DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   8 / 48

21K to 24K   out of 141.3K words

laushi ya ce, “Welcome back, Indo. The world missed you.”




Washegarin nan bayan azahar, hasken rana ya ragu, sai iska mai sanyi ke busowa ta taga. Dakin asibitin ya cika da ƙamshin magani da farin sheet. Indo na kwance, ta dan fara murmushi bayan kwana ɗaya cikin rashin natsuwa. A gefe Mama na zaune, ta yi gajiya da kuka har idonta ya kumbura.


Sai aka turo ƙofa a hankali — Atika ce, ta shigo cikin nutsuwa da file a hannunta. Ta yi sallama cikin murya mai sanyi, sannan ta matso kusa da gadon.
“Madam,” ta ce da Mama, “please ki dan fita na ba Doctor result ɗin test ɗin.”
Mama ta yi gaisuwa ta fita a hankali, ta bar su biyu a dakin.


Da Atika ta juya, sai ta ga Dr. Sadeeq ya shigo da stethoscope a wuyansa, fuskarsa cike da damuwa da gajiya.“Atika,” ya ce yana kallon ta, “kin gama analyzing result ɗin?”
Ta gyara tsayuwarta, ta miƙa masa file ɗin.
“Yes, Doctor. We ran full tests: malaria parasite — ++, severe infection — positive. Her white blood cell count is high. Likely from untreated wound or stress.”


Ya karɓi file, ya buɗe da natsuwa, idonsa na sauka kan takardun gwaji. Ya ɗan girgiza kai yana faɗin,
“Hmm... malaria da infection. Wannan yarinyar ta sha ƙazanta sosai. Ba na jin tana samun kulawa yadda ya kamata.”


Atika ta ɗan yi murmushi, ta ce, “Ka manta fa Doctor, wannan ce yarinyar da ka ce ‘no one dies in my hands.’ Ka cika alkawari.”


Ya ɗaga kai yana dubanta da nutsuwa.
“Atika, ba ni ke cika alkawari ba. Allah ne kawai ke bada lafiya. Mu dai mu aikata abin da zamu iya.”Ya ɗauki prescription pad, ya fara rubutu a hankali.
“Give her Ceftriaxone IV, one gram morning and night. Start with Quinine infusion, full dosage. Then give paracetamol every six hours. Ensure she gets enough rest and light food when she wakes properly.”


Atika ta karɓi pad ɗin, tana kallonsa da idanu masu cike da tambaya.
“Doctor, ina ganin kana damu da wannan yarinyar sosai. Ko dai tana da wani dalili na musamman?”


Ya ɗan tsaya, yana kallon tagar da iska ke shigowa, ya miƙe, ya sa hannu cikin aljihu, ya juya zuwa ƙofa.
“Bari in fita na duba wasu patients. Idan drip ɗinta ya kare, ku maye gurbin. Ki tabbata ta samu rest sosai. Ba na son a yi mata magana da yawa yanzu.”


“Alright, Doctor,” Atika ta ce cikin ladabi, tana kallonsa da ido har ya ɓace a ƙofar dakin.






A gefe Mama ta dawo da tray ɗin ruwa da ɗan abinci. Ta zauna a bakin gado tana kallon Indo
tana jin daɗin yadda jikinta ke dan motsi a hankali.
Sai ta yi dariya cikin hawaye, “Yarinyar nan ta bani tsoro, wallahi. Da na san haka, da ban bari ta je kasuwa da waccar rigima ba.”


A hankali Indo ta motsa, ta buɗe idonta kamar mai mafarki.“Mama…” ta furta da rauni.
Mama ta ruga kusa da ita da murna, “Alhamdulillah! Indo! Na gode ma Allah, kin farka fa! Na kira Doctor duka suna cewa za ki farfado.”


Indo ta ɗan yi murmushi da rauni. “Mama ina Dr Balarabe”Indo ta juya kanta a hankali, ta kalli tagar inda hasken rana ke shigowa.
“Doctor Balarabe?” ta tambaya da ƙaramin murya.
Mama ta ce, “Eh, shi kenan. Allah ya saka masa da alheri. Ya ce sai an tabbatar kin farfado.”cikin ƙasa Indo ta murmusa. “Shi ne ya ce... duniya ta rasa ni?”
Mama ta ce, “Eh, ai shi ma ya shiga hankalin sa da wanan warin naki ,kullum ina gayyama ki kina tsafta da Tsarki mai kyau to yanzu ciwon ƙazanta ke damun ke yace .”


