KIRJIN MAI HANKALI BOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Tknovels

Chapter   1 / 40

1 to 3K   out of 119.4K words

WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE... AKAN NERA DARI BIYAR KACHAL.TUNTUBENI TA 09134848107 DON MALLAKAR NA KU...


*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO:_*


بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai..... Assalamu Alaikum Wa Rahamatullahi Wa Barakatuh!!_

_Barkan mu da dawowa daga hutun Ibadah!! Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Allah yasa muna daga cikin yantuttun bayin sa. Allah kuma ya biya mana dukkanin bukatun mu. ya kuma yafe mana kurakuren mu. Aameen. Fatan anyi sallah lafiya? Toh Allah ya karba mana Amin... Zafafa na miko gaisuwa da dinbin fatan alkhairi agare ku😍🎀_


_PAGE 1:_

°•°•°•°•

**Tamkar* a mafarki, tana jin kamar zuciyarta ta fada cikin wani irin nauyi da ba ta taba jin irinsa ba. Kalaman Fawaaz sun kasance kamar wani sako daga duniyar da ba ta taba tsammani ba, amma a lokaci guda, suna da karfi fiye da yadda take iya dannewa.

Hannunta yana rawa, ta sauke ajiyar zuciya, amma kafin ta samu damar kara tunani, karar kararrawar motar yan fashin dake gefe ya katse ta. Ta dago kai da sauri, zuciyarta tana dukan uku-uku, tana kallon yadda daya daga cikin 'yan fashin ya matsa kusa da su da wata matsananciyar fusata a fuskarsa.

"Nace maki kiyi shiru, ko kuwa kina bukatar a koya maki darasi?" Ya fadi cikin tsawa, yana daga hannunsa da wata sanda kamar zai buga musu.

Nabeeha ta razana, ta rufe idonta a firgice, amma kafin ma ta iya tunanin yin wani abu, Hajiya Zaytunah ta tare ta da jikinta, tana cewa da murya mai sanyi,

"Don Allah, ku yi hakuri. Ta dan razane ne, amma ba zata sake ba."

Nabeeha tana jin kamar ana karanta mata labari ne daga wani littafi na soyayya. Amma wannan ba labari bane, Fawaaz ne, mutum mai rai da numfashi, wanda bai taba nuna wani irin motsi na soyayya a kanta ba, sai yau.

Tana jin bugun zuciyarta yana karuwa, amma a lokaci guda tana cikin wani hali mai wahala. Wani bangare na zuciyarta yana son amsa sakon nan take, yana son fadin abin da ke zuciyarta,. Amma wani bangare kuma yana ji kamar ba wannan ne lokacin da ya dace ba. Yanzu haka suna hannun 'yan fashi, cikin yanayi na tsoro da fargaba, kuma har yanzu ba su san yadda za su kubuta ba.

A hankali ta dauke idonta daga kan hannunta da aka daure da igiya, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Idanunta suka sauka kan Hajiya Zaytunah wacce ke kokarin kwantar musu da hankali.. Ta dan kakaro murmushi tana kokarin danne hawayen dake kokarin zuba daga idanun tah...

A zuciyarta, Nabeeha tana jinjina irin tashin hankalin da suke ciki. Amma zuciyarta ba za ta iya musun yadda sakon Fawaaz ya shigeta ba. Tun farkon haduwarsu, ya kasance mutum mai nisa, miskili wanda bai fiye magana da ita ba sai idan ya zama dole. Musanman da shi din magana ta fatar baki ma bata dame shi ba. Ki cikin yan uwansa da suke ciki daya baka Jin bakinsa..Amma yau… yau ne rana ta farko da ya furta wani abu mai kama da soyayya a gare ta.

Hannunta na rawa, sai ta sake duban hannun ta..Tamkar wayar ce agabanta. Idanunta da kwakwalwar ta suna tariyo mata sakonnin fawaaz,

“Ki min alkawari cewa za ki tsaya min, Nabeeha. Ko bayan wannan wahala, kar ki guje ni.”

Sai ta runtse idonta, ta jin cunkoso a KIRJIN ta. Me zai hana ta amsa? Idan har akwai lokacin da zata fara tunanin Fawaaz da gaske, ba a cikin irin wannan hali ba. Amma zuciyarta ta riga ta furta amsa tun kafin kwakwalwarta ta tantance.

