KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   6 / 40

15K to 18K   out of 119.4K words

goyon bayan Bala. Sauran suka fara yin tunani.

Shugaban ya gane cewa idan har zai cigaba da tilasta su, to zai iya rasa hannun wasu daga cikin nasa.

Ya hura hanci, sannan ya girgiza kai.

“To, tunda haka ne, sai dai mu mayar da ita ga Hajiya Rumanah ta yi da ita yadda take so.”

Ya juya yana fita daga wajen, yana huci da takaici. Sauran ‘yan fashin suka bi shi, amma akwai wadanda suka yanke shawarar cewa wannan shine lokacin da za su daina wannan aiki.

Bala ya dubi Gora, sannan ya ce cikin sassanyar murya:

“Mun ceci rayuwar su, amma ba mu san makomarsu ba.”

Bayan shugabansu ya bar wajen da fuskar rashin jin daɗi, Bala da Gora suka kalli juna, kowanne yana nazarin abinda ke zuciyar ɗan uwansa. Sun san cewa sun yi kuskuren yin adawa da shugabansu, kuma hakan na iya jawo musu matsala. Amma sun yanke hukunci rayuwar Hajiya Zaytunah da Nabeeha ta fi komai muhimmanci.

Daga can gefe, wasu daga cikin ‘yan fashin suka ja baya, ba sa so su tsoma kansu cikin lamarin. Wasu kuwa sun riga sun yanke shawarar cewa wannan aiki ba zai ci gaba ba.

Bala ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa tana dukan uku-uku. Ya san cewa idan aka mayar da Hajiya Zaytunah da Nabeeha ga Hajiya Rumanah, to babu shakka za su fuskanci matsananciyar azaba. Dole ne su yi wani abu da wuri.

“Gora,” ya ce da ƙasa da murya. “Dole mu ceci su kafin a kai su wajen Hajiya Rumanah.”

Gora ya gyada kai, yana jin wani irin karfin gwiwa na ratsawa cikin zuciyarsa.

“Amma yaya za mu yi hakan?” Gora ya tambaya. “Shugabanmu yana da ido a ko’ina. Idan muka yi kuskure, mu da kanmu za mu rasa rayukanmu.”

Bala ya dube shi, yana murmushi mai cike da rashin tsoro.

“Idan muka tsaya muna tunani sosai, lokaci zai kure mana. Mu aiwatar da shirinmu kafin su kai su wajen waccan muguwar mata.”


Bala ya sake duba dakin da aka daure Hajiya Zaytunah dasubNabeeha. Idanunta sun cika da hawaye, sai dai yanzu ta fahimci cewa akwai wani abu da ke faruwa tsakanin ‘yan fashin. A ganinta, kamar dai ba dukkansu ne suka amince da azabar da aka bukaci a yi mata da ‘yayanta ba.

Bala ya juya ya dube Gora.

“Zan nemo wata mota, sai mu fita da su cikin dare.”

Gora ya sauke numfashi. “Kana nufin mu fitar da su ba tare da wani ya gane ba?”

Bala ya gyada kai. “Haka nake nufi. Idan muka yi hakan cikin sauri, kafin shugabanmu ya dawo daga shirin aikawa da Hajiya Rumanah sakon cewa an kama su, to za mu iya fitar da su lafiya.”

Gora ya sake duban sauran ‘yan fashin da ke gefe. “Me kuke tunani?”

Daya daga cikin su ya numfasa. “Ni dai na san cewa idan suka koma wajen waccan mata, za su fi shan wahala fiye da yadda aka yi musu a nan.”

Wani daga cikinsu ya ce: “Ina tare da ku. Idan dai zamu cece su, dole ne mu yi hakan yanzu.”

Da dare sosai, Bala da Gora suka shiga cikin dakin. A hankali, suka warware igiyoyin da ke daure Hajiya Zaytunah da Nabeeha da Hammad.

“Ku yi shiru,” Bala ya ce da su, yana duban kofa don tabbatar da cewa babu wanda ya lura da su. “Za mu fitar da ku daga nan, amma dole ne ku bi umarninmu.”

Hajiya Zaytunah ta kasa magana, zuciyarta cike da tsoro da fargaba. Ita dai ba ta fahimci dalilin da yasa wasu daga cikin ‘yan fashin suka canja ra’ayi ba, amma duk da haka, ta san cewa wannan shi ne damar da zasu iya samu don su tsira.

