Author : Nana Kanwar Soja Category : Hausa Read
bright, even in the darkest night
Indo ta miƙe da gajiya a jikinta, tana jin ciwon ƙafarta da gajiya ta sa zuciyarta ɗan sassauta. Ta juya ta kalle shi da idanu cike da ƙarfin hali:
“Dr… idan har zan kwana a nan, sai ka fita daga ɗakin,” ta faɗa a hankali.
Dr Sadeeq ya ɗan yi murmushi mai laushi, ya matsa ƙasa da ƙasa ta gefenta, ya shafa gashinta daga fuska:
“Toh… my queen, an gama yanzu. Zan fita.”
Ya daga kai ya yi murmushi mai natsuwa, zuciyarsa cike da farin ciki da jin daɗin kasancewa kusa da ita, sannan ya juya ya fita daga ɗakin, yana rufe ƙofar a hankali.
Indo ta kwanta a gadonta nan da nan, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin zafi da natsuwa mai ban mamaki. Duk gajiya da ciwon ƙafarta sun ɓace a hankali yayin da take jin kwanciyar hankali, tana rufe idonta a hankali.
Bacci mai daɗi ya shigo mata nan take, zuciyarta na cike da tunani da jin daɗin kasancewa cikin kulawar Dr Sadeeq, duk da cewa a ranta, har yanzu tana ɗauke da ɗan haushi da takaici saboda abin da ya faru a baya. Amma wannan dare ya kwashe ta cikin nitsuwa, cikin kwanciyar hankali mai cike da ɗan jin daɗin zuciya.
Ya zauna a kujera, zuciyarsa cike da tunani, ya lura da cewa Indo na raye da hankali amma akwai ɗan allura a jikinta wanda ke taimaka mata bacci mai natsuwa. Nan ya shafa kanta a hankali, murmushi a fuska:
“Thank you so much, A’ishatu Indo. Kin bani farin ciki a lokacin da nake bukata, kin taimaka min a lokacin da nake bukata, kin faranta min rai a matsayin na mijin ki. Sai dai kuma nace Allah ya miki albarka. Amanar Mama, ban yi miki hakan da sani ba. KIYE ha’kuri. Inason ke… na tabbatar wa kaina da cewa ina sonki, so na gaskiya da amana. A yau, kin mayar dani babban mutum, na zama cikakken namiji. Allah ya saka miki da alkhairi, kuma Allah ya nuna mana ranar da zamu zauna ne dake a inuwa ɗaya matsayin ma’aurata.”
Ya tsaya dan lokaci yana kallonta, zuciyarsa cike da natsuwa da godiya. Gaskiyar cewa Indo ta kasance a gefensa, cikin kulawa da soyayya, ta sa shi jin wani irin kwanciyar hankali wanda bai taba jin irinsa ba.
A hankali, ya taɓa hannunta, ya rike shi a cikin nasa, yana jin dukkan bugun zuciyarta ta amsa natsuwarsa. A wannan lokaci, duk gajiya da wahala da suka sha, sun ɓace, suka bar shi da jin daɗin kasancewa tare da wanda yake kauna, cikin kwanciyar hankali mai cike da albarka.
A haka ya ɗauke ta da kansa, ya goya ta cikin natsuwa kamar jaririya, yana jin nauyinta amma zuciyarsa cike da wani irin farin ciki da mugun tsoro — farin cikin samun ta a matsayin matarsa, tsoron kada a kama su ko a zarge su, musamman ganin tana cikin rauni sosai.
Ya fito da ita daga ɗakinsa a hankali, hannunsa ɗaya na riƙe da bayanta, ɗayan kuma a ƙafafunta. Duk da cewa nauyin jikinta yana masa yawa, bai bari ta ji motsin wahala ba — ko numfashinsa ya rage don kada ta farka.
Har ya isa part na Kaka, babu kowa a falon, sai ƙamshin attarun Kaka da shiru mai sanyi. Ya buɗe ƙofar ɗakinta Indo da hankali kamar mai tsoron farka wata aljana. Ya mayar da ita kan gadonta ya jawo bargon ya rufe ta, ya gyara pillow ɗin kanta ya matsa mata gashinta gefe sauke ajiyar zuciya.
