DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   13 / 48

36K to 39K   out of 141.3K words

Sadeeq ya ce “Kamal, tsaya nan. Wannan ne layin su.”






Motar ta tsaya a hankali. Dr Sadeeq ya fito a hankali daga motar, yana duban unguwar — duk da talaucin wurin, akwai wani irin annuri mai ban mamaki. Yaran suna wasa, wasu manya suna gaishe da juna da murmushi.


Kamal ya fito shima, yana murmushi yana faɗin:
“Wannan itace unguwar Indo kenan?”
Dr Sadeeq yana kallon gabansa Ehh, wannan kenan "sai jikinsa ya ɗan saki, numfashinsa ya yi nauyi.


Yayin da suke tsaye a bakin layin, sai iska mai sanyi ta busa ƙasan rigarsa, ya lumshe ido yana jin kamar yana jin muryar Indo tana cewa: “Dr Balarabe don Allah kar ku rabani da Mama, ita ce gatana…”


Kamal ya kalle shi, sai ya ce a hankali:
“Let’s go bro. Ka kwantar da zuciyarka. Mun iso, kuma wannan tafiyar ta da ma’ana.”






Sai suka fara tafiya a hankali cikin layin, suna wucewa cikin gidajen ƙauye masu ɗauke da ƙamshin ƙasa da hayaƙin girki.


Da suka matsa kusa da gidan mai unguwa, Dr Sadeeq ya tsaya. Yana kallon ƙofar gidan da idonsa suka ɗan cika da hawaye. Rana ta riga ta fadi, hasken yamma na haskawa a gefen fuskarsa yana sa ta yi wani irin annuri mai zurfi Kamal ya tsaya a gefensa, ya ɗora hannu a kafaɗarsa yace “We’re here right, Doctor. Indo’s world.”




NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️🤌





















https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM?mode=wwt





COMMENTS SECTION GROUP 2
👇👇👇
ONLY FOR COMMENTER'S


https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1?mode=wwt



✨🩺DR SADEEQ 🩺✨
by
NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





Dr Sadeeq and Indo's contrasting personalities are bound to create some sparks, their love was written in the stars, but they needed a little drama to find it....
24 / 11 / 2025
بسم الله الرحمن الرحيم , اللهم صل على النبي محمد صلى الله عليه وسلم تسليما كثيرا.




https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲






P 2️⃣4️⃣


Tun safiyar yau, yau sati na biyu da rasuwar Mama.
Indo ta farka da kasala, zuciyarta cike da kewar uwa. Gaba ɗaya jikinta ya yi nauyi, idonta kuma ya cika da hawaye da ta kasa zubarwa. Kamar yau ne ta rasa abin da ya fi muhimmanci a rayuwarta.


Da rana, tana fita ɗebo ruwa a rijiyar unguwa, wasu yara suka tsokane ta suna dariya kamar ba su san halin da take ciki ba. Indo ta kalle su da idanu masu cike da ƙuna, ta ce da ƙarfi,


“Kada kuga don Mama ta rasu, na zama shiru-shiru, wallahi ban yi sanyi ba! NICCE nan dai Indo! Indo ta Mama! Ku taɓani ku gani, zan rama! Amin mugunta, na duke yaro a banza!”
yaran suka watse da tsoro, wasu suna dariya, wasu kuma suna mamaki. Indo kuwa ta tsaya a wurin tana haki kamar wadda ta yi gudu mai nisa.






Da ta dawo daga rijiyar nan da bala’i, Indo ta shigo gida tana huci kamar an kore ta daga fada.
Tana shiga ta ajiye guga, ruwan ya zuba ƙasa frrrrrr, sai ta kalli ruwan tana cewa:
“Kai ni Indo, ko ruwa ma yanzu baya girmama ni. Da Mama tana nan, da ruwan nan da kansa zai tsaya min.”






Tana faɗin haka, sai ƙaramar yarinya mai suna Hajara mai wayo ta shigo tana dariya.
“Indo wai suna cewa kin yi wa yaro duka saboda ya kira ki ‘Indo mai hawaye’.”






Indo ta ɗaga ido da fushin gaske:
“To meye? Ni ce Indo mai hawaye, ko Indo mai dariya, ai ina da suna biyu yanzu — Indo ta Mama kuma Indo mai ɗanƙo! zagi na yayi Ni kuwa na masa shegen duka”






Hajara ta fashe da dariya ta gudu.
Indo ta girgiza kai, ta ce da murmushi:
“Wallahi idan Mama na tana gani, sai ta ce ni dai Indo ba zan taɓa zama mutum mai nutsuwa ba.”