Kafin ta iya cigaba da dulmiya a duniyar fawaaz data lula, Razananniyar karar sautin muryar wani daga cikin yan fashin ya kurma kururuwa yana cewa,

"Lokacin lallasa yazo.."

Yan fashin sukayi kansu, Suka sake tamke daurin hannayensu da kafafuwansu, sai suka fara azabtar da su ta hanyoyi daban-daban.

Hajiya Zaytunah, wacce take da jiki da nauyi, an rike ta da karfi yayin da take kokarin kare 'ya'yanta Nabeeha da Hammad. Wani daga cikin 'yan fashin ya watsa mata mari mai karfi da ya gigita ta. Idanunta sun yi jajir saboda zafin dukan da ta sha. Kafin ta farfado daga girgizar marin, wani daga cikinsu ya fizgo gashinta da karfi, yana jan kanta zuwa gefe.

Nabeeha kuwa, duk da kokarin karfafa zuciyarta, ta kasa jurewa azabar da take sha. Wani dan fashi ya dunkule hannunsa ya kwada mata naushi a gefen cikinta, wanda ya sa ta zube a kasa da radadin ciwo. Ta narke, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Hawayen da ta kasa shanye wa sun zubo kan kumatunta.

Ya yinda wani daga cikin 'yan fashin ya rike hannun Hammad, wanda bai cika girma sosai ba, ya yi kokarin daga shi sama yana mai tsoratar da shi. Hammad ya yi kururuwa da murya mai tsanani, yana rokon su su sake shi. Amma maimakon su tausaya masa, sai suka dinga dukansa da sanduna a cinyoyi da hannayensa.

A cikin wannan halin, Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Ta durkushe tana rokon su,

“Don Allah, ku yi hakuri! Ku bar yaran nan haka, ku duke ni a madadin su!”

Amma 'yan fashin sai suka fashe da dariya, daya daga cikinsu yana cewa

"Ai ba mu dauko ku don sauki ba! Za ku dandana bakin ciki kafin mu raba ku da iska"

Duk azabar da suke sha, babu wanda ya kawo musu dauki. Duhu ya lullube su, tsoro ya cika zukatansu, kuma babu alamun kubuta a gaban su…

A yayin da azabar ta kara tsananta, Nabeeha ta kasa motsi, jikinta yana karkarwa saboda radadi da tsananin tsoro. Idanunta sun cika da kwalla, amma ta runtse su da karfi, tana fatan mafarki ne kawai, ko kuma wata rana mai kyau za ta farka ta ga komai ya wuce.

Hajiya Zaytunah ta kokarta ta tashi, amma wani dan fashi mai dogon gemu da idanu masu kaushi ya yi birgima da ita gefe, yana dariyar mugunta. Ya kama mata hannu, yana matsawa da karfi, har sai da ta saki wata kara mai tsanani.

“Ai yau ne ranar ku! Babu wanda zai cece ku!” ya fada da wata murya mai cike da izgilanci.

Hammad ya ci gaba da kiran mahaifiyarsa, yana kuka da karfi. Amma maimakon jin tausayinsa, daya daga cikin ‘yan fashin ya rike shi da karfi ya wurgar da shi gefe, har sai da ya bugi bango, Hammad ya saki wata kara, jikinsa yana rawar sanyi.

Daya daga cikin ‘yan fashin, wanda yake kamar su ne shugabansu, ya matso kusa da Hajiya Zaytunah yana kallonta da mugunta yace,

"Meyasa ake son aga bayan ku? Ku din su wanene? Kuna da babban daraja a wajen wadanda suka turo mu!” ya fada, yana gyara bindigar da ke rataye a kafadarsa.

Hajiya Zaytunah ta kasa magana. Hankalinta yana kan yaranta da ke kuka da radadi. Sai dai kafin ta iya cewa wani abu, sai daya daga cikinsu ya zaro waya ya fara daukar bidiyo.

“Muna so ki amsa mana tambayoyi!” ya fada yana zungurin Nabeeha da gefen takobinsa.

