Author : Nana Kanwar Soja Category : Hausa Read
da yasa cikin baya zama .."
Atika ta duba baby girl ɗin, hawaye na zuba a idonta, tana murmushi kadan:/ “Na gode… amma… wannan cuta daga Allah ne Inason na haihu a duniya ko ban rayu ba nasan zanyi alfahari na haifa maka ɗa don Allah ka kula min da ita ka bawa Indo haƙuri bisa abubuwan da yayi ta faruwa a tsakanin mu…”
Dr SADEEQ ya matsa kusa, ya ɗaga kanta:
“Ba komai, za mu fuskanci komai tare. Baby ɗin ki ce haske a cikin wannan wahala.”
Mommy kuwa tana kallon Atika da Dr SADEEQ, zuciyarta na cike da tausayi da jinƙai duk da ƙunci, sun ji rayuwa ta ci gaba saboda ƙaramin rayuwa da aka haifa.
Yanayin ya cika da shiru. Kowa a dakin na kallon yanayin da ya faru, zuciyarsu cike da damuwa.
Dr SADEEQ ya tsaya a gefen gado, ido cike da damuwa da rashin iya magana, yana kallon abin da ya faru. Nurses suna gyara kayan aikin asibiti, amma duk wani sauti ya tsaya a zuciyar masu duba.
Mommy ta rungumi kansa da hannu mai ƙarfi, tana ƙoƙarin samun ƙarfin guiwa.
“Allah ya ba mu hakuri…” ta faɗi a hankali, idonta cike da hawaye.
Kowa na shiru, kowa cikin tunani mai nauyi labari ya tabbata Atika ta mutu.
Dakin ya cika da tausayi da jimami, har zuciyar Dr SADEEQ ta cika da nauyi da nadama saboda abin da ya faru.
HOSPITAL – WASHEGARI
Washegari, bayan dare mai nauyi na makoki, an shirya dakin kamar don nuna girmamawa ga Atika. Indo ta tashi daga Kano, zuciyarta cike da tunani da damuwa, amma ta ƙara ƙarfi domin ganin jaririyar.
An kawo jaririyar a hankali, kyakkyawa kamar haske ne a cikin wannan baƙin ciki. Nurses suka miƙa mata jaririyar, Indo ta rike ta da kulawa, tana ba ta madara.
Ko da kasancewar tana da ciki a jikinta, Indo ba ta ji tsoron ba, zuciyarta ta cika da annushuwa. Ta fara shayar da jaririyar cikin nutsuwa, kamar ta fahimci cewa zuciyarta za ta iya sauƙaƙa wannan baƙin ciki ta hanyar kula da wannan ɗa mai rai.
Mommy da Dr SADEEQ suna kallon Indo da murmushi mai tausayi. Ko da yake ranta na cike da nadama saboda Atika, amma ganin Indo tana kula da jaririyar ya kawo ɗan annashuwa ga dukan waɗanda ke nan.
SHARADA HOUSE – KANO
A kowane mako, Dr SADEEQ yana zuwa Kano domin ganin Indo. Duk lokacin da ya shiga gidan, murmushi mai cike da soyayya yana bayyana a fuskarsa, ganin Indo da Amirah, jaririyar Atika.
Indo tana kula da Amirah sosai, tana ba ta kulawa da ɗan tausayi da zuciya mai laushi. Duk da tsohon cikinta da damuwarta, tana ƙoƙarin zama cikakkiyar uwa da abokiyar kulawa ga jaririyar.
A wannan lokaci, Indo tana cikin final year a makarantar Nursing. Duk da karatun, da kula da jaririyar, da tsauraran darussa, zuciyarta tana cike da natsuwa saboda Dr SADEEQ na nan, yana ba ta ƙarfi, yana tabbatar mata cewa tana da goyon baya a kowane lokaci.
Indo tana jin farin ciki mai nauyi a zuciyarta. Duk da cewa tsohon ciki na damunta, ganin jaririyar da kulawarta da soyayyar Dr SADEEQ ya kawo ɗan annashuwa da karfin guiwa.
Yayin da Dr SADEEQ yake kallonta, zuciyarsa na bugawa da tsananin soyayya. Yana ganin yadda Indo ta girma, yadda ta zama mace mai ƙarfin hali, tausayi, da natsuwa, kuma yana tabbatarwa kansa cewa ba zai bari komai ya raba su ba..
