DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   9 / 48

24K to 27K   out of 141.3K words

INA GODIYA DA NUNA MIN KUKAWA DA ƘAUNAR KU , TABBAS LITTAFIN DR SADEEQ NAKU NE , NAWA NE , NA KOWA NE,




🩺🕯️ DR SADEEQ🕯️ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣ 6️⃣


15 / 11/ 2025








Yau asibitin MODIRRE ya cika da motsin safe ƙamshin disinfectant ya gauraye da ƙamshin sabbin furanni da aka kawo sashen marasa lafiya rana ta dinga haskawa ta tagogin gilashi, tana dukan bango kamar ana shafe zuciyar asibitin da sabuwar rayuwa.


Mama ce ke tsaye bakin gado, tana share idanu da mayafi, tana kallon Indo wadda take zaune a gefen gado cikin farin doguwar riga, hannunta na daure da bandeji kaɗan. Fuskarta ta dawo da annuri — ba kamar wanda suka zo ba da ta kasance kamar wacce ta yi shekara biyu ba tare da dariya ba.


Dr. Balarabe kuwa ya shigo da takardun discharge a hannu, cikin farar rigar sa mai tsafta da agogon sa mai haske. Bai yi magana da yawa ba, kamar yadda aka saba, sai kawai ya ɗaga kai ya dubi Mama sannan ya ɗan murmusa da muryarsa mai sanyi yace:


“Lafiyar ta da kyau yanzu amma sai ta dinga kula da kanta sosai. Magungunan nan uku ne safe, rana da yamma.”






Mama ta karɓa da godiya, tana maimaita “Allah ya saka da alheri, ranka ya daɗe, ” saboda ya hana a karɓe kuɗin su , asali ma shi ya biya komai Indo kuwa ta zuba masa ido kamar wacce ke kallon abin mamaki; sai ta yi ƙasa da kai tana wasa da yatsunta.


Shi kuma Dr. Balarabe ya ɗan tsaya gefe yana duba fomar discharge ɗinta, amma zuciyarsa tana tafasa da wasu sabbin tunani da bai saba da su ba. “Wannan yarinyar…” ya ce a ransa,
Indo ta ɗago ta ce da muryarta mai laushi:
“Dr. Balarabe… zan iya zuwa in gaidaka idan na dawo lafiya z sai ka bani kaza?”






Sai ya ɗan kalli gefe, yana murmushin da ya fi magana daraja:“Idan kina da lafiya sosai, babu laifi.”
Mama ta yi dariya tace “Kai Indo, baki da kunya wallahi.”
Dr. Balarabe ya juya ya fita a hankali, yana riƙe da takardun da ke nuna cewa Indo — yarinyar ƙauye mai halin drama — ta gama jinyarta.
Ranar ta zama kamar sabon farawa, ba kawai gareta ba — har ma ga zuciyar likitan da bai saba barin motsin rai su rikice shi ba.


$$$$$$$$$$$$
Tana sauka daga napep a kofar gida, sai ga Dijje da Haule sun ruga da gudu kamar wadanda suka hango sabuwar Indo daga sama “Ke Indo! Me kika shafa haka kika yi haske kamar fitilar gidan gwamnati?”
Indo ta fashe da dariya, tana tura jakar ta gefe.
“Kuɗi ku bare. Dr. Balarabe ne yasa ake min wanka, na yarda don yana bani abubuwa masu daɗi.”


Haule ta rike baki tana dariya “Amma ai yanzu jikinki kamar sabuwar jaririya yake, wallahi.” Indo ta karkada kai tana murmushi:
“Yanzu ai na dawo gida, ba zan sake wankan nan ba. Ruwan fa kamar acid! ai kamar yana ƙona fatar jiki.”






Mama da ta fito daga ciki ta tsaya bakin ƙofa tana kallonsu tana murmushi, amma a idonta akwai ɗan gargaɗi “Karki ce haka Indo, ruwan nan magani ne. na sha wahala a asibiti fa, kuma nan da kwana bakwai zamu koma mu karɓi sauran maganin.”


Indo ta ja dogon numfashi tana kallon Mama da wasa a idanu “To Mama, ki gayawa Doctor din naki cewa ya daina min wankan da acid ɗin nan, idan ba haka ba zan gudu.”
Mama ta yi dariya tana girgiza kai “Sai in ce mai magani, ai tunda yanzu kin samu lafiya.”






