DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   22 / 48

63K to 66K   out of 141.3K words

ɗauki akwatin ta tana dariya a zuciya da ɗan firgici mai ɗan barkwanci. Ta tafi zuwa part nasu na maid, tana murmushi:
“Wannan Dr. Balarabe, wallahi… ya fi ban tsoro da barkwanci a lokaci guda!”


Dariya mai laushi ta biyo bayan ta, a hankali ta sake juya kanta ta duba dakin sa—amma bai sake kallonta ba, yana gyara kansa da natsuwa, yana mai juyawa cikin tunani








Laila ta shigo part na Dr. Sadeeq, sanye da skirt mai ɗan tsawo da riga mai kyau, guntun hula a kan kai, gashinta a waje yana sheƙa da iska, yana ba ta wani irin kamannin na stylish. Ta ɗauki aikin da Mommy ta ba Dr. Sadeeq, tana kallon dakin cikin kulawa da sirrin aiki.


Sai idonta ya kama fitowar Indo daga dakin, tana ɗauke da akwatin mai kyau da tsada, tana tafiya da nutsuwa amma da ɗan jaruntaka—kamar wadda ba ta da tsoro ko kunya. Laila ta dinga kallonta daga kai har ƙafa, idonta na bibiyar kowanne motsi da kamshin kayan da Indo ta kawo. A zuciyarta ta tabbatar da cewa wannan karamar yarinya, wadda aka tashe daga kauye, ba ta da tsoro ko kunya—amma akwai wani abu mai ban tsoro da ƙarfi a cikin halinta, Laila ta furta mata
“Jar uba waya… baki, wanan kayan jikin ke ne? Ga wani kamshi… ta taɓa Indo ta tabbatar—ittace! Ina tambaya, ke, sata ke kazo ki ɗauko akwatin nan fa?”


Indo ta kalle ta kai tsaye, idonta cike da natsuwa da ɗan ƙyama mai kyau, amma tana tsayawa da girmamawa, ba tare da jin tsoro ko kunya ba. Tashin kauyen da ke cikin ta ya bayyana a fili—ba wani matsin lamba, ba wani tsoro, kawai jaruntaka da ƙarfin hali.


A gefe kuma, Laila, wacce kanwar sace ce, tana da ɗan tsana a ranta game da Indo. Sun tsani Indo saboda ta fito daga kauye, marainiyyar mara gata, kuma talakaa ce. Amma duk da haka, akwai wani ƙaramin sha’awa da mamaki a cikin kallonta, musamman ganin yadda Indo ke tafiyar da kanta cikin nutsuwa da jaruntaka........








#₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦₦
Da gudu-gudu Laila ta juya tana kwaɓe baki, ba tare da ta isa ko ta sake zungurar Dr. Sadeeq ba—saboda abinda ta gani ya girgiza mata zuciya Indo? fa akwati? Mai tsada?
Sannu a hankali take cewa cikin ranta:
“Anya wannan yarinya ba ta fara samun gata a gidan nan ba kuwa?”


Ta fisge kai da sauri, ta yi tafiya irin ta mutanen masu cike da matsayi, ko da yake zuciyarta ba ta da natsuwa. A wucewar Indo kuwa ta wuce cikin nutsuwa, bata ma tsaya kallonta ba, kamar wadda aka saba ganin ta a irin wannan wuri—haka ta kara ba Laila haushi sosai.


Indo na sauka zuwa part ɗin su, zuciyarta cike da wani sabon annuri, irin wancan farin cikin da mutum ba zai iya boyewa ba. Da zarar ta shiga ɗakinsu, ta rufe ƙofa da sauri, kamar wadda ke boye wani asiri, sannan ta zauna a tsakiyar matress tamkar yarinya da aka sake mata sabuwar baby doll.


Ta ja akwatin kusa da ita kamar wanda daga sama aka saukar masa da aljannar duniya. Hannunta yana rawa—ba saboda tsoro ba—amma saboda murnar da ta fi ƙarfin zuciya.


