DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   42 / 48

123K to 126K   out of 141.3K words

bala’i, yana rusa mai shi kafin ya taɓa wanda ake kishi a kansa. You need strategy, not anger.”


“Wace strategy kuma?” Atika ta tambaya da sauri.


Ihsan ta ɗan yi murmushi, akwai ɗan barkwanci a ciki. “First—ki gyara kanki. Not for Dr alone, for yourself. Second—ki daina nuna cewa Indo tana da iko a zuciyarki. Maza suna gudun mata masu hayaniya. Third—ki sa hankali. Indo yarinya ce, ke kuma mace ce. Time is on your side… idan kin san yadda za ki yi amfani da shi.”


Atika ta yi shiru. “Amma Ihsan, sometimes ina jin kamar Dr yana kallona ne kawai saboda aure, saboda buƙatar sa da kuma iyayen mu Amman nasan baya sona”


Ihsan ta matso kusa, ta kama hannunta. “Listen. A marriage is not a competition. If kina jin barazana, ki nemi hanyar gyara gidan ke "




Ihsan ta matsa kusa da Atika, muryarta ta sauya daga tausayi zuwa tsauri. Idonta ya ɗan yi duhu kamar wacce ta yanke hukunci.


“Atika,” ta faɗa a hankali amma da nauyi, “kar ki yarda ki zauna kina kallo ana cin mutuncinki a hankali. This is your marriage. If you don’t fight for it, nobody will.”


Atika ta ɗago kai, zuciyarta na bugawa. “Me kike nufi, Ihsan?”


Ihsan ta ɗan yi murmushi—ba na farin ciki ba. “Indo. Ke kanki kika ce tana shiga harkar Dr fiye da kima. Yanzu lokaci ne ki tsaya tsayin daka. Ki kira ta. Ku haɗu—ke da ita—face to face.”


Atika ta ɗan ja baya. “Mu haɗu? Don me?”


Ihsan ta matsa murya ƙasa. “Don ki sa ta gane iyakarta. Ba duka ne yake bukatar ihu ba. Sometimes, words are sharper than knives. Ki nuna mata cewa wannan gidan naki ne, wannan aure naki ne. Ki gajiyar da zuciyarta har ta fahimci cewa best option ɗinta shi ne ta fita daga harkar Dr SADEEQ.”


Atika ta girgiza kai, hawaye na taruwa. “Ina tsoro, Ihsan Kuma Dr—”


Ihsan ta katse ta. “Forget Dr for now. This is between you and her. Ki kira ta cikin Ki ce kina son ku yi magana sai mu zama mata layi ƙarfaffa




“Ke har yanzu kina ta tausaya? Wannan yarinyar fa tana shirin kwace miki miji a hankali.”


Atika ta fashe da kuka. “Ihsan wallahi na gaji. Ina jin kamar zuciyata zata fashe. Duk inda ya je, Indo"”


Ihsan ta yi tsaki. “That’s emotional manipulation. Kuma ke kina zaune kina kallo?”


“Atika,” Ihsan ta matsa kusa, ta rage murya, “mace idan bata kare aurenta ba, duniya ba zata kare mata shi ba.”


Atika ta ɗaga kai. “To me zan yi?”


Ihsan ta murmushi—murmushin da bai da alheri.
“Za mu kira ta. Mu haɗu da ita. Amma ba don magana ba.”


Atika ta razana. “Ihsan…”


“Ki saurare ni,” Ihsan ta katse ta. “Tsoro ne kawai zai cire ta daga harkar Dr SADEEQ. Threat. Humiliation. Idan ya zama dole—duka.”


Atika ta rufe fuska. “Ina jin kamar na hallaka ta har abada.”


Ihsan ta ce sanyi-sanyi: “To ki fara.”


Indo na kwance a kan gado, jikinta a naƙude. Yau tana period, cikinta na mata mummunan ciwo har ta kasa miƙewa da kyau. Idonta rufe, hannunta ɗora a ƙasan ciki, numfashinta na fita a hankali., yanzu ta samu tasha maganin pain relief domin samun sauki


Sai wayarta ta kifar da ƙara.


Ta buɗe idanu da ƙyar, ta ɗauki wayar.
Aunty Nazifa calling…ta amsa cikin sanyin murya.
“Hello… Aunty…”


Muryar Nazifa ta fito sanyi kamar ba komai.
“Indo, Atika na kiranki a part ɗinta ban san dalilin kirar ba, amma kije sai kiji.”


Indo ta yi shiru na ɗan lokaci. Ciwon ya sake ratsata.


