DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   14 / 48

39K to 42K   out of 141.3K words

da ƙiyayya.
Wasu kuma kallonsu na iya ɓata zuciya.


To Indo, ki ɗaga kai da imani, ki ɗaure zuciya da addu’a.
Ki tuna Mama tana kallonki daga sama.
Ki zama abin alfahari ga ta, ba abin kunya ba.
Ki koya da gaske, ki yi karatu, ki zama mai taimakon jama’a.
Kar ki manta — rayuwa kamar wuta ce: idan kika yi wasa, sai ta ƙone ki, amma idan kika koyi sarrafa ta, tana maka haske.


Indo ta sunkuyar da kai, hawaye suka gangaro mata a hankali.
Sai ta ce da murya mai rauni,
“Baba, in Allah ya yarda, zan canza. Zan zama yadda Mama take so. Ban sake wasa da rayuwata ba.”


Mai unguwa ya yi murmushi cikin tausayawa,
“Hakan nake so in ji. Ki tafi ki kwanta lafiya. Gobe sabuwar rayuwa za ta fara — ki fara da addu’a.”


Sai ta tashi cikin nutsuwa, zuciyarta cike da tausayin Mama, tana jin cewa wannan daren ne ƙarshen rayuwarta ta da, da farkon sabuwa.

















NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️🤌


















PG 2️⃣6️⃣






A hanya suna tafiya cikin motar da hasken fitilu ke haskawa ta gefen hanya, Dr Kamal ya kalli Dr Sadeeq da wani murmushin annashuwa ya ce, “Bro, I can’t believe what just happened today! Ka ɗauki village girl kamar yadda ake ɗaukar project .”Dr Sadeeq ya ja tsaki cikin kasala “Kamal, please stop this your wahala. Ba project ba ce, ai taimako nake mata ne. You know how the situation was.”






Kamal ya sake dariya yana girgiza kai, “Taimako fa? Really? Taimako har da secret marriage? Wallahi idan Daddy ya ji, sai ka gane babu abinda ake ɓoye masa. This your ‘taimako’ yana da special feelings wallahi.”






Dr Sadeeq ya kalle shi da murmushi mai sanyi, “You and your imagination. Ka sani ni ba haka nake ba. Girl ɗin nan fa ba ta san komai ba, tana kamar yarinya. All I want is to help her, not to hurt her.”


Kamal ya daga gira, yana zaro ido kamar yana tsokana,“Hmm… Help her ko fall for her? Kai dai kasan zuciya bata da iko. Ka tsaya da ni, zan iya karɓar ta a matsayin maid ɗina ma, idan ka ga baka son wahala.”






Sadeeq ya kalle shi da harara cikin dariya,
“Kamal, you are crazy! Na san kai baka da mutunci wallahi. Ka bar ta lafiya. Ba komai tsakaninmu — kuma ka rufe bakinka kafin na jefar da kai daga mota.”






Dariya kawai Kamal yake yi har sai motar ta cika da nishadi, yana cewa,
“Dr Sadeeq da village wife — perfect combination! Wallahi zan saka a TikTok idan ka aure ta da gaske .”
Dr Sadeeq ya sake ja tsaki,“Kai dai kawai ka cigaba da dariya, amma ni dai na gaji. Let’s get to the hotel and rest — I’m starving.”
Kamal ya “No problem, my chief. Na san kana bukatar peace of mind — da kuma hot shower. Haba ai wancan abincin da Indo ta zuba a jikinka zai iya kashe kowa.”






Duka suka yi dariya sosai har sai Dr Sadeeq ya ce,“You’re mad, Kamal! Wallahi idan na tuna yanda miyar kuka ta manne min a riga sai dariya nake yi. That girl is trouble in human form.”
“And you like trouble,” Kamal ya katse shi yana dariya.






Daga nan suka shiru, sun gaji, sai motar ta ci gaba da tafiya cikin natsuwa har suka iso wani hotel a inda suka sauka ,cikin nutsuwa, suka shiga ciki, sukaye order abinci ,, ,


Dr Sadeeq ya cire rigarsa yana jin gajiya sosai, ya murmusa yana cewa cikin zuciya “Tomorrow is another day... Indo — ke dai kin fara zama jarabar zuciyata.”






Sai ya wuce bathroom, ya yi wanka mai sanyi, ya fito ya ci abincin dare da Kamal, daga nan suka kwanta duka suna jin daɗin nutsuwar dare — gajiya da dariya na haduwa a cikin hotel ɗin da hasken fitila ke launi





A Safe Ta Fara Tafiya...