Yana kallonta, tana numfashi irin na baccin da ya fito daga magani. Fuskar ta kamar fara da safe, babu tashin hankali, babu kuka.
Sai ya ɗauko wayarta daga gefen gado ya buɗe, ya yi rubutu, amma ganin ba zai iya faɗa komai cikin rubutu ba, sai ya dannan voice note, ya yi magana da ƙasa-ƙasa kamar yana magana da wata zuciya da yake tsoro ta fashe:
“I’m sorry Indo… but I love you.
Keep it… it is our secret.
Our first night…”
Ya aika mata. Ya maida wayar inda ya ɗauko ta. Ya tsaya na mintuna biyu yana kallonta kamar zai dawo ya rungume ta, amma ya maida kai gefe saboda tsoron Allah da tsoron a kama shi da ita.
Ya janye numfashi ya fita a hankali, har ya dawo part ɗinsa.
Da Asuba tagari, ƙarar sallar farko ta tashi. Yana shigowa ɗakin sa ya jingina da ƙofa, yana rufe idanuwa kowanne yayi ja saboda kuka da tsoro da soyayya.
A ransa yace:
“Ya Allah Ka rufe mana asiri…
ka bani ikon gyara tsakanin iyayyena da Indo…
Ka bani Indo ranar da duniya zata shaida ne halal nata ne …”
7️⃣7️⃣
💔❤️🔥DR SADEEQ ❤️🔥💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
MORNING UPDATE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
BARKA DA SHIGOWA SABUWAR SHEKARA
Da sassafe lokacin da ake kiraye-kirayen Asuba, Dr. Sadeeq ya fita a hankali daga ɗakin, ya tabbatar kofar ta rufe ba tare da hayaniya ba. Zuciyarsa cike da farin ciki, nutsuwa da wani sabon nau'in soyayya da bai taɓa ji ba a rayuwarsa.
Ya tsaya ɗan lokaci a bakin ƙofa yana kallonta tana bacci — baccin da shi ya kawo mata, mai nauyin allurar hutu da ya yi mata saboda ta huta. A ransa ya ce:
“Ke ce kyautar da ban taɓa zato ba Indo… Allah ya tsare min ke.”
Washegari…
Indo na farkawa, idanunta har yanzu nauyi suke yi. Tana ƙoƙarin tashi sai ga hasken wayarta yana walƙiya — one new voice note.
Ta ɗaga wayar a hankali, zuciyarta tana dukan dumm… dumm… kamar ana buga ganga. Ta kunna sakon.
Murya mai sanyi, mai raɗaɗi, murya da ta saba sanyaya zuciyarta, ta ji shi yana faɗa:
“I’m sorry Indo… but wallahi I love you. Ki bar komai a tsakaninmu sirrinmu… our first night.
Kiyi hakuri idan na yi over. Amma ke kika mayar da ni cikakken namiji jiya. Allah ya saka miki da alkhairi.
Please ki kula da kanki My Queen.”
Sakon ya ƙare da wata ajiyar zuciya mai nauyi da ya yi — mai kama da na mutum da yake riƙe da wani abu a ransa.
Indo ta tsaya jingine da gado, hannu a kirjinta, hawaye masu sanyi suka gangaro. Ba na bakin ciki ba — hawaye ne na soyayya da jin daraja.
Ta ce a hankali:
“Ya Salam Dr. Sadeeq…”
Indo na kwance har yanzu tana jin nauyin jikinta, banda jin daɗi. Idonta ya kumbura saboda baccin ya yi nauyi, zuciyarta kuma kamar an jefa ta a cikin ruwa — tana ji tana ɓuya tana jin kunya da tsoro iri biyu.
Sai kawai ta hurgar da wayarta gefe, kamar ma ba ta son ta ga sunansa.
“Bazan sake magana dashi ba… wallahi bazan yi ba.” Ta maimaita a ranta.
Tana kwance haka har ƙarfe takwas.
Kaka ta zo da mamaki, domin Indo ba ta saba yin baccin safe ba, musamman a weekend.
Ta tura ƙofar ta shiga, tana kallon yadda Indo ke bacci kamar wata mai shayarwa da ta gaji.