GRADUATION DAY – CAPITAL CITY UNIVERSITY, KANO
Rana ta kasance mai haske da annashuwa. Indo ta shirya cikin abaya mai kyau fara mai ƙyalƙyali da kayan ado masu sauƙi amma masu kyau, fuskar ta na haskakawa da murmushi. Duk wanda ya kalle ta yana jin daɗi Mommy, Daddy, da sauran mutanen gidan su Layla suna kallonta cike da so da alfahari.
Mommy ta rungume ta, tana cewa “Indo, ke ce ta ban mamaki. Gaskiya sonki ya ratsa zuciyata, kina da tausayi, kina kula da yar kishiya, kin kasance .”
Daddy kuma yana kallonta, ido cike da jin daɗi, ya ce:
“Ke ce dalilin farin cikinmu yau. Mun ga yadda kika girma, yadda kika zama mace mai ƙarfi da hankali.”
A bangaren yan uwan Indo, duk sun hallara: Dijje, Haule, Mairo, Mai Unguwa, da sauransu. Kowa yana dariya, suna taya ta murna. Labarin Indo da irin kulawarta da tausayinta ga jaririyar Atika, Amirah, ya burge kowa.
Sai ƙarwarta Ilham, wacce ta kasance a India, ta dawo ta taya ta murna. Duk da hutu da gajiya, bata yi ƙyale wannan rana ba. Ta tsaya, idonta cike da farin ciki, tana cewa:
“Indo, kin cancanci wannan rana. Kin yi ƙoƙari sosai, kuma kowa ya ga yadda kika kasance haka rayuwa yaki , kinye kuka sosai a BORDING na rashin ƴan uwa da kaɗaice yau gashi family guda suna tayaki murna .”Indo ta rungume Ilham da murmushi, tana jin zuciyarta cike da annashuwa. Kamar kowanne mai tsananin buri, wannan rana ta nuna mata cewa duk ƙoƙarin da tayi a makaranta, kulawa da Amirah, da jajircewa ta biya mata.
A cikin taron, soyayya da tausayi sun cika filin, kuma duk wanda ya kalli Indo yana ganin mace mai ƙima, mai ƙarfi, tausayi, da natsuwa
GRADUATION CEREMONY – CAPITAL CITY UNIVERSITY, KANO
Filin taron cike da ɗimbin mutane, masu duba dalibai suna taya su murna. Indo ta tsaya a layin karɓar takardar shaidarta, zuciyarta na buga da farin ciki. Mommy da Daddy suna tsaye a gaba, idonsu na haskakawa, suna kallonta cike da alfahari.
A lokacin da sunan ta aka kira:
“A’ishatu Abubakar Sadiq!”
Indo ta miƙe, murmushi a fuska, tana tafiya zuwa stage. A kowanne mataki, tana kallon Dr yana mata murmushi mai kwantar da hankali tana jin Annushwa mai girma.
Ta karɓi takardar shaidar kammala karatu daga Dean of Nursing. Duk filin ya yi ta ihu da taya ta murna. Indo ta juya, taga Dr SADEEQ yana tsaye a cikin masu kallo, murmushi a fuska, ido na kallonta sosai. Zuciyarta ta buga da sauri, a ranta tace “ I'm happy Dr Balarabe U make my day”
Dr SADEEQ ya nuna hannu yana cewa:
“Congratulations, my wife.”
Indo ta fara dariya, idonta cike da haske. Duk wanda ya kalle su ya fahimci cewa akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin su.
Mommy ta matsa ta ce “Indo, wannan ne sakamakon ƙoƙarinki da hakurin ki. Har yanzu ina alfahari da ke sosai.”
Daddy kuma yana cewa “Wallahi, ke ce dalilin farin cikinmu yau, kuma za mu kasance tare da ke koyaushe.”
Ilham, da ta dawo daga India, ta yi dariya cike da farin cik “Finally! kin cancanci wannan rana, Indo. Gaskiya kin yi ƙoƙari sosai.”
Indo ta kalli Dr SADEEQ, hannayensu na haɗuwa, murmushi na wucewa tsakanin su. Har yanzu a ranta, tana jin tsoron farin ciki da soyayya, amma zuciyarta tana cike da natsuwa.