Nabeeha ta kalli Bala da Gora, tana jin wani irin fargaba. Amma lokacin da ta kalli idon Gora, ta ga baƙon abu a ciki, ba irin mugunta ba ne da ta saba gani daga sauran ‘yan fashin, sai dai

Bala ya riko mayafin hannun Nabeeha , Hammad da Hajiya Zaytunah yana matsawa cikin duhun dare. A hankali suke tafiya a gefen shinge mai katanga da ke kewaye da sansanin ‘yan fashin. Gora kuma ya tsaya yana saurarawa, yana jiran lokacin da zai tayar da hankali don jawo hankalin sauran ‘yan fashin zuwa wani wuri daban.

Hajiya Zaytunah tana jin jikinta yana rawa, ba don sanyi ba, sai don tsananin fargaba. Idan har suka yi kuskure, to ba shakka za a kama su kuma wannan wata babbar matsala ce da ba za ta iya fatan tsira daga gare ta ba.

Nabeeha kuwa ta kasa gane yanda ake tafiyar da lamarin, zuciyarta cike da addu’a da fatan samun mafita. Duk tsawon rayuwarta ba ta taba jin tsoro irin wanda take ji a wannan lokaci ba.

“Ku ci gaba da tafiya a hankali,” Bala ya rada musu a kunne. “Muna kusa da inda na ajiye wata mota da za ta fitar da mu daga nan.”

A cikin wannan lokaci, Gora ya matsa zuwa wani wuri da yake kusa da wani babban gangare. Ya dauki wata babbar duwatsu, ya jefar da ita a wani bangare na sansanin da ke kusa da inda wasu daga cikin ‘yan fashin suke gadin shinge.

A take, hayaniya ta tashi!

“Wane ne a can?” Wani daga cikin masu gadi ya daka tsawa, yana juyawa da bindiga a hannunsa.

“Wata kila wani abu ya fado,” wani ya ce.

“Sai dai mu duba don tabbatarwa,” wani daga cikinsu ya kara da cewa.

Suna tafiya don duba wajen, hakan ya samar da dama ga Bala da su Hajiya Zaytunah su ci gaba da tafiyarsu ba tare da an gano su ba.

Bala ya kai su zuwa wata tsohuwar mota da ke kusa da wata hanya da ke gefen daji. Ya bude kofar motar cikin hanzari, yana duban Hajiya Zaytunah da Nabeeha.

“ku shiga cikin mota,” ya umarce su.

Ba tare da bata lokaci ba, suka shige motar, zuciyarsu na bugawa da sauri. Bala ya kunna motar, sai dai a lokacin da ya fara juyawa don fita daga wurin, wani mummunan abu ya faru.

Daya daga cikin ‘yan fashin ya lura da motsin motar, sai ya daka wata tsawa da karfi.

“Waye ke cikin waccan mota?!”

A take, karar harbi ta biyo baya!

“Sun gano mu!” Nabeeha ta furta cikin tsananin firgici.

Bala ya cije lebe, yana danna motar da karfi don ya fice daga wurin. Motar ta yi kara, sai ya ja birki da karfi, yana kokarin kaucewa harsashin da ke shigowa.

Wani daga cikin ‘yan fashin ya ruga zuwa inda suke, yana kokarin harbawa, amma kafin ya samu damar yin hakan, Gora ya bayyana daga gefe, yana rike da bindiga!

“Ka ajiye makamin nan ko kuma na harbe ka!” Gora ya daka masa tsawa.

Mutumin ya tsaya cak, yana kallon Gora da mamaki. Bai taba tunanin cewa daya daga cikin ‘yan uwansa zai yi masa haka ba.

Kafin ya samu damar yin wani abu, Gora ya kwada masa kwallo da hannu, ya fadi a kasa sumamme!

Bala ya kalli Gora, yana jin zuciyarsa tana bugawa da sauri.

“Shiga mota!” Bala ya ce da Gora.

Ba tare da bata lokaci ba, Gora ya bude kofar motar, ya shiga cikin hanzari. Bala ya danne motar da karfi, suka fice daga sansanin da gudu.

‘Yan fashin da suka lura da abin da ke faruwa sun ruga da gudu suna kokarin bin su da harsasai, amma Bala ya ci gaba da tafiya da sauri, yana kaucewa harsashin da ake harbawa.

