Author : Nana Kanwar Soja Category : Hausa Read
Indo ta tsaya a bakin motar tana kallon ta tamkar wacce ke kallo aljanna tana kyalli kamar wadda aka fitar yanzu daga showroom.
Sai da Dr. Sadeeq ya zagaya ya buɗe mata murfin bayan, don yasan taayawar da taye kinan batasan ta yanda zata buɗe ta ba ba Irrin taxi ta ƙauyen su bane ya ce “Shiga, Indo.”
Ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon kujerar cikin motar.
“Dr, ba zan ɓata maka kujerar ka ba?”
Ya yi murmushi mai sanyi “Indo, wannan mota ce, ba tabarma ba shiga kawai.”
Cikin kunya ta shiga, ta zauna a hankali kamar wacce ke tsoron ta karya wani abu.
Ya shiga gaba yana cewa:
“Bismillahir Rahmanir Rahim.” yayi ignition, motar ta ɗauki ƙara cikin sanyi, sai kuma ya kunna suratul Kahfi daga speaker muryar Mishary Alafasy na tashi a hankali cikin nutsuwa mai gadin gidan ya buɗe gate ɗin, suka fara tafiya cikin shiru mai daɗi.
Iskar AC ta cika motar da sanyi, tana haɗuwa da ƙamshin car freshener mai launin vanilla — Indo ta ji kamar iska ce ta aljanna.
Ta fara kallon komai da mamaki
windows, mirror, dashboard — har ma da maɓallan mota tana shafar su ɗaya bayan ɗaya.
“Dr, wannan kuma?” ta tambaya tana matsa AC vent “Iska ce Indo.”
“Wannan?” ta matsa seat adjuster.
“Kujera ce, ta naɗe da wuta.”
“Subhanallah!” ta ce tana tura baki, idonta a buɗe kamar yarinya a magic show Dr. Sadeeq kuwa, bai iya hana kansa murmushi ba.
Yana kallonta a gefe, yadda take motsa hannayenta cikin halin ƙauyanci da gaskiya a zuciyarsa ya ce“Wannan yarinya..” sai ya raƙe ƙarfin AC sosai ya ce:
“Indo, kina jin sanyi kuwa?” ta kalli shi da fara’a, ta girgiza kai.
“Ina ji kamar cikin gajimare, Dr. Balarabe.”
Ya sake murmushi mai laushi, ya mayar da hankalinsa kan hanya — amma zuciyarsa tana wasa da kalmarta “gajimare”, saboda ita kanta Indo yanzu tana masa kamar gajimare — ta rufe zuciyarsa da wani sanyi mai dadi.
“Kin taɓa hawa mota irin wannan ne?” ya tambaya cikin nutsuwar muryarsa.
Ta ɗaga kai da sauri, tana murmushi cikin kunyarta,
“Wallahi bansan ko irin ta wace ce ba… amma daɗinta kamar ba duniya ba ne. ina zanga Irrin wanan motar a Modirre ai sai dai nan in aljanna duniya ”ya murmusa, yana gyara zaman hannunsa a kan steering.
“Da lokaci, za ki saba, Indo.”
Sai ta ɗan yi shiru, tana kallon window, tana ta bin titi da ido — zuciyarta na cike da sabuwar farin ciki da ɗan tsoro, tamkar yarinya da aka fara ɗauka zuwa wani sabon duniyar da ba ta taɓa zato ba.
Motar ta tsaya a gaban wata babbar ƙofa mai rubutun zinariya:
“ AL NOOR ACADEMY – For Bright Future”.
Ganuwar makarantar ta yi tsayi, an lulluɓe ta da flowers da greenery, ƙamshin fresh paint da flowers ke tashi — ga tsabtataccen filin ajiye motoci da yara masu sanye da uniform suna gudu-gudu.
Indo ta ƙara bude ido, kamar wacce aka kawo wani sabon duniya.
“Subhanallah…” ta furta a hankali tana kallon hasken tiles da sassan ginin.
“Wannan makarantar ba ta Kama da ta ‘yan gari ba wallahi.”Dr. Sadeeq ya yi murmushi, “Ai dole ki saba, nan ne za ki koyi komai.”
Ya fita daga mota ya buɗe mata ƙofa. Indo ta fito a hankali tana duban kowane bangare da mamaki, har sai da wata malamar English ta wuce tana cewa da yaransu,
“Good morning students!”