Sai ta nufi turakar Inna Sabuwa, ta ce,
“Inna, wallahi yau bana yin sallah sai na ci abinci na farko. Idan ba haka ba, zan yi sallah da cikina yana kuka.”Inna ta ce da dariya,
“To Indo, ai ke ce kawai kika fi Mama surutu. Mama ta tafi ta bar min yarinyar da idan ta yi shiru, to tana bacci!”






Duka suka yi dariya sosai. Indo kuwa ta jefa kanta a kan tabarma tana dariya har hawaye na fita, sannan ta ce cikin nishadi:
Ta zauna a kan tabarma da ta tsufa, da zani kampala da ya fita hayyacinsa saboda tsufa da datti. Dankwali babu a kanta, gashin kanta na nan a buɗe, bai sha gyara ba, sai ga ƙurajen goshi da rana ta busar.


Sai Inna Sabuwa, matar mai unguwa ta fito daga ɗaki tana tauna goro, ta ce cikin tausayi “Indo na, sallar la'asar ga ta wuce mangariba ma har ta yi ja. Ki tashi ki daura kallabi, ki tafi ki yi alwala , kafin kice towon.”






Indo ta ɗago kai a hankali, idonta jajaye, muryarta ta dushe. Ta ce a hankali kamar wadda take magana da zuciyarta:
“Mama, da kina nan, da ba haka rayuwa take min ba…”Sai hawaye suka zubo kamar ruwan sama.
-


Tawon dawa ne da miyar kuka Indo ke ci tana zaune bakin ɗaki, tana shraɓe hanci tana murmushi da hawaye lokaci guda.


“Kai Mama… da kina nan da sai ki ce, Indo, kinacin towon nan kamar an yi a gidan sarauta.”


Sai ta ɗaga kwanon, tana kai harshe tana lumshe ido — miyar kuka ta sauka gefen leɓenta Kafin ta kai cizo na gaba, sai ta ji ƙarar mota a kofar gida.
Numfashinta ya tsaya cak “Wayyo Allah! Dr Balarabe ne ya dawo!”


Ta miƙe da gudu — towon a hannu, miyar kuka a baki, takalmi babu, rigar jikinta ƙwance da kura da hanzari ta buɗe labulen zauren gida, ta tsaya chak! motar ta tsaya — iska ta busa miyar kuka a hannunta tawon ya makale a maƙogwaronta ta fara tari: “Kah! kah! kahhh— wayyo! Dr Balarabe ya dawo!”
Tana ihu da tari sai ta ga mutum ya fito daga cikin motar — dogo, farin kaya, gilashi a fuska.
“Dr Balarabe! Dr Balarabe!!”






Kafin ya ce komai, Indo ta yi ihu ta faɗo jikinsa da gudu — Dr SADEEQ! ai kuwa da kwanon miyar kuka ya shafe rigar sa gaba ɗaya!
Sai ruwan miyar kuka mai kore ya zuba a farar rigar sa har ƙasa!


Dr SADEEQ ya tsaya kamar an ɗaure masa jiki, ya kalli Indo da ido biyu cikin mamaki.
Indo kuma tana ihu tana fadin:
“Na faɗa muku zai dawo! Wallahi Dr Balarabe ya dawo!” hankali?
Dr SADEEQ ya tsaya kamar an jefa masa ruwa mai zafi — idanunsa suka firfito, numfashinsa ya tsaya cak.
“Oh my goodness!” ya faɗa da ƙarfi, yana ja da baya.






Ga miyar kuka tana kakkarwa daga rigar sa, tana zubewa ƙasa kamar jini.
Sai ya tsare ƙazantar da idanunsa, yana fadin:
“Ya Allah! Wannan miyar kamar... kashi kore sharrr... Indo!!!”