Sai da Nabeeha ta saki kara, jikinta yana karkarwa. Sannan daya daga cikinsu ya matso kusa da ita yana fadin,

"Da alama ke ce kadara a cikin ku! Domin an ja mana kunne akan ki sosai, Wannan ne zai sa mu ci gaba da azabtar da ku har sai mun ji daga gare su"

"Dan Allah kuyi hakuri. Wallahi mu ba kowa bane." Nabeeha ta fada cikin muryar ban roko da lallashi

"Bude muryar ki sosai kiyi magana..."

"Wallahi mu ba kowa bane. Dan Allah kuyi hakuri ku sake mu" Ta karasa fada tana fashewa da matsanancin Kuka..

Tsoro ya sake lullube su. Wane irin hali ne sukatsinci kansu? Shin akwai mai ceton su?...


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09032345899_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____






MX🎀
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_


*_The Vault Of His Secrets_*


_®️NANA HAFSATU (MX)_


_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*


_PAGE:2_


Azaba da tsoro sun cika sararin da suke ciki. Numfashin Nabeeha yana fita da kyar, jikinta yana karkarwa yayin da yan fashin ke ci gaba da azabtar da su. Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa ganin yadda suke dukan 'yarta da danta. Ta yi kokarin tashi amma wani daga cikin yan fashin ya hankada ta da karfi, ta fadi a kasa.

"Ke dai ba kya jin magana, ko?" Shugaban yan fashin ya fada da murya mai cike da tsawa.

"Ki gaya mana gaskiya! Wacece ke? Kuma menene SIRRIN da wasu ke kokarin karewa game da ke?"

Hajiya Zaytunah ta dan kalli Nabeeha da Hammad da ke kuka da radadi. Ta san cewa ba zata iya bayyana komai ba, amma azabar da ake yi musu na neman ya tilasta ta yin magana. Sai dai kafin ta iya cewa komai, daya daga cikin yan fashin ya janyo gashinta da karfi.

"Idan baki gaya mana ba, kiyi tunanin abin da zai faru da 'ya'yanki!" Ya fadi yana daga wuka.

Hammad ya kara fashewa da kuka.

"Don Allah ku kyale mu! Ba mu da laifi!"

Nabeeha kuwa ta kasa cewa komai. Kawai idanunta ne suka cika da kwalla, tana kallon mahaifiyarta cikin tausayi. Baki daya tausayin mahaifiyar tasu take bata. Taga rayuwar tsanani a baya. Yanzun da rayuwa take kokarin sauyawa musu sun fara Jin dadi kuma ga abunda ya biyo baya...

A wannan lokacin, wata yarinya daga cikin yan fashin ta matso kusa da su, tana kallon su da alama kamar tana jin tausayinsu. Amma kafin ta iya cewa wani abu, shugabansu ya daka mata tsawa.

"Ke kuma me kike Shirin yi? Idan baki da zuciyar cigaba da aiki, sai ki bar nan yanzu!"

"Sorry sir.... " Yarinyar fashin ta fada tana juyawa baya ta koma...

Zuciyar Hajiya Zaytunah ta buga da karfi. Shin akwai wanda zai taimaka musu daga cikin su? Shin akwai wata hanyar tsira?

A wani sashe na daban, cikin wani katafaren gida mai dauke da kayan alatu, Hajiya Rumanah zaune take akan wata kujerar alfarma, hannunta rike da kofin shayi. Idanunta sun kada sun cika da tunani., Hajiya Karama da Hajiya Ladi suna zaune atare da ita , Da juice a hannayen su. kowacce na da fuskar da ba ta bayyana yarda ko damuwa.

Hajiya Karama ce ta fara magana, tana dube-dube kamar mai son tabbatar da cewa ba wanda ke leken su.

"Yanzu dai an kama su. Kuma an tafi da su wurin da ba wanda zai iya samun su." Ta fada da murya mai cike da kwanciyar hankali.

Hajiya Ladi ta gyara zaman mayafinta, ta kada kai tana murmushin jin dadi.

"Wannan ai babban nasara ne. Har yanzu ba wanda ya fahimci cewa mu muka tsara komai."

Hajiya Rumanah ta ajiye kofin shayinta a hankali, sannan ta dago kai, idanunta sun cika da wani irin kallo mai cike da natsuwa amma har yanzu ba ta nuna wata alama ta farin ciki ba.

"Ku tabbata cewa babu wata matsala. Ban yarda da waɗancan mutane ba sosai. Ko sun tabbatar mana da cewa sun yi abin da ya kamata?"