A ƙarshen taron, Indo ta juya zuwa ga yan uwan ta da tsohuwar ƙawayenta Dijje, Haule, Mairo, suna taya ta murna, suna dariya da ihu. Duk wannan ya tabbatar mata cewa ranar ta kammala makaranta, soyayya tana tare da ita, kuma kulawa da tausayi sun bayyana a rayuwarta
INDO & DR SADEEQ – PRIVATE CELEBRATION AT HOME
Bayan taron, Indo da Dr SADEEQ sun dawo gida cikin motar su, hannu cikin hannu. Indo tana murmushi da farin ciki, zuciyarta cike da annushwa Dr SADEEQ: “Finally, my wife, we did it. I’m so proud of you.”
Indo: “Thank you… na gode da kasancewa tare da ni, har yanzu ina mamaki da yadda ka kula da ni da kuma dukkan dangi na.”
Suka shiga cikin gida, Nazifa ta tsaya a bango tana kallon su, murmushi a fuska. Indo ta yi dariya:
“Aunty Indo yanzu kinga husband ɗin ki yaya ne , dole nace miki hakan cute couple!”
Indo ta juya ga Dr SADEEQ, ta rungume shi sosai, hannu nata a jikin sa “I love you… please kada ka barni kaɗai.”
“I will never leave you, my love.”
Suka zauna a parlour, Indo ta fara dariya da dariya, tana cewa“Kai dai… kai ne chef ɗinmu yau?” Dr SADEEQ: “Yes, today I cook for my wife!”
ABUJA – INDO’S PART RENOVATION
Bayan sun isa Abuja, Indo ta samu sabuwar part nata da aka gyara gaba ɗaya. Gidan ya cika da modern furniture, pastel colours da soft lighting. Ko da ta shiga, ta ji sanyi a zuciya saboda girman canjin da aka yi Indo (a ranta): “Kai… wannan gida, wannan part… ashe Dr SADEEQ ne ya kula da komai a boye. At least ashe yana damu dani.”
Ta zagaya dakin, ta tsaya a kusa da taga tana kallon birnin Abuja. Hasken rana yana shiga dakin, yana kawo warm glow a fuskar ta. Tana tunawa da tsofaffin memories a Kano, amma yanzu tana jin peace da security a nan.
Sai ta lura da wasu personal touches—photos ɗinta da Dr SADEEQ, wasu kayan gida na zamani, har da corner da aka tanadar mata don study space.
Indo (ta murmushi): “Kai… kullum yana tunani a gareni, ina jin kamar… wannan gida cike ne da soyayya.”
Nan ta zauna a couch, ta fara drinking tea da rumfar kwanciyar hankali, tana jin soft music in the background da kuma calmness da take bukata bayan dogon lokaci na wahala da rikici.
Har ta fara planning yadda zata ciyar da rayuwarta a Abuja work life da kuma kulawa da yarinya ta Amirah. Wannan part nata yanzu ya zama sanctuary nata, wurin da zata iya focus on herself da future nata.
LABOUR ROOM – DRAMA & COMEDY MOMENTS
Indo tana kururuwa sosai, jin ciwo kamar za ta fashe. Dr SADEEQ yana ta shiri da kulawa, yana rike hannunta, yana ƙoƙarin sanyaya ta:
“Honey, numfashi… numfashi… Ina tare da ke, everything will be fine.”
Amma Indo bata iya tsayawa, tana ƙara ihu:
“Uuuu… Dr… ina jin… ina jin kamar… ohhh Allah…” Nazifa ta zauna kusa da ita, tana rike ta “Indo, na san zai zamo da sauki nan da nan, kaɗan kaɗan…”
Kawai Indo ta juya, ta faɗi:
“Dr… why you always calm… Ina jin kike daɗi da kulawarka, amma ai ina tsorata sosai!”
Dr SADEEQ ya yi murmushi, yana jin dadi a zuciyarsa “Ina son ki sosai… kawai kiyi haƙuri… very soon zaki ga baby!”
Indo ta ƙara kururuwa, “Okay, okay… stop crying for a moment,
LABOUR ROOM – TWIN BOYS BIRTH
Indo tana cikin dakin haihuwa, Dr SADEEQ yana tsaye kusa da ita, yana rike hannunta da kulawa sosai.
“Honey, numfashi… numfashi… very soon zaki ga baby,” in ji shi cikin laushi.
Nurses sun fara shiryawa, sa’annan Nazifa tana zaune kusa da Indo, tana ta dariya da ƙoƙarin sanyaya ta “Indo, wannan shi ne comedy moment ɗin ki—za ki yi dariya da baby nan!”
