DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   6 / 48

15K to 18K   out of 141.3K words

neman ki!”Indo ta zaro ido, ta fara girgiza kai. “Ni wallahi ban yi komai ba Mama! ko kadan! In akwai wanda ya ce na yi masa laifi to karya yake! Karya ne Mamaaa!”






Sai ta fara kuka, tana bin bango.
Mama kuwa sai ta ce “Ai ni ma ban sani ba Indo. To ki fito su ganki.”
“A’a Mama! Ba zan fito ba! ni dai ina tsoron su! ni fa ban son rigima!” sai ta rufe kanta da zane ta shige bayan labule da wannan halin, Mama ta fito ta ce: “To dan Allah kuyi haƙuri, bari ta shirya ta fito.”
Yan sanda suka tsaya suna jiran ta, yayin da Talatu ke ta huci kamar wacce aka cinye mata buhun wake.
Daga ciki kuwa ana jin Indo tana shirin fitar da hayaniya kamar kullum:
“Mama! Ni dai ban fita ba! Idan sun kama ni ai sai su fasa kai na kamar Talatu!”
Wani yaro na gefen gida ya ce da dariya:
“Wai ita ce Indo? Waccan mai ihu da gudu? Ai fa yau sai an ɗauke ta da hannu!”






Sai dariya ta kaure.
Yan sanda suka kalli juna suna murmushi, ɗaya daga cikinsu ya ce “Wannan yarinyar da take ihu kamar ta sha kayan maye ce kuwa?”
Da ƙyar Mama ta shigo da Indo, tana riƙe da hannunta da ƙarfi. Indo ta fito da ƙyalli, zani daban, riga daban, gashin kai a kwance kamar wacce aka taso daga kasuwa.
Sai ta dubi ‘yan sanda, ta ɗan matsa baya tana cewa da fargaba:
“Don Allah, kuyi haƙuri! Na rantse ban fasa wa Talatu kai ba, itace ta fara zagi na!”
“Shiru ki yi!” inji ofisa. “Za mu je ofis mu ji duk bayanin.”Indo ta kalli Mama tana kuka:
“Mamaaa! Kice musu fa! Ni dai ban yi komai ba! ni da raina!”
Mama ta share gumi tace:
“Kuyi haƙuri, malamai, ku ɗan tausaya. Yarinyar nan da alama ta raina ne kawai ta ke.”
Sai Talatu ta tsalle ta ɗauki dariya, tana cewa:
“To ai da raina ake fara aikata laifi. Ai yau sai taji! Da sa hannun ‘yan sanda taji!”
Daga nan ‘yan sanda suka ja Indo zuwa mota. Indo na ihu kamar wacce ake yankan rago:
“Wallahi ba ni neee! ba ni neee Mamaaa! Mamaaa ki bi su ki ceto ni!”
Unguwa ta kaure da hayaniya.
wasu suna ta dariya, wasu suna cewa:“Ai Indo ta shiga uku yau!”


Kamar wasa, mota ta ɗaga ƙura ta tafi, Indo a ciki tana ta ihu, yayin da Mama ta tsaya bakin ƙofa da hawaye.
Sai ta kalli sama ta ce “Ya Allah, kai ka san halin wannan yarinya, ka kawo mata mafita.”













Me yake shirrin faruwa ...?










https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


🩺 DR SADEEQ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣0️⃣




*10 / 11/ 2025










Monday morning iska mai sanyi ke kadawa, rana kuma na fitowa a hankali. A yau Dr. Sadeeq ya farka tun da wuri, ya shiga bathroom yana wanka da ruwan sanyi saboda bai so makara ba. Bayan ya fito, ya ɗaura towel a kugunsa, yana gaban mirror yana goge gashin kansa da towel ɗin.
A hankali yake magana da kansa:
“Hmm… yau dai sai na gama da wannan aikin. Allah ya sa babu wahala ga meeting…”


Ya fesa body spray, ya sanya white shirt mai kamshi, navy blue trouser, da brown shoe da ke haske kamar sabo. Ya ɗaura tie ɗin sa daidai, ya ɗauki car key ya fito. Wani kamshi mai sanyi na fita daga jikin sa — irin wanda ke ɗaga kai ko da a cikin jama’a.