Dijje da Haule suka yi dariya sosai har suka rike ciki. Indo kuwa ta juya ta shige gida tana tura ƙofar da salo, tana faɗin “Ai yanzu babu ƙamshin wari, ku bar ni da ni. Na zama Indo mai turare.”
Mama ta biyo ta da ido tana murmushi, zuciyarta cike da godiya ga Allah domin duk da barkwanci da zancen Indo, ta san a ƙasan zuciyarta Indo ta tsira ne daga wani yanayi mai hatsari.









Mama na shiga ɗaki bayan ta gama kallon Indo da dariyarta, ta jingina da bango tana murmushi. Amma sai can ta fara jin wani abu yana motsi a kirjinta — tuni ta fara tari, da farko ƙanana ne, sai kuma suka ƙaru.


Ta sa hannu don ta rufe baki, amma sai ta ji zafi da ɗumi a tafin hannunta. Tana dubawa, sai taga jini — ba kaɗan ba, harda guda guda kamar wanda ya tsaya a zuciya.


Wani irin sanyi ne ya ratsa jikinta gaba ɗaya. Ta saurin ɗaukar tsumma, ta goge bakin ta da rawar hannu, ta fito waje tana kwaɓe fuska, amma tana ƙoƙarin kada Indo ta lura.


Tana kuskure bakin ta a bayan gida, sai ta daga kai ta hango Indo tana dariya da Haule, tana buga ƙafa kamar wacce babu komai a ranta. Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskar Mama, amma kafin ta ankara, hawaye suka zubo daga idonta.


Ta goge su da hanzari, ta dafa bango tana jan numfashi, zuciyarta cike da addu’a.


“Ya Allah, kai kadai kake da iko. Ka dawwama da farin ciki a rayuwar ɗiyata. Ka kare min ita daga kowanne sharri ka bata komai cikin sauƙi, Allah... kar ka ɗauki wannan farin cikin da na fara gani yanzu...”






Ta sake tari a hankali tana runtse idanu, tana jin nauyin jiki yana lullube ta sai ta koma ɗaki, ta kwanta cikin nutsuwa, idonta yana kallon rufin ɗakin amma zuciyarta na yawo tsakanin tsoro da addu’a.
Wani irin bacci mai nauyi ya kama ta, kamar wanda aka ɗaura da ruwa.


Gaban kofar ɗakin, ana jin muryar Indo tana dariya tana cewa “Mama, ni dai yanzu Indo mai turare ce!”
Amma Mama ba ta amsa ba — ta riga ta nutse cikin baccin da yake cike da sirri da sanyi.




##$$$$$$$$$$######









Dr. Sadeeq yana kwance a gadon sa, jiki na kakkarwa kamar wanda ya kamu da zazzabi mai zafi. Idonsa sun yi ja, numfashinsa yana fita da wahala duk wani karfin da yake da shi a asibiti wajen taimakon mutane, yau babu shi yau shi ne mara lafiyan da yake bukatar taimako.


Zufar gumi ta cika goshinsa, yana murɗa hannuwansa yana neman wuri ya samu sauƙi. Ya runtse idanu yana mai ambaton sunan Allah a hankali “Ya Allah, ka bani sauƙi. Ba zan iya ba, Allah Ka bani sauƙi...”






A hankali, ya ɗauki pillow ya rungume kamar wanda yake neman taimako daga abu marar rai kamar jariri cikin ciwo, yana birgima a hankali, yana ƙoƙarin kada wani ya ji motsinsa.


Duk da haka, ciwon cikin bai bar shi ba. Ya ɗaga kansa ya kalli agogo — karfe biyu na dare part da yake ciki shiru ne, sai ƙarar fan ɗaya da yake rawa.


Ya miƙa hannu ya lalubi wayarsa, amma ta faɗi daga kan gado. Da ƙyar ya tsugunna ya ɗauka, yana ƙoƙarin kiran abokinsa Dr Kamal wanda ya fi kowa fahimtar irin wannan ciwo.


Sai dai kafin kiran ya shiga, ido ya lumshe, jikinsa ya saki, zuciyarsa ta cika da tambaya ɗaya:“Shin haka nake ji saboda damuwa, ko akwai wani abu da ke neman zama a jikina?”