“Okay Aunty,” ta faɗa a gaggauci


Ta katse kiran, ta zauna a hankali. Ta sauko daga gadon kamar wadda take ɗauke da dutse a cikinta. Ta buɗe wardrobe ta ɗauko doguwar jallabiya Arab, ta saka, ta ɗora mayafi, duk jikinta babu kuzari ko walwala.
ta fita gaba ɗaya ba tare da ƙarfi ba.




Da ta shiga part ɗin, Ihsan ce ta fara gani kafin ta ga Atika.


“Ke Indo, ke fa kina ganin kanki wacece?” Ihsan ta fara da baƙar magana.
“Gidan aure fa wannan, ba hostel ba.”


Indo ta tsaya a tsakar parlour, ta dafe ciki.
“Wallahi ban da lafiya… cikina na ciwo sosai. Yau banajin magana yanzu ku bari sai zuwa anjima”


Atika ta tsayai, idonta cike da tsana.
“Kar ki raina ni!” ta ɗaga murya.
“Ko kina da lafiya ko baki da ita, dole sai kin girka mana Indomie kuma ke tabbata kin gyara kitchen in don akwai wanke wanke”


Indo ta ɗaga kai a hankali, idonta cike da tsana
“Atika… wallahi bazan iya ba. Jikina babu ƙarfi.”


Ihsan ta yi dariyar raini.
“Ke dai kina amfani da ciwo ne a matsayin uzuri. Ki shiga kitchen.”


Atika ta ɗaga hannu ta nuna kitchen.
“Yanzu nan! kar ki sa ni na sake tsawata miki.”


Indo ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa. Ta ji kamar ana tsinka mutuncinta ɗaya bayan ɗaya. Ta juya a hankali, tana jan ƙafafunta, ta nufi kitchen—
ba don tana so ba, amma don ba ta da ƙarfin kare kanta a wannan lokacin.


A ranta ta ce:






Indo na cikin kitchen, hannunta na juyawa a hankali amma zuciyarta na tafarfasa kamar wuta.


A zuciyarta take… ba ta furta da baki ba.
“Da na san wahala za ku sani da banzo ba ".



Ta ɗauki tukunya, ta ajiye a kan murhu, cikinta na murɗawa sosai amma ta daure. “Ga uban wanke-wanke, wato ga baiwa ta samu..






Ta lumshe ido na ƴan dakiku, ta jawo numfashi mai nauyi “Wallahi sai na yi maganin ku.”
Ruwan famfo na sauka kan hannunta, sanyi amma zuciyarta zafi “Bani da sauƙi yanzu,
ba Indo da kuke sani ba ce a baya.”
Ta tuna da wulakanci, da tsawa, da kallo irin na raini. “Kun ɗauka shiru raini ne,
kun ɗauka haƙuri rauni ne.”
Ta ɗan jingina da bango, ta rufe idanuwanta.
“Amma zan nuna muku cewa, Indo ma tana da zuciya, kuma idan ta tashi,ba kuka take yi ba tana ɗaukar fansa"




Ta buɗe idonta, ta share hawayen da suka taru, ta kama girke kamar babu abin da ke damunta.


A parlour kuwa,
Atika na ta magana da Ihsan cikin dariya,





Indo na zaune a kan kitchen table, kofin tea a hannunta, numfashinta ya fara daidaituwa.
Ciwon period ɗin da ya dameta tun safe ya lafa kaɗan.
Bournvita da madara sun sauka a jikinta, zuciyarta ta ɗan samu nutsuwa.


Ta jingina da kujerar, idanuwanta a rufe na ƴan daƙiƙu.A zuciyarta“Allah na gode akalla na samu sauƙi kaɗan.”

Nan bachi ya ɗan kwashe ta , ta manta da cewa ta ɗaura Indomie akan wuta gashi yana ƙonewa wanda yasa Atika shigowa a firgice.
Idon Atika cike da tashin hankali da ɓacin rai, zuciyarta kamar wuta.
Ta kalli kofin tea, ta kalli Indo da yadda hankalinta ya kwanta Kafin Indo ta motsa—


tsaff!


Ruwan cup ɗin tea ya watsu a jikin ta


Indo ta miƙe a hargitse, zuciyarta ta buga, idonta ya cika da mamaki da zafi.


— “KAN BURA UBAN CHAN!
WAYA WATSA MIN RUWAN TEA ?!”


Atika ta buɗe baki da mamaki, sannan ta saki muryarta da raini “Ni ce nan, isashshiya.”
“Na sake aiki ki zo ki sha tea “Nan gidan uban ki ne?”