Kaka ta ce da ƙarfi:
“Ke tashi ki zo kimin kitso! Kince yau zakimin, ko sai na buga miki sanda? Yaran zamani da baccin banza!” Indo ta buɗe idonta a hankali, idon jajaye kamar mai zazzabi.Ta ce da murya mai rauni:
“Kaka… yau banda lafiya ciki na ke ciwo sosai.”
Kaka ta tsaya cak, ta zaro ido:
“Ayyo! Ayyo Indo? To shikkenan, Allah ƙara lafiya Dr. Sadeeq yazo na gayyemai yazo ya baki magani.”
Indo ta tsaya shiru kamar an caka mata wuka.
Da sauri ta miƙe zaune tana girgiza kai:
“A’a Kaka! Don Allah kar ki gayyamai komai…
Ina jin zan warke da kaina. Kar ki dame shi.”
Kaka ta ja dogon tsaki:
“Aikin banza. To dai ki sha magani ko kishi ruwa. Ni na tafi.”Ta fita tana gunguni.
Amma Indo kuwa — da magana ɗaya Kaka ta faɗa — zuciyarta ta rikice banda ciwon ciki dai, kunya da tsoro ne ke murɗa ta.
Ta ɗora hannu a kirji tana jin bugun zuciyarta kamar ana dokawa da guduma.
“Fusata nake dashi. Bai da wayo wallahi. Ni ma ai mace ce… ya yi tunanin ina iya kallon idonsa yau?”
Ta sake maimaitawa a ranta:
“Alkawari na dauka… daga yau ba zan sake magana dashi ba.”sai wayarta ta sake yi vibration a gefen gado ta runtse ido Sunansa ne. Dr. Sadeeq. Calling…
Indo ta ga kiran Dr. Sadeeq yana shigowa… ta ɗaga idonta ta kalle shi da tsana, zuciyarta ta hau tsalle.
“Wallahi bazan amsa ba.”
Ta kashe wayar nan take.
Wayar ta sake ringing…
Ta ƙara kashewa.
A karo na uku ya sake kira… nan fa ta dakan wayar gaba ɗaya ta switch off.
Ta tashi a hankali, tana rik’e ƙasan cikinta saboda zafin nan na budurci da bai saba da abin da ya faru ba.
Ko da tana jin tsoro, Indo ta ɗan yi wayo: ta hada ruwan zafi a bucket, ta naɗe kanta da towel, ta shiga bathroom ɗin su.
Ruwan zafi ya taba jikinta ta tsinci kanta da ƙara:
“Ayyooo…!”
Zafin ya motsa mata tunaninta, hawaye suka cika mata ido.
Amma ta daure saboda ta san hakan zai sauke mata radadin.
Ta yi wanka a hankali kamar wacce ke ladabtar da kanta.
Bayan haka ta sa simple riga, mai laushi, ba wata ado.
Ta koma ta kwanta, ta ɗaura hannu sama tana jin baccin ya dawo, amma zuciyarta cike take da fushi – baccin bai isheta ba a bangaren Dr. Sadeeq kuwa da farko ya zuba ido a wayarsa kiran na zuwa busy yayi murmushi mai sauti, ya tafa hannunsa:
“Fushi take… ai dole ta yi. Amma tawa ce.”
Ya kwantar da kansa a gado ya numfasa da nishadi kamar mijin da aka gama yi wa faɗa amma ya ji daɗin komai.
Ya wuce gym, ya yi wanka da kumfa farare, cikin bathtub mai ɗumi.
Ya lumshe ido yana tuno daren jiya,
yana murmushi,yana ganin Indo ta rikice,
yana jin yadda ta yi kuka, yadda ta yi ƙoƙarin gudu…
Shi kaɗai yasan irin farin cikin da ya shiga jiya.
A yau ya zama namiji cikakke — kuma Indo ce ta ba shi hakan.
Ya fito daga wanka yana shafa kansa wadda ruwan kumfa ke zuba a gwiwowinsa.
Cikin nutsuwa da annuri, ya saka farin T-shirt, ya shafa turare, ya nufi part ɗin Mommy.
