Author : Nana Kanwar Soja Category : Hausa Read
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
Dalibai suka hallara a big assembly hall na girls’ boarding, an sa carpet blue, an kawata da balloons pink & white. Kowa ya zauna a sashen da aka ware musu; parents area na gefe, students area a gaba. Ana ta kiran ajin su daya bayan daya, ana ba su certificates, ana ɗaukar hotuna.
Indo da Ilham zaune kusa, suna sanye da uniform nasu na Candy Presentation.
Sai aka fara kiran iyayye suna fitowa suna rungumar ’ya’yansu. Ana dariya. Ana hoto.
Amma Indo tana kallon su… zuciyarta ta fara karyewa kaɗan-kaɗan.
Ta tuna lokacin da take ƙarama… Mama na janta da hannu, tana tsintar ta daga titi, tana bata abinci, tana yi mata kallo ɗiyarta mai ciki da gata sa barkwanci
Ta tuna mai unguwa, yana bata farin ciki da kulawa baya bare kowa ya taɓata ko an kawo ƙararta baya mata tsanani kasancewar sa kuma na yayan mahaifin ta ...
Ta tuna Dijee, yarinyar da ta taba zama abokiyar ta kafin rayuwa ta watse, wacce ta kasance da ita a kowani lokaci basa rabuwa , Haule ƙawar amana duk wani shashashan ci a tare suke lamarin su ,,, tana tuna Mairo kawai taye ajiyar zuciya domin tunu su a wanan lokacin bashi da wani amfani , kamar a gaske hotunan sun fara dawowa a idonta…
Sai zuciyarta ta matse sosai.
Hawaye suka fara cicciko mata.
Ilham ta dubeta cikin mamaki “Indo? Me ya faru?”
Indo ta girgiza kai, amma hawaye suka cigaba zubo mata. Ta ce cikin murya mai rauni:
“Ilham… kowa yana tare da iyayensa. Ni kuma… babu Mama, babu mai unguwa, babu kowa. Babu su dijee Ban san ko suna raye ba…”
Ta runtse ido sosai kamar tana ƙoƙarin hana zuciyarta ta fashe:
“Na tuna abubuwa da yawa… lokacin da ban san komai ba. Wallahi nayi missing su… nayi missing gida… duk da ba ni da wani gida.”
Ilham ta kama hannunta sosai:
“Karki ce haka. Ke kina da gida yanzu. Kina da mu. Daddy ya ce kinyi kyau domin kina da tarbiyya. Mommy tana treating ɗinki kamar nata… Indo, kina da mu wallahi.”
Sai Indo ta share hawayenta da gefen uniform dinta, tana murmushi mai raɗaɗi:
“Na sani… amma zuciyata yau ta tuna da komai.”
DJ ya kunna soft instrumental, ana kiran sunayensu kusa da su, amma Indo ta zauna shiru tana kallo sama — tana jin kamar Allah yana can yana kallonta da ido mai tausayawa.
A zuciyarta take faɗi:
“Ya Allah… idan suna raye ka kare su. Idan sun mutu ka jikan su. Ka bani ƙarfin zuciya.”
Ilham ta rungumeta ta gefen kafaɗa, murmushi ƙarami a bakinta:
“Ki duba gaba Indo… mu ne iyalanki yanzu.”
Indo ta yi ajiyar zuciya…
Da karfin hali ta mike — domin ana kiranta domin karɓar award ɗinta.
Aka kira sunanta da murya mai ƙarfi, kamar ana kiran wata fitacciyar baiwar Allah “THE BEST STUDENT IN CHEMISTRY…
THE BEST IN SCIENCE DISPLAY…
OUR PRIDE OF REGENT GIRLS’ BOARDING…
A’ISHAHTU ABUBAKAR SADEEQ!”
Hall ɗin ya cika da tafi
Dalibai suka mike suka yi ihu, Ilham ta ɗaga mata hannu da murna.
Indo ta miƙe a hankali, jikin ta a sanyaye, zuciyarta na bugawa kamar ana buga ganga. Ta taka steps ɗin stage da natsuwa amma idan ka kalle ta sosai, zaka ga wani sanyi ya lullube ta.
Ta tsaya a gaban mic.
Sai anchor ɗin event ɗin ya ce da murya mai cike da farin ciki:
“Will her parents come forward, please?”