A hankali ta buɗe akwatin…


Sai fara’a ta cika dakin.


“Allahuuu… waaaaiii!! Ta faɗa da wata murya mai kama da tsalle-tsalle.
Kayan ciki sun yi mata tsauri kamar ƙayn daga kasashen waje Wando da riga iri-iri—na zamani, masu sheƙi Dogayen riguna na daidai shape ɗin ta. Towel mai laushi kamar gashin jariri. Mayukan shafawa masu ƙamshi irin waɗan da bata taɓa ganin a kauyensu ba.
Mayukan wankan jiki masu ɗauke da rubutun Natural Glow, Shea Butter, Whitening Scrub
Sai cream mai sheƙarwa, wanda Indo ba ta san me ake nufi da shi ba—amma kamshi ya gama bayyana mata cewa matan birni na amfani da shi.


Ta ɗaga cream ɗin, ta ƙanshe shi sosai, ta rufe idanu:
“Daaagoooooo… kai! Lallai Uncle Kamal yayi min kokari. Allah ya saka masa… Allah ya yi masa albarka… Allah ya kara masa kuɗi…”


Ta yi addu’a kamar wata tsohuwa, tana maimaitawa tana godiya.
Ta ɗauki doguwar rigar da ke gefe, ta jingina a jikinta tana murna:
“Ni kaɗai? Indo? A’a akwai dalili. Wannan dai babbar kyauta ce…”


Ta sake buɗawa ganin akwai Body Mist, ta feshe kanta:Fushhhhhhhhh…Kamshin ya tashi ya cika ɗakin.


Sai ta juya cikin dariya:
“Ahhhh… kai ni kam, yanzu ko Mommy ta ganni za ta ce Indo ba Indo ba…”A waje kuwa, Lami na bi ta da kallo daga window:
“Hmmm… wannan yarinyar, idan Mommy ta gano abinda ake mata kuwa?”
Amma Indo ba ta san da wani abu ba.
Ba ta san cewa kyautar da ta zo da ita tana iya tayar da rikici a gidan nan ba.
A gare ta kyauta ce ta gata ta kulawa ta farinciki Ta ci gaba da buɗe kayan tana murna tana rawa.




Laila ba ta tsaya ko da minti ɗaya ba. Da gudu ta shige babban falon Mommy—falon nan mai sheƙi da ƙamshi irin na mata masu kudi, inda kowane bangon dakin yana ɗauke da frames masu tsada. Mommy kuwa zaune take cikin wata lace mai launin goro wacce ta yi mata kyau fiye da misali—kamannin mace tagari, mai gata, mai mulki da nutsuwar manyan mata.


Idanuwanta na kan wayarta, tana danna screen cikin kwanciyar hankali kamar ba abin da zai tarwatsa mata natsuwa.
Amma Laila na shigowa da numfashi na hawa sama da kasa, Mommy ta ɗago kai cikin nutsuwa “Lafiya Laila? Me ya faru haka?”
Laila ta dafe ƙirji saboda gudu, ta kama hannun Mommy kamar wadda ke kawo gaggawa:
“Mommy wallahi… Mommy wannan yarinyar… yarinyar da Brother Sadeeq ya kawo gidan nanIndo—kin san ta?”
Mommy ta ɗan runtsa ido, tana kallon Laila ba tare da wata firgici ba:
“Me kuma tayi?”Laila ta huro iska kamar wadda ta sha wuta:“Mommy kin san yanzu na ganta a dakin Brother Sadeeq fa!”
Mommy ta tsaya cak har numfashinta ya yi nauyi ɗaya.Idanunta suka ɗan murɗe.


“A dakin Sadeeq?” ta sake tambaya da murya mai zurfi, wadda ke nuni da cewa zuciyarta ta fara tashi.


