DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   16 / 48

45K to 48K   out of 141.3K words

Sadeeq ya ɗago, idonsa ya cika da fushi amma yana ƙoƙarin riƙe nutsuwarsa.
“Mommy, please. Just once... try to see her as I do.”






Sai ya juyo ya kalli Indo, ya murmusa a hankali yana ce mata da sanyi,
“Ki kwantar da hankalinki, Indo. I’m here.”


A lokacin Daddy ya ɗan ja numfashi yana kallon su duka, sai ya faɗa da murya mai nauyi: “We will talk after prayer. in Sha e For now, take her out of my sight.”






Sai Dr Sadeeq ya kama hannun Indo, suka juya zuwa part ɗin sazuciyarsa na tafasa kamar ruwan zafi...
amma a cikin zuciyar sa, wani muryar ciki ta furta:“Abinda nake yi gaskiya ne... ko da babu wanda zai fahimce ni yanzu.”











##$$#####$##$#
Dakin ya yi shiru mai nauyi — irin shiru da ke cike da hararra. Kowane idon da ya sauka kan Indo kamar yana duba abin da aka cire daga ƙasa: ƙazanta, rashin ilimi, da abin kunya a idon wasu. Layla da Na’iba suna kallon ta da ƙyama, kamar wadda ta zo daga wata duniya da ba ta dace da gidan su ba.


Daddy ya miƙe yana irin kallon da zai iya gaya maka komai — fushi, kunya, da rashin yarda. Ya ɗan yi tafiya a ɗaki da sauri, ya tsaya kan window, ya juya ya kalli Dr. Sadeeq da murya mai nauyi:


“Ka bani hujja, Sadeeq. Me ya sa ka kawo tanan? Me yafi kawo mata a gidana? Kai likita ne — ka san dokokin al’umma. Wannan abu ba zai yiwu ba.”


Dr. Sadeeq ya ɗan yi shiru, ya dafa kansa, sannan ya kalli Daddy da idonsa ya cika da tawali’u:


“Daddy, ni na sha alƙawari. Mahaifiyarta ta mutu a hannuna, ta bani amanar ta a lokacin da take son ta wanke lafiya. Ta roƙe ni in kula da ita. Ni likita ne — ba zan iya mantawa da amanar ba. Don Allah ku bani dama in sauke wannan alƙawari.”


Hajiya Binta ta ɗan yi dariya mai ƙyama, ta turo baki. Ta miƙe tsaye tana ciro ƙafaɗa kamar wadda za ta yi wasiyya:


“Alƙawari? Kai kam Sadeeq, ka san alƙawari da suka je? A gidan mu ba mu ɗauki waɗanda za su dinga biyan min kunya ba. Ina son a gayyace su makaranta, amma ba a nan gidan mu. Mu ba gidan tallafi bace.”


Mommy (Hajiya Zainab) ta zauna a gefen kujerar ta, idonta na ta kallon Indo amma babu zafi a fuskarta — sai tausayi. da kuma ƙyama lokacin guda don tasan zafin rashin uwa Ta miƙe a hankali, ta matso kusa da Daddy, tana cewa a ƙasa amma da murya mai nauyi:


“Sadeeq, na san kai mai zuciya ce. Amma ka gane cewar Ina tsoron yadda jama’a za su fahimta? Ka sani, wannan gidan yana da suna amma hakan bai hana ni jin tausayi ba.”


Indo ta ja jiki, ta sunkuyar da kai. Hannunta na rike da gefen rigar Dr. Sadeeq kamar tana neman tsaro. Idonta na cike da hawaye, amma ta kame baki. A jikin ta akwai rawar rashin fahimta — “ina nan? me nake yi a wannan wuri?” — duk wannan ya bayyana a fuskarta.


Kamal ya matso ya zauna kusa da Dr. Sadeeq, ya ɗan gyara murya mai laushi don ya rage tashin hankali:


“Boss, mu ji dabara. Mu basu hujjar kirki. Ina da tabbaci, idan muka sanya ta a makaranta, a cikin wata uku za ku ga canji. Amma muna bukatar permission, mu fara da small steps.”


