Author : Nana Kanwar Soja Category : Hausa Read
cikin irin wannan aikin ba. Ga turaren da Kamal ya kawo, yanzu dakin ya koma kamar dakin emergency room.”
Sai ya sake tsaki, ya miƙe kamar wanda ke tsoron mantuwa, ya nufi dakin inda Indo take.
Yana buɗe ƙofa, sai iska ta bugo masa fuska, warin turare da jinin allura suna haɗuwa da sanyin AC. Indo na can kan gadon, ta kwanta cikin nutsuwa, numfashinta daidai, fuskarta cike da salama kamar wadda bata san komai ya faru ba.
Ya tsaya yana kallonta, idonsa ya cika da haushi da dariya a lokaci guda.
“Kai Indo... wallahi ke ce bala’in da ya fi cutar zuciya.” ya ɗauke kai yana harararta, sannan ya juyo da natsuwa “tunda ke kina bacci kamar jaririya, ni kuma sai in kwana da ciwon wuya saboda royal chairs ɗina.”
Ya koma palourr, ya ɗauke pillow ɗaya da blanket, ya shimfiɗa kansa a kan kujerar mai laushi yayi juyi sau biyu, sau uku, amma ko ta taushi, kujerar ta ki karɓarsa.
Ya dafa goshinsa yana furta a hankali:
“Wai ni Dr. Sadeeq, likitan da ake ta yaba tsafta da nutsuwa... yanzu haka na kwana da blanket a kan kujera saboda Indo. Allah dai Ya cire min wanan tausayin mata ko zan koya mata hankali.”
Sai ya yi murmushi mara daɗi, ya lumshe ido, yana ji kamar kujera na masa zafi duk da sanyin AC ɗin dakin kafin ya jima, barci mai nauyi ya kwashe shi — barcin wanda zuciyarsa ta gaji da rigimar wata yarinya mai suna Indo.
Ƙarfe uku na dare.
Dakin ya cika da shiru mai nauyi, sai ƙarar fan mai sanyi da ƙamshin turaren “Oud Supreme” dake yawo cikin iska.
Indo ta fara motsawa a hankali, kanta yana juyi kamar mai mafarkin nisan zango.
Ta ji hannunta na taɓa wani abu mai taushi, mai ɗan sanyi — ta ɗaga kai da wahala, ta hango hasken fitilar bango yana haska ɗakin da bata taɓa shiga ba.
Ta lumshe ido, tana ƙoƙarin tuna inda take, amma sai wani sanyin ɗakin ya ratsa ta gaba ɗaya, kamar iska ta firgita ta ta shafi cikin ta a hankali, a mamakinta taji ciwon da ya dame ta dā ya lafa — kamar bai taɓa zama mai tsanani haka ba, ta ja dogon numfashi tana shirin kwanciya, sai kuma taji kamar wani abu ya shafi ƙafarta — santsi ne, amma da ɗan zafi kaɗan.
Ta ɗago kai a hankali, ta sauke ƙafarta daga gadon...
Sai ta ji wani abu mai kauri da laushi, tana shafar sa da yatsunta — kuli-blanket ne, irin masu taushi da kamshi, da kaɗan ka taɓa su sai sanyi ya lulluɓe jikinka.
Ta ƙurawa kayan kallon mamaki, tana ƙoƙarin fahimtar yadda suka zo nan, sannan ta shafa tausa ta blanket ɗin a hankali, tana shirin tashi.
Sai dai kafin ta miƙe sosai, taji wani irin zafi mai sanyi ya ratsa mararta ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa a hankali ta leƙa ƙasan rigarta — sai taga pad a jikinta, ga ɗan jini a gefe.
Da sauri ta runtse ido, zuciyarta na dukan bam-bam kamar ana jifan ta da dutse.
Tayi maza ta ja numfashi, ta sake leƙawa... tabbas, ba mafarki ba ne, ta juya kuma taga ba dakin ta take ba , shikkinan daman tanaji a unguwar su ana an tsinci wata yarinya da jini akace fyade aka mata abinda kullum Mama take ce mata ta daina faɗa da maza kinan ...
sai kawai ta saka hannu ta dafe ciki, ta fara rawar jiki “Innalillahi... meye ne wannan?”
Kafin ma ta kammala magana, ihunta ya faso shiru — muryarta ta cika ɗakin, ta tsorata kanta, ta maida numfashi kamar wadda aka farka daga mafarki mai ban tsoro.
Indo ta dafe cikinta, jikinta yana rawa.