A wannan lokacin Dr. Sadeeq ya dawo. Ya tsaya a ƙofar, yana kallon yadda Indo ke murmushi da Mama. Wani sanyi ya sauka masa a zuciya Tabbas uwa mai daɗi “Yauwa Indo,” ya ce da murya mai nutsuwa, “kin tashi?ta ɗago kai da girmamawa, “Na tashi Doctor, Allah ya saka maka da alheri.”


Ya kalli Mama, “Zata fi kyau idan ta huta sosai. Kada ta damu da komai yanzu. Infection ɗinta da malaria zasu warke, insha Allah.”
ya ɗan tsaya, yana kallon Indo, sannan ya ce da dariya mai laushi,
“Amma fa, yarinya, da rigima irin naki, sai a kawo miki office ɗin ‘Peace Committee.’”


Kowa ya yi dariya — Mama har ta share hawaye saboda dariyar ta. Indo ta sunkuyar da kai tana murmushi, tana cewa,
“Na tuba Doctor. Wallahi na daina fada.”
sai Dr. ya dubi Atika, ya ce, “Good. Akwai nasara idan mara lafiya ta iya dariya.”


Atika ta ce, “That’s true, Doctor. You’ve got the magic touch.” kawai ya ɗan ɗaga gira yana murmushi,
“Magic? A’a. Imani.”


Ya juya ya fita daga dakin, yana jin zuciyarsa na cike da wani abu da bai iya fassara ba — tausayi, kulawa, ko wata alaƙa mai nisan gaske?


A gefe Indo ta lumshe ido tana jin numfashinsa har yanzu yana ɗauke cikin zuciyarta — kamar muryar da ta ɗaga ta daga duhu zuwa haske.










https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM?mode=wwt


🩺🕯️ DR SADEEQ🕯️ 🩺
by


NARNAH KANWAR SOJA ✍️
MY 15th Novel Comedy love drama.
08101235739





CHAPTER 1️⃣ 4️⃣ ➡️ 1️⃣5️⃣




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨


🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
Typing...📲


13 / 11/ 2025
Night Update




This one is for you Namecy Khadijah Noorah Safiyan ................












Dr. Balarabe yana cikin motarsa yana murmushi kamar wanda ya tuna wani abu mai daɗi. Hasken rana yana shigowa ta gilashin motar yana bugun fuskarsa, sai murmushin ya ƙara faɗa, idonsa na ƙyalli kamar wanda zuciyarsa ke faɗin “kai wannan yarinya, drama ɗinta ya fita.”


Lokacin tafiyar sa kenan — 5:30 na yamma amma maimakon ya tafi gida kai tsaye, sai zuciyarsa ta ɗaure shi, “ka tsaya ka ga yadda suke drama ɗin nan.”
Ya juya motarsa zuwa sashen da ake kwantar da masu jinya. Cikin ɗan nisa sai ya hangi su Indo da wasu Indo ta riƙe faranti tana cewa da w “Ni fa ban yarda ba! wannan abinci nama nakiso ne, ni dai in ba nama kaza ba bana ci ,, idan an kawo mutum asibiti ai naman kaza ake kawo wa..”