Ya shiga mota, engine ya kunna vroom! sai glass ya rufe glass nasa tana sheƙi kamar wadda aka wanke yanzu yana tafiya cikin nutsuwa har sai da ya zo kusa da layin da ke kaiwa hanyar gidan su Indo. Kamar wasa, sai kawai motar ta fara bada wani irin sound kamar tana gajiya — grrrrgrrr! — nan take ya tsaya gefen hanya.
“Oh no, not now…” ya furta cikin ƙasa da murya.


Ya buɗe bonnet, yana dubawa, yana gani kamar overheating ne sai ya ɗauki bottle water daga bayan mota, ya zuba ruwa a radiator. Zafin iska da tururi suka tashi — shhhhhh! — yana mai jan numfashi.
Cikin wannan lokacin sai yaji hayaniya daga nesa. Wm, wasu mutane na tafiya suna cewa:
“Ƴan sanda sun zo gidan Talatu! Indo ta dake ta jiya, yau sai sun kaita station!”






Ya ɗago kansa da mamaki.
Sai kuma yaji wata murya daga nesa, mai ƙarfi, mai cike da tashin hankali — murya da ba zai taɓa manta ba a duniya:
“don Allah kar ki tafe dani ba dangangan na mata ba " .
Ya tsaya cak. Hannunsa a cikin bonnet.
Sai zuciyarsa ta fara dukan boom boom boom ya furta cikin harshen turanci “Oh no… not this girl again. The village perfume herself.”
ya jingina da motar, yana murmushi da mamaki “Of all places, I must see her again? Maybe she’s cursed or something…”
Sai ya ɗan jinjina kai yana dariya, amma zuciyarsa tana cewa wani abu daban:
“She’s trouble, but… something about her makes me curious.”
“Should I just mind my business… or should I help?”ya tuna lokacin da Indo ta ce da shi a kasuwa:
“Kana zuwan layin mai makaranta, idan ka tambaya gidan su Indo, za’a kaika har dakin kwana na.”


Sai murmushi ya kwace masa, yana tunanin irin confidence ɗin da take da shi.
Ya shiga motarsa, ya juya cikin layin, yana ganin yara suna ta ihu suna gudu da motar Sai ya tsagaita tafiyar ya bude glass nasa " kai come here zo ina ne gidan su Indo " yaron yace ai yanzu ƴan sanda suka tafe da ita muje mukaika gidan su Indo mai ƙamshin wari
Yana dariya a zuciyarsa, yana cewa:
“Kai, even these kids know her as Indo mai wari. What a title…”




Sai yara suka fara gudu suna ja gaba, shi kuma yana binsu da mota a hankali har suka shiga cikin unguwar “Oh, what a nickname. Indo mai wari. This girl will never change.”






$$$$$$$$$$$$



Motar ‘yan sanda ta riga ta tafi da Indo, amma har yanzu kofar gidan cike take da jama’a. Mata na ta kuka, maza na ta tsaye da hannu a kugu, yara na ta kurma ihu suna cewa:
“Wallahi Indo aka tafi da ita! Indo ta buge Talatu! Indo mai turaren wari ta shiga hannun ƴan sanda!”


Mama kuwa, tana tsaye a tsakiyar kofar gida da zani ɗaya daure da rigar bacci, ta dafe kai tana kuka: “Ya Allah! Wannan fitinar Indo ta wuce kima! Ai wallahi duk da haukata, Indo ba mai cutarwa bace! Indo ce Indo fa!”


Wani makwabci ya yi ƙara da muryar ƙwaro yana cewa: “Haba Mama! Ke ki ce haka? Ta fasa wa mutum kai mana!” a haka mai unguwa ya iso, yana tuƙa keken sa yana cewa:
“Ku rabu! Ku rabu! Ku gyara hanya, mu je Police Station yanzu! wannan yarinyar ƴar ƙaraama a hukuma !”