Kalaman suka faɗa kan zuciyar Indo kamar wuka.


Jikinta na rawar sanyi da zafi a lokaci guda.
Ruwan tea na sauka daga fuska zuwa wuyanta, amma abin da yafi zafi shi ne maganar.


A zuciyarta Indo ke cewa:
“To nan ne kuke so ku karya ni?”
“To nan ne zaku ga Indo ta rushe?”


Ta share fuskarta a hankali, ta ɗaga ido ta kalli
Sai da kallon da ya sa zuciya ta tsaya.






Indo ta cafke cup ɗin da ke kusa da ita,
tsaff! ta watsa wa Atika ruwan cikin a fuska.


Da murya mai sanyi amma cike da barazana ta ce “Na faɗa miki ki fita harkata.”
“Idan kika shiga gonata, zan nuna miki kalata.” “Wallahi bani da mutunci,
duk wanda ya fara min, zan ɗauka.”**


Atika ta girgiza da fushi Ba tunani ta mare ta.


Indo ba ta tsaya ba taye tsalle ta tsinka mata mari ta rama.


Cikin daƙiƙa kitchen ɗin ya rikide fagen yaƙi.
Duk abin da Indo ta kama, plate, jug, towel—
duk ya sauka kan Atika.


Atika ta ja baya, ta rikice.
Ta saki ƙarfi ta faɗi ƙasa.


Indo ta hau kanta,
ta dora gwiwa kan cikinta,
hannaye biyu suna jan gashinta da ƙarfi.
“Ku kalle ni yanzu!”
“Ba Indo ɗin da kuka sani ba ce!”


Atika na ihu, numfashinta na yankewa.


Sai Ihsan ta shigo da gudu,
fuska a firgice


“Innalillahi!”
Ihsan ta tsaya tana jan Indo da ƙarfi, tana ƙoƙarin hana ta ci gaba.
Amma Indo, ta dawo da kanta da masifa,
duk jikin su na rawa da faɗa, kamar aljannu a cikin dare.


Cikin ƙarfi da sauri, Indo ta fara dukan Ihsan,
ta damba da ita, tana nuna ƙarfin zuciyarta ba tare da tsoro ba.


Atika kuwa, da rarrafa wayarta, ta danna number Dr SADEEQ cikin sharri da fushi:
— “Indo zata kashe ne, Honey, ta kashe wayar!”


Amma Indo ta ji hakan, ta tashi da ƙarfi kan Ihsan,
sai kuma ta sake cafke Atika “Ne zakewa sharri? Wallahi sai na yi maganin ke!”




Indo ta ƙara ƙarfi kamar wadda aka cire mata tsoro daga zuciya.
Idanuwanta sun yi ja, numfashinta na fita da sauri, hannunta na rawa amma zuciyarta ta ƙafe.


Ta ture Ihsan ƙasa da ƙarfi “Ki rabu dani! Ke ba zaki hana ni ramawa ba!”


Ihsan ta faɗi tana ihu, kafin ta tashi, Indo ta sake cafke Atika da rigarta, ta jawo ta kusa da ita har numfashinsu ya gauraya:
— “Na sha wahala shiru, na sha kuka shiru, amma yau? ban tsokani ke ba ina rayuwa ta na kau da kaina akanki ke da mijin ke Amman kin kaine bango ba karfi kika fini ba ke tafe school namu ke tambaya wacce ce Indo ”


Ta turɓune Atika da bango, ta ɗaga hannu tana girgiza ta “Ki sani, ni ba yarinyar da kika tsoratar a baya ba ce na waye, na girma, kuma idan kika ƙara taka mutuncina… wallahi sai na manta da komai!”


Atika na kuka, jikinta na rawa, baki na karkarwa,
Ihsan kuwa ta tashi da wahala tana roƙo:
“Indo don Allah! Ki bari! Za a samu matsala!”


Amma Indo ta juya da tsawa:
“MATSALA TUNI TA SAMU NI! Wannan gidan ya raina ni, ya wulakanta ni, yau kuma kowa zai san ni wacece!”









₦@₦@₦@₦@₦@@₦@₦₦@₦@₦@






Dr SADEEQ ya shigo da sauri, idanuwansa a kan Indo da Atika.


Ya matsa kusa da Indo, ya kama hannunta yana ƙoƙarin ja ta daga kan Atika: “Indo, ki bar ta ke nitsu ke bar haukar nan.”


Indo ta janye hannunta a hankali, idanuwanta babu hayaniya, muryarta ƙasa:
“Dr, banason rashin hankali. Ina cikin hayyaci na yau zakuga ba nicce mahaukaciya ba Atika zakiga hauka .”


