa. Idan sojoji suka kama shi, kuma suka matsa masa, zai iya tona sunanta da duk wata alaka da take da wannan shiri.
"Dole mu nemi hanyar dakatar da binciken nan." Muryarta ta fito da karfi fiye da yadda ta zata.
"Hajiya, ai kin san wannan abu ba mai sauki bane. Idan har su sojoji sun riga sun kama su, to kuwa abu ya fi karfinmu."
"Baka gane bane?! Idan aka bincike su, kuma suka fadi sunana fa? Ka san me hakan ke nufi? Na gama, na mutu! Kuma ba ni kadai ba, hatta kai ma wannan abu zai shafe ka!"
Tayi tsit na ‘yan dakiku, tana kokarin daidaita tunaninta.
"Yanzu haka Alhaji Amiru bai san komai ba," ta furta a hankali, kamar tana magana da kanta. "Idan kuwa ya gano...!"
Sai ta dafe kanta, zuciyarta na lugude. Tun daga wannan rana, komai zai iya sauyawa. Ta san halin Mai gidan nata Alhaji Amiru, mutum ne mai tsananin taka tsantsan da mutunci, kuma yana da karfin iko. Idan ya gano cewa ita ce ta shirya sace mutanen da aka cece, me zai faru?
A lokaci guda, ta ji wani irin faduwar gaba. Idan ta gaza hana wannan bincike cigaba, to kuwa za ta iya rasa komai!
"Dole ne mu dauki mataki yanzu!" Ta kara nanatawa, da muryar da ta nuna ba za ta amince da wani shiru ba.
"Me kike so muyi, Hajiya?" Muryar namijin ta dawo da taka tsantsan.
Ta dan yi shiru na ‘yan dakiku, sannan ta furta cikin murya mai cike da karfin hali,
"Dole ne mu dauki matakin da zai hana wannan bincike kaiwa garemu. Kuma dole ne a gaggauta!"
Jikinta yana kerma, zuciyarta na bugawa, amma yanzu ta san cewa ba ta da wani zabi. Asirinta yana kokarin tonuwa, kuma dole ne ta dauki matakin da zai hana hakan faruwa.
Tirqashi!!!
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:19_
Jin shiru daga dayan bangaren ya tabbatar mata da cewa maganarta ta yi tasiri. Dole su dauki mataki, kuma dole su gaggauta kafin lokaci ya kure.
"Hajiya, ina jin tsoron cewa..."
"Kada ka ce min haka! Idan muka tsaya muna tsoro, to fa kowa zai sha da kansa!" Ta katse shi da wata irin kasala a muryarta.
Ta tashi daga inda take zaune, ta soma yawo a dakin, kafafunta suna bugawa da sauri a kan falon dakin kamar wadda take kokarin watsa duk wata damuwa da ke zuciyarta.
"Mun riga mun shiga, babu hanyar janyewa. Idan mun yi sake, sai dai mu shirya da kanmu zuwa gidan yari!"
A dayan bangaren, namijin ya sauke ajiyar zuciya. Sai can ya ce,
"To me kike ganin za a yi?"
"Binciken dole ne ya tsaya! Kamar yadda muka saba, dole ne mu hada hannu da wanda zai iya murkushe wannan magana kafin ta fita waje."
"Amma Hajiya, wannan binciken ba karamin abu bane. Idan har su sojoji ne suka sa hannu, ai kinsan ba lallai ne a iya hana su ba."
"Ba su ne matsalata a yanzu ba" Ta katse shi, tana kokarin hadiye tashin hankalinta. "Babban abin da ke gabana shi ne, ina fargabar cewa mai gidah na zai iya jin wani abu! Idan ya fara bincike, to kuwa babu shakka zai gane komai!"
Da zarar ta ambaci sunan Alhaji Amiru, sai shiru ya sake biyo bayan su. Kamar kowane lokaci, wannan sunan yana da nauyi, domin duk wanda ya san shi, ya san cewa ba mutum ne da za a iya yaudara da sauki ba. Idan ya gano cewa matarsa tana da hannu a cikin wannan danyen aiki, babu shakka zai dauki mataki. Kuma ita ta san cewa matakin ba zai zama mai kyau ba!