Daddy ya nufo Kamal da harshen idanuwansa, cikin ƙarfi ya amsa:


“Kamal, wannan ba abu ne da za a yi wasa da shi ba. Idan har akwai hujja, to ku kawo ta a rubuce. Amma a yau — wannan ba zai wuce ba.”




Hajiya Binta ta naɗe hannayenta, ta yi wani irin kallon da yake cika da ƙyama. “Ba zan yarda wannan ta zauna a gidan mu kamar ba komai ba. Idan har za a taimaka, a shirya wuri daban maid’s quarter ko hostel. Amma kar ku zubar da mutuncin gidan nan.”




“Zan ba ku damar tattaunawa. Amma wannan zai kasance a karkashin sharadi: kada a yawaita hayaniya... cewar Daddy


Daddy alfarma ɗaya nake Nima zan ajiya ta ko a maid part ta zauna zan sata a makaranta ko bani dama na sauke alƙawarin da na ɗauka kafin fitar ruhi nasan zaka saurarre ne Daddy, Mommy Please " ya faɗa cikin raunin murya mai ban tausayi


Kallo kallo sukaye Daddy yayi gyaran murya " tunda kake baka taɓa neman abu a guna na hanaka ba Amman kasani kaga Irrin wanan mutane ba abun yarda bane sadeeq nasan Allah ya baka zuciya mai tsaushi da tausayi Amman kar kasa kanka cikin damuwa da bala'e"


in Sha Allah Daddy ba'a binda zai faru just kubani dama " ba damuwa ka ajiye ta a chan in but banason taye hulda da yara na ko kaɗan banson tarbiyyar waje and then kar ta kuskura ta zo hanyar part na masu gida that's all ..





Ya miƙi ya gyara rigar sa magana ya ƙare .. Mommy ce ta hura hanci da harara ta bisu ta bude sama part nata " Nagode Daddy"


Ita dai Na'eema ko a jikin ta tana latsa wayar ta hankalin ta ma baya kansu , Nazifa ce tabi Bayan Mommy tana ta kallon Indo kamar cewa zamu haɗu , Laila da Na'iba suka hararre kansu suka wucce ɗakin su , don sunsan idan har Dr sadeeq na nan basu da daman magana duk da cewa yana da sanyin hali hakan bai hana su tsoron sa ba don yana hukunta su dai dai da laifin su .....





Dr Kamal suka fita harabar gidan ya dafa kafaɗarsa da cewa " komai zai wuce naga tashin hankali da ƙiyayya dudde make sure ba wanda yasan maganar nan zamu rufe ta har lokacin yayi musan matakin da zamu ɗauka just relax and pray" in Sha Allah Kamal Thank you ka huta gajiya gd night,"


Indo na biye dashi cikin tsoro da fargabar da ta shiga ganin kamar za'a babbbaka ta da ranta su yi tafiya mai ɗab nisa a cikin gidan nan ya tsaya sai ga wata macce bazata haura shekaru talatin ba ta fito da plate na ta ganin sa yasa ta durgusa inya mura ce da alama ko Hausa bataji ba yaceata ta kirawo Lami maid haka suke ce mata da okay sir


yana tsaye yasa hannu a cikin aljihun sa sai gata ta fito tana ɗan sauri don tsoron ganin sa take a part nasu, kusan tunda take aiki bai taɓa zuwa nan ba sai dai ya kira ta a waya " yallaɓai Barka da dare ta faɗa cikin zagewa Barka ya aiki ta amsa da zumudi saboda ko ba komai yau Dr sadeeq ya mata dogon magana ( batasan da cewa Indo ta fara sauya shi ba ne )


Lami maid ga wanan yarinyar her name is Indo Inason ke bata kulawa a bata daki ke nuna mata komai da zataye amfani dashi Please zan ƙara miki salary akan hakan " okay sir no problem in Sha Allah zan kula da ita " OKAY Indo gd night " nan tasa ido zata marairaicewa zagaye kuka " No Indo anan zaki zauna zan shigo gobe " ya faɗa ba alamar dariya hakan yasa tasha jinin jikin ta duk da cewa bata jin tana tsoron a'a Amman sai ya mata wani kwarjini na musamman, tana ganin sa har ya ɓace