Sauran matan suka yi dariya.
Dr. Balarabe kuwa sai ya tsaya a gefe yana kallon su cikin murmushi. A ransa yace,
“Wannan yarinyar wallahi kamar barkwanci ya zauna a jinin ta.”
Da ya ga ta sake faɗin “ni dai in ba nama kaza ba, bana ci” sai ya ɗaga murya da nutsuwa:
“Alright Indo,” — muryarsa ta sauka a hankali cikin kwarjini — “zan kawo miki nama kaza. Amma... da sharadi guda ɗaya.”
Indo ta ɗago kai da mamaki, ido biyu sun haɗu. “Sharadi kuma, Doctor?”
“Eh. Sharadi ɗaya kacal,” inji shi yana saki ɗan murmushi.
“Ki shiga nan, Nurse za ta miki wanka, ta miki brush. Amma fa idan kin yarda ne kawai.”
da sauri Indo ta amsa cikin sautin dariya “Na yarda Doctor! ka dai tabbata kazar wacce ta girma ce ba ƙarama ba!”
Dariya ta kama shi sosai, sai ya ɗan jinjina kai , ya juya ya kira Nurse Larai , wata nurse mai sanyi da natsuwa, mai murya kamar ruwa mai laushi. Ya gaya mata cikin sirri:
“Ki taimaka ki wanke wannan patient ɗin, ki yi mata brush sosai. Ta yi infection mai tsanani, alamar rashin tsafta ta dade tana jikin ta. Ki sa ta zauna sit bath mai magani.”
Nurse Larai ta gyara rigarta, ta amsa da ladabi,“To Doctor, zan kula da ita sosai.”
ta shiga ɗakin, ta tarar Indo ta na kallo da murmushi. “Nurse, wai kai ce za ki min wanka?”“Eh mana, Doctor ya bada umarni ki zo mu fara kafin ruwa ya huce.”Indo ta yi dariya tana cewa:
“To ai ni kam ban saba da irin wankan nan na asibiti ba, ku kar ku ce wai nayi rawar jiki idan ruwa ya zubemin kai.”






Nurse Larai ta yi murmushi kawai ta zuba ruwa a bowl, ta fara kwankwasa kanta da ƙyalli. Sabon sabulun hospital ya cika ɗakin da kamshi. Indo tana motsa baki tana cewa:
“Lallai kam, ruwan birni ba kamar na kauye ba ne, wannan kamar ruwan Faro yake.”
Nurse ta yi dariya cikin sanyin murya,
“Yanzu kin fara shan jin daɗin tsafta kenan, ai haka lafiya ke farawa.”
A gefe kuwa Dr. Balarabe yana tsaye a kofar yana magana da Mama amma hankali ba ya wurin aiki kamar yana jin murya Indo tana cewa “yi min brush da kyau don bana son bakin ya ƙone min”.
Sai ya girgiza kai da murmushi:
“Kai wannan yarinya, Allah ya taimake ni da jarabar dariya.”
Mintuna ashirin kacal ya koma. Ya ba Nurse kuɗi masu yawa,
“Ki siya mata kayan wanka, sabulun mata, brush, da homour ”Sai ya fice ya tafi gida a hanya yana tuka motarsa, raina cike da nishaɗi wani ɗan raɗa a zuciyarsa na cewa “me yasa Indo ta zama daban? ba kyawunta kawai ba, akwai wani abu mai dariya da tausayi a tattare da ita.”






Ya isa gida ya cire rigarsa ya shiga wanka a cikin ruwa yana murmushi da tunanin yadda Indo ta ce,“Ka tabbata kazar babba ce, Doctor!” yayi murmushi ya ce a hankali:
“Indo... drama village girl indeed.”






Ya gama wanka, ya fesa turare mai sanyi, ya zauna bakin gado yana lumshe ido.
Wani abu cikin ransa yana faɗa masa wannan bai zama wasa kawai ba yana ƙaunar ganin Indo lafiya.









####$##
Bayan sallar Isha’i, Dr. Sadeeq ya zauna a kan kujera yana duba jadawalin ayyukansa na gobe. Cikin nutsuwa yake, amma zuciyarsa tana wata irin rawar da ba zai iya fassara ba. Duk yadda ya so ya manta da Indo — wannan yarinyar da ta shigo masa rai kamar iska mai kamshi — sai zuciyarsa ta ƙi natsuwa.
“Kai, ai nace zan kawo mata kaza tunda nayi alƙawarin”ya furta a hankali yana lumshe ido kamar mai jin daɗin tuna wani abu mai daɗi.


Ya miƙi daga kujerar cikin salo , sannan ya ɗauko white shirt mai taushi, ya haɗa da blue jeans da ya zauna masa kamar an narka shi a jikinsa.


Agogon hannunsa kuwa — ƙirar Apple mai sheƙi — ya ɗaura a hankali. Bai ɗauki gilashi ba, sai ya gyara gemonsa mai santsi, ya fesa turaren Versace Blue wanda kamshinsa ke haɗa nutsuwa da tsantsar ƙamshi.


Cikin mintuna kaɗan, ya kama key ɗin motarsa. Yana fita daga ƙofar gida, iska mai daɗi ta busa ƙamshin turarensa, tana jefa masa wani nishadi mara misaltuwa.




