DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   40 / 48

117K to 120K   out of 141.3K words

ki bar maganar Mairon. Ai tunda ta koma can, labarinta ya daina zama trending nan.”Indo ta yi dariya tana girgiza kai:
“Hmmm… Mairon nan dai. Allah ya kyauta mata nayi matuƙar kewarta a sanadin ta aka rufe ne a gidan ƴan sanda maye kewar ƙawata”
Suka yi shiru na daƙiƙa uku, sai Haule ta runtse ido ta zabura kamar wacce ta tuna wani sirri “To Indo… akwai magana fa.”Dijee ta ce da sauri:
“Eh! Mu dai mun ga kamar akwai soyayya tsakanin ki da Dr. Balarabe…”






Da wacce dariya Indo ta fashe?
Wacce ta danne pillow ta rufe baki domin kar Dr Kamal dake parlour ya ji hayaniyar ɗakin?Indo ta narke da dariya har hawaye:
“Ayyyyyy! Ku dai nan! Ashe har yanzu ba ku manta sunan mutumin nan ba?”






Ta sake yi musu tsokaci tana dariya sosai “Dr. Balarabe fa? Hhhh! Ni da shi? Soyayya?”Dijee ta ce a tsokana “Ai yanda yake miki kulawa sai ace akwai wani abu.” Indo ta yi murmushi na ladabi, cike da kunya da kamun kai:
“Ke dai ki sani… babu komai face mutumci. Yana min mutunci, ina girmama shi. Shikenan.”
Ta ɗan yi nisa kamar wacce ta shiga tunani “A birni dai… kulawa ba soyayya ba ce. Yafi kama da educator da student, ko dai professional respect.”






Haule ta yi dariya ta tafa:
“Ai komai ne fa Indo, ko da mutumci ne… sai ya fara daga mutumci ya koma soyayya.”
Indo ta harare ta cikin wasa:
“Ke Haule, ke dai kin fara sanin soyayya tun kafin mu. Ni fa yanzu gaskiya… hankali na bai ma san inda soyayya take ba "Dijee ta matso kusa:“To amma… idan ana maganar wanda ke da matsayi a zuciyarki…?” Indo ta yi shiru, ta kurɓi iska kadan, ta ɗan murmusa “…hmm… wannan sai lokaci ne zai nuna.”
Dariyarsu ta sake ƙara ɗaukar ɗakin, suna shagalin hirar soyayya da tsofaffin abubuwan Boarding — kamar basu rabu ba na tsawon lokaci ba





Indo ta ɗora hannu a kirjinta tana murmushi irin na mai cike da natsuwa da zurfin tunani. Su Dijee da Haule kuwa sun zuba mata ido kamar suna kallon wata sabuwar Indo da suka sabo da ita a birni Indo ta ce a hankali:
“Ni fa yanzu banda wani buri face in zama cikakkiyar Nurse. Inason wani sabon makaranta dake Kano — Capital City University Kano, Nursing Science. Nasan Dr zai barni in sha Allah. Amma tukunna… ban san me zai ce ba.”






Dijee ta yi saurin bude baki:
“Ke? Indo? C C.U.K!? Wato makarantar masu kuɗi?!” Haule ta rike kafaɗar Indo tana dariya:
“Lallai birni ya koya miki abu. Amma wallahi muna jin daɗi, kina da burin kirki.”
Sai ta dan kusanto da murmushi “To amma… aure fa? Baki taɓa tunani ba?”
Indo tayi dariya mai taushi ta ɗaga hannu alamar a dakata “Aure?”
Ta girgiza kai a hankali, idonta ya sauka ƙasa cikin murmushin kunya da gaskiya “Ba yanzu ba. Na gama tunani zan ɗan cigaba da makaranta, na cika mafarkin Mama. Tun ina ƙarama take cewa ta sha Allah ina so ki zama Doctor ki taimaka wa mutane. To yanzu da na girma… sai naga wannan shi ne burina.”
Ta ja numfashi, idonta ya yi kauri kamar tana tuna wani abu mai nauyi “Ina so ace Mama tana nan tana gani… amma komai yana tafiya kamar tana tare da ni.”