"Hajiya," murya mai cike da taka tsantsan ta sake bayyana, "ko kin tabbata babu wani da ya riga ya sanar da shi wani abu?"
Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ji wani irin jiri yana neman daukarta. Idan har akwai wanda ya riga ya sanar da shi, to lamarin ya fi ta karfin tunani.
Ta hadiye yawu da kyar, ta ce,
"Ba zan iya cewa da tabbaci ba, amma zan tabbatar kafin gari ya waye. Ka tafi ka kula da abin da na fada maka. Idan wani daga cikin wadanda aka kama ya fara magana, dole mu samu labari kafin sauran mutane!"
"Hajiya, na fahimta. Amma fa wannan lamari yana bukatar shiri sosai."
"Ni zan shirya abin da ya kamata a bangarena. Kai kuma ka kula da naku."
Ta kashe wayar a fusace, sannan ta jefa ta a kan gado. Ta zura ido a cikin dakin, zuciyarta tana tafarfasa.
Kawai lokaci ne yake tsakanin ta da faduwar asiri! Idan ba ta yi gaggawa ba, rayuwarta za ta shiga ruftawa kamar gida mai tushe mai rauni.
Ta dubi agogon da ke gefen gadonta karfe uku da rabi na dare. Tana jin zuciyarta na tafarfasa da damuwa.
" dole ne na fara binciken sa!"
Wannan tunanin ya tsaya a zuciyarta kamar dutsen da aka kafa. Idan har yana da wani bayani da zai kai shi ga gano abin da take boyewa, to dole ne ta dakatar da shi, kafin lokaci ya kure!
Hajiya Rumanah ta kasa zama. Hankalinta ya gama tashi, zuciyarta na tafarfasa da tsoro da fargaba. Ta san cewa idan ta yi sake, komai zai fita hannunta.
Ba tare da bata lokaci ba, ta dauki wayarta, ta fara laluben lambar Hajiya Karama. Hannunta yana kerma yayin da ta danna kiran. Wayar ta fara ringin, zuciyarta na bugawa da karfi.
Bugu na uku, aka dauka.
"Hajiya Rumanah?!" Muryar Hajiya Karama ta fito da alamun bacci a cikinta. "Lafiya kuwa kike kirana a wannan dare?"
"Karama!" Hajiya Rumanah ta furta da wata irin murya da ba ta saba da ita ba,muryar mace mai cike da damuwa da fargaba. "Mun shiga matsala! Babbar matsala!"
"Subhanallah! Me ya faru?" Hajiya Karama ta tambaya, yanzu hankalinta ya fara dawowa hayyacinsa.
"Dan daban nan da muka tura... ya kira ni yanzu!" Ta sha jinin jikinta, sannan ta cigaba. "Karama, sojoji sun tarwatsa su! Duk an kama su, shi kadai ne ya tsira!"
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Hajiya Karama ta furta, zuciyarta na harbawa. "Me kike nufi da an kama su?! Kin tabbata?!"
"Na tabbata, Karama! Kuma kin san me hakan ke nufi?! Idan suka fara magana, to fa...!"
Shiru ya ratsa tsakaninsu. Kowannensu ya fahimci girman abin da ke tafe. Idan har ‘yan fashin suka fadi hakikanin wanda ya dauke su aiki, to babu makawa SIRRIN su zai tonu!
A can bangaren, Hajiya Karama ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce,
"To yanzu me za mu yi?"
"Dole mu dauki mataki kafin su fara magana!"
"Wane irin mataki?"
"Abu na farko shi ne dole mu tabbatar da cewa Alhaji Amiru bai ji wani abu ba. Abu na biyu, dole mu san yadda binciken nan ke tafiya ko sun riga sun samu wata hujja da zata iya kai su gare mu!"