Ta sake matsawa gaba, ba don faɗa ba, don kare kanta.
Dr SADEEQ ya sake ƙoƙarin kamota, amma Indo ta baga jikin sa da ƙarfi ta ture shi gefe.


Nan take Dr SADEEQ ya fusata.
Ya juya da sauri, ya fisgo Indo daga kafada cikin hargitsi “NA CE KI NITSU!”


Indo ta girgiza, ta fara garuruwa saboda ciwo da tashin hankali “Ku barni! Ku barni!!”
kafin kowa ya motsa


CHAF! Mari ya sauka a fuskarta Indo ta tsaya cak kukan ya tsaya garuwa ta mutu.


Ta ɗago kai a hankali, ta taɓa kumatunta, idanuwanta suka cika da hawaye amma ba kuka.


Ta kalli Dr SADEEQ kai tsaye tace cikin murya mai sanyi, mai rauni, mai karya zuciya “Yanzu na fahimta."Shiru ya mamaye gidan.


Atika da Ihsan suka tsaya suna kallon juna.
Dr SADEEQ ya kalli tafin hannunsa, zuciyarsa ta buga da ƙarfi.


Indo ta gyara mayafinta a hankali,
“Ban zo nan don raini ba. Ban zo nan don a daka ni ba. da kansu suka kira ne suna musguna min kuma ita ta fara faɗar Amman amma ”.”
Ta juya ta fita ba tare da waiwaya ba.
Dr SADEEQ ya tsaya a wuri ɗaya, zuciyarsa ta fadi ƙasa mari ɗaya
ya rusa abin da shekaru ba su iya gyarawa ba.






Indo ta nufi part na Kamal cikin fushi da raunana zuciya. Kafin ta kai ƙofa, Dr SADEEQ ya gane abin da ya aikata
bai san sanda mari ya fita daga hannunsa ba ya bita da sauri
Indo ta shiga ɗakin ta ta rufe ƙofa da ƙarfi.
BANG!Dr SADEEQ ya tsaya a wajen, numfashinsa na rawaya jingina da ƙofar, ya runtse ido, murya cike da nadama:
“Indo… I’m sorry.” “Wallahi ban nufin hakan ba.”“Please, ki buɗe.” shiru, kamar da kurma yake magana.


Ya ƙara matsawa kusa da ƙofar, muryarsa ta yi sanyi, ta karye “Indo, ki ji ni. Ki ba ni minti ɗaya.” “I messed up… I know.”


Shiru acikin ɗakin, Indo ta zame ƙasa ta zauna, ta rungumi gwiwoyinta Hawayen ba su zubo ba sun tsaya a ido kamar sun gaji.


Ta faɗi a zuciyarta:
“A yau ne na gama fahimtar komai.”


A waje, Dr SADEEQ ya ja numfashi mai nauyi, ya sake magana cikin tausayi “I’ll wait. Ko dare ne.”shiru mintuna suka wuce gidan ya yi sanyi.
zuciya ta yi nauyi.


Dr SADEEQ ya ja jikinsa daga ƙofar a hankali, ya tsaya a gefe ba ƙarfi, ba magana.


NARNAH KANWAR SOJA 💯💕






PG


1️⃣0️⃣0️⃣ ↔️ 1️⃣1️⃣0️⃣



❤️DR SADEEQ 🤍


BY


NARNAH ƘANWAR SOJA
My 15novel comedy love and drama



https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM



THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*





🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲




BUSSINES GROUP


👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT


SPECIAL THANKS TO


NOVEL ELITE WEBSITE
HAUSA NOVEL GROUP WEBSITE
ABOKIYAR HORA WEBSITE
CREATIVE NOVELS WEBSITE
TK NOVELS WEBSITE
HAUSA EBOOK'S
TASKAR HAUSA NOVEL
E..T...C

TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night




A GURGUJE
BOOK 3 – DR SADEEQ


Dr Kamal ya shigo da sallama ganin kofar gidan a bude abun ya bashi Mammaki yana rigi da bag in Nazifa tana bayan sa da karamin cikin ta da take fama dashi ganin Dr sadeeq tsaya a bakin kofar Indo abun ya ɗaure masa kai bill haqqi ya tsaya " Lafiya Honey" cewar Nazifa itama ta tsaya ganin abinda Dr Kamal ke kallo Dr Sadeeq a kofar yana zaune " Dudde what are u doing here Indo ce ta rufe ma ƙofar " hararra kawai Dr yayi don ganin Nazifa baison girman sa ya faɗi ya fita ko hi bai musu ba nan suka bishi da kallo Nazifa ta taɓe baki" wallahi Bansan yaushe Dr Sadeeq zai sauke wanan girman kai ya gayawa Indo yana sonta ba " ta zauna tana nishi Kamal yayi dariya " No kinsan miskillancci yana damunsa sai yayi asarar ta ga wani zai gani bashi da wayyo tunda yanzu haka yana shirin turata University shine babban ganggancin da zaiye akan Indo".