Haule ta share kwalla “Indo… Allah ya albarkaci burinki kin san dai… duk wanda ya fara birni kamar ke ba zai tsaya a baya ba.”






Dijee ta yi dariya don ta karya yanayin tausayi:
“Ai kam idan kika zama Nurse, ni zan fara zuwa ki duba ni ko da ciwon kai ne.”
Suka yi dariya gaba ɗaya,


Indo ta gyara zama " sis Dijee ya akaye kukazo min Candy naga ku da yara hakan yana nufin duk kinye aure ta this age harda yara " Haule yaye dariya tace " aikin banza yoo ai kuma da kuma chan yanzu yaran ke biyu watakila ma yara ukku " Allah ya kiyaye "cewar Indo


Dijee ta daura da cewa ai Wallahi Dr Balarabe ke yana zuwa a azumi yana kawo mana kayan alkaire kuma yana nuna mana hoton ke a shekara yana zuwa sai ɗaya amman ya tafe India daga nan sai yanzu ya roqe maza mu suka barmu akan muzo Miki candy zakiji daɗi, bayan tafiyar ke ai abubuwan dewa ya faru a sanadin Dr SADEEQ sai dai muce Allah ya saka mai da alkaire a sanadin ke ne kuma komai ya faru ".............





taye ajiyar zuciya yarinyata daya gata nan shekara ta biyu sunanki ne nasa mata muna kirar ta Indo ,Haule kuma namiji ne Faisal , Mairo kuma bayan ta dawo aikatau kishiyar mamanta ta mutu , anan taye aure ta a gaidake cikin ta ya tsufa ..."





A haka suka ci-gaba da hirar rayuwa..






A harabar gidan Dr Kamal, ƙarƙashin hasken fitilar da ke yaye wutar dare, Dr. Sadeeq da Mai unguwa suka zauna gefe suna tattaunawa cikin natsuwa, dukansu suna kallon yadda yara ke ta wasa a bangon waje.


Mai unguwa ya gyara zaman rigarsa, ya kalli Dr. Sadeeq cikin lallashi:
“Dr… a yanda naga Indo yanzu? Sai dai mu yi godiya. Ta gyaru, ta waye, iliminta ya ƙaru… ko da ban ce ba, Allah ya saka maka da alheri.”






Dr. Sadeeq ya yi murmushin da bai kai ido ba, kamar wanda zuciyarsa ba ta cikin jikinsa.
Mai unguwa ya matsa kaɗan “Amma yanzu… ya maganar auren ku? Ina fatan dai… ta sani ko? Indo fa ba ƙarama ba ce yanzu.”
A nan ne zuciyar Dr. Sadeeq ta buga kamar ana danna ƙaho. Ya sauke numfashi a hankali, ya ce da murya mai taushi “A’a… bata sani ba.”
Mai unguwa ya ɗan yi shiru, ya ɗan tattara numfashi kafin ya ce “Meye yasa, Dr? Kai ka zaba. Ka shirya komai. Ita kuma ita ce matar da kace mahaifiyarta ta baka amana. To me ya hana ka sanar da ita?”






Dr. ya ɗaga ido a hankali ya dubeshi, fuskar sa cike da damuwa da wani nauyin da ya dade yana ɓoye “Mai unguwa… Indo yanzu ta girma. Ta gina rayuwa, ta samu buri. Tana da ilimi. Tana da ‘yanci.”
Ya ɗauki numfashi mai nauyi, kamar yana sauke wani dutse daga zuciya “Ban son in gaya mata haka kawai sai na takura mata. Bana son zuciyarta ta ji kamar dole ne. Indo ta samu sanda nake tsare mata rayuwa… yanzu ina son ta zabi rayuwarta da kanta.”






Mai unguwa ya gyada kai da jin kai “To amma Dr… ka duba fa. Ko da ka ajiye soyayya a gefe, Indo tana ganin ka kamar ginshiƙi. Idan ba kabar zuciyarta cikin duhu ba, ka gaya mata.”






Dr ya ɗan runtse idanu, ya kama gefen kujera hannunsa ya matse “Zan gaya mata. Amma… a hankali. Ba yanzu ba. Bari ta fara sabuwar makarantar ta, ta nutsu. Idan ta shirya… zan gaya mata komai.”