A lokacin ne aka ji wani irin gyaran murya daga nesa — muryar da ta cika da iko da nutsuwa “Excuse me…”
Duk suka waigo a lokaci guda.
Nan suka hangi mutum ɗaya tsaye — Dogon mutum mai kyakkyawar fuska, cikin farin rigar doctor mai tsabta, da tabarau a idanu, da car key a hannu.
Wani ƙamshi mai daɗin gaske ya cika wajen — ƙamshin turaren da ke haɗa “class” da tsabta, wanda maza da mata suka juya suka kalla.


Yaran unguwa suka yi ihu “Ga Dr mai mota! Ga wanda Indo ke ce wa Balarabe!”


Mama ta kalleshi sosai, sannan tace da murya mai ɗan rawa: “Kai ne likitan da Indo ke ta ambata? " Yes " Dr. Sadeeq ya ɗan yi murmushi, ya ɗaga hannunsa cikin girmamawa. Ya ce da Hausa mai ɗan rauni “Ki ce… ke ce Mama ta? Okay… please, tell me, what exactly happened?”


Mama ta ɗan yi shiru tana kallon sa, duk da bata fahimci maganar ba Amman tagane yana son sanin me yafaru ne “Ai wallahi likita… ba laifin ta bane. Talatu kishiyar maman wata yarinya ce, sun fara gardama ne jiya, daga nan Indo ta ɗauki dutse ta jefa mata… kai kuwa yaji rauni. Sai ta kira ƴan sanda, sun zo suka kama Indo, suka tafi da ita. Amma wallahi da ka ga yadda Indo ta ke kuka, da ka tausaya mata. Ai duk saboda soyayyar yarinyar nan ta Mairo ce da aka tura birni aikatau!”






Dr. Sadeeq ya tsaya yana kallonta cikin hankali, yana son fahimtar komai, amma ba komai yake gane ba.
ya ɗan juya kai, ya ce a hankali cikin Turanci:
“So… someone called the police because Indo… threw a stone?”
Mai unguwa ya shigo cikin hirar, yana kallonsa da murmushi: “Ai hakane Doctor. Indo ta buge kishiyar matar ɗan gidan nan. Amma wallahi duk saboda tsiya ce, ba da niyya ba.”


Ya ɗan sosa kansa, yana fesar da iska daga hanci. Zuciyarsa ta ce “Why am I not surprised? Indo… always in trouble.”
Sai ya kalli Mama da nutsuwa yace:
“Okay, ku zauna. Zan je station yanzu, zam dawo da ita ".
Mama ta ɗago da sauri, tana cewa:
“Kai ne kawai zai iya cetonta, Doctor. Kai Indo ke cewa mutum mai imani ne. Allah ya saka maka da alkhairi.”
Mai unguwa kuma ya ƙaraso, yana dafe cikinsa yana murmushi:
“Allah maka albarka, ranka ya daɗe. Ni ma zan bika, mu tafi tare, in tabbatar babu matsala.”


Dr. Sadeeq ya jinjina kai, ya ce: “Alright, let’s go.”









###############


Motar sa ta tsaya a gaban station ɗin, ya fito yana tafiya da mai unguwa a gefensa. Mutane suka rufe baki da mamaki, suna kallonsa kamar an aiko musu da angel daga sama.


A lokacin Indo na zaune a bayan ofishin, an daure hannunta da igiyar jeka ka dawo. Fuskar ta ja kamar wuta, ga hawaye da majina sun haɗu, tana sharɓa tana ihu:
“Na ce ba ni ce ba! Wallahi ba ni ce! Ku kira Mama ta ku tambaye ta!” Cikin kuka da gajiya, ta ƙara da cewa:
“Ku bari in tafi gida… zan wanke ma ofishin nan! Don Allah ku bari in tafi gida!”
Ƴan sanda biyu suna gefe suna dariya, ɗayan ya ce “Wannan yarinyar ai abin dariya ce. Tun ɗazun ba ta tsaya shiru ba.” Cikin wannan yanayi ne Dr. Sadeeq da mai unguwa suka shigo ofishin.
Da zarar Indo ta hangoshi, ta ɗago kai cikin sauri ta ce da muryar da ta haɗa kuka da murna: “ Laaa Balarabe! Na sani… Allah ya kawo min kai! Ka gaya musu ni ba mai laifi bace!”