Indo ta ƙara ihu, amma a lokacin da aka fara fito da first twin boy sai Dr SADEEQ ya yi murmushi sosai, yana kalle ta “Look at him… he is strong just like his Mama!”
Indo ta yi murmushi cikin ƙyar, tana jin dadi da kulawa “Ohhh… suna da kyau… suna da kyau sosai are twins I can't believe it …”
Nan aka haifi second twin boy, sai dakin ya cika dariya da murna Iliham ta yi barkwanci:
“Kai, Indo, yanzu ke da double trouble! Ko za ki iya kula da su biyu lokaci guda?”
Indo ta yi dariya cike da gamsuwa, ta kalli Dr SADEEQ:
“Ina son ku duka… ni da su ma, na gode Dr… yanzu zan zama Mama da farin ciki.”
Dr SADEEQ ya rungume ta sosai, yana sumbatar ta a goshi:
“Ina son ki, Honey… yanzu mu more kulawa da duka ɗalibai biyu nan.”
Dukkan nurses sun yi dariya, suna taya murna, Indo ta zauna raye, tana kallon twin boys ɗin nata, zuciyarta cike da annushuwa da murna.
GIDA – BAYAN KWANA BAKWAI – SHAGALI DA BABY TWINS
Bayan kwana bakwai, Indo da Dr SADEEQ sun dawo gida daga hospital, suna ɗauke da Muhammad Ayman da Mu’azzam, yaran da zasu ci sunan Daddy, suna kiransu Arman.
Kowa a gidan na murna da dariya. Mommy da Daddy, Kaka da sauran yan gida suna zagaye Indo da Dr SADEEQ suna taya murna:
“Alhamdulillah! Wannan shi ne babban albarka! Double joy!” in ji Mommy.
inda Dr Sadeeq fan's suka hallara suna ta kwasan takaway da kayan arziki Irrin su sister Khadija Sufyan, chan na hango Sister Rabi'tu adam tana ta jan Amirah da wasa , don Dr Sadeeq ya karɓi account number ta also sister Yusraty tana ta dambe da naman kaza ,abin mamaki banga sister Sopiyya Baliya ba ashe tana chan tana neman ƙulla zumunci da Dr Indo , Umcy baby da Ummu Nasreen suna ta zumɓura baki photographer na ɗaukan su hoto, chan hango muku Sister Sa'awdatu a tana zuba juice a cikin bag nata abun dai da ban mammaki nayi dariya na wucce ciki ina neman sister Fatima H Nasir da Miemie ashe suna zaune da Nazifa tana basu wasu Sirrin da Bansan ma me zan gayyamu ku ba ,kunsan mata da gidan baki , Sister Hindu billa tana daga ƙife tana ta kallon Indo daga nisa kamar taje tace mata ta rama marin da Dr Sadeeq ya mata a baya Amman ta makara Saboda sister A'ishatu Usman ya gama gayawa Indo hakan a kunne , ai kuwa ta musu ƙwalelle da cewa Amina Hassan Abba ta kira shugaban tawagar su Kanwar soja suzo su bar mata gida kafin su kashe mata aure ,, haka kuwa akaye sai da na tabbatar duk na kora su waje na lallaɓo na dawo domin ganin ƙarshen labarin su don naga ba wani drama sai nabar mata gidan na tafe chan GUGUWAR GRADUATION naga meke faruwa ko me zai faru ..
Indo tana zaune a kan kujerar parlour, tana riƙe da Muhammad Ayman, sai Dr SADEEQ ya riƙe Mu’azzam a hannunsa. Indo ta kalli Dr SADEEQ da murmushi:
“Kai… yanzu mu ne Mama da daddy… kuma su Arman!”
Dr SADEEQ ya yi dariya cike da kulawa:
“Honey… look at them… they look just like you… amma su ma suna da kyau sosai.”