Bayan tafiya da gudu har na tsawon mintuna, Bala ya shiga wata hanya da ke cikin daji, ya rinka bi da hankali don kada su bar wata alama da za a iya binsu da ita.

Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah, tana jin hawayen da suka cika mata idanu.

“Mun tsira, Ammi?” Ta tambaya cikin rawar murya.

Hajiya Zaytunah ta rungume ta da karfi, tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Daya hannunta Kuma takamo na hammad tana damtsewa

Bala da Gora kuwa suna jin nauyin da ke kan zuciyarsu yana raguwa. Sun san cewa ba su gama ba tukuna, amma sun san abu daya sun ceci rayuka, kuma hakan shi ne babban nasara.

Daga nesa, fitilun wasu motoci suka bayyana a bayan su, alamar cewa akwai wadanda suke kokarin bin sawu.

Sai suka ci gaba da tafiya cikin duhun dare, rayukansu suna hannun lokaci…


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*


_PAGE: 11_


A dai-dai lokacin da Bala da Gora suka tsere da Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha, wani sakon gaggawa ya isa wajen Hajiya Rumanah. Wani daga cikin mutanenta ya durƙusa gabanta yana sauke numfashi, alamar gajiya da hanzarin isowa.

“Hajiya, akwai matsala!”

Hajiya Rumanah ta ɗago daga inda take zaune a cikin wani falo mai ɗauke da kayan alfarma. Idanunta suka kaɗa, alamar ba ta da niyyar karɓar wata matsala a wannan lokacin.

“Wace irin matsala?!” Ta tambaya, muryarta cike da ƙwarin gwiwa.

Mutumin ya haɗiye yawu. “‘Yan fashin da aka ba aikin sun yi kuskure. Wataƙila wasu daga cikinsu sun canza ra’ayi, suka fitar da matar da yaranta daga hannunsu.”

Hajiya Rumanah ta tsinci kanta tana matse mayafinta da ƙarfi, zuciyarta na bugawa da sauri.

“Ba abu ne mai yiyuwa ba! Me kake nufi?!”

Mutumin ya sunkuyar da kansa. “Har yanzu ba mu da cikakken bayani, amma an ga wata mota da ta tsere daga sansanin. Shugaban ‘yan fashin yana kokarin bin sawu.”

Hajiya Rumanah ta tashi daga kujerarta cikin zafin rai.

"Ina bukatar su dawo hannuna da wuri! Ku nemo su, ku kamota, ko da kuwa za a kashe wanda ya aikata wannan cin amanar.”

Ta juyo ta kalle shi tana ɗaga hannu.

“Kira Shugaban ‘yan fashin! Ina son jin bayaninsa.”

A can gefen Bala da Gora kuwa, motarsu na cigaba da tafiya da sauri, suna kokarin kauce wa duk wata barazana. Amma duk da haka, suna jin tsoron cewa ba su gama da matsalar ba.

“Mun tsira daga sansanin, amma har yanzu ba mu fita daga haɗari ba, saboda manyan dazuka ne. Sanda Wanda muke cikinsa babban dajine mai zurfin kilomitoci” Bala ya faɗi, yana tsananta riƙon sitiyari.

Nabeeha ta cije leɓe, tana jin tsoron irin makomar da ke gabansu. Hajiya Zaytunah kuwa tana ta yi addu’a a cikin zuciyarta.

A can bayan su, fitilun motoci sun bayyana, alamar cewa suna bin sawu!

Gora ya juya da sauri ya duba ta bayan gilashin mota.

**

Bala ya yi kokarin tsayar da motar da sauri a bayan wani tsohon gini mai fashe-fashe. Wurin ya yi shiru sosai, kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Ya juyo ya dubi Gora, yana busar da iska cikin gajiya.

“Muna bukatar mu ɓuya a nan har sai mun san inda suke.”

Gora ya duba kewayen wurin, zuciyarsa tana bugawa da sauri. “Amma idan sun same mu nan fa? Za su iya harbe mu kafin mu yi wani yunƙuri.”

Bala ya sauke ajiyar zuciya. “Muna da zabin da ya fi haka? Idan muka cigaba da tafiya cikin dare, za su iya bin sawun mu.”

Hajiya Zaytunah ta kalli su cikin damuwa. “Kun tabbata wurin nan zai iya kare mu?”