Cikin Mammaki da Lami maid take kallo tace " zo nan yarinya " Dakuna ne guda shida a Jeri kowace da toilet a ciki dakin ba komai sai matress da karamin pillow da sanyin tiles sai fanka Lami maid ta kuna fanka ta kashe nan tace anan zaki zauna suka shiga toilet ganin Indo a matsayin Yar ƙauye dole ta nuna mata komai a toilet in " Haba ai na iya Lami maid ɗazun Dr Balarabe ya koyamin tace cikin ɗan zagewa , waye Dr Balarabe kuma Lami maid ta tambaya tana miƙiwa daga durgusawa da taye shiru Indo ta mata don ta tuna cewa Dr sadeeq yace mata banda surutu dewa nan ta kwanta kawai ba amsa Lami maid take shiru to idan kinason wani abun ɗaki na ne anan kusa da take " da to ta amsa ta rufe mata dakin





wasu sirarran hawaye ya biyo ta ta dungule gu ɗaya saboda tsoron kwana ita kaɗai da rashin sabo





Gd night












PG





3️⃣0️⃣






Kwana Bakwai Bayan Zuwa Abuja...


Yau kwana bakwai kenan Indo tana zaune a part na maid — wuri mai ɗan faɗi amma cike da shiru da sanyi.
A duk lokacin da safe ta waye, rana ta sake, ko dare ya yi duhu, zuciyarta ta rika bugawa kamar ana kiranta da sunan gida. Kewar ƙauye ta cika mata rai kamar zafi.


A lokacin da ta iso nan, ta taɓa ganin fuskoki biyu kacal — Lami ce kawai, jagorar masu aikin gida, wacce take mata kallon sabuwa kamar wata ƙaramar yarinya. Ita ce ke kawo mata abinci kullum a faranti, ta ajiye ta tafi ba tare da wata magana ba.
Lami mace ce mai sanyi, amma idanunta suna da nuni — irin wanda ke cewa “Ki nitsu ki koyi yanda ake zama a nan.”
Indo kuma bata ma san yadda zata fara shiga ba, ta kan karɓi abincin cikin rawar jiki, ta ce “na gode” da ƙyar, sannan ta koma cikin ɗaki ta ci ta yi shiru.


Kullum ta kan zauna kusa da taga tana duban filin koren lambu da ke bayan gidan. Wani lokaci sai ta ji ƙamshin turaren wuta daga babban ɓangaren Mommy, sai zuciyarta ta tsaya, tana tunanin“Ashe nan ne aljanna da nake tunanin mutuwa ake shiga? To amma meyasa nake jin kewa haka a ciki?i ta juya gefe tana hawaye.
Ta tuna su Dijje, su Mama, da ƙauyen su da ƙamshin ƙasa bayan ruwa.
“Allah ka dawo dani gun su... amma ance in zauna nan, to bari in zauna,”
ta kan faɗa a hankali tana rufe kanta da bargo.






Dr. Sadeeq kuwa bai sake zuwa gunta ba bayan ranar da aka fara zama. Amma Lami ta gaya mata cewa yana wajen aiki sosai, kuma Mommy bata so ta tambaye shi komai.
Hakan yasa Indo ta kulle kanta da shiru, ta zama kamar inuwa a gidan nan.


Sai dai duk da haka — ba ta rasa irin nata ƙauyanci mai dariya ba.
Ranar Litinin, lokacin da Lami ta kawo mata tea, Indo ta tambaya da mamaki:
“Wannan ruwa ne mai ƙamshi da sukan sha da safe?”
Lami ta yi murmushi tace,
“Ai ba ruwa bane, shayi ne.”
Indo ta ɗan kurɓa ta ce,
“To wannan shayi ɗin yayi kamar maganin sanyi!”
ta tabe baki, ta ajiye kofin gefe tana kallon bango kamar tana jin haushi da duniya.






Ranar Laraba kuma, tana share ɗaki sai ta ga kayan ta a wani bag da Dr. Sadeeq ya kawo mata sanda zasu taho tare . Tana buɗewa ta ga wasu riguna farare da tsadaddun takalma. biyu
Ta saka ɗaya ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, ta ɗan murɗa wuya tace:
“Kai Indo, ashe ke ma kin zama mai kyan gani kamar su A'isha Najamu...”
sai ta yi dariya ita kaɗai, sannan ta cire rigar cikin kunya ta ajiye, ta mayar da tsohuwar rigar ta ƙauye, ta sake zaune akan matress tana murmushi.






