DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   10 / 48

27K to 30K   out of 141.3K words

Indo kin buga ni!”
Yara suka hau tsalle suna faɗin:
“Faɗa! Faɗa! Team Indo sai ƙarfi!”






Cikin mintuna, wurin ya koma kamar filin dambe. Bokiti suna tashi sama, ruwa yana zubowa, yara suna dariya, wasu suna kwasar ruwa da kwalaba. Indo tana jefa bokiti kamar jaruma, tana zagin sa da ihu ana janta
“Sai kace kai ne mai mallakar panpanpam ɗin! Ai ni Indo ce, yarinyar Mama !”






Idris yana ta hura hanci yana zaginta har sai da aka shawo kan su da dattijo wanda ya fito daga gidan kusa.
“Ku tsaya! Ku tsaya, ku bama ruwa magana duk wanda bazai ɗibe ruwa cikin sallama ya jira layi ba yi ya bar nan !”






Daga nan duk suka tsaya suna dariya, amma fuskar Indo har yanzu cike da hayaki da ƙura, tana huci. Idris ya ƙaraso kusa da ita ya ce cikin murya mai rauni , " zamu haɗu a gunda ba mutane "
Indo ta ɗago kai, ta ce da murya mai sanyi amma cike da jan hankali:
“Faɗa da ni kamar faɗa da bokiti ne, idan ya zube sai a rasa ruwa " yara suka sake dariya, wasu suna rera: “Team Indo ta ci! Team Indo ta ci!”






A gefe, Idris yana kallonta tana tafiya da bokiti a kai, ƙafafunta suna cikar ƙasa da hankali, hular ɗamarar ta ɗan saki gefe. Sai yaji kamar wannan yarinyar da aka ce ta manya, akwai wani salo a cikinta da ba duk ‘yan mata ke dashi ba — karfi, jarumta, da wani ƙanƙanin mystery da yake jawo zuciya ya a lumshe ido yana murmushi, yana cewa a zuciyarsa:
“Indo kenan... kin fara faɗa da ni da safe, zan ga yadda rana zata kare.”






Thank you guy's love U ,wujigga wujigga....


''sukayi














https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM?mode=wwt


🩺🕯️ DR SADEEQ🕯️ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣ 8️⃣ ➡️ 1️⃣9️⃣


18 / 11/ 2025





بسم الله الرحمن الرحيم , اللهم صل على النبي محمد صلى الله عليه وسلم تسليما كثيرا.
Sometimes, destiny brings you love in the most unexpected way
When a doctor heals with love, even pain becomes laughter.” 🩺








Dr. Sadeeq na tafe cikin nutsuwa, hannunsa ɗaya na kan sitiyarin mota ɗaya kuma ya daura bisa gashin kansa. Wani irin natsuwa ke lullube da shi, amma zuciyarsa ba ta natsuwa ba — tun jiya Indo take yawo a cikin tunanin sa a yau kuma, rana ta waye da wata damuwa mai saurin ƙuna: “Allah yasa ba ita ba ce cikin wannan hayaniyar yara.”


Da ya ƙaraso bakin layi, sai yaga hayaniya kamar ana rabon suya. Yara, manya, matasa, bokiti, ruwa — komai cunkushe ya dan tsaya gefe ya ɗan kwantar da gilashin sa yana kallo, cikin zuciya yana cewa “Kai, wannan unguwa wallahi bata cika da natsuwa ba….”






Sai kuma zuciyarsa ta buga, idonsa ya hango wata yarinya tsaye tana ja da yara, gashin kanta ya watse, rigarta ta ɗan ɗauke ƙura, amma fuskar nan tasa mai daɗin gani tana kyalli kamar an shafa vaseline da tsarki a lokaci ɗaya.
Ya ɗan ɓata numfashi cikin ƙasaita “Subhanallah… Indo ce nan fa!”
Da sauri ya tsaya gefe ya fita daga mota, mutane suka fara matsawa gefe suna faɗin:
“Dr Balarabe ne! Dr Balarabe ya zo!”






Tunda unguwar ta saba da kiran nan, kowa ya san Indo kullum sai ta ambaci sunansa idan ta ga mai mota mai tsabta. Wasu yaran ma suna dariya suna cewa “A’a, ga saurayin Indo fa ya iso! Indo da Dr ɗinta!”