Hajiya Karama ta yi murmushi, sannan ta dan rankwafa kadan cikin muryar rada mai cakude da munafurci tace,

"Kada ki damu, Rumanah. Yan fashin nan sun fi kowa kwarewa. Mun tabbatar da cewa ba wanda zai iya kubutar da su."

Hajiya Ladi ta sake gyara mayafinta dake zumewa, ta dube su tana dariya.

"Yanzu dai abin da ya rage shine mu jira jin yadda za a yi. Idan dai komai ya tafi daidai, wannan maganar ta kare."

Hajiya Rumanah ta runtse idanu na wani lokaci, tana tunani mai zurfi. Daga bisani ta bude su, ta numfasa.

"Idan har suka samu damar kubuta, kun san abin da zai faru, ko?"

Dukansu suka yi shiru na dan lokaci. Sai Hajiya Karama ta gyara zaman rigarta, ta ce da murmushi,

"Ba za su kubuta ba."

"Aameen..Dan akwai babbar matsala idan hakan ta kasance..."

Haka dai suka cigaba da tattauna irin sake 'damarar shirin muguntar da zasu cigaba da yiwa Hajia Zaytunah da yaranta Nabeeha da Hammad...

🎀🎀🎀🎀


Hankalin Gwaggo Hafsatu gaba ɗaya ya tashi, tana a zaune a kan gadon asibitin da aka kwantar da ita. Duk da irin ciwon da kanta ya soma yi, zuciyarta na a tare da Zaytunah da 'ya'yanta.

Major General Dawud yana zaune gefenta, hannunsa rungume da wayarsa. Zuciyarsa na cike da damuwa, amma bai nuna sosai ba. Tun da aka kwantar da Gwaggo, yake jiran su Hajiya Zaytunah su iso. Basu iso ba. Tun dazu Kuma ya sanarwa mai dakin sa Hajiya Maijiddah kanta sanarwa Hajia Zaytunah ..

Ya ɗaga kai ya dubi matarsa, Hajiya Hauwa Maijidda, da ke tsaye a gefe tana gyara zaman hijabinta.

"Hauwa, kin tabbatar da kin sanar da su su taho?"

Ta gyada kai da tabbaci. Tana duban screen din wayarta..

"Eh, na tura mata sako tun dazu."

Ya gyara zama, zuciyarsa na raya masa wani abu. Ya ɗauki wayarsa, ya kira lambar Hajiya Zaytunah da kansa. Wayar ta yi ƙarar bata shiga..

Ya sake gwadawa, amma sai aka nuna "number not reachable."

Ya tsagaita, yana kallon wayar da jajayen idanu. Sai ya sake gwada lambar Nabeeha. A kashe.

Damuwa ta fara shigar masa da kyau. Hammad fa? Shi ma aka kashe tasa.

Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa. Ya dubi Hajia Hauwa da jajayen idanu.

"Ki sake gwadawa mana, ko ta karanta sakon?"

Hajiya Hauwa Maijidda ta sake duba wayarta, ta shiga sakon da ta tura. Ta karanta.. Batare da bata lokaci ba, ta kira lambobin gida. Daya bayan daya, babu wanda ya daga.

Kamar yadda ya zata, babu wanda ke kusa da waya. Sai ya kira lambobin ma’aikatan gidan domin jin halin da ake ciki.

Babu wanda ke ɗauka.

Nan take zuciyarsa ta buga!

Gwaggo Hafsatu ta lura da yanayin fuskarsa.

"Dawuda, me ke faruwa?" Ta tambaya cikin raunanniyar murya.

Ya buɗe baki da ƙyar yana kokarin daidaita kansa yace

"Ba ma iya samun su."

"Me kake nufi da hakan?"

"Bakomai gwaggo. Kwantar da HANKALIn ki.." Bayan yace da gwaggon haka,

Ya tashi tsaye da sauri, yana kiran daya daga cikin masu gadin sa . Ya ɗauka a take. Bayan sun gaysa, Mai gadin ya tanbayi jikin gwaggon .. Major general yace da shi,

"Kana gida?"

"A'a, ranka ya daɗe, ni da wasu daga cikin ma'aikata mun fita siye-siye."

"Kana da masaniya kan inda su Hajiya Zaytunah da sauran yaran suke?"