A ɓangaren Atika kuwa, tana cikin daki tana tattare takardu ne lokacin da ta ji ƙarar buɗe mota. Sai ta leƙa ta hango Dr. Sadeeq na fita da natsuwa, ya kama hanyar ƙofar gida.
“Hmm… yau kuma ina wannan Doctor zai nufa da daren nan?”
ta furta a hankali tana taɓe baki, wata irin kishi ta ratsa zuciyarta kamar wuta ta girgiza kai
“Oho! amma dai ai ba meeting da dare ake ba… ta a koma ta kwanta, amma zuciyarta ta ƙi bari ta huta.




Shi kuma a waje, Dr. Sadeeq ya wuce kasuwar ƙarfe goma na dare, inda ake sayar da kayan ciye-ciye yana isowa, wani dattijo mai jujjuyar kaza ya yi masa gaisuwa da girmamawa.
“, Oga kaza?”
“Eh Baba, soya min guda biyu — mai kyau sosai ka saka masa kayan kamshi,”
ya ce da sanyin murya mai cike da natsuwa.
Baba mai kaza ya yi sauri yana dariya.






Da aka gama, ya biya kuɗin — bai ma tambaya ba — ya kuma ɗauko carton ɗin Fanta guda ɗaya da ruwa bottle ya saka komai cikin motarsa, ya ja fitila mai launin shuɗi, ya nufi asibitin cikin natsuwa a hanya yana tuƙi, zuciyarsa na rawa da mamaki da jin daɗi.
“Me yasa nake jin kamar yarinyar nan ta shiga raina haka?” i think ina tausayin patients na sosai " ya tambayi kansa, amma babu amsa. Sai kawai ya murmusa, yana tuna dimples ɗinta da irin yadda take faɗin “Doctor Balarabe” cikin nau’in hausarta mai nauyi.








A asibiti kuwa, masu night duty suna zaune suna hirar su lokacin da suka hango hasken motarsa ya tsaya a bakin gate. Suka kalli juna da mamaki. “Laa, shi Dr. Sadeeq kenan? Me yake yi da wannan lokaci?”
“Wallahi ban sani ba. Kila emergency ce,”
ɗaya ya ce, yana tura baki da mamaki.
ya fito cikin kamala, ya rufe motar cikin ladabi, sannan ya nufi sashin marasa lafiya kai tsaye. kowane mataki da yake ɗauka sai ƙamshi ya biyo bayansa, har ma wasu nurses suka daina rubuce-rubucensu suna kallonsa.
Sai da ya isa ƙofar ɗakin Indo.






Tana zaune ta jingina da gado, tana wasa da wani hijabi, idanunta suna kallon ƙofa kamar mai jiran wani. Da zarar ta hangoshi — chak! kamar wutar lantarki ta shigo jikinta.


Sai murmushi ya bayyana a fuskarta, dimples ɗinta suka motsa, idanunta suka yi kyalli kamar ruwan sanyi.
Ta buɗe baki cikin raha ta ce:
“Doctor Balarabe, yau dai Allah ya kawo maka alkhairi! Nasan baka manta da kazar nan ba ko?.”
Tsayawa yayi, kamar an tsayar da lokaci.
Idanunsa suka tsaya a kanta yau Indo daban ce — ba irin wacce ya gani a Modirre ba .


Fuskarta ta yi haske, idanunta sun cika da rayuwa, haƙuranta kuwa sun yi tsarki da kyau har sun yi fari kamar na advertising paste.
Sai murmushi ya saki, yana furta cikin zuciya:
“Fara ce… fat ashe dirty ne.”
Ya kalli kazar a hannunsa, sannan ya ce da murya mai sanyi “Toh, ga kazar nan Indo.”






Daman Mama ta fita sallah, tana ganin shigar sa ta tsaya a bakin ƙofa, sai ta murmusa tace,
“Eh toh, ai basai na shiga ba,” sannan ta janye jikinta gefe cikin nutsuwa.


Shi kuma ya shiga da nutsuwa kamar wanda ya saba da dakin.
Sai ƙamshin turarensa ya mamaye dakin gaba ɗaya, wanda ya haɗu da ƙamshin maganin asibiti, suka haɗu suka zama wani irin sanyi a zuciya.