WASHEGARI


Da sauri Dr SADEEQ ya shirya yasan Indo na kitchen a wanan time in wanan shine babban damar dazai ganta Atika ce ta biyo sa tana masa magiya" Please kifita daga idona sai da nagayamiki kar kishaga harkar yarinyar nan ,domin ne kika taɓa ,itta rayuwata ce kawai Inason ta dawo hankalin tane nayi hakan batare da sanin hakan zai jawo min Matsala da ita ba " ya fita ya barta zama taye akan kujerar sai ga hawaye a idon ta " Son masu wani ƙoshin wahala Amman Nima ba laifi nabane ƙaddara tace a hakan kasani inason ka har ga Allah ko wa wani nace zan aure ka ,kuma nayi nassara Amman na kasa samun nasarar shiga zuciyar ka ,har zaka iya ganin ido na kace wata ce rayuwar ka , lallai hausawa sunyi gaskiya da suke cewa So mai sonka , soyayya gaskiya ce , ƙiyayya ma gaskiya ce ba mai sa wani a zuciyar sa ta dole sai Allah ya tsara hakan .









A gefe guda kuma,
Dr SADEEQ ya tsaya a bakin kitchen, yana jin karar cokali da tukunya ƙamshin shayi ya buge shi amma zuciyarsa tafi tafasa ya ɗaga hannu zai yi sallama sai ya tsaya.



Indo tana tsaye a kitchen,
sanye cikin Pakistan wando da riga, launin milk da ɗan green
rigar ta laushi, wandon ya zauna mata dai-dai,
ta yi tsaf kamar ba ita ce jiya cikin hargitsi ba.


Gashinta a ɗaure, fuskar nan babu kwalliya mai yawa,amma kyau na halitta ya fito fili.


Ta na juya cokali cikin tukunya a hankali—
cikin ta bai gama wucewa da zafi ba,
amma zuciyarta tafi jin zafi , tana rera sabuwar waƙar Naziru Sarkin wa'ka da Fati Niger me sunan Balaraba


A dai-dai lokacin nan,
Dr SADEEQ ya tsaya a bakin ƙofar kitchen.


Ya yi sallama a hankali “Assalamu alaikum…”
kafin ya ƙara wani kalma Indo ta dago kai.


Idanuwansu suka haɗu lokaci ya tsaya ba murmushi na gaisuwa , sai kallon da ya ɗauki dukkan labarin rayuwarsu.


Idon Indo ya sauya launi, zuciyarta ta bugo,
amma ta ɗaure fuska, ta mayar da hankalinta kan tukunya,
kamar bata ganshi ba.


Dr SADEEQ ya ɗauki mataki guda ciki,
muryarsa ta ɗan karye “Indo…”


Ta katse shi cikin sanyi mai zafi:
“Dr, idan magana ce da Atika, ya wucce kabarni kawai”


Kalmomin sun soka shi fiye da wuƙa.


Ya haɗiye yawu, ya ce “Ni da ke nake so muyi magana.”Ta ajiye cokali a hankali.
ya juya ta kalle shi kai-tsaye, idonta babu tsoro “Babu abinda zamu tattauna.” “Abinda kake so ka riga ka zaɓa.”


Ya matsa kusa da kitchen table,
amma bai kuskura ya taɓa ta ba “Indo, ki saurare ni.” “Wallahi ba haka nake nufi ba.”


Ta yi dariya ƙanƙani dariya mara daɗi:
“Kullum haka kake faɗa.” “‘Ba haka nake nufi ba’,
amma sakamakon kullum ni nake ɗauka.”


Ta ɗauki plate ɗin , ta matsa gefe: “Don Allah ka bar kitchen. Ina aiki.”Ya tsaya cak “Ina sonki.”


Kalmomin sun faɗo cikin kitchen kamar dutse Indo ta ɗan tsaya—amma ba ta juya ba.


Ta ce cikin murya mai ƙarfi amma sanyi:
— “Idan so naka yana sa ni kuka, tsoro, da

42 / 48