“Jiya... jiya ina nake? Lami ce ta tafi da ni... ko Dr. Balarabe...?”
Tayi saurin kifa kanta kan gado, tana fidda numfashi mai zafi. Hawaye suka cika idonta.
“Wai ni... ni ce nake cikin dakin Dr. Balarabe?”
ta zaro ido da tsoro zuciyarta ta dinga bugawa da ƙarfi kamar ana shirin karya ƙirjinta. Sai kawai ta rufe kanta da bargo, tana jijjiga kanta da hawaye , “Innalillahi! me yasa na bari ya gani ni haka? Ko ya taɓa ni ne?????
Ihun Indo ya faso dakin kamar ƙarar ambulance!Dr. Sadeeq, wanda yake barci da bargo a kujera, ya tashi da tsalle kamar wanda aka harba da shocker.
“Wayyo Allah! mutane ne suke ihu a part ɗina!?” ya faɗa yana miƙewa da gaggawa.
a hanzarce ya yi yunƙurin saukowa daga kujera, amma sai ƙafarsa ta makale da blanket ɗin da ya lullube da shi — wufff! ya faɗi a ƙasa kujerar ta juya sa table ɗin gefenta kuma ya buga kansa taaa! “Wayyo kai na! Indo wallahi kin kashe ni!”
Ya riƙe goshinsa da hannuwa biyu yana zaro ido, yana yawo a wajen kamar wanda ya rasa inda zafi yake.
Sai kuma ya tsaya tsaf, yana sauraron ihun da ke fitowa daga ɗakinsa “Subhanallah… Indo ce kenan!”
Cikin tsoro da gaggawa, ya fice daga palour ɗin da slippers ɗinsa ɗaya ne ma ke kafarsa ɗaya ɗaya, dayan ya bar shi a ƙasa
Da sauri Dr. Sadeeq ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, bai ma jira amsa ba — kwaaa! ya tura ya shigo a lokaci guda ya danna switch ɗin fitila, hasken ya cika ɗakin kamar rana.
Indo na tsaye tsakiyar gadon, gashinta a warwatse, idanunta jajaye kamar wata karamar aljana da zarar idonta ya sauka kan Dr. Sadeeq, sai ta ƙara ihuuuuu tana ɗaga hannu sama kamar wadda ta ga fatalwa!
Kafin ta ƙarasa, sai Dr. Sadeeq ya yi wufff! ya ƙarasa kanta cikin tsalle kamar mai ceton rai daga gobara ya toshe mata baki da hannunsa yana zaro ido — saboda ba don komai ba, sai saboda kanshi da ke ƙulle-ƙulle daga buguwar table ɗin dā.
“Shhhh Indo! Ki yi shiru! Don Allah kar ki tasar min da gidaaa…”
Yana magana yana riƙe kanta da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana dafe kansa da zafi.
Sai kuma ya yi wata irin murya mai rauni:
“Ai yanzu idan ban mutu da bugun kai ba, zan mutu da ihunki Indo…”
Indo kuwa ta kasa tsayawa, tana ƙoƙarin ƙwace bakinta daga hannunsa tana“mmm-mmm!” cikin rawar jiki yana ƙoƙarin daidaita kanta, sai kuma numfashinta ya yi nauyi ta ce a hankali “Dr. Balarabe, ni a ina nake ne…?”
Ya tsaya, yana kallonta da ido biyu da ke rawar gajiya, sannan ya furta da muryar kuka da dariya a lokaci guda “Ke a inda kika bani hauka Indo — a gadona! A cikin part ɗina!”
Ganin ta ɗan natsu, ta daina ihun da ke neman tayar da gidan, sai Dr. Sadeeq ya sassauta hannunsa daga bakin ta a hankali.
Ya ɗan ja numfashi, yana shirin tambayarta da tausayi: “Indo, kina lafiya ? ki daina tsoro..
Kafin ya ƙarasa, Indo ta riƙe cikinta da hannu biyu, ta ɗan zaro ido kamar wadda ta gane wata sirri mai ban tsoro.
Ta furta da rawar murya cikin tsoro:
“A dakin ka…? To shikkinan kenan! Ashe ni da gaske aka…”
Ta tsaya, ta ɗan ja numfashi, sannan ta dafe kai tana ƙara faɗin, “Wayyoo na shiga uku! A kauyen mu ai akwai yarinya da aka yi mata fyade aka ganta da jini… yanzu shikenan, Dr. Balarabe ya min fyade!!!”