Ya jawo kujerar da ke kusa da gadon ya zauna, yana kallonta cikin natsuwa.
Hannunsa ya kai ya tsaya a jikin drip ɗin da ke cikin hannunta, yana tabbatar da cewa yana tafiya yadda ya kamata. Sai ya ɗan saki ajiyar zuciya.


Yana kallonta cikin sabon kayan da ya umarci nurse ta kawo mata, fararen kaya masu tsabta da suka yi daidai da fata irin nata.
Sai murmushi ya subuce masa, murmushi irin na wanda yake farin ciki da abin da yake gani.


“Good girl,” ya furta cikin murya mai taushi, yana kallon ta “ke daina zama da dirty, kin ji?”


Indo ta ɗan lumshe ido, ta saki wani siririn dariya da ya bayyana dimple ɗinta ɗaya da yake ɓoye a gefen kuncinta, ta ɗan jinjina kai, amma idonta na kan fuskar sa — yana kyalli cikin farin shirt ɗin sa, rigar da ta bayyana kyawun fata da ƙirar jikinsa.




Lokaci ɗaya, dakin ya zama kamar shiru ya cika shi — babu sautin komai sai numfashinsu biyu da sautin drip ɗin da ke sauka a hankali ya jawo ƙafafuwansa gaba kaɗan, yana ƙara matsowa kusa da ita.
Idonsa ya sauka kan bakinta — wanda yake ɗan bushewa saboda shan magani da rashin ruwa.


Sai ya ɗan matsa da hannu, yana ɗaukar hankalin ta gaba ɗaya ta buɗe baki a hankali, ba tare da ta san me zai yi ba. amma kafin ta yi magana, sai kawai ya ɗan saki murmushi, yana cewa,
“Zan koya miki yadda ake kula da kai, Indo... don ni bana son ganin ke mutum cikin ƙazanta .” zuciyarta ta buga wani irin sanyi ya ratsa ta daga kai har ƙafa ta ɗan yi ƙoƙarin amsa, amma bakin ta ya tsinke da yawu saboda hanunta na ɗaure da drip.
Sai shi kansa ya kama hankici a gefe, ya share mata baki da nutsuwa, kamar yaro da yake kula da wanda yake so sosai.


Hankalin Indo ya tashi gaba ɗaya, idanunta suka cicciko da ruwa, ba saboda ciwo ba, sai saboda jin daɗin yadda yake da tausayi da kulawa ,wanda zatace ba'a taɓa kula da ita Irrin haka ba



Dr. Balarabe ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta, kamar yana son ya fahimci sirrin murmushinta. Akwai wani abu a cikin idanunta — cike da rashin wayewa, gaba ɗaya bazata haura shekaru goma sha ukku ba don ko ƙirjin ta baigama bayyana ba balle shape nata kallon ta yayi sosai , yana ganin ta kamar sa'ar Autar su .


Ya ɗauki farantin kazar, yana tsinke naman a hankali, ya samata a baki
“Ga naki… amma ki ci a hankali,” ya faɗa da murya mai taushi, wacce ta sa Indo ta yi murmushi kamar yarinya da aka yiwa wasa.


Ta ɗan kai hannunta tana son karɓa, amma sai drip ɗin ya hana ta motsi sosai. Ta ɗaga ido ta kalle shi da yanayin roƙo.


Dr. Balarabe ya yi murmushi. “To ai yanzu kin koma baby patient fa,” ya ce yana ƙara kusantowa, ya ajiye farantin a gabanta. “Ki bari, zan taimaka miki.”


Sai ya ɗauki cokali, ya motsa nama cikin sauce ɗin, yana miƙa mata a bakin ta Indo ta buɗe baki a hankali, tana dariya tana cewa,
“Dr., ai ni ba baby ba ce.”


“Ina ganin haka,” ya amsa da murmushi mai cike da natsuwa. Sai suka yi shiru na ɗan lokaci, su biyun suna kallon juna. Cikin zuciyar Balarabe akwai wani abu mai sanyi, irin na tausayi da kulawa da ke juyawa zuwa wani abu da bai bayyana ba.


A cikin wannan shiru, iska ta kaɗa labulen taga, turaren warkarwa ya gauraya da ƙamshin kazar. Kamar lokacin ya tsaya.











BYE 😎 😎 😎😎😎😎


MORE COMMENT MORE TYPING


8 / 48