A haka cikin azabar da ba kalma zata iya misaltawa ba, bacci mai nauyi ya fisge shi. Wani irin bacci ne wanda ba daga nutsuwa yake ba, sai daga gajiya da rauni. Kamar mutum da ya yi fama da ciwon da jiki da zuciya suka haɗu wajen gwada shi.


A cikin baccin, ya shiga wani irin dream mai cike da duhu da haske a lokaci ɗaya. Ya ga kansa cikin wani fili mai fadin gaske, babu kowa sai shi da iska mai sanyi da ke kadawa a hankali. Kamar yana jin murya daga nesa tana ce masa, “Ka tashi, lokaci yayi… sallah ta kira ka…” a tsorace ya waiga, amma babu kowa. Murya ta sake maimaituwa cikin natsuwa kamar daga sama “Sallah... ka tashi.”






Sai gumi ya soma keto masa duk da cewa a mafarki yake. Zuciyarsa na dukan dum! dum! kamar ana buga gangar zuciya a cikin sa.


Da ƙyar ya motsa hannun sa, ya fara farkawa daga baccin nan mai nauyi. Idonsa suka buɗe a hankali, numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya dawo daidai.


Asubar farko.
Haske mai taushi daga gefen taga ya shiga ɗakin, yana haskaka fuskar sa. Idanunsa sun cika da kwanciyar hankali — kamar wanda ya yi fama da guguwa, amma yanzu ya samu nutsuwa.


Ya zauna a bakin gado, ya shafi kansa a hankali yana jin sanyi a zuciyarsa ya miƙe, ya cire kayan jikin sa, ya shiga wankan tsarki da nutsuwa da hankali.


Ruwan yana zuba a jikin sa kamar yana wanke duk wani ciwo da damuwa da suka dami zuciyarsa tun jiya. Bayan ya gama, ya yi wankan jiki cikin tsafta, ya nufi wardrobe ya ɗauko farin kaya masu kamshi, ya feshe jikin sa da turaren Oud Wood da ya saba amfani da shi idan yana son farawa da sabuwar nutsuwa.


Sai ya ɗauki tasbihi, ya fice cikin shiru.
Lokacin asuba ta kira.
A hankali ya ja ƙofar gidan, ya fita cikin sanyi da kamshin ƙasar da ruwa ya wanke da dare.
kamar wanda aka sake haifarsa — Dr. Sadeeq ya nufi masallaci da zuciya mai natsuwa, da fatan Allah Ya ba shi sabuwar rana mai albarka da lafiya.
Har ya dawo daga masallaci, zuciyarsa ta kasa kwanciya. Duk yanda yake ƙoƙarin mantawa da abin da ya gani a baccin sa — fuskar Indo tana dawowa cikin tunanin sa.
“Indo kuma?” Ya tambayi kansa cikin mamaki, yana runtsa idanu kamar mai son ya kore hoton nan daga tunanin sa.


Sai dai abu ɗaya ne ke masa nauyi ya yadda ma zai yi mafarki da ita?
Yarinya ce fa, mai rashin wayewa. Amma dalilin me yasa mafarkin nan ya zo masa da irin wannan siffar? Kuma me yasa tun farkawa yake jin kamar an zuga masa wani abu a zuciya — wani abu mai zafi da sanyi lokaci guda.


Ya sauke numfashi mai nauyi.
Ya ɗauki Al-Qur’ani, Suratul khafi ya buɗe muryarsa ta taushi kamar ana saukar rahma daga sama. “A’ūdhu billāhi mina sh-shayṭāni r-rajīm…
Bismillāhir-raḥmānir-raḥīm…”
Kowane ayah yana shiga zuciyarsa kamar ruwa mai sanyaya wuta ya karanta har sai da zuciyarsa ta lafa, sai ya jingina da bango, yana jin wata nutsuwa mai daɗin gaske tana yawo a jikinsa..............











Ummmmmm 😎😎😎🙈🙈


🩺🕯️ DR SADEEQ🕯️ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣ 7


17 / 11/ 2025



















BAYAN WANI LOKACIN





Bayan ɗan lokaci, safiya ta fara haskawa.
Ya miƙe cikin natsuwa, ya sake shiga wanka wankan safiya wanda yake masa kamar sabuwar farawa ruwan sanyi yana zuba a jikinsa, yana jin kamar yana wanke dukkan wani abu da ya tsaya masa a rai.