Laila ta ɗaga kai da gaggawa:
“Wallahi Mommy! Na ganta da idona! Ba wai kawai ta fito daga dakin ba—akwati ne a hannunta. Akwati mai tsada. Kuma kaya a jikinta… Mommy kayan sun fi na kowane maid kyau! Wannan ai kashe mata kuɗi yake yi!”
Daga maganar nan, kamar an jefa ƙanƙara a cikin zafin Mommy.
Ta rufe wayarta a hankali—amma cikin nauyin da ke nuna cewa ranta ya jiƙe da bacin rai.
Idanuwanta suka yi kauri kamar sila.
Mommy ba ta yi ihu ba.
Ba ta yi masifa ba.
Sai dai kwanciyar zuciyarta ta gushe nan da nan Ta kira Sadeeq kiran farko: Busy ya sake kira busy na uku ma bai ɗauka ba.
Ta lumshe ido, ranta ya ƙara murɗewa cikin takaici mai zafi.
Ta miƙe tsaye ta ɗauki wayarta, ta ɗauki glass ɗin ruwa ta ajiye gefe “Ina ta inji?”
Laila cikin murna marar boyewa:
“A sashen maids Mommy. A dakinsu.”


Mommy ta juya cikin sauri kamar wadda aka jawo mata igiyar zuciya.
Kafafunta suna dukan tiles ɗin falon kamar karar takalmi na fushi.
Kallon Laila kuwa ya nuna mata ta biyo—kamar wata ƙaramar ministresa wadda ta bayar da rahoto.
''Sukayi tafiya har part ɗin maids—
kafin Mommy ta isa, zuciyarta ta cika da tambayoyi:


“Me ya hada shi da yarinyar kauye?”
“Me take yi a dakinsa?”
“Har zai fara kashe mata kudi a bainar mutane?”
“Anya wannan yarinyar ba ta fara samun gata ba?”Har suka iso bakin ƙofar sashen maids.
Mommy ta tarar da zuciyarta ta ƙulle.
Bakin ta ya matse.Hannunta ya soma rawar bacin rai.













DR SADEEQ


MY 15 NOVEL ROMANTIC LOVE COMEDY'S DRAMA


4️⃣8️⃣





Lami maid ta hango Mommy tun daga nesa rigid face, tsayayyen tafiya, da irin murƙushe-goro attitude ɗin da ke nuni da cewa akwai tashin hankali yau kanta ya yi nauyi, zuciyarta ta faɗi.
a ranta ta ce “ yau Indo ta shiga uku. Wallahi yau akwai bori idan ya ƙi fita.”
Mommy ta ƙaraso gabanta tana huci kamar mace mai shirin ɗaga ministan gida.
Ta tambaye ta da murya mai ƙarfi:
“Ke Lami, ina kofar yarinyar nan—waccan jahilar Indo?”


Indo kuwa a ciki, da take jin sautin ƙafafun Mommy a tiles, ta ɗan leƙo ta gefen labulen tagarta, ta ga takalman Mommy masu sheƙi.
Nan take ta ja da baya ta murɗa baki “Tooo… yau ga rigima.”Lami ta nuna dakin Indo da yatsarta tana rawar jiki Mommy ta matsa gefe kaɗan, tana jiran a buɗe Lami ta yi hantara ta buga kofar: “Indo… ki buɗe. Mommy ce take neman ki.”
Indo ta amsa da murya cikin iska, kamar ba ita ake nema ba “Waye?”


Kafin Lami ta ce komai, Mommy ta ciro murya, mai kaifi, mai iko:
“Ni ce MOMMY ke buɗe nan yanzu don uwar ke .”Indo ta yarma dariya a ciki, sannan ta yi magana cikin ƙauyanci mai nauyi:


“To don zan buɗe? Wallahi kar wanda ya sake zagin Mama na. Ba’a zagin ta!na yafe, amma sai na rama!”Lami ta rufe baki da sauri.
Mommy ta kasa gasgata jin kalmomin nan.
Idanunta suka faɗa da mamaki.