"Tabbas!" Hajiya Karama ta ce cikin wata irin murya mai nuna damuwa. "Yanzu haka ya kamata ki kira Hajiya Ladi mu sanar da ita. Wannan magana fa ba karamin abu bane! Dare yayi ballantana naje wajenta.."
Hajiya Rumanah ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta koma cikin lissafi. Ta san cewa Hajiya Ladi tana da muhimmanci a cikin wannan shiri. Ita ce ta fi sanin yadda za a yi da wannan lamarin, domin ta saba da irin wadannan dabaru.
Ba tare da bata lokaci ba, ta lalubi lambar Hajiya Ladi, ta danna kira.
Bugu biyu kacal aka dauka.
"Rumanah?" Muryar Hajiya Ladi ta fito da karfi, kamar wadda take cikin bacci. "Lafiya kuwa? Me ya faru?"
"Ladi, mun shiga matsala!"
"Matsala kuma?!"
"Eh! Sojoji sun kama su!"
A nan take, Hajiya Ladi ta mike a zaune. "Me kike nufi da sun kama su?"
"Na ce an kama ‘yan fashin nan baki daya! Daya ne kadai ya tsira, kuma ya bar garin gaba daya. Ya kira ni yanzu, yana cewa mutanen da muka saka a sace, sojoji sun kubutar da su!"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Hajiya Ladi ta furta, zuciyarta tana bugawa da sauri. "Rumanah, wannan abu yana da hadari sosai!"
"Na sani!" Hajiya Rumanah ta ce cikin tsawa. "Shi yasa na kira ku, don mu san matakin da za mu dauka kafin komai ya rikide!"
"To yanzu me kike ganin za a yi?"
Hajiya Rumanah ta lumshe idanu, tana kokarin tara duk wata dabara da zata iya amfani da ita.
"Na farko, dole mu samu cikakken bayani kan abin da ya faru. Dole ne mu san inda aka kai wadanda aka kama, su waye ke da alhakin binciken, sannan mu san ko akwai wanda ya riga ya fadawa Alhaji Amiru."
"Kwarai kuwa!" Hajiya Ladi ta ce, tana tunani. "Dole ne mu dauki mataki cikin gaggawa."
"Ba shakka!" Hajiya Karama ta katse su. "Ba za mu zauna muna jiran abin ya zo mana ba. Idan aka gano mu, to mu duka mun shiga uku!"
Hajiya Rumanah ta numfasa a hankali, tana jin zuciyarta tana tafarfasa. Ta san cewa daga wannan dare, dole ne ta tashi tsaye. Komai ya kusa rugujewa, kuma idan ba ta yi taka tsantsan ba, to babu shakka za ta iya rasa komai!
Hajiya Rumanah ta lumshe idanu, zuciyarta na tafarfasa. Hankalinta ya gama tashi, saboda tasirin wannan labari ya fi karfin yadda ta zata. Idan har sojoji sun kama su, kuma aka matsa musu da tambayoyi, babu makawa za su tona asirin ta!
Muryar Hajiya Ladi ce ta katse shirun da ya biyo bayan hirar su.
"Rumanah, lokaci ya kure! Dole mu dauki mataki yanzu kafin komai ya fita hannun mu."
Hajiya Karama ta gyada kai kamar tana kallonta, duk da cewa suna waya.
"Kwarai kuwa! Amma menene mafita? A ina aka ajiye su yanzu?"
Hajiya Rumanah ta dafe goshi, sannan ta ce cikin in'ina, "Ban sani ba har yanzu, amma na aika wani yaronmu da ya binciko. Da zarar ya dawo da bayani, zan sanar da ku."
"Ya kamata mu nemo wanda zai iya dakatar da wannan bincike tun kafin ya zurfafa," Hajiya Ladi ta ce da wata murya mai nuna karfin hali.
Hajiya Rumanah ta gyada kai. "Hakane. Idan muka samu wanda ke da karfi a wannan lamarin, zai iya hana maganar ta fita. Amma fa..." Ta yi shiru na dan lokaci.