'Mai unguwa ya yi murmushi“To Dr, Allah ya baka ikon daidaita zuciyar biyu… naka da nata.”
Dr. Sadeeq ya dan yi murmushi mai rauni, cikin zuciyarsa kuwa tunanin Indo na kawo masa nauyi da farin cikin da bai iya kwatanta ba “Indo…” ya raya a zuciya,
“…kin dawo girma. Amma har yanzu rai na ya kasa daina kiranki ‘ƙaramar amana ta.”








9️⃣2️⃣❤️‍🔥9️⃣3️⃣
9️⃣2️⃣



🌟⭐DR SADEEQ✨ 🌟


BY


NARNAH ƘANWAR SOJA


BOOK 2
My 15novel comedy love and drama



https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM



THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*





🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲




BUSSINES GROUP


👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT






TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night



Bayan sallah insha’i, parlour ɗin gidan ya cika da hira da dariya. Dr. Sadeeq na zaune, yana ta kallon Indo a hankali, kamar zuciyarsa na ƙoƙarin fahimtar duk wata motsin ta. Ita kuwa, Indo a hankali take, kamar ba ta lura da shi sosai, ko da yake zuciyarta na ɗan ɗaukar sa ido.


An ci abinci cikin natsuwa, kowa na hira, amma idan ka lura, ido biyu suna ta matsa daga Indo zuwa Dr. Sadeeq da sauƙi. Bayan an gama, an watse da shirin cewa washe gari su Haule za su tafi Modirre. Sai dai kafin su tafi, sun yi wata hira mai tsawo cikin dare, suna ta dariya, suna ta bada labarai, kamar yaran da ba su ga juna ba tsawon lokaci.


Washegari, lokacin bankwana, an haɗu da murmushi da fuskoki masu kyau, dukansu suna jin rikitaccen kewa. Indo, tana cikin kewarsu, ta kwana da tunanin su, ta tashi da safe tana jin ɗan ƙarfin zuciya da rashin samun sa a kusa, amma kuma tana ɗaukar shi a cikin tunaninta, kamar yana nan tare da ita a cikin gida.





Bayan kwana biyu da tafiyar su Haule da Mai Unguwa daga Abuja, har yanzu gidan Dr Kamal cike yake da natsuwa. Indo ce kawai a ɗakinta, tana kwance tana kallon silin, zuciyarta cike da tunani marasa tsari.


Ranar dai ba kamar kowacce ba.


Da rana ta fara binciken c ɗakin da aka ware mata, Indo kamar bata gane ba.


Daɗin abin shine: duk abubuwan da suka taɓa kasancewa nata—akwatunta, atamfofinta, books ɗinta na Al Noor academy, har da ɗan ƙaramin kwandon kwalayen karatunta—duk an dawo dasu ɗaki ɗaya a ɗakin.


Hannunta na rawa ta ɗaga tsohuwar wayarta da ta bari tun kafin ta shiga boarding.
Wayar na buɗewa, hotuna suka fara tatsi a idonta.Hotonta da Dr. Sadeeq…
Hotonsa da ita a parlour…
Hoton da ta ɗauke su tare lokacin da ya kwanta yana bacci…
Hotunan sirrin da babu wanda ya sani Numfashinta ya kafe. Idonta ya cika da hawaye.


A hankali jikinta ya soma rawa. Ta durƙusa ƙasa ta jingina da gado tana kallon hoton da ya taɓa mata zuciya fiye da kima. Duk kalamai da ya taɓa faɗa mata suka dawo—“Indo I love you… keep it between us…”


Sai wani ƙarfi daga cikin cikin ta ya motsa. Numfashinta ya soma taruwa a wuya kafin ta sani, zafafan hawaye suka zubo masu raɗaɗi kamar ƙaiƙayi Tace a hankali amma cike da ciwo “Allah ya isa…
Dr Sadeeq Allah ya isa tsakanina da kai.
Na baka amana, ka amsa da… fyade.
Ka yi amfani da ƙaramin tunanina, da ƙuruciyata, da mummunan jahilcina a lokacin.
Ka ɗauke min mutunci… ka dauke min komai.”