Bala ya juyo ya dubeta. “In Allah Ya yarda, muna da damar tsira. Amma dole ne ku bi umarninmu.”

Nabeeha ta kalli kewayen ginin, zuciyarta na dukan uku-uku. Wurin ya yi tsit, sai dai shure-shuren namun daji da iska mai kaɗawa. Ta kama hannun Hajiya Zaytunah, tana jin fargaba.

“Ammi, me zai faru da mu?” Ta tambaya a hankali.

Hajiya Zaytunah ta dafa kanta, tana murmushin da ke boye tsoro. “Za mu tsira, In Sha Allah.”

Bala da Gora suka fita daga motar suna lekawa don ganin ko akwai wata hanyar guduwa idan har abin ya tashi. Sun san cewa idan ‘yan fashin suka iso, ba za su tsaya da sunan neman bayani ba za su iya harbinsu a take.

A can gefe, hayakin tayar motoci ya bayyana daga nesa. Fitilun su na haskawa cikin duhun dare, alamar cewa ‘yan fashin sun kusa isowa.

Gora ya runtse ido. “Bala, ba su yi kasa a gwiwa ba. Har yanzu suna binmu.”

Bala ya furzar da iska mai zafi. “Idan sun shigo nan, za mu yi yunkurin juyar da hankalinsu. Idan na ce ku gudu, ku gudu babu ja da baya.”

Hajiya Zaytunah ta dubi Bala cikin damuwa. “Ya kuke tunanin za mu tsira daga gare su?”

Bala ya numfasa. “Ina da wani shiri, amma dole ne mu kasance cikin shiri.”

Gora ya kalli Bala cikin shakku. “Kana nufin za mu ƙaddamar da hari?”

Bala ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin da zai faɗa. “Ba mu da wata dama. Ko dai su kama mu su kai mu hannun wadda tasa aka kawo ku, ko kuma mu yi kokarin tsira da kanmu.”

Nabeeha ta ji jikinta yana rawa. Wannan shi ne karo na farko da take jin yadda rayuwa ke iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci.

Kafin su samu damar ci gaba da magana, karar harbi ta tashi!

“Sun gano mu!” Gora ya faɗi da murya mai ƙarfi.

Bala ya yi sauri ya ja Hajiya Zaytunah da Nabeeha zuwa bayan ginin don su kauce wa harbin.

‘Yan fashin sun riga sun kewaye yankin. Muryar shugabansu ta tashi cikin tsawa.

“Kun zata za ku tsere daga gare mu? Ku fito ko kuma mu cinna wuta a wurin nan!”

Bala ya matse hakora. “Dole ne mu yi wani abu yanzu ko kuma su kama mu!”

Gora ya janyo wata tsohuwar sanda da ke kusa, yana duban Bala. “Ko da zan mutu, ba zan bar su su kama su ba!”

Bala ya dubi Gora, sannan ya dube su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Lokaci ya yi da za su yanke hukunci, zai zama ko dai tsira ko shan wahala a hannun Hajiya Rumanah.

“Mu shirya. Komai zai iya faruwa a wannan daren.”

🎀🎀

A daidai lokacin da harbin ya lafa, Bala da Gora suka sami damar janye Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha daga wajen. Sun fice daga ginin da suka buya, suka samu wani wuri mai tsaro inda za su huta kadan.

Duk da cewa har yanzu suna cikin fargaba, sun san cewa sun tsira daga hannun ‘yan fashin, amma har yanzu akwai tambayoyi da ke bukatar amsoshi.

Hajiya Zaytunah tana dafe da kirjinta, zuciyarta na bugawa da sauri. Bata fahimci dalilin da yasa aka kama su ba, balle kuma wanda ya kitsa wannan sharrin. Ta kalli Gora, murya na rawa.

“Don Allah, ku gaya min, waye ya sa aka kama mu? Me muka yi da har za a dauki hayar ‘yan fashi don su tsare mu kamar wasu ‘yan ta’adda?”

Gora ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya. Ya san cewa dole ne su fada gaskiya, domin babu wani dalili da zai hana hakan. Ya dube ta, fuskar nan tasa cike da alamar tausayi.

“Hajiya…” Ya furta a hankali. “Wata mata ce mai kudi ce ta biya mu don mu kama ku. Ita ce ta sa a kawo ku sansanin ‘yan fashi.”