"Me fa?" Hajiya Karama ta tambaya.
"Idan har Alhaji ya samu labari, ko kuma wani daga cikin su ya fadi sunana, to ko mene ne sai dai mu fuskanci hukunci."
Wani irin shiru ya ratsa tsakanin su. Kowannensu yana jin nauyin wannan magana.
Hajiya Ladi ce ta daka tsawa. "Ba zai yiwu hakan ba! Babu wanda zai tona mana asiri! Dole mu dauki matakin hana hakan faruwa."
"To yaya za mu yi?" Hajiya Karama ta tambaya, muryarta na nuna damuwa.
Hajiya Rumanah ta dube su cikin tunani. "Dole mu raba kan wadanda aka kama! Dole mu hana su yin magana tare, ko su hadu da wanda zai tunzura su su tona asirinmu."
Hajiya Ladi ta ja dogon numfashi. "Hakane. Amma har yanzu ba mu san wanda ke da alhakin binciken ba. Idan sojoji ne suka karbe shi gaba daya, to kuwa abu ya fi karfinmu."
"Zan bincika. Dole mu san da wa muke yi," Hajiya Rumanah ta ce, sannan ta kara da cewa, "Duk da haka, akwai abin da nake so ku kula da shi."
"Muna jinki," suka ce a tare.
Ta rage murya, kamar tana tsoron wani na sauraren su. "Dole mu yi taka-tsan-tsan da yadda muke mu'amala da Alhaji Idan muka nuna wata alama da zai sa ya fara tunani, zai iya gane komai."
Hajiya Karama ta gyada kai. "Hakane. Amma fa ya kamata mu shirya yadda za mu hana shi samun labarin nan gaba daya."
"Zan dauki matakin hana hakan faruwa," Hajiya Rumanah ta ce da wata murya mai cike da kaushin azama. "Idan har akwai wanda ya fara bincike ko ya samu wata shaida, dole mu dakatar da shi kafin ya kai labari wajen Alhaji"
Hajiya Ladi ta gyada kai, zuciyarta na bugawa da karfi. "Idan dai haka ne, to dole mu hada kai. Komai zai iya faruwa nan gaba kadan."
"Tabbas," Hajiya Rumanah ta ce. "Tun daga wannan dare, dole mu tashi tsaye! Dole mu yi komai don ganin ba a gano mu ba!"
Sun yi shiru na dan lokaci, kowannensu yana tunanin irin hadarin da ke gabansu. Wannan ba karamin aiki ba ne. Idan suka yi kuskure, to komai zai iya rikidewa zuwa masifa!
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞
*PG :20*
*AREWABOOKS VVIP:👇*
https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb
___
Bayan sun kammala waya, Hajiya Rumanah ta sake komawa gefen gadonta, zuciyarta na bugawa da karfi. Dole ta yanke shawarar da zata kare ta kafin komai ya rikide.
Ta janyo wayarta, ta kira wani lambobi da ba kasafai take amfani da su ba. Tana danna kira, numfashinta ya sauya, hannunta yana kerma.
Bugu daya kacal aka dauka.
"Hajiya Rumanah," wata murya mai zurfi ta karanto sunanta, kamar wanda ya san dalilin kiran nata.
"Abubakar," ta furta cikin nutsuwa, "muna da matsala!"
"Na riga da na samu labari," ya ce, yana mai shafar gashinsa da ke gefe. "Meye kike so in yi?"
"Ina bukatar ka binciko min cikakken bayani, wa ke da alhakin binciken nan? Ina aka kai wadanda aka kama? Kuma ina so in san ko wani abu ya riga ya isa kunnen Alhaji Amiru."
"Zan yi hakan," ya ce ba tare da wata jinkiri ba. "Amma fa Hajiya, yana da kyau ki rage motsi a yanzu. Idan kika yi gaggawa da yawa, zai iya jawo hankali."