Sai ya fito, ya bushe jikinsa, ya buɗe wardrobe ɗinsa yana zare shadda mai launin ruwan sama, ya haɗa da half-jumper white, sannan ya ɗauki hular Hausawa mai ɗinki mai laushi.


Da ya tsaya gaban madubi, sai ya ga kamalar asalin namiji mai addini da mutunci. Fuskar sa tana haske, gemun sa a gyare, idanunsa cike da annuri — annurin musulunci.


Ya feshe turaren Mukhallat a wuya, ya saka wrist-watch ɗin admin Hausawa style, sannan ya ɗauki mukullin mota wani murmushi mai taushi ya bayyana a fuskarsa.
a ransa yace “Wannan safiyar, ta zo da sabuwar nufin Allah… komai da yake faruwa, akwai dalilinsa. domin yau zai kammala aikin sa yayi singn out ”






Sai ya fice cikin natsuwa, yana jin kamshin turarensa yana gauraye da sanyi safiyar Modirre sabuwar rana ........







####$$$$$$$$#####


“Haba Mama,” Indo ta furta da ɗan shagwaɓa, tana taɓa ɗan hancin ta da hannun da bai gama bushewa da ruwa ba. “Nace miki idan na dawo zan ɗebo ruwa, me yasa sai kin fita? Malama Larai ce fa ta ajiye ne wai yau sai na iya alƙalamin allo na.”


Mama ta tsaya a bakin ƙofa, kanta ɗan ɗaure da zanin ƙirji, hannunta riƙe da kwalban ruwa da ta samo da ƙyar a fuskarta akwai gajiya, amma murmushi mai cike da nutsuwa da ƙauna ya waro a gefen leɓenta, kawai ta ce da muryar da ta taushi zuciya:
“Zo nan, Indo… zo ɗiyata.”


Indo ta taho da ƙanana matakai, tana jin ƙamshin ƙasashen ruwa da ke ɗiga daga jikin kwalbar Mama. Ta durƙusa, sannan ta kwanta a cinyar Mama kamar yanda take yi tun tana ƙarama.
Mama ta ɗora hannunta a kan kanta, tana shafa ta a hankali, kamar tana lissafa shekaru da ba za ta dawo da su ba.
“Banda abunki Indo,” ta fara magana a hankali, muryarta kamar wadda ke magana da zuciyarta.
“Karatunki fa na da kyau sosai , kiye karatu, don ni da mahaifinki zamu yi alfahari dake. Ina so ki zama mahaddaciyar Al-Qur’ani… kuma ki zama likita kamar Dr Balarabe.”






Indo ta ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sai ta ɗago kanta tana kallon Mama, idanunta cike da walƙiya da dariyar yarinya mai mafarki.
“Mama,” ta ce tana murtuke fuska da wasa, “idan na zama kamar Dr Balarabe, zan sa su kira ni ‘Dr Indo Balarabe’ ko?”






Mama ta kyalkyale da dariya. “Eh mana Indo. me kike tunani?”Sai Indo ta ƙara cewa,
“To Mama, ina so mana, saboda idan na zama likita sai nayi kuɗi, kullum in saya mana kaza mu ci da lemo, ba kamar yanzu ba da muke wahala da ruwa baa ”






Mama ta daure fuska tana yin kamar mai faɗa, amma murmushi ya kasa ɓoyuwa.
“Indo shashasha! Ai ba kaza da lemo nake so ba, albarka da karatu nake so ki tara.”
Indo ta marairaice fuska, tana dariya tana cewa, “To ai albarka da lemo da kaza duka suna tafiya da juna, Mama. ”






Sai Mama ta girgiza kai, tana dariya mai taushi. “To Allah ya miki albarka Indo. Allah ya raya ki cikin natsuwa da ilimi. Ki zama abin alfahari, ki zama abin tausayi ga marasa ƙarfi. Ki zama mai addu’a, ba mai kuka ba ke kasance mai gaskiya .”






Tayi shiru na ɗan lokaci, ta lumshe ido tana shafar kanta a lokacin, iska mai sanyi ta shiga ɗakin, tana motsa labulen da ya rufe taga. Rana ta fara haskawa ta ɓangaren gabas, hasken ta ya daki fuskokin su, kamar hasken fatan uwa ga ɗiyarta.