Nan fa zuciyarta ta tsaya cak.
Tana kallon jama’a…
Parents suna miƙowa gaba domin ’ya’yansu… amma babu kowa da ya taso saboda ita.
Ta buɗe baki, ba ta da magana.
Ta runtse idanu… amma hawaye sun fisge ta kafin ta kai ga boye su Hawaye suka gangaro mata kwance Anchor ya kuma tambaya:
“Her parents? Anyone for A’ishah Abubakar Sadeeq?” kallon kowa ya juya gareta.
Abin ya ɗaure mata kai.
Jin nauyin zuciya, jin wani sanyi mai radadi — tunanin “Ni dai ba ni da kowa.”
Ilham ta miƙe da sauri tana kuka, tana son zuwa gareta amma ba a bar dalibi zuwa stage ba, hakan yasa su Daddy da Mommy Ilham suka ƙara yunƙurin zuwa bayan sunje na Iliham
Indo ta rufe idonta da hannunta, muryarta na rawa sosai ta ce a hankali kamar tana magana da zuciyarta “Ya Allah… Ni kadai ce kenan?”
Amma kafin ta gama jin zafin kalmar —
Sai aka ji murya daga bayan hall ɗin… murya irin ta namiji, mai ƙarfi, mai nutsuwa, mai kama da wanda ta taɓa ji a ƙwaƙwalwarta tun tana ƙarama:
“I AM HERE FOR HER.”
Hall ɗin ya yi shiru kowa ya juyo!
Indo ta bude idanunta a hankali… sannan ta juyo a hankali kamar a cikin dandalin zuciyar ta , Wani mutum dogo, mai tsananin kamala, ya ƙara kyau da nagarta sanye da farar shadda, ya nufo stage.
Dr. SADEEQ.
Babu dariya a fuskarsa. Babu wasa.
Idonsa kawai ya cika da abu guda — tsananin tausayin Indo.l ya taka har gaban stage, ya tsaya a kanta, ya ɗaga mic ya ce:
“I am her Brother And I am proud of her.”
Hall ɗin ya sake ƙara yin shiru… sannan tafi mai ƙarfi ta biyo baya Indo kuwa ta tsaya cak kamar an dasa ta.
Zuciyarta ta karaya… ta kuma warke… a lokaci guda tace da murya mai rauni, tana kuka:
“D-Dr… ka zo?”
Ya matsa kusa sosai, ya share mata hawayen da yatsunsa a hankali:
“Na kasa bari yau ta wuce ba tare da gani na ba.”
Ilham tana ƙasa tana fashewa da kuka.
Anchor ya faɗi cikin nutsuwa
“Congratulations, Dr. Sadeeq and your Sister”
Indo ta fashe da kuka mai rauni ta faɗa jikin sa Karo na farko a rayuwarta yanda taji yaye kewar iyayyen ta fiyyeda hankali
Indo ta goge hawayenta da baya na hannunta a hankali. Anchor ya mika mata award plaque da certificate. Ta karɓa da ladabi ta matsa kusa da mic, zuciyarta na rawa amma muryarta mai taushi ta fito yadda kowa ya ji:
“Good afternoon everyone…”
Tayi murmushi mai rauni, hawaye suna kan gefen idonta amma tana ƙoƙarin zama strong girl kamar kullum.
**“I want to say a very big thank you to Regent Girls’ College… To all my teachers…
To every student here today…
For helping me become who I am.”**
Hall ɗin ya yi tafi sosai
Indo ta lumshe ido ta ja numfashi sannan ta ce cikin wata murya mai nutsuwa sosai “I am very grateful. Thank you so much.”
Sannan ta juya a hankali zuwa ga Dr. Sadeeq da har yanzu yake tsaye a gefen stage din, hannunsa a sakale, shi ma idonsa ya sauya kala saboda irin muryarta.
Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce cikin ladabi:
**“Thank you, Dr. Sadeeq for everything u make me who I'm today u make me so happy…
Na gode sosai da ka zo… da ka tsaya min…
Allah ya saka maka da alkhairi.”**
Kalmar ta fito a hankali, cike da mutunci da jin ƙai, ba don tana son shi ba, sai don yau ya taɓa wani gurbi a zuciyarta da duk rayuwarta bata taɓa samun mai cike shi ba.