“Subhanallah! Wace irin yarinya ce wannan Dr. Sadeeq ya kawo mana gidan nan?”ta matso gaba, ta yi murya mai nauyi
“Ke Indo! Ni kike yi wa irin wannan zancen? Kin san da wa kike magana kuwa?”


Indo tayi tsaki a ciki tana share gashin kanta:


“Nicce nan Indo kuma wallahi… wallahi ba zan buɗe ba! Har sai Dr Balarabe yazo. In ba shi ba, ba wanda zai shigo ɗakinan ”Mommy ta ja dogon numfashi.
Ta ware ido.
Ta yi murmushi mai ba da tsoro—murmushin uwa mai gata da ta saba ganin mutane suna durƙusawa.“Lallai yau na ga abinda ban taɓa gani ba. Yarinyar ƙauye… tana ce min ba za ta buɗe ba? To mu gani.”
Lami kuwa a gefe tana kame baki, tana cewa a zuciyarta “Kai Indo… kin mutu yau.”




Mommy ta zagi ta cikin haushi da tsawa mai ƙarfi, idanuwanta na walƙiya kamar za su fitar da harshenta daga bakin ta:
“Uban me ya kaike dakin yaro na?! Wallahi yau sai na tashi tsaye na kore ki daga gidan nan!”


Indo kuwa, a jikinta akwai ƙaramin girma da ƙarfin hali, ta ɗago kai cikin nutsuwa tana furta “Ni dai sako kawai na karɓa, Mommy ba abin da nayi laifi ba.”
Mommy ta ɗan ja numfashi, ta kalli Laila da idanu masu zafi: “Laila! Wuce yanzu! Ki je dakin Dr. Sadeeq. Yau saiya fitar min da wannan jakar gidan nan!”


Laila, da dan firgici da tsoro a zuciya, ta yi saurin juya kanta ta tafi cikin sashi mai saurin motsi kamar wacce za ta buga rekodi a Olympics. Tana zuwa tana kallon Dr. Sadeeq da idanu masu tambaya:
“Brother… Mommy na kirar ka a part na maid, yanzu kazo ka fitar da wanan wawiyar gidan nan…”


Dr. Sadeeq a gefe guda, yana zaune cikin tsantsar rashin jin daɗi da ciwo a ciki, ya ɗan ja hannun kansa yana tunanin:
“Allah ka bani hakuri… yanzu me ya faru a part na Indo? Ko ta kwana a gunna jiya ne? Wai ina Indo a cikin wannan rikicin na gidan nan?”


Cikin sauri, ya tashi daga kujerarsa, ya ɗauki jallabiyar sa, yana daɗe da tunanin yadda abubuwa suka rikide haka cikin ƙanƙanin lokaci. Duk da firgitar da ya fara ji, zuciyarsa na buga da sauri kamar wacce take jin tsoron abinda zata tarar a part na Indo.


Yana tafiya cikin ɗan shiru da hankali, yana mai lura da ko wane motsi zai iya faruwa. Idanunsa sun hade da tunanin yadda za a warware wannan rikicin, yana da hankali sosai, amma a zuciyarsa akwai ɗan damuwa, da kuma irin sha’awar ganin Indo lafiya da natsuwa.


“Laila, me ke faruwa?” ya furta cikin murya mai ɗan tsanani, amma a gefe guda a hankali, kamar yana ƙoƙarin samun gaskiya ba tare da tashin hankali ba.


Laila ta ɗan goge hawaye a idonta, sannan ta fara magana da sautin ƙasa, tana jin tsoron abin da zai iya faruwa:
“Ke… gaskiya… Indo ne a dakin ka. Ta fito da akwatin nan… sai na gaya wa Mommy mu ka zo nan…”


Dr. Sadeeq ya ɗan ɗaga hannu, ya ɗan nufi baya, ya faɗi cikin firgici da mamaki:
“Oh my God…”
Ya ɗan durƙusa, zuciyarsa na cike da haɗe-hɗen tsoro, mamaki da ɗan farin ciki—amma ya bar Laila a bayansa, yana mai shan numfashi da sauri, yana tunanin yadda zai shawo kan wannan yanayi cikin natsuwa.