Sai Indo ta amsa cikin sauri, “Morning!” tana ɗan yi da hannu kamar budurwa ta fara hawa jirgi.
Da suka shiga cikin building ɗin, suka wuce reception, aka kai su ofishin Principal — wata mata ce mai kyan jiki da nutsuwa, tana sanye da hijab mai tsabta.
“Good morning, Doctor Sadeeq,” ta faɗa cikin murmushi.
“Good morning, Principal Rahma,” ya amsa cikin ladabi. “Ga yarinyar da na kawo, za ta fara karatu a nan.”
Principal ta dubi Indo da murmushi,
“What’s your name, dear?”
Indo ta ɗan sunkuyar da kai, “Ni? Indo ce…”
Principal ta murmusa, “Okay, Indo How old are you and ur full name ?”
Sai ta tsaya tana kallo, ta jingina kai gefe, ta ce,
“Uhmm... ai wallahi ban san daidai ba, amma sun ce ina kusan shekara sha hudu ko sha ukku Suna na dai AISHATU INDO banɗaki san sunan baba na ba .”
Principal ta dan ɗaga gira, tana murmushi, tana kallon Dr. Sadeeq da nufin “ƙauyancinta ya fito.”
Shikam shiru yayi jin wani abun tausayim da ya ratsa shi ya ce " A samata AISHATU ABUBAKAR SADEEQ
“Alright,” inji Principal, “Za mu fara da test domin mu san matakin da ta dace da shi.”
Dr. Sadeeq ya ce, “To, a taimaka mata da lesson din extra idan akwai.”
Principal ta kira wata malama, “Teacher Maryam, ki kai ta class 5 idan kin ga ta iya wasu abubuwan yawa, ki ɗaga zuwa class 6”
Indo ta yi tsaye tana zuba ido, tana kallon ɗaliban da ke wucewa da littattafai.
Sai ta ɗan kama hannun jakarta tana kallon Dr. Sadeeq da dariyar kunya, “ni yanzu zan zauna a cikin su nan? duk suna Turanci fa!”ya yi murmushi yana tafiya, “Ki je ki zauna, zaki iya. ki dage, Indo banda tsokana ko faɗa Please.”
Malamar ta ja hannunta a hankali suka shiga cikin corridor mai ƙamshi da haske.
Yara suna ta karatu, wasu na “Good morning ma!”Indo kuwa ta tsaya tana zazzage littattafai da ido, zuciyarta na bugawa.
“Sit here,” inji malamar.
Indo ta zauna, ta jingina hannunta a kan tebur, tana kallon allon da aka rubuta:
“Lesson: Nouns and Pronouns.”
Ta ɗaga kai a hankali, ta ce da wata yarinya a kusa da ita,“Ke, ‘noun’ ai ba suna bane irin Indo da Sadeeq?”
Yarinya ta yi dariya sosai.
Sai Indo ta ɗan rufe baki da hannu cikin kunya, ta furta a ranta:
“Ko meye dai, sai na dage. Ba zan koma baya ba.”
Malama Maryam ta kammala rubuta darasi a kan allo, ta juya da murmushi, hannunta na riƙe da marker.
“Okay class, who can answer this simple question?”
Sai ta tsaya ta kalli Indo da ido.
“Indo, let’s try you. What is the past tense of go?” Indo ta kalli allon, ta kalli Malama, sannan ta ɗan karkatar da kai gefe.
“Ma’am… ehh... going?”
Cikin aji aka fara dariya — wasu har da tafi.
Ilham ta yi saurin matsawa kusa da ita, ta ce a hankali, “No, not going, Indo. It’s went.”
Malama Maryam ta yi murmushi cikin ladabi, ta ce,“It’s okay, Indo. You’ll learn with time. Everyone makes mistakes, right class?”
Amma wani ɗalibi a tsakiyar aji ya daga murya da murya mai sauti:
“Madam, she sounds like she came from the bush!”Cikin sauri Indo ta juyo, idonta ya firfito.
“What did you just say?”sai ɗalibai suka ƙara yin dariya, wasu suna kiran sunan ɗalibin:
“Fahad, stop it nau! Don’t tease her!”
Indo ta haɗa fuska, ta tura baki gaba “A’a, idan ba makaranta bace, da na maka duka wallahi.”