Dr. Sadeeq ya ɗaga kai ya kalle ta da murmushi mai sanyi — murmushin da baya komai sai yarda da alfahari da ita.
Sai Indo ta sauko daga stage, Ilham ta ruga da gudu ta rungume ta. Sai suka tafi wajen iyayen Ilham.Iyayen Ilham suka rungume Indo kamar ’yarsu, Momy Ilham
“Congratulations, A’ishah… we are very proud of you.”
Indo ta ɗan sunkuyar da kai ta ce cikin turanci mai laushi: “Thank you so much, ma…
Thank you sir…
Na gode sosai da kulawa da taimako tun farkon zuwana boarding.”
Suka yi murmushi, suka share mata hawayen idon da ya rage Ilham kuwa ta kalleta ta ce cikin taushi:
“Indo… yau kin zama star.”
Indo ta yi murmushi kadan amma a zuciyarta tana jin sanyi mai zafi.
Domin yau ta yi armashi a duniya… amma ta tuna cewa bata da iyaye — sai dai wanda allah ya kawo mata a matsayin shi ne yau ya tsaya mata.
Dr. Sadeeq ya dan matso gaba yana kallon Indo da wani murmushi da ya gama rikita zuciyar kowa dake kallo.
Ya dan sunkuya ya ce da ita cikin muryarsa mai nutsuwa “Indo… I have a surprise for you.”
Ta daga ido a hankali, zuciyarta na dukan tara-tara “Surprise? me ne ne?”
Bai amsa ba, sai kawai ya yi murmushi ya janyo hannunta ya rufe mata idanu da tafin hannunsa. Ilham ta yi tsallen murna, Kamal ya ce:
“READY, OGA!”
Sai Dr Sadeeq ya ce “Open it… Kamal.”
A nan Kamal ya danna remote ɗin motar — kirrrrrr — motar ta bude.
Brand new white Lexus RX350, ta sheƙa kamar rana, ta leƙa da ɓarna mai walwali. Kyauta ce babba, tsadadde da kowa ya runtse ido Sannan Dr. Sadeeq ya bude mata idon a hankali Indo ta tsaya cak tayi ja kamar jinin jikinta ya tsaya.
Idonta ya cika da hawaye ta dafe kirjinta “This… is mine?”
Dr Sadeeq ya ce mata cikin natsuwa:
**“Yes, Indo. Congratulations on your Candy Day This one… is for YOU.”**
A take biiiii–iiiiiiirrrrrr~
A bude bayan motar suka fito: Mai unguwa,
Dijee,
Haule,
da ’yan karamin gidan su biyar — duk cikin sabbin kaya, fararen riguna, suna murna da shewa.
Indo ta fashe da kuka mai sauti—kukan farin ciki da baƙin tarihin rayuwa da ya tsaya mata a wuya.
Ta ruga da gudu ta rungume Haule da dijee da kyar.
Mai unguwa ya ce:
“A’ishatu Indo! Allah ya miki albarka yarinya mai hakuri a ƙarshe gashi kinye karatu kin zama abun alfahari.”
Sai ta juya cikin hawayen murna ta ga Dr Sadeeq tsaye yana kallonta, idonsa raye da motsin zuciya.
Ba tare da ta shawo kanta ba— sai kawai ta rungume shi da ƙarfi, kamar zata fashe. Jama’a suka yi awwwwwww
Shi ma ya dago hannunsa a hankali ya rike ta, amma cikin kunya da nutsuwa.
Sai bayan ta sake shi sannan ta koma ga ’yan uwanta tana kuka tana murmushi tana dariya duka lokaci guda Ilham ta ce:
“Indooo today is your day!”
Dr. Sadeeq ya tsaya gefe yana kallonta, idanuwansa sun yi laushi…
Zuciyarsa kuma ta na cewa:
“Alhamdulillah da Allah ya bani ikon faranta ranki… Indo.”
A lokacin da hayaniyar murna ta dan lafa kadan, Dr Sadeeq ya yi alamar a kawo special cake ɗin da ya yi order tun kwanaki — babban 3-tier vanilla & strawberry cake mai rubutun:
**“CONGRATULATIONS A’ISHAHTU INDO
BEST STUDENT OF THE YEAR”**
A kawo cake ɗin aka ajiye a gaban Indo.