Tana faɗin haka ta rufe fuskarta da hannu, ta fara karkarwa kamar wadda aka zarge da laifi.
Dr. Sadeeq kuwa Bai iya tsayawa ba.
Ai kamar barkono ne aka zuba masa a ciki — sai kawai ya kwashe da dariyar wahala yana kame ciki “What?! Indo! Ni?? kin ce ni??”
Ya kasa ci gaba da magana saboda dariya, sai yana riƙe ciki yana juya gefe yana cewa “Oh my God… wannan yarinyar zata kashe ni da hauka!”
Indo kuwa, ganin yana dariya kamar mai yi mata dariyar zalunci, sai ta ɗaga murya zata ƙara ihu, tana faɗin “To ni wallahi zan kira Mama! Ba zan bari ba—”
Kafin ta ƙara wani ƙara, ya yi wufff! ya kai hannu ya toshe bakinta karo na biyu cikin rawar dariya da gaggawa.
“Indo shiru! Don Allah kar ki tada ni da duniya! Wani fyade kuma? ni Dr Sadeeq?? A kan gadona??”
Sai kawai suka faɗa cikin ƙanƙarar juna, ya riƙe bakinta yana dariya, ita kuma tana ƙoƙarin kwacewa kamar mai dambe — ƙarshe blanket ɗin gadon ya lullube su duka.........................To be continued
DR SADEEQ ✨
4️⃣1️⃣💥4️⃣2️⃣
Ai blanket ɗin ya rufe su da gaske, Indo ta fara rawar jiki tana kakkarfan ƙoƙarin kwacewa, tana jijjiga hannayenta tana faɗin cikin murya mai cike da tsoro “Toh na shiga uku! Wallahi yanzu zai ƙara.min wani fyade! Wayyoo Mama ki zo ki ceci Indo!”
Dr. Sadeeq kuwa, yana cikin dariya har hawaye ke fitowa, yana ƙoƙarin tashi daga blanket ɗin amma sai ta ci gaba da jujjuyawa tana tangarɗe shi a ƙarshe blanket ɗin ya manne musu gaba ɗaya kawai suka faɗi a gefe na gado duka biyu Ya ɗaga murya yana faɗin cikin dariya " Shut up Indo Jinin haila ce "
Tana numfarfashi da sauri kamar wadda ta yi gudu, ta ɗan leƙo fuskar sa a ƙarƙashin blanket ɗin, tana murmushin yaro-yaro cike da kunya da ruɗani “Toh… ai jini na gani… shine na zaci—”
“kin zaci fyade akayi miki kenan?” ya katse ta da dariya mai ƙarfi, yana tura blanket ɗin gefe yana gyara zama Ya dafa kansa da hannu ɗaya yana faɗin: “Kai Indo, wannan jinin da kika gani ba fyade bane… period ne fa, menstruation! kin ji?”
Tana kallonsa da idanunta a zare, tana magana kamar wadda aka tura ta cikin sabuwar duniya “Shi kenan? Toh menene wannan… period ɗin?”
Ai nan ne ya sake fashewa da dariya, yana riƙe ciki, yana faɗin: “Na gama! Indo wallahi zaki kashe ni! Kin fito daga ƙauye ba tare da kin san menene period ba??”
Tana jin haka ta turo baki, tana hararar sa cikin shagwaɓa “toh ai ba kowa ne yasan irin abubuwan birni irin naka ba! ti ba mu da doctor a can!”
Sai ya ɗan lafa dariyar, yana kallonta da idanu masu cike da nishaɗi da ƙauna mai taushi.
Ya furta cikin sanyi: “to yanzu kinga, babu wanda ya miki komai, ki huta kuma kar ki ƙara faɗin fyade kin ji? idan ma bukata ce nake dashi badai akan ke ƙwailar ƙauye ba ,kin kusan bani heart attack!”
Tana murmushi da ɗan kunya, ta ƙura masa ido ta ce cikin ƙasaita:
“Toh ni ba ƙwaila bace "
Ai sai ya sake fashewa da dariya yana faɗin“Indo… wallahi ke bala’i ce!”
Ya kalle ta yana murmushi cikin miskilanci, yana faɗin da murya mai sanyi:
“Kin ji ko Indo, wannan ai al’ada ce. Idan mace ta kai shekara 13 ko 14, idan al’ada ta zo, ba a sallah a lokacin. Ba abin tsoro bane.”