Duk ofishin suka juyu Dr. Sadeeq ya tsaya yana kallon ta kamar ba zai iya magana ba — a fili yake ganin wannan yarinya ta haɗa hauka, a kanta , kawai ya girgiza kai, yana murmushi cikin sirri, ya ce “Let her go. I’ll handle the rest.”
Ofishin yayi tsit.
Kowa ya ɗago da mamaki Indo ta tsaya da baki a buɗe, tana kallonsa kamar ta ga mala’ika Mai unguwa ya ce cikin nishaɗi:
“Wallahi Doctor, Allah ya saka da alkhairi. Indo ta tsira yau!”
Cikin zuciyarsa kuwa Dr. Sadeeq ya ce:
“What a girl. She’s a full story on her own…”






Yanzu aka fara drama a police station naga ruwan comments........





Zan haɗa document from page one to ten saboda masu tambaya daga farko


Narnah ƙanwar soja ✍️










https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM


🩺🕯️ DR SADEEQ🕯️ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣1️⃣







12 / 11/ 2025







“Baza mu barta ta tafi ba!”
cewar ɗaya daga cikin ‘yan sandan da ke zaune a kan kujerar ƙarfe, yana bubbuga biro a saman tebur kamar mai lissafi. “Laifin ta yaye! Ta fasa wa mutum kai da dutse, jini ya zuba wannan ai ba wasa ba ne!”


Indo ta durƙusa a ƙasa, ta dafe kanta, ta kama kuka mai ƙarfi kamar wacce aka raba da duniya.
“Wallahi ban yi niyya ba! wallahi ban so ba!”
muryarta ta ɗauka da rawa, kamar ta wacce aka hana numfashi, a gefe Dr. Sadeeq ya tsaya, hannunsa ɗaya riƙe da wayar sa ɗaya kuma da ID card nasa, gaba ɗaya ihu ta ya gama rkitashi ya juyi ya ganta a karo na biyu " shut up your mouth" ai kuwa ta fahimta saboda ana musu haka a makarantar a kamar mutum yayi shiru ....Yana kallon ɗan sandan cikin natsuwa, idanunsa sun nuna ba takaici ba ne, amma akwai wani irin nutsuwa da ƙwarewa da suke fitowa daga cikin sautin muryarsa.


Ya ɗan ƙara gaba, yana cewa a hankali:
“Excuse me, Officer. The law doesn’t allow you to detain a 13-year-old girl for a street fight. She’s just a minor. You can only issue a fine, not jail her.”
Ɗan sandan ya ɗan tsuke fuska, yana kallon takardar da ke gabansa, ya ce da ƙasa da murya:
“Sir, ba mu san wannan doka ba, amma idan zaku biya kuɗi dubu ashirin…”




Dr. ya ɗaga ID ɗin nasa ya miƙa. “Dr. Sadeeq Muhammad, consultant, National Medical Center.” " and then idan kukace zaku tsananta to ku tabbatar zaku rasa aikin ku now "
Sai aka ɗan jinjina kai — duk wani kishi da naci da ke fuskar ɗan sandan ya lafa tamkar ruwan sama ya shawo ƙura wani daga cikinsu ya miƙe, yana cewa da ladabi:
“Ka yi haƙuri, Sir. Ga takardar da muka rubuta. Sai a biya fine ₦5,000, sannan ku tafi.”


Dr. ya karɓi takardar, yana kallon rubutun da biro mai launin shuɗi. A zuciyarsa yana faɗin:
“Hmm… fine ɗin nan ma kamar karya yake. Amma ai kuɗin da ta ƙone na jiya ya fi haka.”