Ta furta a ranta cikin ɓacin rai, tana jan numfashi, tana ƙoƙarin hana hawaye.
Malama ta ɗan tsare Fahad da ido,
“Fahad, that’s very rude. Say sorry to her.”
Yaron ya sunkuyar da kai,
“Sorry.”
Indo ta ɗan ɗaga kafaɗa, ta ce cikin kasala,
“ To Allah ya taimake ka aji ya sake yin dariya, sai Malama ta bugahannunta a tebur,
“That’s enough! Everyone, open your exercise books.”
Sai da lokaci ya ja sosai, kafin karfe sha ɗaya aka buga ƙararrawar break.
Sautin kararrawar ya cika makarantar da amo —
Tring! Tring! Tring!
Indo ta yi tsalle kamar wata yarinya mai farin ciki, ta yi dariya ta ce,
“Allah sarki, ana sauti kamar masallaci.”
Ilham ta kama hannunta tana dariya,
“No, that’s break time. Let’s go to the canteen before it gets full.” Indo ta turo baki,
“Canteen kuma? wane irin masallaci ne canteen? Ilham ta yi dariya sosai, ta riƙe cikinta,
“Oh my God, Indo, you’ll kill me with laughter.”
Ilham ta kama hannun Indo suna fitowa daga cikin ɗakin karatu zuwa harabar makaranta.
Gidan makarantar ya cika da yara suna ta dariya, wasu suna wasa da kwallon kafa, wasu kuma suna tsaye a layin canteen suna jiran snacks , Ilham ta ce da murmushi,
“Come on Indo, let’s go and buy food before the line gets long break is just thirty minutes.”
Indo ta tsaya cak, ta ɗan shafi cikinta, sannan ta tura baki gaba kamar ƙarama.
“Ni yunwa nakeji sosai, amma… ban da kuɗi fa.” Ilham ta tsaya tana kallonta da mamaki,
“Eh? Baki da kuɗi ko flask?”
Indo ta ɗaga kai a hankali, tana lumshe ido,
“Eh, Dr. Balarabe bai bani ba… watakila ya manta.” Ilham ta lumshe ido ta murmusa,
“Ohh… so shi ne Brother ɗinki kenan?”
Indo ta yi saurin gyara magana da ɗan kunya,
“Eh… kamar haka mana.” Ilham ta ce da taushi,
“It’s okay, come with me. I’ll buy for you, ba matsala. We’ll say it’s one plate, okay?”
Indo ta yi dariya mai daɗi,
“Tooo, ai Allah ya saka da alkhairi!”
Suna tafiya suna hira cikin nishadi, sai Indo ta ɗaga kai kamar wadda ta ji ƙamshi.
Sai ta tsaya cak, numfashinta ya tsaya na daƙiƙu biyu.
Idonta ya sauka a can bakin get — motar Dr. Sadeeq ce, mai sheƙi da haske, yana tsaye yana jingina da gefe, riƙe da takeaway pack mai girma a hannu.
Iska mai sanyi daga motarsa ta buso tana ɗauke da ƙamshin turaren sa wanda Indo ta saba ji tun daren da ta fara rayuwa dashi a gida ɗaya zuciyarta ta buga “Subhanallah… shine fa.”
Kafin Ilham ta fahimta, Indo ta riga ta da gudu
tuf! tuf! tuf! — takalminta na danna ƙasa, rigarta na yawo da iska Ilham ta tsaya da mamaki, ta dafe kai “Indo! Indo! Ina zaki je haka?!”
Dr. Sadeeq yana tsaye yana duba agogo, fuskarsa cike da nutsuwa kamar wanda yake jiran wani muhimmin abu.
Yana daure fuska amma idanunsa suna da taushi.
Cikin mintuna kaɗan, ya ga Indo tana karasowa da gudu, hannunta ɗaya na riƙe da Cap ɗaya kuma tana ɗan ɗaga rigar ƙafarta kada ta kife yana ganin hakan sai ya ɗan ɗaga murya cikin mamaki: “Indo?! What are you doing here—” amma kafin ya ƙarasa, ta tsaya gabansa, tana shan numfashi, fuskarta cike da farin ciki da mamaki.
“Dr. Balarabe! kai ne fa! ka dawo ”
Ya sauke murmushi, ya kalleta sama da ƙasa rigar makarantar, socks, da hCap ɗinta duk cike da ƙauyanci amma da wani innocent charm mai ban sha’awa.