Tun da safe, rana bata fito sosai ba, sararin samaniya har yanzu yana da ɗan duhu.
Dr Sadeeq ya fito daga ɗakinsa cikin rigar marron casual shirt da wando black jeans, yana ɗan murmushi mai cike da gajiya.
Ya juyo ya kalla Dr Kamal, wanda ke tsaye gaban mota yana zuba perfume kamar zai je dinner.
“Wallahi dude, tafiyar nan akwai wahala,” inji Dr Sadeeq yana jan dogon numfashi.
“Amma ai dole, ka hanamu kama Flight Allah yasa ma muna tare da driver muna rarraba driving in .”






Kamal ya kalle shi yana dariya yana daga gira.
“Ka bar wannan damuwar, next time mu shiga flight kawai. But for now — your bride deserves to see the road, ai ta ga gari, ta san me ake kira da tafiya.”
Dr Sadeeq ya kalle shi da faɗa mai taushi.
“Seriously, ka daina cewa mata ta, please.”
Kamal ya yi dariya sosai, yana cewa, “Okay sir! Amma dai wallahi you sound jealous.”Sadeeq ya girgiza kai yana murmushi,
“Uuhh! You’ll never change, Kamal.”






Suka yi dariya tare, suka shiga mota. A zuciyar Dr Sadeeq yana jin wata irin nauyi — tsakanin alhaki, tausayi, da wani abu mai kama da jinƙai mai haɗe da ƙauna.


Motar ta kama hanya cikin natsuwa, iska tana busa ta gefen titi.
Sun isa kofar gidan mai unguwa inda Indo take Da suka isa, sai suka tsaya a gefe.


Indo na tsaye tare da su Dijje da sauran matan. gidan kukan rabuwar su ya cika gidan.
Idonta ya kumbura saboda kuka, ga ƙamshin turaren Mama da ya rage a dakin ta har yanzu yana cika zuciyarta da kewar da bata da misali.


Dijje ta rungume ta tana kuka tana cewa,
“Indo ki kula da kanki wallahi, kinji? Ki tuna Mama kullum tana ce mana ‘ki zama mai gaskiya’. Ki yi karatu ki zama likita kamar yadda take fata.”
Indo ta share hawayenta tana murmushi mai rauni,
“In Sha Allah, Dijje. Zan zama likita, zan zama Indo da Mama ke fata.”
Mai unguwa ya fito daga cikin gida cikin riga da hula, yana kallon su da murmushi mai cike da tausayi. “Indo, ki kula da kanki. Wannan tafiya ba kamar sauran tafiya ba ce. Karki manta addu’a. Ki zama yarinya mai ladabi, ki kaɗa da gaskiya, ki guji hayaniya. Mama ta yarda da kai, yanzu mu ma zamu yarda.”






Sai ta durƙusa ta ce, “Na gode Baba.”
Kamar wata mutuminyar arziki




A wannan lokacin, Dr Sadeeq ya tsaya gefe yana kallonta cikin shiru, zuciyarsa na bugawa da sauri.
Wani abu mai nauyi ya tsaya masa a wuya kamar kalmar da yake so ya faɗa amma yana jin bai dace ba.


Dr Kamal ya tsokano shi da ƙaramin elbow, yana faɗin, “Guy, stop staring, you’re scaring her.”
Ya yi murmushi ya ɗan yi ƙasa da kai, yana mai cewa a hankali,“I’m not staring, Kamal. I just… I just hope she’ll be fine.”






Suka gama sallama, Indo ta ɗauki ɗan ƙullin kayanta – akwatin Mama, zaninta ɗaya, da ɗan jaka ƙanana mai ƙunshe da hoton Mama.
Ta ɗan waiwayi gidan kafin ta shiga mota, hawaye na sauka a kumatunta.


Ta zauna a baya tare da Dr Sadeeq, yayin da Dr Kamal da driver ke gaba.
Motar ta kama hanya. Indo tana kallon titi ta taga duwatsu, gonaki, da ƙananan yara suna wasa da ƙwallo a bakin hanya.
Wani abu ya motsa mata a zuciya — sabuwar rayuwa da bata san ta yaya zata kasance ba.


Dr Sadeeq ya kalleta cikin madubi daga gaba, yana cewa da murya mai taushi, “Indo, kin ci abinci kuwa?”
Ta girgiza kai a hankali “A’a, bani ci komai ba.”