Hajiya Zaytunah ta kara matse mayafinta, zuciyarta na tsananta bugawa. “Wacece wannan mata? Wacece take da wannan azancin da za ta iya yin haka a kaina?”

Gora ya yi shiru na dan lokaci, yana tunanin ko zai iya fadin hakan. Bala ya jefa masa harara, yana nuni da cewa lokaci ya kure, kuma bai kamata su boye komai ba.

A karshe, Gora ya numfasa, sannan ya ce da karfi,

“Sunanta Hajiya Rumanah.”

Wani irin razana ya bayyana a fuskar Hajiya Zaytunah. Ta ji kamar an jefata a wata duniya da ba ta da alaka da ita. Kafafuwanta sun yi sanyi, zuciyarta ta yi nauyi.

“Me… me kace?” Ta tambaya, kamar bata ji abin da Gora ya fada ba.

Gora ya sake numfasa, yana jin tausayin yadda fuskar Hajiya Zaytunah ta rikice.

“wasu mata ne, Amman babbar ciki Hajiya Rumanah ce ta biya mu don mu kamo ku. Itace Kuma duk ta tsara dukkanin nau'ikan azabobin da akai mu ku."

Hajiya Zaytunah ta ja da baya, hannunta yana rawa. “Hajiya Rumanah?” Ta sake maimaitawa da murya kasa-kasa.

Wata zufa ta fara keto mata a goshinta. Kamar yadda take tsaye haka ne zuciyarta ta dauki nauyi, numfashinta ya soma hauhawa. Matar yayan mijin… ‘yar uwarta ta jini… . Yar wan mahaifin ta. Da aka haife su rana daya, akai auren su rana daya, Suka Kuma auri mazaje yan gidah daya. Ita ce ta jefa su cikin wannan azaba?

“Ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba!”

Hajia Zaytunah ta fada tana girgiza Kai cikin tabbatarwa..

Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah cikin mamaki. Ita ma bata fahimta ba. “Wacece Hajiya Rumanah, Ammi?”

Hajiya Zaytunah ta ji zuciyarta kamar zata fashe. Ta runtse ido, tana jin yadda wannan gaskiya take cin ranta. Tana jin tamkar ba ainihin duniyarta take ba...Sam bata samu damar amsa tambayar Nabeeha ba.

Ta kara kallon Gora, zuciyarta cike da shakku da rashin yarda.

"Don Allah, ku fada min, me ya sa ta aikata haka? Me yasa ta dauki hayar ‘yan fashi don su kama ni? Me nayi mata?” hajia zaytunah ta tanbaye su don baki daya kwakwalwar ta da tunanin ta sun ki amincewa da Hajia rumanah ce tayi haka.

Bala ne ya amsa wannan karon. “Ba mu da cikakken bayani, amma daga abin da muka ji daga bakin shugaban ‘yan fashin, Hajiya Rumanah tana so ta wulakanta ku, a yi muku wani abu da ba zai taba mantuwa ba...a Kuma kashe ku a sanda ta umarta. "

Idanun Hajiya Zaytunah suka ciko da hawaye. “Na amince da ita… Na dauke ta tamkar uwar mu daya ubanmu daya. mijinta yayan mijina ne, Mahaifin ta yayan mahaifi nane. Rana daya aka haife mu. Tare muka tashi tun yarinta. Karewarta rana daya aka daura auren mu. Kai komai namu iri daya ne. … yaya za ta iya min haka?”

Nabeeha ta matso kusa da ita, ta rike hannunta. “Ammi…” Ta kira sunanta da murya mai rauni.

Hajiya Zaytunah ta girgiza kai, tana jin zuciyarta tana karyewa.

“Hakan ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba…”

Amma zuciyarta ta sani, Idan har Gora da Bala sun fadi haka, to akwai gaskiya. Kuma hakan yana nufin akwai wani abu da take bukatar sani.

Bayan ‘yan dakiku, Hajiya Zaytunah ta dago kanta. Idanunta sun canza, sun yi ja. Ba hawaye take ba yanzu, Ba tsoro take ji ba, sai fushi da ƙudurin gano dalilin da yasa Hajiya Rumanah ta aikata wannan danyen aiki.

“Dole ne in san gaskiya.”

Ta juyo

6 / 40