Indo kuwa tana tsaye tana share gumi, sai ta ɗaga kai ta hango shi. Ta ɗan firgita, ta ɗauke kai da sauri kamar wacce aka kama tana laifi. Amma Dr Sadeeq ya ƙaraso cikin kwanciyar hankali, rigarsa tana tana sheƙi, kamshinsa ya mamaye iska. Ya tsaya gabanta yana kallon ta da murmushi mai nauyi “Indo…”


Tana murza tafin hannunta da ƙasa ta ce da sauri“Ina kwana Doctor…”
Ya ɗan sosa haɓarsa yana murmushi, ya ce “Ina ruwa haka? Wannan fa hayaniyar ce? Ai kin jike tun kafin ki gama.”
Ta yi dariya cikin kunya, ta ce:
“Ai babu ruwa ne, shi yasa muka fito duk.”
ya ɗan ɗaga girarsa yana kallon bokitin da ke gefe:
“To, naji… amma ai akwai ruwa a siyarwa, me yasa baki siya ba?”tana dariya ta ce:
“Doctor, ai wane ne zai siya ruwa da kuɗi? 500 ne fa!”






Ya ɗan girgiza kai yana murmushi, ya buɗe motar sa, ya fito da briefcase nasa. A hankali ya buɗe, ya zaro kuɗi ya bata, sai kamshin turarensa ya bige hancinta. Indo ta ɗan ja baya tana murmushi cikin rashin nutsuwa.
“Ga shi nan, ki tafi gida. Zan sa a kawo miki ruwa gida, kin jike sosai.”
Tana karɓar kuɗin ta ɗan ce " na gode Doctor… amma ai…”
Kafin ta ƙara magana sai ya ce cikin murya mai laushi “Indo, tafi gida za'a kawo muku ruwan .”
Indo ta ƙara jin kunya, ta daura bokiti a kai tana tafiya da sauri, gashinta yana biyo bayan ta. Duk inda ta taka yara suna dariya, wasu suna yi mata clap clap suna cewa:
“Sai Indo! Doctor Balarabe ya kawo ruwa!”






Dr Sadeeq kuwa ya tsaya yana kallonta ta nesa, har sai da ta ɓace cikin layi. Sai ya lumshe ido, murmushi ya fito da kansa.
“Wannan yarinyar fa… tana da wani salo, da jarumta, da rashin kunya.”
Ya shiga motarsa, ya daidaita gilashinsa, ya ce cikin nutsuwa “To yau dai zan gama aikin asibiti, na huta” ya ja motar sa a hankali, hayaniyar yara tana biye da shi da waƙar su ta barkwanci“Sai Indo! Sai Indo! Dr ya kawo ruwa!”






Motar ta bace cikin layin ƙura, amma kamshin sa da murmushin sa suka rage a zuciyar Indo har ta isa gida — cikin raini, kunya, da wani irin farin ciki mai daɗin gaske wanda bata san me ya haddasa shi ba.


Indo na shigowa da gudu kamar wadda ta ci gasar farin ciki, muryarta na cike da annuri da dariyar ƙarfin rai.
“Mamaaa!” ta kira cikin jin daɗi, tana daga kuɗin da ta riƙe a hannunta.
“Dr. Balarabe ne Mama! Yabani kuɗi, Kinga dubu biyar ce kuma yace zai turo mana ruwa kyauta, wai sai dai mu zauna a gida kawai za’a kawo!”


Muryarta ta cika ɗakin, tana ta faman dariya da murna, sai kallon ƙofar ɗakin take tana jiran ganin murmushin mamarta mai sanyin hali — wacce kullum ke amsa da, “Allah ya saka masa da alkhairi Indo.”







Amma yau, babu amsa.
shiru sai ƙamshin turaren wuta da iska ke busawa a hankali
Indo ta tsaya cak. Murnar fuskarta ta fara raguwa kamar ƙurar da iska ke shafe wa.
“Mama... Mama Kinga kuɗin... zamu ci kaza yau ko?”
Ta ƙaraso da murmushi, amma zuciyarta ta fara ɗan harbawa.


Da ta matsa kusa, sai ta lura Mama bata motsi, ta kwanta shiru, kamar mai bacci amma fuskar ta saki, hannunta ya yi sanyi.
Indo ta durƙusa da sauri, ta taɓa hannunta.Sanyi Sanyi kamar ruwan da take ɗebo da safe zuciyarta ta ɗan doka, numfashinta ya tsaya na daƙiƙa biyu.
“Mama?” ta kira da rawar murya.
Babu amsa.


Ta sake girgiza ta.
“Mama, tashi mana... Kinga kuɗin da Dr. Balarabe yabani... zamu ci kaza da lemo yau, Mama tashi mu tafi kasuwa mana...”


Hannunta na rawa, zuciyarta na bugawa da sauri. Sai ta ga wani ƙwayar ja ya fito daga bakin Mama — jini.
Ta daskare kamar an tsayar da duniya.