"Eh, ranka ya daɗe. Ai sun fita tun dazu da motar Hammad. Sun ce zasu taho asibiti."

"Amma har yanzu basu iso ba!"

Mai gadin ya yi shiru na wasu dakiku..kafin yace,

"Allah Sarki, ranka ya daɗe. To ban san inda suka wuce ba. Ko sun samu cunkosu a titi"

Major General ya kashe wayar a fusace...

Gwaggo Hafsatu ta dafe KIRJIN ta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Dawuda, kar ka ce an samu matsala!"

Hajiya Hauwa Maijidda ta dube shi da tsananin tashin hankali.

"Ko dai hatsari suka yi?"

"Haba Hauwa. For heaven sake. " Ya karasa bata amsa yana narka mata uwar harara.

A wani yanayi mai cike da firgici, Major General Dawud ya sake duban wayarsa, ya fara kiran lambobin da suka dace don a fara bincike.

Zuciyarsa na bugawa da sauri. Bai taɓa jin irin wannan tsoron ba. Wannan ba al'ada ba ce..

Gwaggo Hafsatu ta rungume kanta da tafin hannayenta, idanuwanta sun kada.

"Allah Ka tsare su! Allah Ka kawo su lafiya!"

Major General ya furta da ƙarfi,

"Ba zan zauna ba har sai an gano inda suke. Inshaaa Allah gwaggo ba matsala." Ya shiga cewa da ita haka yana kokarin karfafa mata gwiwa..

"Tohm dawuda..." Ta fada tana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hade da rarumar carbinta ta cigaba da lazimi tana rokon Allah ya kawo musu mafita.



_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09032345899_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_BOOK TWO_*

_PAGE:3_


Gabanta ya shiga dukan tara tara, yayin da ilahirin gabobin jikinta suka soma yi mata sanyi. Ganin an sake daukar wasu lokutan shiru ba alamar su ba labarin su.. Gashi su Raudah har sun taho asibitin daga gidah..

Gwaggo Hafsatu ta fashe da kuka mai ban tausayi, jikinta na karkarwa. Duk dakiyar da take da ita da kauda kai a abubuwa da kokarin boye damuwa.. kasancewar ta tsohuwa mai kamun kai da jan girmanta..Amman a ranar ta gaza boye dukkanin damuwarta. Tashiga tsananin dimuwa mai wuyar fassarawa. Domin tana jin kaunar Hajiya Zaytunah tamkar yar data haifa daga cikin cikinta. Hakama su Nabeeha tamkar su Raudah suke awajen ta. Ma'ana jikokin ta. Takance hajia zaytunah da yaranta amanace Allah ya damka a hannayen su itada major general dawud.

"Dawuda, Kada ka bari wani abu ya same su! Wallahi zuciyata tana kara nauyi!"

Major General Dawud ya daure, amma a ciki jikinsa shi kansa ya gama sanyi.. Duk makota, da sauran shagunan sayayya da aka san zasu iya biyawa anje basa nan... Don haka major general ba shida wasu sauran zantukan kwantar da HANKALI da zai fadawa mahaifiyar sa gwaggo Hafsatu akansu hajia zaytunah.. Ya numfasa kawai yana kada kai cikin girmamawa yace,

"Inshaa Allah Gwaggo..Allah ya datar da mu.. Kiyi hakuri"

Ya sake ɗaukar waya ya kira Brigadier General Mukhtar dake military intelligence unit. abokin aikin same wanda yake a karkashin sa yake a baya kafin yayi retire, Bayan sun gaysa ne. Brigd Gen.. Mukhtar ya numfasa,

"Yallabai!" Brigadier General Mukhtar ya amsa da girmamawa.

"An samu matsala! Ana buƙatar gaggawar bincike kan bacewar kanwata da yayanta daga gidana. Duk hanyoyin sadarwa sun katse, Kaganmu atare da Gwaggo ma a asibiti. Munyi iyaa mai yiwuwa wajen tattambayar makota, shaguna da wuraren da akasan zasu iya biyawa. Yes asibitin zasu zo...Ah Alhamdulillah da sauki. Okay zataji.. No gaskia basa zuwa ko'ina. Ba masu fita bane. Dan yarinya daya cema ke zuwa jami'a tare da daya yarinyata. To kuma driver ne ke kai su ya

1 / 40