Ta ɗaga wayar tana kallon hoton su biyu tana karyewa “Me zan kai gidan miji?
Da wane tarihin zan tsaya a gaban wani namiji, bayan kai ka riga ka raba min jikina kafin lokaci?” ta had'e fuskarta da tafin hannunta, hawayenta na gangarowa.


Yau ne karo na farko da Indo ta fuskanci gaskiyar abinda ya faru ba tare da soyayya ko jin tausayin sa ya rufe mata ido ba.


Zuciyarta ta cika da haushi, ciwo da takaici.
Tace cikin murya mai sanyi amma mai nauyi “Na tsani duk abinda ya faru.
na tsani amincewata na tsani duk wanda yayi min wannan ciwon…”
Sai ta tsaya ta rufe idonta da ƙarfi “…amma ban iya tsanarka ba, Dr Sadeeq.
wannan shi ne abinda yafi ciwo.” “Rayuwa ta fara daga farko… kuma wannan karo babu wanda zan bari ya cutar da ni.”


Indo Ta Fashe Kuka Da Gaskiyar da ta jima ta guje‑wa


A dakin nan mai sanyi amma cike da turare mai kamshi, Indo ta ci gaba da kallon hotunan da suka taɓa zama farin cikinta, yanzu kuma suna huda mata zuciya kamar wuƙa.


Ta matse wayar a kirji. Zuciyarta tana bugawa da sauri fiye da yadda ta taɓa ji numfashin ta ya fara hauhawa…


Sai hawaye suka fara gangarowa ba tare da izini ba da farko tana goge su suna ƙaruwa.
Har suka zama zafafan hawaye masu raɗaɗi.


A hankali ta furta cikin rawar murya “me na yi , me ya sa dole wannan abu ya same ni?
Me yasa ba zan iya komawa cikakkiyar budurwa kamar sauran ‘yan mata ba?”






Ta dafa ƙirjinta kamar ana murɗa mata zuciya kukan ya ƙara ƙarfi—kukan da ba na kuka bane kawai, kukan ciwo ne, kukan tunanin cewa rayuwarta ta lalace tun kafin ta san me rayuwa take nufi ta durƙusa ƙasa gaba ɗaya ta jingina kanta da kafet ɗin ƙasa “Lokacin can… bakar rana ce.
rana da na yi tunanin kalaman ka soyayya ne…
Rana da na ba ka dukkan amana…
Kuma kai ka maida ni... ba budurwa ba kafin lokaci.”






Ta rufe fuskarta da duka hannaye biyu, tana kuka mai amo, mai zafi, mai girman tunani.
“Allah ya isa! Ina jin kamar babu wanda zai yarda dani idan na gaya masa.
Ina jin kamar na riga nayi asarar abin da ya fi kowane abu daraja a rayuwar mace…”
ta buga ƙirjinta da wuya tana faɗa cikin zafin hali: “Kamar yadda na karo shekaru… zuciyata ba ta kara komai ba face tsoro!
Tsoron maza… tsoron aure… tsoron rayuwa gaba ɗaya!”Ta miƙe tsaye cikin rawar jiki, tana haɗiye kuka, ta dubi madubi ta ga kanta. Idonta jajir. Fuskarta ta kumbura.


Ta tambayi kanta da ƙasa‑ƙasa “Wannan ce Indo?Indo da ta yi burin zama nurse?
Indo da Mama ta yi mafarkin gani a matsayin mace mai daraja?”






Ta sake fashewa da kuka, babu ƙarfi a jikinta.
“Na tsani wanan bak’ar rana! ta raba min mutunci ta dawwama cikin rayuwata.
Kuma yanzu… ina tsoron in gaya wa kowa cewa…
ba budurwa bace Indo da kuke gani…”






Sai ta durƙusa ta rungume kanta, kukanta ya rikide zuwa irin kukan da zuciya ke tsagewa but ta kasa fidda muryar gaskiyar da take motsa cikin ta “Me zan ce wa mijin da zan aura?Wa zan gaya masa dalilin?”