Yace cikin natsuwa,
“Na manta ban baki kuɗin abinci ba... shi yasa na kawo miki.”
Ya miƙa mata takeaway pack ɗin, yana kallonta kai tsaye cikin ido.
Indo ta karɓa da hannaye biyu, ta ɗan sunkuyar da kai, idonta ya cika da hawaye na farin ciki “Na gode Dr. Balarabe... wallahi Allah ya saka da alkhairi... ni yunwa nake kamar zan fadi.”
" ke daina gudu bakiga kin fara girma ba kawo cap nin na gyara miki " ya faɗa with his full confedence ta bashi nan ya gyara ya sauya dai dai kanta , dake chunkushe girgiza kai kawai yayi ta sunkuya da kanta ya kafa mata ita kanta har taji wani kunya da batasan tana dashi ba , cikin hanzarin ya juya Ilham ta ƙaraso tana dariya ta ce,
“Wow Indo, you know this handsome man?”
Indo ta ce da izza,“Eh mana, shine... shine Brother ɗina!”
Dr. Sadeeq ya ɗan yi murmushi, ya lumshe ido cikin natsuwa, sannan ya ce cikin sanyi:
“Go and eat, Indo. Don’t be late for class.” ya juya ya shiga mota, yana jin kamar zuciyarsa ta cika da wani abu — ba a iya fassara shi da kalma.
3️⃣5️⃣💥3️⃣6️⃣
Canteen ɗin makarantar ya cika da hayaniya yara suna ta shawagi, wasu suna dariya, wasu suna latsa drinks ɗinsu da straw, sai ƙamshin abinci mai daɗi ke yawo a iska.
Indo da Ilham suka samu kujera a ƙarƙashin wata bishiya mai inuwa Ilham ta buɗe takeaway ɗinta, Indo ma ta buɗe nata cikin sauri kamar wadda ta dade tana jiran ƙofar aljanna a buɗe kawai sai kamshin jollof rice da chicken stew ya daki hancinta.
Ta ɗauki spoon ɗin ta fara ci da wani irin kuzari da ƙauyanci, tana buge abincin kamar tana fafatawa da shi , ganin spoon in baya kaimata yanda takeso ta ajiye sa kawai Ilham ta zuba mata ido, ta kasa jurewa.
“Indo... Indo! Calm down mana! Haba... kina cin abinci kamar kina tseren gasar gudu ne,”
ta faɗa tana dariya.
Indo ta ɗan ɗaga kai, fuskarta cike da farin ciki da ɗan dariya,
“Wallahi yunwa nake, yunwa irin wacce idan baka ci ba, sai kake ganin rana tana juyawa kuma kaza ce fa .”
Ilham ta buga kafa a ƙasa tana dariya sosai,
“Hahaha Indo! Ai baki da kyau kina yin magana haka. Ke yanzu kina birni, ki nitsu.
A birni, idan kina cin abinci, ki yi sannu, ki ɗauka a hankali, ki ɗan rufe baki, ki yi murmushi kawai.”
Indo ta ɗan ɗaga gira cikin mamaki,
“Ni na rufe baki ina ci? To ai sai abincin ya tsaya min.” Ilham ta ce,
“Uhmm... ba haka ba Indo. Ki dai dinga koyi, zaki ga yanda komai zai canza.”
Indo ta yi shiru na ɗan lokaci tana kallo, sannan ta ce da murmushi,
“Toh... zan koyi, idan haka kike faɗa. Amma fa sai in ƙare wannan plate ɗin tukunna.”
Ta cigaba da ci har ta share plate ɗin gaba ɗaya, da yatsun ta ɗan shafi ciki da murmushi mai daɗi Ilham ta girgiza kai tana dariya,
“Ke fa Indo, wallahi zaki zama labari a nan makarantar. Amma dai kina da sa’a, saboda Brother ɗinki yana kula da ke sosai.”
Indo ta ɗan sunkuyar da kai cikin kunya, ta taɓa gefen spoon ɗinta,
“Eh... Dr. Balarabe yana da kirki sosai ..