Yayi kamar zai kai mata duka, sai kawai ya rike kansa da haushi Indo kuwa, maimakon ta tsorata, sai ta rike ciki tana dariya tana cewa:
“Dr Balarabe! Lallai na bata maka riga. Kai haƙuri bare in kawo maka ruwa in wanke maka ta!” Dr SADEEQ ya kalleta da mamaki da takaici haushi ya mamaye shi har bakinsa ya kasa furta kalma ɗaya.
Dr Kamal kuwa, wanda yake tsaye a gefe yana kallo, ya rik’e ciki da dariya.
“Wai wannan ce amaryar sirrinka? Hahaha! Wallahi gaskiya rayuwa bata da kyau, Dr Sadeeq!”






Dr SADEEQ ya juyo da mugun kallo yana fadin:
“Kamal, wallahi zan mare ka.”
Kafin su rufe maganar sai ga mai unguwa ya iso da hanzari, yana kallon abin da ya faru.
“Subhanallah! Indo ce ta haka? Ta zuba miyar kuka a jikin bako? Allah ya kiyaye!”






Sai ya ce da ladabi:
“Ku yi haƙuri malamai, ku shiga ciki, a ba shi ruwa ya wanke jikinsa.”






Dr SADEEQ ya dafe kai, yana shakar numfashi cikin takaici, sannan yace cikin haƙuri:
“It’s normal… it’s okay. Bari kawai in canza kaya.”






Ya wuce cikin mota, ya buɗe jakar sa, ya janyo t-shirt mai launin blue.
Ya cire rigar da miyar ta jiƙa, ya sanya sabuwa, yana goge jikinsa da tissue.


Da ya fito, Kamal ya ce da dariya:
“Toh an gama! Amaryarka ta fara ba ka hot bath da miyar kuka! Hahaha!”
Dr SADEEQ ya jefa masa mugun kallo, ya ce cikin ƙasa-ƙasa:
“Kamal, if you laugh again, wallahi I’ll make you drink that soup.”
Kamal yayi dariya har yana sosa kai mai unguwa ya ja hannun Dr SADEEQ yana cewa:
“Ku zo ciki, don Allah, kuyi alwallah .”
suka shiga cikin gidan.
Indo kuwa tana tsaye a bakin ƙofa tana dariya sosai tana cewa: “Ai na ce muku zai dawo! Ku dai kun ce ina hauka!”


Dijje da su Haule kuwa suna gefe suna dariya suna cewa:
“Indo kin fara da ruwan miyar kuka! Wallahi wannan murna ba da sauƙi ba ne!”
Sai Indo ta saki murmushi tana shafar ƙirjinta ta ce cikin siririyar murya
“Toh ai sai da na gaishe shi da abincin gidan mu” kuna ganin ya ƙara kyau da haske Dr Balarabe na ya dawo ".....












more page's ? more comments!!!
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️ ✍️ 🤌 🤌 🤌












PG 2️⃣5️⃣






Suna yin alwala da girmamawa suka nufi masallaci tare da mai unguwa.
Mutane kuwa suna kallonsu, domin ganin wasu manya daga birni — attajirai, masu tsafta da kamshi — sun tsaya sallah cikin masallacin su ƙaramin gari.
Kallon duniya ne; wasu suna fadin:
“Subhanallah, wai likitoci ne daga Abuja!”
Wasu kuma suna dariya cikin sirri suna cewa: “Indo ce ta kawo sa’ar ta yau.”
Bayan an idar da sallar Isha’i, mai unguwa ya tsaya ya yi musu kyakkyawar gaisuwa, sannan aka kawo abinci.
Tuwon masara ne da miyar ganye mai ƙamshi, an jera a faranti, aka kawo da ruwa mai sanyi da gorar nono.


Amma da aka ajiye gaban su, Kamal da Dr SADEEQ suka kalli juna da murmushi.
Kamal ya ɗan matsa gaba, ya kalli mai unguwa da ladabi yace: “Mun gode sosai baba, Allah ya saka da alheri. Amma gaskiya muna jin ƙoshi… mun ci kafin tafiya.”






Mai unguwa ya kalle su da dariya, yana cewa:
“Ai ba laifi ne ba. Dama ban kawo don cikinku ba, don alheri ne.”
Suka yi murmushi da girmamawa, suka amsa da “Allah ya saka da kyau.”






Sai suka zauna suka ɗan huta, sai mai unguwa ya ɗanyi gyaran murya, ya dubi Dr SADEEQ cikin natsuwa ya ce“Yaron nan dan uwanka ne?”Dr SADEEQ ya ɗan gyara zama, ya ce da ladabi“Eh baba, dan uwana ne, muka taso tare tun ƙuruciya.”