Amma duk wannan ba ya hana mata tsoron fita daga part ɗin.
Dr. Sadeeq ya gargade ta sosai cewa kar ta fita, saboda Mommy ba ta son ganinta a cikin gidan.
Saboda haka Indo ta mayar da kanta tamkar gidan yari, tana ganin ko ɗakin ta ma sai an ba ta izini kafin ta leƙa.


Sai kuma lokacin dare — lokacin da zuciyarta ke ta kai da komowa.
Ta kan ji sautin kiran sallah tace Dr. Sadeeq daga babban sashen gidan, muryarsa mai taushi tana ratsawa cikin zuciyarta.
Ta kan ɗago kai ta saurara, sannan ta ce a hankali “Allah Ya saka maka da alheri. Kai mutum ne mai kirki... amma gidan ka fa yana tsoro.”






Haka Indo ta ci gaba da rayuwa a Abuja cikin makonni na farko — tsakanin taushin rayuwar birni da ƙuncin kewar ƙauye.
Gidajen nan masu sheƙin fitila da ƙamshin turare sun zama kamar daji mai ado a idonta; abin kallo da tsoro a lokaci ɗaya.
Sai ta daura hannayenta a ƙirji tana cewa:


“Allah kai ne ka kawo ni nan, kai ka fi sani. Amma wallahi, duk inda suke yanzu, da su Dijje, da su Mai unguwa… na fi son in zama tare da su fiye da nan.”










Wannan daren Abuja ya kasance cike da natsuwa. Iskar sanyi tana kadawa cikin shuke-shuken da ke gefen gidan, fitilun lambu suna ta walƙiya kamar taurari a ƙasa.


Motar Range Rover black edition ta tsaya a bakin ƙofar babban gidan, fitilarta ta kashe a hankali.
Driver ya fito da girmamawa ya buɗe ƙofa ga Dr. Sadeeq ya fito cikin nutsuwa — sanye da zaffafan kananan kaya masu launin red , rigar t-shirt ɗin da ke manne da jikinsa mai ƙamshi, da three-quarter trouser da ya sa a ƙasa.


Hankalinsa a kwance, amma idanunsa sun nuna alamun gajiya da wahalar aiki. Duk da haka, ɗaukakarsa da salo ba su gushe ba — yana tafiya kamar wanda lokaci yake bin sa da ladabi.
Yana jawo car key, ya buɗe boot, sai aka ga manyan ledoji wasu na ruwan lemo, wasu kayan ciye-ciye, wasu kuma kamar kayan sawa


Yayi ƙaramar ajiyar zuciya.
“Alhamdulillah… at least yau na samu in huta.”


Yayi nuni da hannu ga driver ɗin,
“Kai Musa, kai kai kayan nan a part nawa. Ka ajiye su a parlour, sannan ka rufe min motar ”
Musa ya amsa da, “To, yallaɓai,”
yana ɗaukar kayan da girmamawa.
Sadeeq ya tsaya daga nesa yana kallon fitilun gidan, sai iska mai ɗauke da ƙamshin turarensa ta busa, ta haɗu da ƙamshin rain mint da yake shafa bayan wanka.
A lokacin agogo ya nuna 9:07 pm — daidai lokacin da shiru ya lullube gidan.


Ya shiga cikin sashen nasa, parlour ɗinsa ya amsa ƙamshin tsabta da wutar diffuser mai ƙamshin Oud & Amber.
Tiles ɗin suna sheƙi, kujerun leather sun yi sanyi, hasken fitila kuma yana ta walƙiya a hankali.


Yayi nufin bedroom ɗinsa kai tsaye.
A can ya jefa wristwatch, stethoscope, da coat ɗinsa a kan kujera, sannan ya shige toilet.
A cikin mintuna biyar, sautin ruwan shower yana ta zuba da sanyi.


Bayan ya fito, sai kallo ɗaya ka masa ka fahimci cewa gajiya ba ta iya ɓata masa kyan hali — jikinsa yana sheƙi kamar wanda aka shafa masa mai mai kamshi, gashin kirji mai taushi yana kwance kamar na wanda yake jin daɗin natsuwa.
Ya ɗauki tawul ya shafe kansa, ya sa vest farar fata da three-quarter ɗinsa, sannan ya fesa turare a ƙirjinsa.