4:00 Dr Sadeeq ya shigo inda yaga motocin iyayye dewa ga school bus na ƴan makaranta wani tunani ne ya motsa masa girgiza kai yayi murmushi " that's the best solution" chan ya hango Indo da leader takeway da Jakar ta kamar wacce ta fito a bakin kura duk taye sequiszen " Hasbunnallahu wani'emal wakil"yace yana kawar da kansa tazo tsaya ta kasa bude kofar ta ciki ya matso ya tura ƙofar kawai taga ya bude ai ta razana tana ganinsa " ke zubar da wanan bolar a dusbin chan " bataye musu ba ta yasar , ta shiga ya rufe suka fara tafiya ganin ko magana bai mata ba ya haɗa fuska yasa taye shiru sai tana wasa da yatsun hannunta tana maimaita Noun is a name of place , animal, sai yaye shiru alamar ta manta ya girgiza kai kai tsaye , Saloon ya wuce da ita ganin ba gida bane ta fara zare ido ya zagayo ya bude mata kofar ta fito " drop ur bag " ya ajiye tagani abinda yake nufi ,suna shiga tana ta kallon kamar gidan masu shirye shiryen bidiyo Film ta faɗa a ranta " oga welcome"wata inyamura ta faɗa tana matsowa "Thank you" yana magana cikin izzarsa " Indo come here za'a wanke miki kai banason hayaniya " nan ya wa matar bayani Ya kuma mota ya zauna yana jiran su.....
Matar ta warware mata gashin sai tsaki yakiye Duk da cewa Lami maid ta wanke mata Amman Indo taƙi tsayawa a wanke mata mai kyau a gida ruwan sanye ta zuba mata har saida Indo ta yi karamar ƙara , ta nitsu aka fara wankewa sai hawaye a idon ta domin azaba dirjewa , ana gamawa aka fara busa kai tanajin zafin Island ta zabura ta tashi da ihu " Wallahi baki Isa ke ƙona Min kai da wanan busar ba kawai zaki kashe ne lokacin mutuwa ta BAIYE ba azzaluma " sorryy babu girl it's hand dryer " amma. Indo sai masifar takiye ta miƙi tsaye harda kama quggu matar ta tsaya ya rasa me zagaye ,nan ta aika ƴar gidan ta tana zuwa ta buga mai glass na mota ya sauke a hankali yana waya da Kamal yana ganin ta kawai yasan Indo ta fara haukarta " I will call you back Kamal " ya datse wayar ya fito cikin hanzari jin Muryar Indo sama sama , yana isowa sukaye ido huɗu nan taja bakin ta taye shiru kawai an shanye ruwan sama a ƙasa .....
"Indo what happened"ai batasan lokacin da ta fashe da kuka tayo kansa da gudu ba , bai hana ba ya dafa kanta "is okay " yaja ta " Madam sorry please kimata a hankali " wallahi Dr Balarabe zata cinye min kaina " kallo ɗaya yamata yaye shiru ya zaunar da ita hannun sa yasa cikin hannun ta "now I'm here ba abinda zai miki " a haka akaja kai in tana son taye ihu Dr Balarabe na kusa da ita hannun cikin hannu har aka gama gyara kan " Masha Allah" abinda ya faɗa kinan a fili nan yaye mata paking ya kwanta Lufff luff yayi tsaye sosai ta gama ganin har 6 yaye yace a mata gyaran ƙafa kafin ya dawo sallah, haka akaiw ya fita ya barta yana ta zafin matan da fulatanci da Hausa kasancewar matar batajinta kawai ta chigaba da aikin kudin ta sosai ƙafan Indo ya gyaru ,
A haka ya dawo ya ɗauke ta duk ta kumbura fuska Don tasha wahala ga ciwon kai suna isowa gidan aka buɗe musu gare nan yace "wait ke koya yanda zaki na bude mota I'm not ur maid " " and don't forget KIYE wanka gobe 7 zake fito " ya faɗa yana ɗan cizza bakin sa na ƙasa da azabtar da yake sha tace too nan ta juya ta tafe ko godiya babo don fushi takiye dashi..... tana zuwa ko uniform bata cire ba ta kwanta ba sallah bare sallati ( Su Indo manya ) ....
AFTER ONE WEEK
Kullum yana tambayata ko naci, yana bani kuɗi, yana sa Musa yazo da abinci.
Kullum da ƙarfe sha ɗaya ina ganin motar su, wallahi idan na gani sai nayi dariya a zuciya.”Iliham ta ce,
“Hmm...