Tana gyada kai a hankali, idanunta na kallo ƙasa cikin kunya da rashin fahimta sosai.
Ya ƙara cewa“To yanzu ki nitsu, kar ki sake ihu. Ba a cikin bushiya kike ba fa, gidan likita ne nan. Kin tashe ni da ihu kamar wadda aka yi wa tsafi.”Ta ɗan yi dariya a hankali tana rufe fuska da hannu:“Toh ai ban san me ke faruwa ba… sai na ji jini kawai.”
Ya yi ƙoƙarin miƙewa gaba ɗaya, sai dai kansa na ɗan juyawa saboda bugu da ya sha. Yana murmushi ya ce “Ni kam kin kusa kashe ni da ihunki yau. Allah ya tsare, ke bala’i ce Indo.”
Ta ɗago da murmushi mai taushi ta ce:
“Toh ai baka faɗa min ba tukunna cewa al’ada ce… na zaci wani abu ne…”
Ya kalle ta, ya yi ɗan shiru yana murmushi cikin jin daɗi, sannan ya furta da dariyar siririya “Wannan Indo sai dai a saka ta a film wallahi.”
Indo ta sauke rigarta a hankali, fuskarta cike da kunya, rigar kuma ta chukuikuye kamar wadda ta fito daga faɗa da guguwa.
Ta miƙe da kyar, tana jingina da bango, hannunta ɗaya a ciki ɗaya kuma tana dafe ƙirji.
Dr. Sadeeq ya kalleta yana dafa goshinsa da murmushi mai rauni.
“Wai ke Indo… rigar nan kamar ta fito daga yakin Gaza, kaza ga dirty "..
Ta ɗan murmusa cikin rauni, muryarta a sanyaye “Ai kai ne da kanka baka ce min me ke faruwa ba, sai dai ka toshe baki na kamar kidnapper.”
Ya girgiza kai yana ɗan cizza ƙassan lebbansa
“Ni kam ban san yadda na tsira da ke ba… yanzu, kiyi hakuri, sauran kiyi hira da kawayen ki, ko ma ki faɗa musu kin fara, ni dai in ji salama. Da safe zan kira ki, in miki bayanin komai. Amma yanzu— please go…”
Sai ta gyada kai, tana ta juyawa a hankali, ta nufi kofa cikin tafiya mai cike da kasala da ɗan turo baki.
Yana kallonta har ta fita, sai kawai ya juya ya koma part ɗinsa yana riƙe da kai.
“Wallahi wannan yarinyar zata bani ulcer… Allah ya kare ni daga Indo.”
Ya cire bedsheet ɗin gadon da gaggawa, ya jefa a gefe, sannan ya shimfiɗa sabon ɗaya, yana kwanciya a hankali kamar wanda ya fito daga tiyata.
Cikin numfashi mai nauyi, ya rufe idanu yana furta “At least yanzu zan samu relief kafin asuba… idan dai Indo bata dawo da sabon labari ba.”
Indo ta kai kanta cikin dakin ta, ta shimfiɗa a kan matress ɗinta tana sauke dogon numfash sai ta ji wani kamshi mai ɗanɗano — irin wanda har yanzu yake manne a jikinta, kamshin sa na Dr. Sadeeq da turaren sa daki jikinsa da shi.
A hankali, zuciyarta ta fara yin wani irin sauti a ciki — kamar wani sabon motsin zuciya da bata taɓa ji ba. Ta dinga tuna yadda ya kuke da ita, yadda ya daidaita magani da dukkan hankali, da yanda suke tare sai murmushi ya bayyana a fuskarta.
“Toh… ashe wannan ne ake cewa period,” ta furta a cikin ranta, tana jin wani ɗan tsoro amma kuma daɗi a lokaci guda.
Sai ta tuna a makarantar Islamiyya, lokacin da malamai suka yi magana akan yadda yaran mata suke fara fahimtar jiki da canje-canje. Ita bata taɓa fara ba, amma yanzu… sai ta ji kamar ta shiga wani sabon duniya.
Ta ɗaga hannu ta shafa fuskar ta a hankali, tana murmushi: “Wallahi… wannan abu yana da ban sha’awa, amma me ya sa zuciyata ke bugawa haka?”
Ta lumshe ido na ɗan lokaci, tana jin daɗin wannan sabon tunani da bai taɓa zuwa gare ta ba. Wannan shi ne farkon lokacin da Indo ta fara gane period, sai ta ɗan girgiza kai, murmushi ya wuce a fuskarta kamar hasken safe, tana jin kamar wani sabon labari ya fara a rayuwarta.