Yayin da Dr. Sadeeq ya isa, ya hango Mommy cikin tarzoma, fuskarta cike da ɓacin rai da tsanani. Ta hurɗe hannu, tana kira:
“SADEEQ! Zo nan ka fitar da yarinyar nan daga gidan nan ko na ci ubanta!”


Dr. Sadeeq ya ɗan ɗaga hannu cikin ladabi, ya yi ƙoƙarin natsar da kanta:
“Mommy, ki yi haƙuri… I’m sorry… mu tafi part nake… ba girman ki bane zuwa nan…”


Amma fuskar Mommy cike da tsananin bacin rai, idanunta na kai ga Dr. Sadeeq, zuciyarta ta cika da fushi:
“Amman, Ina tsananr Indo! Ta mata yawa a zuciyarta. Lallai Indo ta fito, sai ta fuskanci duka kuma ta bar gidan nan!”


Dr. Sadeeq ya ɗan yi ajiyar zuciya, ya ɗauki numfashi mai zurfi, sannan ya fara magana da murya mai laushi amma mai ƙarfi:
“Is okay, Mom… za mu warware wannan a hankali.”


Ya yi nisa a hankali zuwa wajen Indo, yana ƙoƙarin rarrashin Mommy daga tsananin fushi. Indo, tana cikin tsoro, ta dan sassauta hannu da kafarta, amma idanunta sun kama Dr. Sadeeq ta window—cikin hankali tana kallon yadda yake magana da Mommy.


A gefe kuma, Laila ta tsaya bakin kofar, idonta cike da mamaki da bakin daɗin faɗan da aka yi. Ta ga irin kulawa da natsuwar da Dr. Sadeeq ke yi wajen rarrashin Mommy, tana tunanin yadda wannan yarinya ta kauye zata iya jan hankali cikin gidan nan.


















4️⃣9️⃣💥5️⃣0️⃣






Dr. Sadeeq ya ja Mommy hankali zuwa part nata, yana matse hannunta a hankali, amma cikin ladabi da kulawa—irin matakin da za ka ga yaro mai tarbiyya zai ɗauka yayin da yake son karfafa fahimta ba tare da tashin hankali ba. Ya sunkuya da hankali, ya yi murmushi mai laushi, sannan ya fara furta kalamai a hankali:


“Mommy, ki saurara… ki ɗan zauna, kada ki firgita. Ni zan bayyana komai a hankali.”


Mommy ta ɗan ɗaga idanu, fuskar ta cike da tsanani, amma har yanzu tana sauraron sa, saboda a zuciyarta ta san cewa akwai wani iko mai zurfi da nutsuwa a cikin kalmomin sa—ba kamar duk wanda ke kai mata magana da tsanani ba.
Dr. Sadeeq ya matsa kusa, ya ɗauki hannu daya na Mommy a hankali, ya riƙe shi, yana kallonta cikin idanuwa masu cike da hankali da ladabi “To… me ya kai Indo dakin sa? Kuma a ganta da kayan da ake ganin masu tsada sosai?” Ya ɗan ɗaga murya, amma cikin ladabi da nutsuwa, kamar likita mai hankali wanda ke son bayani a hankali, ba tare da tada tashin hankali ba.
Mommy ta ɗan ja numfashi, tana jin wasu abubuwa sun ɗan sauƙaƙa a zuciyarta, amma har yanzu akwai tsanani a fuskar ta. Ta furta da ɗan ƙarfi:


“Amman… Dr. Sadeeq, wannan ba zai yuwu ba! Ta shiga dakin ka, ta fito da irin waɗannan kaya masu tsada… ba zan iya fahimta ba.”