Idanuwanta suka faɗaɗa, hawayenta suka fara zubo kamar ruwan sama.
“Mamaaa! Mamaaa!!” ta faɗa, tana girgiza ta da ƙarfin da ta samu, tana kuka mai sosa rai.
“Mama ki tashi... kin ce zaki bani labarin yadda Baba ya rasu... Mama kin ce zamu ci kaza... Mamaaa!”


Kukan Indo ya cika ɗakin, ya haɗu da karar zuciyar da ke bugawa da sauti, kamar ana dukan ganga a tsakar gida.
Sai ta rarrafa ta rungume Mama jikinta ya dinga rawa, tana faɗin:
“Mama kar ki tafi ki bar ni... Mama ki farka... kin ce idan na zama likita zaki shaida ni... Mamaaa! ”


Ruwan hawaye na haɗuwa da jinin bakin Mama, suna gudana su zamo ɗaya a ƙirjin Indo.
Ƙarar shigowar iska ta taga ta haɗu da ƙaran zuciya, ta zama shiru mai nauyi. a waje, ana jin muryar yara suna cewa:
“Sai Indo! Sai Indo!”
amma ba ta iya amsawa.


Domin wannan karo, Indo bata da ƙarfin dariya bata da ƙarfin magana.
Sai kuka — kuka mai ɗauke da tambayoyi, kuka mai zafi da tsoron rasa mafaka.
Kuka da kowa a unguwar zai ji, amma babu wanda zai fahimci irin ramin da ke zuciyarta.


Ta kwanta a gefen Mama, tana kiran sunanta, tana jin zuciyarta na sarƙewa da tsoron “me zai biyo baya?”


Duniya ta tsaya. Indo ta rasa hasken da ta saba gani a idon mahaifiyarta.




Ihun Indo ya tsaga sararin unguwa kamar kiran annuri ya rikide zuwa kuka.
“MAMAAAAA!!!” ta faɗa cikin murya mai cike da azaba, ihu mai ƙarfi da ya girgiza zuciyar wanda ya ji shi sai ƙarar ta ɓarke tamkar ana fashe ƙaho na bala’i — duniya ta tsaya, iska ta tsaya, mata chak


Kamar numfashin duniya ya tsaya na ɗan lokaci rana ta ja da gajiyawa, ta ɓoye a bayan gajimare cikin minti kaɗan, ƙarar fitowar mutane daga ƙofar gidajensu ta cika unguwar.


“Indo me yake faruwa?”
“Subhanallah! Wace irin ihu ce haka?”
“Ku gudu gidan ! Indo ce! Indo ce!”


Da suka shiga ɗakin, suka tarar Indo na ƙasa tana riƙe da mahaifiyarta, jikin Mama sanyi kamar ƙanƙara.
Hawayen Indo na gangarowa kamar ruwan sama, tana kiran suna cikin rawar murya:
“Mama... Mama... na gaya miki Dr Balarabe ya bani kuɗi... kace mata ta tashi don Allah, NICCE nake kiranta... Mama farka don Allah Mama! ”


Sai ta faɗa jikin makwabci, wacce ta ruga da ita cikin kuka wani dattijo ya tsaya bakin ƙofa, hannunsa na rawa, yana faɗin:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...”
Amma Indo kamar bata ji ba — ta kasa fahimtar kalmar da ta fi tsoro a duniya.


Unguwa ta taru. Muryoyi suka rikice, kowa ya shiga tashin hankali.
“Ku kira motar asibiti!"
“Ku cire yarinyar nan, kar ta karye da kuka!”


Sai da aka kwace Indo daga jikin mahaifiyarta da ƙyar. Hannayenta suna rawa, ta riƙe rigar Mama tana kuka kamar ranta zai fita.
“Babu inda zani!” ta faɗa da ƙarfi.
“Sai na bi Mama! Ku barni kawai... ku barni!”


Jikinta yana rawa, idanunta sun cika da hawaye, numfashinta yana fitowa da sauri, tana shure-shure a ƙasa yara suka tsaya suna kuka, mata suka rufe baki suna faɗin “Ya Allah ka dubi yarinyar nan da rahma.”


Ƙarar siren asibiti ta cika titi, motar ambulance ta tsaya da gaggawa.
A cikin hayaniya, wani likita ya fito, suka ɗauki Mama a gadon asibiti, Indo kuwa ta bi a bayansu kamar wata da ta rasa hasken rana.


A asibiti kuwa, ƙarar Indo ta sake girgiza kofofi.
“Mamaaa! Mamaaa!! Kar ki barni Mama!”
Ta riƙe hannunta, tana kuka har idanuwanta suka kumbura.
Likita ya shiga ciki da gaggawa, nurses suka rufe ƙofa.