Sai ya ce, “Don’t worry, when we get to the hotel za ki yi wanka, ki ci abinci, before mu wucce.”
Dr Kamal ya ce da dariya daga gaba,“Wanka first, abinci later — that’s doctor’s order!”


Dariya suka yi gaba ɗaya, har Indo ma ta yi murmushi karon farko Dr Sadeeq ya lura da murmushin,


Suka isa hotel ɗin da sauri ya buɗe musu ƙofa. Indo ta fito da ɗan tsoro, tana gun
Kamar yadda bata taɓa ganin irin zuciyarta ta buga da mamaki da tsoro lokaci guda.


Dr Sadeeq ya ɗan tsaya kusa da ita ya ce da tausayi:
“Ki shiga ciki, Indo. Ki yi natsuwa, ba za a cutar da ke ba. Wannan gida ne na lafiya.”
Ta ɗan gyara zaninta ta shiga a hankali, kamar wadda take cikin mafarki




Suka shiga ciki.
Hotel ɗin yana sheƙi, ƙamshi mai sanyi ya cika wajen, kalar furanni a gefe, da air-conditioner na busa iska mai sanyi.


Dr Sadeeq ya ɗauko small bag daga hannun Kamal, ya nuna mata ƙofa.
“Indo, ki shiga ki yi wanka. Ga kayan da za ki sa anan cikin jaka. Bayan haka, sai mu tafi — akwai tazara zuwa Abuja.”
Indo ta kalli kayan cikin mamaki — rigar riga da doguwar wando, sabbin takalma, da mayafi mai launin shudi.
Ta ɗago kai ta kalle shi cikin ladabi,
“Na gode, Dr Balarabe.”Sai ya yi murmushi mai sauƙi,“Ki daina kirana Dr Balarabe. Kawai ki ce ‘Doctor’. Kin ji?”Ta ɗan yi shiru, ta ce da ƙasa-ƙasa,
“To... Doctor Balarabe”






Daga nan ta juya cikin natsuwa ta shiga cikin ɗakin wanka.
Dr Sadeeq ya tsaya yana kallon ƙofar da ta rufe a hankali, zuciyarsa na bugawa — wani abu da bai taɓa ji ba yana tasowa a cikin sa.


Dr Kamal ya bishi da ido yana murmushi,
“Hmm… doctor, you are falling already.”






Ya ɗan yi murmushi cikin sanyin murya,
Sai Dr Sadeeq ya kalle shi da tsawa mai cike da wasa, “Kamal! Shut up before I throw you out.”
Kamal ya ɗan yi dariya ya ce, “Just don’t lose yourself in the process.”
Sai suka yi shiru, kowannensu cikin tunanin sa, yayin da a ɗakin wanka Indo ke kallon bayangida kamar ba gun ruwa ,tasa hannu ta taɓa nan ta taɓa nan tana danna kan shower sai ga ruwan zafi da ɗan ƙarfin sa ashe shower ɓangaren ruwan zafi ta latsa wani giggittacen ihu ta fara tsalaawa kamar ana cire mata idon ta,


Kallo kallon sukaye da Kamal,yace " go and check out Allah yasa ba zamewa taye ba cewar Dr SADEEQ yana bude toilet in Yayi tsayin daka a gaban toilet ɗin yana kallon yadda Indo ke rige-rigen rufe jikinta da tawul, idanuwanta cike da tsoro da rashin fahimta. Ruwan zafi har yanzu yana ɗigowa daga gefen bango,


"Hummm ke rufe bakin ke kafin ace ana yanka wuyan ke anan '" yana magana ko kallo na bata ishishe ba ya kashe ya haɗa mata kayan kamshi da ruwan ɗumi yana gauraye da ƙamshin turaren da Dr. Sadeeq ya zuba mata a cikin bathroom ɗin kafin ya nuna mata yadda ake amfani da komai.


Ya dafe kansa cikin rashin yarda, murmushi ƙarfin hali na fitowa daga bakinsa.
“Indo, Indo…” ya faɗa yana girgiza kai. “Wannan duniya ba ta gama da ke ba. Kin firgita saboda shower? Wannan ai ba ruwan sama bane, ruwa ne na heater — wanda ke taimaka jiki ya samu natsuwa.”
Indo ta kafe shi da ido, hannayenta biyu na rike tawul kamar za ta gudu.
“Toh ai ruwa mai zafi ne, sai naji kamar ana kona ni! Wallahi naji kamar ruwan jahannama ne!”