Dr. Sadeeq ya ɗan ja numfashi, ya ɗauki lokaci kaɗan yana gyara muryarsa, sannan ya yi murmushi mai laushi, yana kallonta cikin kulawa da nutsuwa mai zurfi:


“Mommy, ke ki kwantar da hankali… wannan komai ba abin damuwa bane. Wannan kayan da kike gani, Kamal ne ya kawo mata a matsayin kyauta, ba wani abu da za a yi fushi da shi ba. Ina so ki gane cewa ni ina son ki fahimta sosai kafin ki yi hukunci.”
Ya ɗan matsa ƙasa kadan, ya yi nuni da hankali:
“Ki kwantar da hankali, Mommy. Kin ji ko? Wannan ba abin tsoro bane, babu abinda zai cutar da kowa. Ni ne ke kula da ita, kuma komai yana cikin tsari. Ina son ki yarda da ni a wannan lokaci.”


Mommy ta ɗan sassauta fuska, idanuwanta sun ɗan natsu, tana jin cewa kalmomin Dr. Sadeeq suna da nauyi, amma har yanzu tana son ta fayyace masa sharadin da za ta ambata. Ta furta cikin tsanani amma mai ladabi:
“To… Amman ina son jin sharadi guda ɗaya kawai da kika ce.”


Mommy ta ɗan ɗaga fuska, idanuwanta sun haɗu da na Dr. Sadeeq, tana jin karfin ladabi da natsuwa da ke cike cikin kalmomin sa. A hankali ta ja numfashi, tana ɗan sassauta tsanani a zuciyarta. Sai ta yi murmushi kaɗan, tana fahimtar cewa Dr. Sadeeq yana da ikon shawo kan abubuwa ba tare da tashin hankali ba, kuma yana son ganin komai ya kasance cikin tsari.


Dr. Sadeeq ya ɗan jinjina kai cikin natsuwa, ya ƙara matsa kadan, yana tabbatar da cewa Mommy ta fahimci cewa komai zai kasance lafiya, cewa babu wani abu da zai ɓata zamanta ko tsoratar da ita—duk da abubuwan da suka faru da Indo. Yanayin ya ɗan yi laushi, amma a cikin zuciyarsa, Dr. Sadeeq ya san cewa akwai abubuwa da zai kula da su a hankali, kuma wannan shine farkon mataki mai kyau don tabbatar da kowa cikin lafiya da kwanciyar hankali.
, idanuwanta sun haɗu da na Dr. Sadeeq, sannan ta ɗan sassauta haushinta. Ta furta cikin ladabi mai ɗan tsanani amma cike da kulawa:
“Idan kana so, ka yarda ka kawo ta nan… ka tabbata ta bani hakuri kuma ta dawo part nan da zama .”
Zuciyar Dr. Sadeeq ta ɗan tsinke, ya ji wani irin tsananin jin daɗi da natsuwa a cikin ransa. Idan wannan shine sharadi ɗaya kawai da zai tabbatar da zaman lafiya a gidan, ya yarda cikin zuciya ɗaya. Ya amsa cikin murya mai sanyi amma cike da tabbaci:


“To… ina yarda.”


Ya fito daga part ɗin Mommy, jiki a sanyaya kadan, zuciyarsa na ɗan buga da sauri saboda yanayin da zai tarar a dakin Indo. Yana tafiya cikin natsuwa, amma a cikin zuciyarsa, yana jin wani irin firgici mai ɗan haɗawa da shauƙi—idan Indo ta sami nutsuwa, to shi ma zai ji kwanciyar hankali.


Indo, tana cikin dakin nata, ta hango shi yana shigowa. Ta buɗe kofa a hankali, idanuwanta cike da mamaki da ɗan tsoro. Amma ba zato ba tsammani, tana ganin shi ya rufe kofa da natsuwa, ya tsaya a gabanta. Ta rungume shi a hankali, ta fashe da kuka, abin da ke nuna haɗuwar duka tsoro da jin

22 / 48