Mai unguwa ya jinjina kai cikin tausayi, ya ɗan lumshe ido kafin ya ce:
“Toh, Allah ya sanya albarka. Ka saurara da kyau, dan uwana. Indo da kuka gani ba irin ‘yan mata bace da kake gani a gari. Ita marainiyyar Allah ce. Bata da uba, bata da uwa. Mahaifinta ya rasu tun tana cikin mahaifiya, ita ma mahaifiyarta ta rasu a gaban ka”






Ya ɗan ja numfashi, yana kallon ƙasa, sannan ya ci gaba cikin murya mai rauni:
“Ta tashi da gata, babu mai kula da ita sai mahaifiyar ta Shi yasa ta tashi da halin tsokana, fitina, da dariya. Amma wallahi Indo bata da mugunta. Yar tausayi ce, yar kuka, amma zuciyarta tana da kyau kamar zinariya. Don haka ka daure, ka rike ta. Ka jure da halinta, ka tuna amanar mamarta da ta rasu.”






Maganar mai unguwa ta shiga zuciyar Dr SADEEQ kamar wuta da sanyi lokaci ɗaya.
Ya kasa cewa komai — kawai ya jinjina kai, yana shakar iska a hankali.


Mai unguwa ya kalli Kamal, ya ce cikin karfin zance:
“Kuma ku sani, wannan aure sirri ne tsakaninmu. Na san babu wanda ya sani daga wajenku. Ni ne na daura, tare da kai, Dr da da waɗannan mutane uku — yan uwana.”
Sai ya ja ƙaramar kwalba, ya ɗaga ta sama, yana cewa “Ga sadaki nan, dubu ɗari biyu. An biya. Don haka, Indo yanzu halal ce gare ka a bisa shari’a. Allah ya albarkaci zamanku, ya sa aurenku ya tabbata.”






Dr SADEEQ ya ji kamar an daura masa dutsen amanar duniya a ƙirjinsa.
Zuciyarsa ta cika da shiru, idonsa ya ɗan kaɗa, amma ya daure ya ce cikin murya mai tausayi “Na gode, baba. Na yarda. Zan rike ta. Allah ya saka da alheri.”Sai Kamal ya ɗan gyara zama, ya kalli baba da fara’a ya ce:
“Baba, gaskiya za mu faɗi abin gaskiya. Iyayenmu ba su san da wannan aure ba tukuna. Don haka muna roƙonka a bamu Indo a sirri. A yanzu, mu tafi da ita a hankali. Zamu gyara komai a hankali, mu shirya, mu sanar da iyayenmu.”






Mai unguwa ya kallesu sosai, yana duba Dr SADEEQ da Kamal, sannan ya yi murmushi mai cike da hikima.
“Na fahimta. Ku tafi lafiya. Indo amana ce gare ku. Amma ku sani — sirri ba ya ɓoye har abada. Ranar da gaskiya zata fito, ku tabbata za ta yi haske kamar rana.”
Sai ya miƙa hannu ya yi musu addu’a “Allah ya sa aurenku ya zama na albarka, ya kare ku daga fitina da rashin fahimta.”
Dr SADEEQ ya share gumin goshinsa, yana fadin “Amin… amin, Baba.”
Kamal ya kalle shi yana murmushi kadan, ya ce cikin raha “To, Ango Dr SADEEQ, yanzu amaryarka ta sirri fa za ta tafi da mu. Ka shirya?”
Dr SADEEQ ya kalle shi da ido mai nuni da gargadi, amma a zuciyarsa akwai wani nauyi nauyin alƙawarin da bai taɓa tsammanin kansa zai ɗauka ba.


Indo ce ta fito mai unguwa yace da ita tazo
Indo ta jinjina kai, zuciyarta na dokawa. Idonta kuwa ya tsaya ne a gaban teburin da kuɗi ke shimfiɗe a kai kamar furen zinariya.
Ta zauna a hankali, amma hankalinta yana ta yawo tsakanin kuɗi, turaren Dr. Balarabe, da tambayar me ke faruwa.


Mai unguwa ya gyara murya cikin kulawa da tausayawa.
“Indo, Mama ta ce kina da buri ki zama likita. Kin san halin ta — kullum addu’arta ce ta ga ke kin tashi da ilimi da mutunci. Shi yasa Dr. Balarabe zai tafi dake Abuja. Za ki zauna a gidan su, za ki karasa karatun ki can.”