Bayan ɗan lokaci, Mama ta tashi ta dafa Indo.
“Tashi ki ɗebo min ruwan nan ɗiyata, na fita ban samu ba sai a maƙwabta.”
Indo ta miƙe cikin natsuwa, tana riƙe da bucket “To Mama, amma banda faɗa idan na yi jinkiri.”




“Baza a yi ba,” Mama ta amsa tana murmushi, tana kallo yadda Indo ke tafiya tana shan iska kamar wadda ke wa duniya sallama da dariya.






Sai ta zauna ta jingina da bango, tana bin Indo da ido har ta ɓace a bayan bishiyar marke.
Hankalinta ya yi nauyi — amma zuciyarta cike da begen ganin Indo ta zama wacce take mafarki: mahaddaciya, likita, yarinya mai daraja da tsarki.
“Allah ka dawwama da farin ciki a rayuwar ɗiyata,” ta furta a hankali, hawaye ɗaya ya sauko daga idonta, “Ka kare min ita, ka bata komai cikin sauƙi… ka tsare zuciyarta daga munanan mutane.”






Ta lumshe ido, baccin gajiya mai sanyi ya ɗauke ta.
Hasken rana yana haskaka fuskar ta, kamar rahamar Allah na lulluɓe uwa da addu’a a lokacin da ba ta san cewa ƙaddara tana kallo daga nesa ba…










Yau garin nasu ya tashi cikin hayaniyar safiya, rana bata fito ba amma ƙura da hayaniyar yara sun cika unguwa. Ruwa ya ƙare tun jiya, panpanpam ɗin unguwar ya lalace, sai yau aka gyara shi amma yaki bada ruwa sosai — kamar yana tsoron fitowa.


Indo ta fito da leda da karamar ɗamara a ƙugu, ta rike bokitin ruwa guda biyu. Fuskar ta fara sauya launi saboda sanyi da rashin bacci, amma murmushi har yanzu yana daure saman laɓɓanta. “Yau fa sai na samu ruwa, ko da na zauna a nan har rana.”


Tana zuwa bakin panpanpam ɗin sai taga jama’a — yara, manya, da matasa — sun rufe wurin. Bokiti sai zuba suke kamar shinge, ana tura, ana caccaka. Wasu suna dariya, wasu kuma suna ta faɗa saboda ruwa.


Ta tsaya gefe, ta cire takalminta, ta daura ɗamarar da kyau, ta kama bokitin da hannunta. Amma kafin ta kai kusa, sai wani yaro ya banka mata kafada, bokitin ta ya faɗi ƙasa kwas! ya buga da ƙarfi.


Indo ta ɗago kai cikin mamaki ta hango wanda ya yi hakan — saurayi ne, ba yaro ba, aƙalla shekara 18–19, dogo, yana sanye da riga mai datti, hannu ɗaya da bokiti ɗaya.
Ta ce da shi cikin murya mai ɗauke da gajiya amma karfi,
“Kai fa! me yasa zaka banka min kafad'a haka? ko ruwa naka na ɗebo ne?”


Saurayin ya juyo yana dariya, yana kallon ta daga sama har ƙasa, ya ce:
“To ke fa baki da ido ne? Kina ganin jama’a sai kin zo kina rangwame kamar ‘yar Mama kina tura bokitin yara ?”






Wannan maganar tasa yara suka hau dariya, har aka soma waƙar rigima: “Team Indo, Team Idris Ruwan panpanpam sai faɗa da biris!”






Indo ta ja tsaki, ta nufi bokitin ta ta ɗaga, sai kuma ta tsaya. Tana kallon sa ido cikin ido, fuskar ta ta yi ja, numfashinta ya fara nauyi.
“Ni ba ruwana da kai wallahi, idan baka bar hanya ba sai na nuna maka yadda ‘yan mata ke kare bokiti.”
Idris ya yi dariya sosai yana tura yara gefe:
“To bari mu gani fa, ɗiyar mai unguwa ke ce ko?”
Kafin kalma ta ƙare, Indo ta kwace bokitin sa kai masa da ƙarfi — duum! ruwa ya zube, bokitin ya buga ƙafarsa. “Kai

9 / 48