Sai Dr. Kamal daga waje ya kwalla kira cikin raha:
“Doctor, ka duba ko ba aljani bane ke bata tsoro! Mun fara tunanin ko tafiyar nan sai ta koma drama!”
Dr. Sadeeq ya harare shi daga bakin ƙofa, yana maida numfashi cikin gajiya.
“Kamal, please… kai dai ka shirya motar, we’ll be down in ten minutes.”


Kamal yayi dariya yana juyawa, yana faɗin,
Don“Alrght Mr. Gentleman, amma gaskiya ina tausayinka wallahi — first experience da mace daga kauye ba wasa bane.”






Sadeeq ya juya yana kallo Indo da ta zame tamkar yarinya a sabuwar duniya. Idonsa ya tsaya kan kwandon kayan mata da yake gefe — sabulun lux, shampoo, body lotion, towel mai launin milk da turare.
“Ki ji da kyau Indo,” ya ce a hankali, muryarsa cike da nutsuwa da tausayi. “Ki wanke jikinki da wannan sabulun, Bayan kin gama, ki saka wannan riga mai launin sky blue. Muna da tafiya mai nisa, don’t waste time.”






Indo ta ɗan haɗe gira, tana kallon kaya kamar an kawo mata kayan sarauta.
“Ni zan iya saka su? Ba sai an gaya min yadda ake ɗaure wannan ba?”
Yayi murmushi, yana ɗan ɗora hannunsa a kan ƙofa.
“Ki saka kamar yadda kika saba, difference ɗin kawai shine su da kyau — sun fi waɗanda kike amfani da su a gida. Ki tafi a hankali, ki kalli kanki a mirror, zaki ga kin canza.”






Da haka ya fita, yana rufe ƙofar a hankali.
Ya jingina da bango na corridor ɗin, yana sauke numfashi. Kamal yana zaune a gefen kujera yana danna wayarsa, sai ya ɗago yana dariya.
“Bro, gaskiya dole ka rubuta littafi: ‘From Village to Shower — My Wife’s First Battle’.”






Sadeeq ya harare shi, amma daga ƙarshe ya yi dariya ma.
“You’re crazy, Kamal. Amma gaskiya, yau na gane difference tsakanin textbook wife da real wife.”
“Haha!” Kamal ya kwashe da dariya. “Wallahi gaskiya ka faɗa. Amma dai tunda ka zabi ta, ka shirya training. Gaskiya Indo ta buƙaci orientation.”






Bayan mintuna goma sha biyar, ƙofar bathroom ta buɗe a hankali.
Indo ta fito, ta sanya rigar sky blue wacce ta matuƙar amsa jikinta. Gashinta yana ɗan ɗigowa da ruwa, fuskarta ta yi fresh tamkar sabuwar fure bayan ruwan sama.
Dr. Kamal ya buga hannu yana dariya.
“Waaah! Look at our new bride! Dr. Sadeeq, this transformation deserves an award!”


Indo ta sunkuyar da kai tana murmushi, hannunta na murza mayafin da ta ɗaura a wuya.
Sadeeq ya ɗan kalli gefe, yana murmushi cikin sirri. “Alright, that’s enough. Indo, mu tafi.”






Yana miƙa mata jaka ɗaya, yana Suka fito zuwa waje, iska mai sanyi ta bugi fuskarta, tana lumshe ido da jin daɗin sabon yanayi.
Motar ta tsaya a bakin kofar hotel, direba na jiran su.
Kamal ya buɗe ƙofa yana cewa,
“Madam Indo, please after you.”


Sadeeq ya zuba masa harara mai cike da annuri “Kamal, stop that!”


“Haba mana Doctor, ai ba laifi bane. Kawai muna ganin yadda kake kula da matarka kamar princess.”




Indo ta zauna a baya da Sadeeq, yayin da Kamal da driver suka zauna a gaba.
Motar ta tashi a hankali, iska mai ɗauke da ƙamshin yashi ta cika cikin mota. Indo ta jingina da kujerar mota, zuciyarta tana bugawa da sabon farin ciki da ɗan tsoro.


Kamal ya juyo da dariya.
“So Doctor, what’s next? Bayan wannan tafiyar, honeymoon in Egypt or Dubai?”






Sadeeq ya yi dariya kawai.“Kamal, ka bari mu kai gida lafiya tukunna.”
“A’a, gaskiya ni zan fara lissafin tafiyar soyayya. Kai da wannan yarinyar, kai fa ka shiga wahala. Amma wallahi za ka yi missing abinci irin nasu.”