Yana shiga ya rusuna da girmamawa:
“ gd morning Mommy…”
Ta amsa da murmushi mai kama da na mace mai iko “Sadeeq, Daddy zai dawo on Wednesday.” ya gyada kai kuna dan annuri a fuskarsa Mommy ta tsuke fuska nan take da murya mai ƙarfi ta ce:
“Inason ka tabbatar da maganarka da Atika. Wannan ba shawara bace, umarni ne.
Karka manta… ka koreta daga gidan nan saboda hayaniyarta karka yi tunanin ka yi nasara ko ka tsere.
Atika matar ka ce HAR ABADA.” Yana son bude baki, idan akalla ya ce “Mommy—” ta daga hannu cikin masifa “Dakata. NOT even a word. You can go.” ya tsaya yana jin gabanshi ya fadi yayi salati a ransa ya fita daga d'akin kamar wanda ya yi rashin nasara a yaki
7️⃣8️⃣
💔❤️🔥DR SADEEQ ❤️🔥💔
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
BOOK 2
My 15novel comedy love and drama
https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM
THIS BOOK IS DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER ABUBAKAR SADEEQ AND MY LOVELY SISTER AISHATU INDO.......
MORNING UPDATE
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲
BUSSINES GROUP
👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/JjkU7xG4zcWIAvtWRgeFtT
TITLE
Love is a flame that burns bright, even in the darkest night
BARKA DA SHIGOWA SABUWAR SHEKARA
Dr. Sadeeq yana tafiya cikin harbawa, zuciyarsa cike da tunanin Indo murmushinsa ta dabaibaye fuskarsa gaba ɗaya, har sai da ya isa ƙofar part ɗin Kaka.
Ya tsaya ya gyara rigarsa, ya shaƙi kansa da sanyi, sannan ya shigo cikin ladabi:
“Kaka, ina kwana.”
Kaka ta dubeshi, ta yi murmushi tana zolaya:
“Kai Sadeeq yau ka yi kyau kamar sabon angon da aka tayi kwalliya. Me sirrin ne haka? Ko akwai wani abu ne haka Irrin wanan farin ciki?”
Sai ya sosa kai kamar yaro da aka kama da laifi “Kaaaka…” ya ce cikin kunya Ta yi dariya ta girgiza kai sannan ta ce:
“Bar wannan. Indo ce ba da lafiya. Tashi ka duba ta, ka bata magani. Tun safe take cewa ciki na ciwo.”Nan da nan jikin Dr Sadeeq ya yi sanyi.
Ya ji kamar zuciyarsa ta tsaya.
Ya ce da gaggawa “To, kaka. Bari in je yanzu.”
Ya nufi dakin Indo magajin da zuciyar da ke dukan sauri-sauri.
Yana shiga ya ga ta kwance, amma tana ganin sa idonta ya sauka a kansa
Hawaye suka dawo mata fushinta ma ya dawo da sauri.
Tayi maza ta tashi, ta juya gefe, ta kama kwallon baci da mamaki da takaici ya dan matsa kusa da ita da tausayi:
“Indo… ya jikinki?”
Yayinda yake kokarin ta'ba fuskarta
Sai ta fisge jikinta tamkar wuta ce a jikinsa.
Ta kame bakinta, idonta ya kad’a ja, sannan ta sunkuyar da kai, ta ce cikin rawar murya:
“I hate you… mugu. Allah zai sakamin. Wallahi bazan yafe maka ba.”
Dr Sadeeq ya tsaya duuuuurrrr, kamar an zuba masa ruwan sanyi muryar Indo ta sare masa zuciya tamkar wuka.
Ya matsa a hankali yana kokarin zama kusa da ita amma tana ja baya tana kuka, tana girgiza kai kamar wacce aka ci amanarta.
Ya lumshe ido, ya shaƙi numfashi ya ce a hankali “Indo… ki saurare ni…” Amma kafin ya karasa—
Ta daka masa ihu da murya kasa amma cike da zafi:
“Kar kayi kusa dani! Kar ka kara taba ni!! Kai mugu ne! Allah ya isa tsakanina da kai!”
Idanuwan Dr Sadeeq suka cika da takaici, nadama, da tsoro ya kama kansa a hankali.
Kalmar “Allah zai sakamin! Bana sonka!” ta buga masa tamkar wuka mai kaifi.
Zuciyarsa ta tsinke numfashinsa ya ja ya tsaya ya jingina da bango, idanunsa sun yi ja sosai kamar mai shirin fashewa da kuka.