Tayi kyau kamar wata arziƙin amarya, bakinta cike da murmushi da hawaye Dr Sadeeq ya matsa gefe ya ce: “Indo, please… cut your cake.” Dalibai suka fara raira waƙa:
**“Ceee-e—ut your cake ooo,
Indooo cut your cake!”**
Indo ta kama wukar farar da aka bata, Ilham ta rike hannunta sama da murmushi mai kyau.
Suka yanka cake ɗin tare.
Kamal ya yi ihu “Ilham ki buɗe baki ki ci na farko daga Indo!”
Ilham ta bude baki sai Indo ta sanya mata cikin shagwaɓar ƙawa. Su duka suka yi dariya suka rungume juna Sai Kamal ya ce:
“Next! Doctor!! Your turn!”
Dr Sadeeq ya kalli Indo, zuciyarsa ta yi wata irin rawa ta ɗan sunkuyar da kai saboda kwarjininsa
Amma ta ɗebo karamin yanki na cake ta miƙa masa. Shima ya ɗan buɗe baki kaɗan — a hankali ta sa masa.
Kusan duk dalibai suka yi ihu:
“Awwwwwwwwwww!”
Dr Sadeeq ya yi murmushi mai nauyi, ya ce mata “Thank you, Indo.”
Kamal ya miƙa mata wata babbar gift bag mai kyau ya ce: “From your best brother-in-law to be!” Ta buɗe taga Wristwatch, perfume, da notebook mai rubutun “YOU ARE SMART”.
Ta yi tsalle ta rungume shi cikin ladabi:
“Thank you Brother Kamal.”
Kamal ya yi dariya “Anytime, Madam SADEEQ.”
Sai Daddy babban ya matso da murmushi.
Ya miƙa mata kyakkyawar small laptop da envelope mai kuɗi kaɗan don pocket money.
**“A’ishatu Indo, Allah ya basu ikon kula da ke.
Allah ya sa ki yi ilimi mai amfani.”**
Ta durƙusa ta yi masa godiya sosai, zuciyarta cike da ƙaunar iyali da bata taɓa samu ba da wuri.
Sai ga Nazifa, kanwar Dr Sadeeq — yanzu matar Kamal — ta rungume Indo da kyau.
Ta miƙa mata small diamond necklace.
**“Indo, wannan tun daga nesa na kawo miki.
Na san yadda kika yi wahala kafin ki kai nan.” Indo ta sake fashewa da kuka mai sanyi.
Nazifa ta rungume ta. “Kar ki sake jin ke ɗaya we are your family now.”
Ana ta ɗaukar hoto Ilham da Indo,
Indo da Mai unguwa, Indo da ƙannenta,
Indo da Dr Sadeeq (wanda ya tsaya kusan gefe amma hoto ya zama perfect),
Kamal yana dariya,
Nazifa tana gyara veil, Daddy yana yi mata addu’a Hotuna suka cika waje kamar an yi bikin graduation ɗin gida.
Wannan rana ta zama rana mafi farin ciki da Indo ta taɓa samu tun zuwan ta duniya.
TO BE CONTINUED
9️⃣0️⃣ ❤️🔥9️⃣1️⃣
🌟⭐DR SADEEQ✨ 🌟
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
Gidan Dr. Kamal…
Gidan Dr. Kamal suka nufa, babban parlour mai faɗi da kayan alfarma na haske, sai ƙamshin turaren wuta ke yawo cikin iska. Ilham da iyayenta tun zuwan su suka watse zuwa gidan su , sai aka bar parlour ɗin cike da sanyi da nutsuwa.
Indo ta zauna a tsakiyar kujerun, ta zama tamkar abun kallo, kyanta na haskawa fiye da yadda kowa ya zata. Dijee na gefenta, Haule na kallonta ido cike da ƙauna da alfahari. Indo dai ta yi shiru tana murza yatsunta, zuciyarta na dukan da ba ta iya sarrafawa.
A gefe kuma, mai unguwa da Dr. Sadeeq suka yi musayar kallon da ke nuna "mu fita". Nan suka miƙe a hankali.
“Bari mu fita waje mu tattauna,” Dr. Sadeeq ya faɗa da murya mai nutsuwa.