Abin da ya fi mata ciwo shi ne lokacin da ta furta cikin harshen da ya fito kai tsaye daga zuciya “Me ya sa yake min haka alhali ni dai ina sonsa?”






Dakin ya yi shiru.
Indo ta zauna a ƙasa, tana kuka kamar wacce aka yi wa hukuncin da ba ta cancanta ba.


Amma a cikin wannan kukan… akwai sabon karfi da yake tashi a hankali zuciyarta akwai kalmar da ta fara fitowa:
“Sai na gyara rayuwata. Ba zan bar cutarwar da aka min ta karya ni ba.”







@@@@@@@@@@@@@@@@@@



Dr SADEEQ yana kwance a ɗakinsa, hasken ɗaki yana shigowa ta taga ƙanana. Hannuwansa a bayan kansa, idonsa na kallon shiru amma zuciyarsa tana ta motsi cikin sauri.


Tunani na yawo a kwakwalwarsa—Indo. Yana tuna kyawunta, natsuwarta, da duk abubuwan da suka shafe su a baya.
“Ta girma sosai… ta cika ilimi, ta zama mace mai hankali da kima. kuma duk da komai da ta sha, ina ganin tana da ƙarfin zuciya da natsuwa da ban taɓa tsammani ba.”






Ya sauke numfashi mai nauyi. Hannunsa ya miƙa ya taɓa hoton Indo da ya ajiye a cikin wayarsa na Candy Kamshin turarenta na dawowa cikin zuciyarsa, yana jin wani nauyi amma a lokaci guda farin ciki da marmari.
“Dole ne ta zama tawa, matata a gaskiya. Abin da nake marmari a rayuwata… yana nan a gabana. Allah ya bani ta, sai na tabbatar da cewa ina kula da ita, ina son ta ba tare da cutar da ita ba.”






Yana motsa kansa a hankali, yana tunanin yadda za a nuna mata soyayya da girmamawa. Tunani na cewa ko da tsawon lokaci, duk wani kuskure da aka taɓa yi a baya, zai tabbatar da tsarkakakken soyayya yanzu yana ba shi wani jin daɗi.


Ya juya a gado, ido ya rufe, amma zuciyarsa tana ci gaba da magana:
“Indo, ko da yaushe kina nan a zuciyata… matata ce. Kuma zan tabbatar da cewa kowace rana da kika tashi a wannan gidan, kina ganin ni a matsayin wanda ke son ki da dukkan zuciyata.”






Sai ya sauke numfashi mai tsawo, wanda ke ɗauke da farin ciki, kewar soyayya, da nufin kare Indo daga duk wani damuwa.






9️⃣3️⃣❤️‍🔥9️⃣4️⃣
https://youtu.be/4wIojiBbOgA



🌟⭐DR SADEEQ✨ 🌟


BY


NARNAH ƘANWAR SOJA


BOOK 2
My 15novel comedy love and drama



https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM



THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*





🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲




BUSSINES GROUP


👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT






TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night




Atika na toilet ta kara duba abinda idonta ya gani “positive”, alamar ciki da gudu ta fito daga toilet tana tsalle-tsalle, tana murna, tana ihu a hankali don ta gawayawa Dr SADEEQ:
“Na samu ciki!”






Jikinta ya ƙara ƙiba da haske kamar ba ita ba, shape nata ya ƙara bunƙusa, ta zama cikakkiyar mace. Tsalle da tsantsi a jikinta sun bayyana sabon canjin da ya faru. Amma cikin murna , ta faɗi: “Dr batagama ba, kawai ta zame…”






A nan Dr SADEEQ yana cikin tunanin yaganta, zuciyarsa cike da mamaki rashin hankali na ta
“INNALLILAHI… wai ke? yaushe zaki yi hankali? Wayagayamiki ana gudu a toilet ki fito haka…”






Ya juya a hankali, cike daban haushi yana kallon wannan sabon yanayi da Atika ta samu,




Ihu ta buga sosai har ya giggita part ɗin. Dr SADEEQ nan da nan ya tashi, zuciyarsa ta ɗan tsaya, ya hango Atika tana ihu a kwance tana birgima

40 / 48