A hankali ya matso gaban gadon, amma ba tare da ya kusanceta da hannu ba — tsoro ne ya rufe shi.
Tsoron ya kara cutar da ita… tsoron ya ƙara bata tsoro… tsoron ya rasa Indo ya durƙusa gaba ɗaya a ƙasa, kamar yaro da ya rasa hanyar kare kansa.
Muryarsa na rawa kamar wanda ake jingina shi da kukan maza:
“Indo… na san na cutar da ke. Na san ban kyauta ba. Amma wallahi ban yi da nufi ba. Ki kalle ni ko sau ɗaya don Allah.”
Ta yi saurin kawar da kai, hawaye na gudana kamar famfo.
Shi kuma ya kai hannunsa kan ƙasan, yana murza yatsunsa cikin nadama kamar wanda yake neman gafara daga ƙasa.
Ya ce da murya mai sanyi amma cike da radiali:
“Indo, bazan iya kwana rana ɗaya ba tare da na ji kin yafe min ba. Ban san me ya same ni ba jiya… na rikice… na kasa tunani… zuciyata ta kamu da wani abu da ba ta taba ji ba.”
Ta daka masa tsawa cikin kuka “Ka yi shiru!! Ka min mugunta! Ka ɗauke min mutunci! kamin Fyade…”ta kasa magana saboda kuka ya tsare mata maƙoshi.
Kai tsaye sai ya jingina goshinsa da gefen gadon, yana cewa cikin murya mai rauni:
“Ki zage ni, ki la'ane ni… duk zan dauka. Amma ki ce min baki tsani ni gaba ɗaya ba, Indo… ko kadan ne. Don gidana ya rikice yanzu saboda rashin jin lafiyarki.”
Ta girgiza kai tana kuka sosai “I hate you…!!”
Ya lumshe ido, hawaye suka cika masa idanu — ba wanda ya taba ganin Dr Sadeeq cikin irin haka Muryarsa ta kasa fita sosai:
“Ki ce komai… banda wannan, Indo. Kar ki ce kina tsanata. Zuciyata ba za ta iya ɗauka ba.”
Ya ɗago idonsa a hankali, ya kalleta da zuciyar mutum da yake murda cikin wuta:
“Na rantse, bazan taba sake cutar da ke ba. Bazan taba matsa miki ba. Ki bani dama in gyara. Don Allah… ki yafe min.”
Kamar zai rushe da kuka ya ce:
“Ki yafe min kafin zuciyata ta fashe Indo… please.”
Kalaman “I hate you” da ta furta har yanzu suna dukan kunnensa, amma sai kalmar da ta biyo baya ta shake numfashinsa gaba ɗaya:
**“Da kana sona ai baxaka min FYADE kawai don kaga bani da gata a duniya…!!”zuciyarsa ta tsaya.
Numfashinsa ya tsaya kamar an gauraye zuciyarsa da wuka da gishiri.
Ya daga kansa a hankali, idanunsa sun cika da hawaye masu raɗaɗi, ba kamar namiji ba — kamar ɗan yaro da aka karya masa zuciya.
“Indo… fyade? Ni?” Ya murza hannunsa a kirjinsa yana neman numfashi.
Zuciyarsa ta buga da karfi.
Cikin murya mai ƙyarƙyawa da rawar baki ya ce “Na fi kowa sanin cewa fyade babbar zalunci ce… ban taba tunanin zanyi abu irin wannan ba. Wallahi… ban yi miki hakan da nufi ba, Indo… ban tursasa ki ba… ban san me ya same ni ba jiya…”
Ta katse shi da kuka mai tsanani:
“Kar ka min karya!! Ina kuka ne da taimako jiya? Ka yi amfani dani saboda bani da gata! Babu wanda zai nema min hakkina. Kai kawai ka gani kana da iko—ka yi abin da kake so!!”
Ta buga masa magana cikin zafin da bai taba gani ba Shi kuma sai ya rike kansa yana girgiza kai kamar mahaukaci:
“Indo… don Allah ki saurare ni. Ba iko nayi amfani ba. Ba zalunci nayi ba. Na rikice ne…”
Ta kara ihu: “Kai mugun mutum