###$$$############
Washegari, karfe bakwai na safe, Dr. Sadeeq ya makara kadan saboda jiya bai samu bacci mai kyau ba.
Da niyyar yin alwala, ya shiga dakin wanka, amma sai ya tuna artabun da aka samu jiya da Indo — sai ya ɗan yi tsaki a zuciya “Yanzu haka… relief fa wai na samu ? Yarinyar karama, ni fa har gajiya naji a jiki.”
Ya yi wankan tsarki da sauri, ya fetoo, ya yi sallah asuba cikin natsuwa. Bayan haka, ya ɗan karanta Qur’ani kaɗan kafin ya koma wanka na yau da kullum.
Ya fito daga wanka, jiki yana sanyi, sai ya lura da kansa cikin madubi — kamar dai ya kimtsa dakin sa a cikin tunani.
Ya juya ya gyara gadon sa, ya ɗaga bedsheet ɗin da aka yi amfani da shi jiya, ya jefar da shi cikin basket ɗin kayan datti.
Sai ya miƙe, ya ɗauki towel ɗin sa, ya shafa kansa da jiki, yana murmushi da kansa
Ya ɗan zauna a gefen gadon, ya ɗauki numfashi mai zurfi, yana shirin fuskantar sabon rana cikin natsuwa, duk da cewa tunanin jiya na Indo yana manne a zuciyarsa.
Dr. Sadeeq ya tsaya a gaban madubi, ya kalli kansa a hankali, idanuwansa cike da mamaki. Jikinsa mai tsabta, fata mai haske, kafafunsa masu tsawo da ƙarfi, kirjinsa mai ɗan tsawo, hannu mai santsi — duk sun nuna cewa likita ne mai kulawa da kansa. Sai dai idanun sa sun kai kan wancan ƙaramar ja da kulutu da ya ɗauka jiya daga wahalar relief da Indo ta kawo masa.
Ya ɗan girgiza kai, ya yi murmushi mai ɗan ban tsoro “Wallahi, jiya… wannan relief ya bar mini ƙananan alamun da ba zan manta da su ba.”
Ya juya a hankali, ya shafa gashin kansa, ya ɗaga hannunsa zuwa kirjinsa, yana kallon ya gushi alamar yatsun ta na jiya
Sai ya ɗauko kayan yau da kullum — gajeren wando mai launin neavy blue da t-shirt mai santsi, wanda ke bayyana tsokar jikin sa, da kafafunsa masu daidaito da kyau. Ya shafa hannuwansa da turaren sa mai kamshi, yana jin sanyin ruwa da ƙamshin sabulu sa — yana ba shi nitsuwa mai kwantar da hankali
ya duba lokaci, ya ɗan tsaki, sannan ya fito daga dakin, ya wuce part na Mommy, inda hasken rana ke shiga ta taga, yana busa laushin ɗakin. Ya ji yadda zafi da sanyin iska ke haɗuwa, yana jin kamar jiki ya sake sabuntawa. Kafafunsa na yin “flip-flap” a bene, gashin kansa da turaren jiki na shawagi cikin ɗakin, yana sa shi jin kamar mai girman kai amma cikin nutsuwa.
Hummmmmmm 🙅🙅🙅🙅🙅🙅
DR SADEEQ ✨
4️⃣3️⃣💥4️⃣4️⃣
Dr. Sadeeq ya ɗan ja numfashi kafin ya shigo dining room, ya hango iyalinsa suna zaune a bakin tebur — kowa cikin kwanciyar hankali, yana cin breakfast. Haske na safe yana haskakawa ta taga, yana sa kayan tebur da fuskokin su bayyana da kyau.
“Good morning, Mom! Good morning, Daddy!” ya faɗa cikin natsuwa.
Mommy ta ɗan murmusa, Daddy kuma ya ɗan tsugunna da fuska mai kyau, suna kallon shi.
Na’iba da Layla suka ɗago kai, suka yi masa sallama cikin fara’a “Good morning, brother Sadeeq!”
Ya amsa musu da murmushi mai ɗan tsantsa, ya kalli flask ɗin ruwan zafi da aka ajiye a tebur, ya zuba arish da sauce na kaza a gefe, sannan ya sa tea a cikin cup dinsa.
Daddy ya ɗaga kai, ya fansa da fuskar tambaya , “Son, jiya baka fito masallaci ba, ko? Me ya faru kuma a goshin ka ?”ya ɗan