"Ba na bukatar shawararka!" ta katse shi da takaici. "Ina so ka yi abin da na ce, kuma ka tabbatar da cewa na samu bayani kafin gari ya waye!"
Ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya ce, "Zan tuntuɓi mutanena."
"Kuma," ta kara da cewa, "idan akwai wanda ya fara magana, ko ake shirin tuhumarsa dole a dauki mataki kafin su tona asirinmu!"
Muryarsa ta koma mai nauyi. "Kin san me hakan ke nufi, ko?"
"Na sani!" ta furta da karfi. "Idan har muna son mu tsira, dole mu yi komai da zai hana mu faduwa!"
Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Zan yi abin da zan iya."
"Kar ka bari wani abu ya kubuce mana," ta fadi, sannan ta kashe wayar batare da ta jira amsarsa ba.
A wannan lokacin, Alhaji Amiru yana zaune a falo, yana tunanin maganganun da Hajiya Rumanah ta fada masa da daddare. Wani irin matsanancin tunani ya lullube shi.
Me yasa take jin tsoro haka? Me yasa take ta matsawa da jin ko ya samu labari game da Hajiya Zaytunah da yaranta?
Ya dafa goshinsa, yana jin zuciyarsa na bugawa da karfi. Bai taba tunanin cewa wata rana zai fara zargin matarsa ba, amma yanzu yana jin kamar akwai wani abu da take boyewa!
Sai kawai ya dauki wayarsa, ya kira daya daga cikin mutanensa masu SIRRI.
"Baffa, ina bukatar ka bincika min wani abu."
"Ina sauraron ka ranka ya dade..."
"Ina so ka binciko min game da harin da aka kai kwanakin baya... na sace mutanen nan da aka ce sojoji sun ceto."
A dayan bangaren, Baffa ya dan yi shiru, sannan ya ce, "Alhaji, kana nufin garkuwa da mutanen nan? An ce fa an tarwatsa ‘yan fashin gaba daya."
"Eh," Alhaji Amiru ya ce, yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa. "Ina so in san wa ke da alhakin wannan aika-aika. Kuma ina so a binciko min wanda ke da hannu a bayan fage."
Baffa ya numfasa. "Zan bincika, Alhaji. Amma fa wannan batu yana da sarkakiya."
"Kawai ka yi min bincike. Ina bukatar cikakken bayani cikin gaggawa."
Ya kashe wayar, sannan ya jingina da kujerarsa. Zuciyarsa na bugawa...
Idan har akwai wanda ya shigo da Hajiya Zaytunah cikin matsala, dole ya gano! Kuma idan har wannan abu yana da alaka da wani daga cikin iyalinsa… to, babu shakka, hakan ba zai wuce ba tare da hukunci ba!
Hajiya Rumanah ta gama fidda umarni, amma zuciyarta har yanzu bata samun nutsuwa. Wata zuciya na gaya mata ta bar komai haka nan, amma tsoron abin da zai iya biyo baya ya hana ta yin watsi da lamarin.
Sai da ta tabbatar da cewa komai ya kankama, sannan ta koma dakinta ta zauna akan gado. Amma ko da ta rufe idanu, ba ta iya barci. Maganar Abubakar na daukar mata hankali—"Idan har muna son mu tsira, dole mu yi komai da zai hana mu faduwa!"
Ko me hakan ke nufi, ta shirya tsaf!
A daidai wannan lokacin, wayarta ta dauki kara. Ta daga da sauri, tana sa ran jin labari daga Abubakar ko daya daga cikin mutanenta. Amma lambar da ta bayyana a fuskar wayar ba ita bace.
Gaba daya jikinta ya dauki rawa lokacin da ta ga sunan da ke kan allon wayar. Baban Hammad! Wato Alhaji Amiru,
Numfashinta ya kusa tsaya wa. Me yasa yake kiranta cikin dare haka? Ko dai ya fara jin wani abu ne?!
Ta gyara murya, sannan ta danna amsa.
"Assalamu alaikum." Ta fadi da murya mai sanyin jiki.
"Wa alaikum