Mai unguwa ya gyada kai, suka fice su biyun zuwa harabar gidan, suna tafiya a hankali kamar masu tattaunar abu mai muhimmanci game da makomar Indo.
A ɓangaren cikin gidan kuwa, Indo, Dijee da Haule suka shiga ɗaki mai yalwa, suka zauna. Dijee ta kama hannun Indo tana murmushi.
“Indo kin zama wata daban… Allah ya ɗaukaka ki.”
Haule kuwa ta kalle ta da murmushin jin daɗi:
“Munyi kewarki sosai, yau sai kamar mu rungume ki ba mu sake ba.”
Indo ta saki ajiyar zuciya, ta lumshe idanu, sannan ta ce:
“Ku bazai gane irin farin cikin da nake ciki ba… wallahi ban taɓa tsammanin zan yi wannan rayuwar ba”
Dukansu suka yi dariya mai taushi, ƙanƙaninsu na ji lokacin masarautar Indo ya fara dawowa
Indo ta zauna a tsakiyar gadon mai laushi, ta jingina da matashin kai, fuskar ta fes kamar wacce aka goge da lu’ulu’u. Dijee da Haule sun zauna a ƙasa a gabanta kamar yara biyu suna jiran a ba su labarin da sukafi so.
Indo ta yi murmushi, ta kalli kowannensu sannan ta ce“Ku zo ku ji yadda birni ya koya min rayuwa… wallahi kun san Indo ce, amma yanzu Indo ta zama Indo ɗin gaske.”
Dijee ta fashe da dariya “Ai kin canja sosai! Ki fara fa, muji kafin ki koma kalar city girls ɗin nan har mu kasa gane ki.”
Haule ta tafa hannaye tana dariya:
“Indo kin zama mata fa! Kin ƙara kiba, kin tsayi, kin zama kamar 'yar manya sosai.”
Indo ta ɗan sunkuyar da kai tana dariya kaɗan, sannan ta fara basu labari:
“A birni… ai komai aikin kai ne. Da safe makaranta, da yamma library, da dare assignments. Sai Dr. Sadeeq da ke yawan yi min nasiha, duk da shi ba ya zuwa ziyara boarding da naki Amman komai na kuɗi shi Kibiya min…”
Ta yi tsaki kaɗan tana dariya, su Dijee suka yi ihu: “Ai tunda ya selonki! Ba wanda zai kai shi da mantuwa da aiki.”Indo ta gyara zama:
“Haka ne. Amma rayuwar birni ba wasa bace. Na koya yin turanci sosai, har ma yanzu Ilham tana ce min ina kama da 'yar American.”
Suka fashe da dariya.
“Wallahi kuwa! Ki ji yanda kike kiran candy da ‘cankdi’.” Dijee ta yi kwaikwayon murya tana dariya. Indo ta ɗan hankade ta da filo.
“Ke dai bari kawai. Kawai dai ina grateful. Allah ya bani Ilham, ya bani Dr. Sadeeq, ya bani makaranta mai kyau… duk rayuwa ta ta canja.”
Haule ta runtse ido da murmushi:
“Kin zama kamar wacce aka sake haifa… Ina jin daɗi sosai Indo, kina da arziki mai kyau.”
Indo ta yi ajiyar zuciya “Ku dai ku sani… duk inda naje, bana manta irin soyayyar ku. Na tuna ku kullum , ina cikin kewar gida”
Dijee ta share hawayen da ya fara bayyana “Ai yau Allah ya cika mana buri, mun dawo tare kamar da.”
Suka rungume juna su uku, ɗakin ya cika da dariya, labarai, da ɗan kuka mai daɗi — kamar ƙungiyar 'yan uwa da aka raba shekaru masu tarin yawa sannan aka sake haɗuwa Indo Ta Tuna da Mairo
Indo ta jingina da filo tana lumshe ido, fuskar ta cike da farin cikin sake haɗuwa da su Dijee da Haule. Nan take ta ɗago kai da murmushi “Ku fa… har yanzu ba ku faɗa min labarin Mairon nan ba.”
Dijee ta kwaɓe baki kamar wacce za ta yi kuka amma tana dariya:
“Mairo? Ai Mairon nan ta dawo Modirre… tana da tsohon ciki ne shi ya sa bata iya zuwa candy ɗin.” Haule ta gyada kai da gaggawa
“Ke kuma Indo,