Indo ta ɗago tana kallon sa, batajin mai suke faɗa sai dai kawai taye murmushi






Sadeeq ya ɗan lumshe ido, murmushi yana bayyana a fuskarsa. A zuciyarsa yana tunanin cewa lallai, wannan tafiya za ta zama wata sabuwar rayuwa ta gaskiya — daga ƙauye zuwa birni, daga jahilci zuwa wayewa, daga ruɗani zuwa soyayya.


Motar ta cigaba da tafiya a kan hanyar da rana ke fara faɗuwa, yayin da Indo ke jingina a gefe tana kallon waje, tana murmushi cikin nutsuwa. Wannan rana ce da ba za ta manta ba har abada.




NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️🤌












PG 2️⃣7️⃣








Cikin mota, hanyar Abuja duk maganar da su Dr. Sadeeq da Dr. Kamal suke, Indo ko da ƙwarai bata jin komai. Harshen su na Turanci kamar waka ne a kunnenta — sai murmushi kawai take yi tana kallon su, tana dariyar jahilci a zuciya. Ita dai taje ne don an ce za tafi makaranta — bata ma san cewa matar aure ce a zahiri ba.


Dr. Kamal ya juyo yana dariyar zolaya,
“Hey Doctor! your wife no even understand English o!”Sai Dr. Sadeeq ya tsare shi da ido,“Just shut up Kamal.”
Suka yi dariya duka biyu. Indo kuwa sai kallon su take yi, ta ce a ranta:“Wannan uban wayo da murya mai daɗi, Allah yasa ya chigaba da magana Inason wannan ƙamshin nasa.”






A haka suka ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da rana ta fara sauka.
Yayin da suka wuce Kaduna iska mai ɗan sanyi ta ratsa cikin motar. Indo ta jingina kai, sai bacci ya fara ɗaukar ta.


Dr. Kamal ya waiwayo daga gaba yana murmushi, “See your wife don sleep like baby.” Dr. Sadeeq ya ce cikin murmushi,“She’s tired. The village stress is too much for her.”






Har suka shige cikin hanyar Kaduna zuwa Abuja, baccin Indo ya ƙaru tana bacci tana minshari da ƙarfi, irin wanda sai ka ji kamar ana busa ƙaho.
Dr. Kamal ya rufe baki yana dariya, “Kai Sadeeq wallahi this your wife get generator for nose o!”






Dr. Sadeeq ya harare shi, “Stop that nonsense Kamal!” Indo ta motsa ta juyo tana faɗin cikin bacci,
“Dr Balarabe... kada ka tafi... kada ka barni...”
Zuciyar Dr. Sadeeq ta buga – “me take faɗa haka?”
Amma kafin ya furta, tuni ta sake nutsewa cikin bacci, kai nata akan cinyar sa.
A hankali ya ɗan gyara kanta, yanda wuyanta ya kwanta lafiya, yana kallonta da tunani mai nauyi. Kamal kam, yana murmushi a hankali yana faɗin “Oga, love don start o.”






Sai Sadeeq ya kalle shi da fuska a daure, “You never get sense Kamal.” a haka suka isa Maitama, Abuja da ƙarfe 4:00pm.
Garin na cike da hasken rana, motoci suna cike da hayaniya da ƙamshin birni. Indo ta farka tana zazzare ido kamar ta shigo Aljanna — ta kalli titunan da tsabta, gine-gine masu haske, ta ce cikin mamaki:“Kai, wai nan ne Abuja?”






Dr. Kamal ya yi dariya sosai, “Yes my sister, welcome to city of money.”Ta kalli Dr. Sadeeq tana murmushi, “Kai Dr Balarabe, nan zakayi min makaranta kenan?”






Shi kuwa sai ya ɗan juya kai gefe don ɓoye murmushin da ke son fito masa.
Cikin zuciyarsa kuwa, kalmomi suka haɗu — “Yanzu me nake shirin shiga? me zance da Hajiya idan ta ganta?”
Zuciyarsa ta cika da bugun doom doom doom.


Dr. Kamal ya ce da shi cikin nutsuwa,
“Relax, is normal bro. Ka kwantar da hankali. Ka bar komai a hannuna. Muje mu musu bayani — in Hajiya ta ki, to sai mu ce ta zauna a maid room har sai komai ya daidaita.”






Sadeeq ya jinjina kai,“You’re right.”






Ya kalli Indo wacce ke ta dariya tana latsar gilashin motar tana kallon mutane

14 / 48