Sai murmushi ya kwace masa. Yana girgiza kai, ya ce a hankali, “Alright. Let’s make it official.”ya saka hannu a rubutun, ya biya kuɗin da cash.
Indo kuwa tana gefe, idonta sun kumbura kamar gyaɗa da aka jiƙa da ruwa. Da zarar ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya ce, “You can go now,” nan take ta sake kuka – wannan karon ba saboda tsoro ba, saboda farin ciki ne.


Kafin wani ya ce komai, sai kawai ta tashi da sauri ta rungume Dr. Sadeeq, ta kwanta a kirjinsa tana kuka tana faɗin:
“Nagode, Dr.! Wallahi nagode! Allah ya aiko ka saboda ka ceto rayuwar ta .”


Ofishin ya yi tsit. Ko ɗan sandan da ke baya yana rubutu sai da ya ɗaga kai ya kalle su.
Dr. ya tsaya kamar dutse. Idonsa a buɗe, ya ɗan motsa baki yana neman fitar da kalma:
“It’s okay… calm down please…”


Mai unguwa da ke gefe ya yi saurin kama Indo, yana fizge ta kamar ɗan yaro:
“Ke Indo! Ki saki mutum mana! Wannan ba gidan ku ba ne!”
Yana dariya yana fitar da zafi.
Dr. Sadeeq ya ɗan share gumin goshinsa, yana murmushi da dariya mai taushi “It’s okay, let her be. She’s just a child.”9️⃣3️⃣❤️‍🔥9️⃣4️⃣
https://youtu.be/4wIojiBbOgA



🌟⭐DR SADEEQ✨ 🌟


BY


NARNAH ƘANWAR SOJA


BOOK 2
My 15novel comedy love and drama



https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM



THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*





🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲




BUSSINES GROUP


👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT






TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night




Atika na toilet ta kara duba abinda idonta ya gani “positive”, alamar ciki da gudu ta fito daga toilet tana tsalle-tsalle, tana murna, tana ihu a hankali don ta gawayawa Dr SADEEQ:
“Na samu ciki!”






Jikinta ya ƙara ƙiba da haske kamar ba ita ba, shape nata ya ƙara bunƙusa, ta zama cikakkiyar mace. Tsalle da tsantsi a jikinta sun bayyana sabon canjin da ya faru. Amma cikin murna , ta faɗi: “Dr batagama ba, kawai ta zame…”






A nan Dr SADEEQ yana cikin tunanin yaganta, zuciyarsa cike da mamaki rashin hankali na ta
“INNALLILAHI… wai ke? yaushe zaki yi hankali? Wayagayamiki ana gudu a toilet ki fito haka…”






Ya juya a hankali, cike daban haushi yana kallon wannan sabon yanayi da Atika ta samu,




Ihu ta buga sosai har ya giggita part ɗin. Dr SADEEQ nan da nan ya tashi, zuciyarsa ta ɗan tsaya, ya hango Atika tana ihu a kwance tana birgima takasa tashi
Dai dai wannan lokacin, Indo ta fito daga ɗaki tana zagayawa, a gidan tana mamakin girman gidan. Idonta na haske, fuska cike da sha’awa da mamaki. Ta tsaya a wani part,da take jin ihu gadan gadan ta tura ƙofar ɗakin a hankali, komai na cikin ɗakin tsaff, red da black, kayan ado da ƙamshi mai kyau.


Kamshin ya shiga hancinta, ya sa ta ɗan ja numfashi, tana jin daɗin yanayin gidan da tsarinsa. Ta tsaya kaɗan, ta kalli kayan da aka tanada, ta murmusa a hankali, tana jin kamar tana cikin wani sabon duniya.




Tana shigowa, ihu na ƙara ƙarwa. Atika kwance ta faɗi, ido a rufe, fuska ta cike da tsoro da mamaki. Ihu na ƙarawa, sai Dr SADEEQ ya damƙe kai ya tambaye ta cikin azaba "Atika, me ke faruwa?!"
ta ɗan ɗaga fuska, zuciyarta na bugawa da sauri, sannan ta faɗi da ƙarfi:
"I'm pregnant… shine zan gaya maka, na faɗi, muje asibiti! waiyoo ciki na

6 / 48