Sai dai Indo ta ƙi zama a waje.
Ta jingina da ƙofar ɗakin da Mama ke ciki, tana numfasawa da wahala, tana jin yadda ƙirjinta ke harbawa kamar ana dukan ganga.


Wani nurse ya fito yana cewa,
“Ku riƙe ta don Allah, kar ta sake shiga!”


Amma da ƙyar suka iya Indo ta naƙude tana ihu:
“Ku barni in shiga! Ni nake kiranta! Ni ɗiyarta ce!“Mamaaa... wallahi ni ba zan iya ba! Ki farka Mama... ki farka ki ga ni!”


Hawayenta suka zubo suka jiƙe ƙasa.
Ƙamshin disinfectant na asibiti ya haɗu da ƙamshin ruwan turaren da Mama ta shafa da safe — yana motsa tunani, yana ƙara masa zafi.


Ƙarƙashin hasken farin fitila, Indo ta durƙusa a ƙofar ɗakin da mahaifiyarta ke kwance, tana ta faman kuka da kalmomin da babu wanda ya iya tsayar da su.
Ko nurses, ko likitoci, duk sun tsaya suna kallonta da tausayi — yarinya ƙarama amma zuciyarta ta ɗauki nauyin tashin duniya.


A wancan dare, asibitin ya cika da shiru mai nauyi, sai ƙarar Indo kawai ke sakewa daga nesa “Mama ki farka... Mama... na dawo gida da dariya, amma yanzu babu ke...”




Lokacin da suka shigo dakin gaggawa, Dr Sadeeq ya tsaya cak a bakin gadon. Numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci kamar zuciyarsa ta manta yadda ake bugawa. Ya ga Mama kwance, jikin ta sanyi, hannunta babu kuzari. Indo kuma tana riketa kamar wacce take ƙoƙarin mayar da rai da hannunta.


Muryar Indo ta sake karya zuciya:
“Na dawo, Mama… na dawo ina murna… ina cewa ‘Mama ga kuɗi, zamu ci kaza yau, Dr Balarabe yabani’ — amma Mama bata amsa ba… kace ta amsa min don Allah, Dr…”
Dr Sadeeq ya ɗauki numfashi da wahala, ya matse hannunsa a kansa. “Please… please don’t die in my last time,”
ya furta a hankali, muryarsa na rawa.
“This is my time to move from here… Allah, please…”






Idanunsa suka cika da hawaye. Bai san lokacin da hawayen suka gangaro masa ba. Kamar yadda Indo ke kuka da ƙarfi, shi ma zuciyarsa ta karye ƙal, sai yana jin kamar duniya ta tsaya.


Atika, wacce ke gefe, ta rufe bakinta da tafin hannu. Bata taɓa ganin irin wannan zafi ba, zafin da ya cika ɗaki da ƙamshin mutuwa da kuma kukan ƙauna. Ta matse idanunta, hawaye suka zubo.


Indo ta sake ɗaga hannun Mama tana girgiza shi “Mama… ki farka mana… ni ce Indo… kina ji na ko? Ki farka, mu tafi gida Mama! Mu ci kaza da lemo kamar jiya da nake dariya, Mama! ”






Sai da zuciyar kowa ta narke.
Kowa da ke asibitin ya tsaya yana share idanu.
Har likitocin ma da suka saba ganin mutuwa a kullum, yau zuciyarsu ta shaƙu da tausayin yarinyar nan da ta tsaya tana kuka kan uwa kamar ranta ne ke fita a hankali.


Dr Sadeeq ya matsa kusa, ya durƙusa, ya ɗora hannunsa a kan kafadar Indo, muryarsa tana rawa sosai “Indo… shh… ki yi haƙuri… Allah yana tare da Mama… ba ta tafi ba… muna ƙoƙari.”Amma Indo ta girgiza kai cikin kuka mai ban tausayi:
“A’a… ta tafi! Na san ta tafi! Ni ce ta janyo hakan… ni ce na bar ta na tafi neman ruwa!”
Dr Sadeeq ya kasa magana, ya ɗaga ido sama yana kiran Allah a zuciyarsa, “Ya Allah, ka bar wannan uwa, ka bar ta saboda yarinyar nan. Ka ji ƙaunarta, ka sauƙaƙa wannan ciwo.”






Sai yayi shiru, numfashinsa na sanyi, hawaye na zubo masa cikin nutsuwa.
Kallon Indo ya zama kamar kallon wani ɗan yaro da yake rugawa cikin duhu yana kiran sunan mahaifiyarsa da babu amsa.