Haba Indo ta kiye ha'kuri kuma kinjii ko babyn Sadeeq,gashi nazo da corruption na ga kaza nan mai zafi da yaji " zumɓura baki taye corruption naka banso yau " ta tura ɗankwalin ta gabas ta juya mai ƙeya" Oh no My queen zaki kashe ne da wannan salon Please I said a karɓe tuban wanan bawan Allah da ya durgusa gani ga kaza ta , " ka tafe da kazar ka don wallahi bazanbika ba yau nifa kwana ta arba'in da haihuwa kanason na bika ka ƙaramin wani cikin ko to anƙi "
Murmushi yayi "okay fine na miki alƙawarin baxan bare kiye cikin yanzu ba ,mu tafe gida kawai mubar Kaka ta huta mu kwashe yaran mu ko Babyn Dr "
Nifa cikakkiyar nurse ce kanason ka yaudari ne to a banza wallahi ka tattara Kaye gaba sis da safe ta miƙi tsaye zata tafe da saure ya chafko ƙafarta wani yarrr suka fahimci hakan Dukansu biyu " Please Babyn Dr Balarabe " abinda yace ne yasata murmushin wato shi namiji idan yanason abu to ba shakka yasan hanyar da zaibi ya shawo kan rikicin sa, fahimtar yayi nasara ya kwantar da kai a wuyan sa " Umm Indo Dr Balarabe please Allah zan baki Kaza " Mari ta sakar masa a kafaɗa " Dr wallahi ka iya shagwabaa sake ye nagani* Haba my Queen yazakina min hakan sunkuya dakai taye dai dai kunnen sa zata mai magana tasa haƙurin ta ta gantala mai cizo da ƙarfi har sai da yayi ƙara da gudu tasha ta fara gudu ai ko ya bita suka fara shigewa tsakanin kujeru Kaka jin ihu Dr SADEEQ yasa ta fito tana ganin su taja tsaki " kai SADEEQ zo ka kwashe yaranku ku barmin gida kar ku haukata ne aikin banza " ta juya ta kuma ganin juna sukaye suka tun tsire da dariya a tare ya kashe mata ido yana mata gwalo sai ni... DR SADEEQ ....
Dare ya sauko, gidan ya yi shiru amma ba duka ba…
Muhammad Ayman da Mu’azzam (Arman) sun fara kuka lokaci guda.
Indo ta tashi da sauri: “Subhanallah! Duka biyun lokaci ɗaya?” Dr SADEEQ ya buɗe ido daga barci “Honey… wannan kuka biyu fa alarm ne na soyayya , ko zamu kara wasu ”
Ta juyo ta kalleshi " Hubby am , ka daina barkwanci ka taimaka mana.”
Ya ɗauki Mu’azzam (Arman) yana jujjuya shi “Mr Arman… what is the problem sir?”
Yaron ya ƙara kuka
Indo ta fashe da dariya duk da gajiya: — “Ka ga? Yaron nan baya son interview.”
Sai Muhammad Ayman ma ya ƙara kuka kamar yana hassada da kukan ɗan uwan sa
Dr SADEEQ ya tsaya cak: — “Oh Allah… twins fa ba training aka yi mana ba!”
Indo ta ce: — “Kai likita ne ai.” “Eh likita… amma wannan pediatric emergency ne!”
Daga ƙarshe suka raba aikinsu Indo ta shayar da AymanDr SADEEQ yana jujjuya Arman yana waka a hankali“Arman… my son… Daddy loves you… please sleep before Mommy reports me.”
Yaron ya yi shiru.
Dr SADEEQ ya yi tsalle da murna a hankali: — “YES! Na ci nasara!”
Sai Indo ta ce: — “Ka yi shiru… kada ka tashe ɗan uwansa.”
Da kyar suka kwantar da su, suka koma kan gado.
Indo ta jingina da shi cikin gajiya da farin ciki: “Na gode… wallahi ba zan iya ni kaɗai ba.” ya rungume ta sosai: — “Ni da ke… har tsufa. Ke mata ta ce… su kuma amanata"
Da safe Mommy ta kira su a waya
Jararrababu “Ina kwana?”
Indo da Dr SADEEQ suka ce lokaci guda: “Ba mu kwana lafiya ba Mom!”
Mommy ta yi dariya “toh ku saba… wannan shi ne auren gaske.” ta kashe wayan..
Dr SADEEQ ya kalli Indo: — “Honey, wai ke kika ce auren nan romance ne kawai.”
Indo ta masa harara: — “Ka yi shiru, ka tashi ka soya min ƙwai da bread da tea ka tabbatar kasa suger "“ wa ni?”
“Eh kai! Daddy na twins to wa zamgayawa haka”
Ya ɗaga hannu kamar ya mika wuya: — “Yes Ma’am.”
A kitchen yana soya ƙwai, yana magana shi kaɗai: — “Dr Sadeeq emergency work in