Ya zauna a kan kujera kusa da gado, ya ɗauki wayarsa da take kan side table.
Sai ya danna lambar Lami – Maid Supervisor.


Ring ɗaya, ring biyu — ta ɗaga cikin ladabi “Yallaɓai, ina yini?”
Ya ɗan gyara murya cikin natsuwa, yana kallon agogo, “Lami, ki kawo min Indo nan zuwa part nawa yanzu. Ki faɗa mata ta zo.”






Lami ta ɗan yi shiru na kusan dakika biyar kafin ta ce“To yallaɓai… yanzu?”“Eh. Yanzu.”
Murya mai daɗi amma cike da umarniTa amsa da “Tooo…”






Sai ta sauke wayar tana murmushi a hankali cikin mamaki.
A ranta tana faɗi “Wannan ai abin mamaki ne… Dr. Sadeeq wanda baya ma kira ko a ɗakin girki, yau yana cewa a kawo masa baiwa? Lallai akwai dalili wacce ce Indo.”






Ta mike a hankali, ta tashi daga kujerar da take zaune, ta tafi wajen part na maid — zuciyarta tana bugawa da tambaya iri-iri.
“Wacece Indo haka da har yallaɓai kansa ke neman ganinta?”






A gefe guda kuma, Dr. Sadeeq yana zaune cikin shiru, yana latsa wayarsa, hasken screen ɗin na haskaka fuskarsa.
Idanunsa suna cike da natsuwa, amma akwai wani abu a ciki — wani nau’in tunani mai zurfi, tamkar wanda zuciyarsa ke ƙoƙarin fahimtar dalilin da yasa yake tunanin waccan yarinyar tun safe har yanzu.


Sai ya ɗan jingina, ya furta a hankali kamar yana magana da kansa “Indo… I hope she’s fine.”








Indo na kwance cikin doguwar riga, rigar da Dr Sadeeq ya bata tun ranar da suka hadu a cikin tashin hankali. Idonta jajaye kamar ta shafe awanni tana kuka, fuskarta cike da bacin rai da gajiya.


Sai kawai taji an tura kofar da sanyi — ƙarar “kreeeech” ya katse shiru. Ta tashi a razane tana zaton wani ne, sai taga Lami ce, mai girman jiki, hannunta riƙe da wayarta.
Indo, Dr Sadeeq na kiranki… yace na kawo ki part dinsa.






Indo ta tsaya cak — zuciyarta na bugawa da karfi. Murmushi mai rauni ya bayyana a fuskarta.Dr Balarabe da gaske?






Lami ta kalleta da ɗan mamaki Lami: Eh, shi da kansa yace. Ki shirya mana, ai bamu da lokaci.






Indo ta tashi a hankali, tana murza hannayenta cikin sanyi. Tana tafiya, zuciyarta cike da tunani — me yasa ya nemeta bayan kwanaki bakwai?
Kuma tana zumudin ta gansa ko zataji sauki
Suna isa harabar part ɗin Dr Sadeeq. A cikin gidan shiru ya mamaye, sai ƙamshin turaren oudh da iska ke yawo dashi. Lami ta tsaya a bakin ƙofa, tana duban Indo da tambaya a idonta.
To, gata nan Yallaɓai Ta juya zata tafi.
Dr Sadeeq (muryarsa mai zurfi): Okay, you can leave, Lami.






Lami ta fita tana girgiza kai, zuciyarta na tambaya — wace irin maid ce wannan da Dr yake nema da kansa?


Indo ta tsaya cak. Su haɗa ido — Dr Sadeeq yana zaune a kujera mai fatan nan, sanye da three-quarter da vest, gashin kirjinsa a warware, fuskarsa a cike da nutsuwa amma idanunsa suna da wani launi daban — kamar yana cikin tunani mai nauyi.


Ganin Indo ta rame, ta faɗi ƙasa, idonta kumbure, yasa shi miƙewa Dr Sadeeq: Subhanallah, Indo… what happened to you?






Cikin rawar murya ta fashe da kuka. Ta gudu kai tsaye ta faɗa jikinsa kamar

16 / 48