A wancan lokacin, babu wanda bai yi kuka ba ko ma’aikatan asibitin, ko marasa lafiya, ko masu jiran aiki. Duk zuciyoyi sun narke da tausayin Indo.
“Mama ki farka… don Allah Mama ki amsa ni…”
Akwai wata murya a cikin kukan Indo wacce ta fi kuka komai zafi: murya mai ƙara daɗa bugun zuciya, mai sanya kowa ya juya gefe ya share hawayensa cikin asiri.






Asibitin ya ɗauki nutsuwa mai nauyi, ana jin sautin kuka da addu’a a tsakanin mutane.
Har Dr Sadeeq, wanda ake ganinsa a matsayin mutum mai ƙarfi da hankali, ya durƙusa yana share idanu, yana faɗin a hankali:
“Ya Allah… ni ma zuciyata ta yi kuka.” 💔








A lokacin da kowa ya fita daga ɗakin, sai aka bar Dr Sadeeq da Mama kaɗai, nurses biyu na tsaye a gefe suna jiran umarni.
Jikin Mama ya yi sanyi, numfashinta yana fita da wahala. Sautin na’urorin dakin ICU suna ƙara karyar da zuciya, pip… pip… pip… amma sautin yana raguwa a hankali.


Dr Sadeeq ya durƙusa, ya sa hannunsa yana jijjigarta a hankali,
“Mama, ki daure, please… kina jin ni? Don Allah ki daure saboda Indo…”
Sai taja wani nishi mai rauni, idonta ya ɗan buɗe kadan, jinin da ke bakin ta ya sake fitowa.
Nurse ɗaya ta matsa da oxygen mask, ta ƙoƙarta ta saka mata, amma Mama ta hana da rauni, ta tura hannunta a gefe tana kallon Dr Sadeeq da wani kallo mai zurfi – kallo na amana da nasiha a lokaci guda.


Muryarta ta fito da kyar, kamar iska ce ke ɗaukarta:
“Ba zan… rayu ba… Dr Sadeeq… don Allah… ka rike min Indo… amana nake baka…”
Sai hawaye suka zubo daga idon Dr Sadeeq, ya matse hannunta cikin nasa yana girgiza kai “Kiyi shiru, Mama, za ki rayu, Allah zai taimake ki…”Amma ta girgiza kai cikin ƙarfi na ƙarshe,
“Tun ranar da na ga farin cikin ta… nasan… kai ne madafin ta… Indo… Indo zata samu gaskiya da kai…”






Sai ta numfasa, idonta ya fara sauka ƙasa.
Atika ta yi saurin shigowa da kiran Indo a waje amma kafin ta isa ƙofa, sai suka ji Mama ta soma maimaita kalmar shahada a hankali.
“La ilaha illallah… Muhammadu Rasulullah…”






Dr Sadeeq ya zube a gefenta yana maimaitawa tare da ita, hawaye na zubo masa kamar ruwan sama sai suka ji shiru… monitor ɗin ya yi beep ɗaya mai ƙarfi sannan ya tsaya.


Wani natsuwa mai ban tsoro ta cika ɗakin.
Nurse ɗin ta saki huci, ta ɗauki labulen ƙirjinta ta rufe Mama da tawul mai launin fari.


Dr Sadeeq ya tsaya a wuri ɗaya, kamar mutum da aka cirewa rai. Idonsa ya zaro hawaye, yana maimaita maganarta cikin raunana murya “Ban mutu ba… don in baka amana ce… Sai jikinta ya nitsu.


A waje kuwa, Indo na zaune tana jiran fitowar su. Da suka fito da lulluɓe da farin zanen, sai Indo ta kalle su, ta ji jini a jikinta ya tsaya.
“Mama… Mama…”ta rugo da gudu, ta zube ƙasa tana ihu mai sosa zuciya.
Sai jiki ya yi mata sanyi, idanunta suka yi duhu ta suma a wurin.


Nurses suka ruga da ruwa, suka fesa mata, suka saka mataa fuska.
Da ta farka, sai kuka mai ban tausayi ya tashi daga bakinta, muryarta na rawa sosai tana cewa: “Ku tashi Mama… ku tashi mu ci kaza… Mama… ki amsa ni…”






Dakin gaba ɗaya ya cika da hawaye.
Dr Sadeeq ya juya gefe yana share nasa cikin asiri, zuciyarsa ta narke, ya ce a zuciyarsa
l “Amanar ki ce Mama… Indo zata zama amana a idona… har karshen rayuwata.”










What a painful drama is going here, is double page fan's
Thank you with your love


😭 Kullu nafsin za'iqatul maut










10 / 48