Indo ta ware ido, ta ce cikin farin ciki,
“Ni? Abuja? Wallahi na yarda! yaushe zamu tafi?”


Dr. Kamal da ke gefe ya danne dariya, yana kallon yadda ta rude cikin farin ciki.
Mai unguwa ya girgiza kai yana murmushi.
“Da safe, Indo. Amma ki tuna da wannan maganar — gaskiya, riƙon amana, da haƙuri. Ki bar rigima da tsokana. Idan kika ci gaba da haukarki, Abuja zata koya miki hankali.”


Indo ta rufe baki tana dariya, ta ce da rainin hankali:
“Ni dai naji. Amma ku fa, idan kuka je, ku roƙi Allah ku dawo da ni da likitancin gaske.”


Mai unguwa ya ɗaga hannu sama,
“Ameen, Indo. Allah ya tsare ki.”


Su mata suka yi mata wa’azi sosai — kowa da nata shawara, wasu na dariya, wasu na tausayawa. Ita kuwa Indo sai murmushi take, tana jin ƙamshin turaren Dr. Balarabe yana ratsawa cikin zuciyarta.
“Abuja,” ta maimaita a ranta cikin nishaɗi, “to yanzu ashe ni ma zan shiga jirgi… babu ruwan su Dijje da masararsu!”


Indo ta ɗan sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, idonta yana bin Dr. Balarabe da murmushi.
Sai ta ce da ƙaramar murya mai cike da wasa:


“Dr. Balarabe… idan dai har gaskiya ne zaku tafi da ni Abuja, to sai ka sayo min kaza da lemo kafin mu tafi fa.”


Su Kamal da mai unguwa suka yi dariya sosai.
Dr. Balarabe ya kalle ta da murmushi yana girgiza kai,
“Indo, kaza da lemo? Ai da ke babu rashi! Amma fa idan har kin yarda za ki bimu Abuja, zan saya miki kaza da lemo, har da cake idan kina so.”


Indo ta saki dariya tana bubbuga kirjinta da hannunta,
“Na rantse ma zan biku! Wallahi ni ba zan tsaya a nan ba. Abuja, kaza, lemo da cake — ai rayuwa ta can ta fara yanzu!”


Dr. Kamal kuwa ya fashe da dariya yana kallon ta,
“Ke dai Indo, baki canza ba — kullum da rigima da dariya. Allah dai ya kiyaye hanya.”
Indo ta ɗaga kai cikin izza tana murmushi,
“Ku dai ku gani, na tashi daga rigima zuwa birni!”


Mai unguwa ya gyara rawani yana kallon su cikin nishadi,
“To shikenan, tunda kin amince, gobe da safe zaku tafi. Allah ya sa alheri, ya kuma ba ki natsuwa Indo.”


Ita kuwa Indo sai dariya take, tana ta murmushi tana cewa a ranta:
“Kai ni Indo — daga towon dawa zuwa jirgin Abuja! Lallai duniya daɗ---


DARE


Mai unguwa ya zauna a kujerarsa, yana kallon Indo da murmushin tausayi, sai ya nisa kadan.
“Indo…” ya kira sunanta da sanyi, muryarsa ta sauya daga barkwanci zuwa ta tausayi.
“Kin ga rayuwa tana da darussa da yawa. Wani lokaci tana baka dariya, wani lokaci kuma tana baka kuka. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ki san inda kike nufa.


Mama — Allah ya jikanta — ta bar miki kalmomi masu nauyi. Ta ce za ki zama mutum mai daraja idan kika rike gaskiya da mutunci. Ki tuna, Indo, mata kyawunsu ba a jiki yake ba, yana a zuciya ne da halayya.


Yanzu ga wata dama Allah ya kawo miki. Kiba kanka kunya da natsuwa, kada ki zama kamar da. Ki guji rigima, tsokana, da wasa da mutane.
Abin duniya ba komai ba ne, Indo. Abin da yafi komai daraja shine mutunci da amana.


Idan kika shiga birni, za ki ga mutane iri-iri — masu arziki, masu kudi, masu ilimi, da masu wayo. Amma ki tuna: ba duk wanda yake dariya dake yana sonki bane.
Wasu dariyarsu cike take

13 / 48