DR SADEEQ COMPLETE HAUSA NOVELS BY NARNAH KANWAR SOJA.txt

Author :  Nana Kanwar Soja Category :  Hausa Read

Chapter   15 / 48

42K to 45K   out of 141.3K words

a titi, ta ce,
“Kai duk sun yi kyau wallahi, gashi kowa yana sanye da riga mai haske, ba kamar mu da kaya na ƙasa ba.”






Kamal da Sadeeq suka yi murmushi, suka ce a tare, "Welcome to Abuja.”






A haka suka tsaya a bakin gidan. Indo ta kalli su Dijje waɗanda ke kuka a kofar gida lokacin da suka tafi, sai hawaye ya fara zubo mata. Ta kalli Dr. Sadeeq ta ce,
“Na bar su suna kuka, amma zan dawo na ɗauke su idan na zama babbar likita.”






Dr. Sadeeq ya ji kalmar likita ta sosa masa zuciya. Ya ɗan gyara murya cikin taushi,“In sha Allahu, za ki zama likita. Amma yanzu ki yi haƙuri. Mu shiga ciki.”






Ya buɗe ƙofar mota, Indo ta sauka tana ta kallon gidan mai tsabta, har sai da ta ce: “Subhanallah! ai nan sai manya suke zama.”






Sai ya kalle ta da murmushi mai ɗan sanyi a fuskarsa.
A zuciyarsa kuwa yana faɗin, “Allah ka bani ikon kare amanar da aka ɗora min.”




Suna sauka daga mota Indo ta fara zare ido kamar wacce ta shigo duniyar da bata taɓa gani ba. Gidan yana sheƙi da haske, korayen shuki da furanni suna ta rawa da ruwan ban ruwa, iska kuma tana kaɗawa cikin sanyi da ƙamshin turare mai daɗi. Indo ta saki baki tana kallon ko’ina, ta ji kamar an jefa ta cikin aljanna.


Ta leƙa ta taga tiles masu sheƙi tamkar madubi, sai ta sunkuya ta taɓa — sanyi! Tana ɗaga hannu ta ce a hankali, “Wayyo Allah na, wannan ƙasa ba ƙasa bace wallahi!” Ga ƙauyanci nan ya bayyana duk da ƙoƙarin da take yi ta boye.


Masu gadi suka tsaya suna kallonta suna murmushi, shi kuma Dr Sadeeq ya ja hannunta cikin ladabi ya ce, “Let’s go in, Indo.”
Amma jikinta har rawa yake — ko takunta a cikin wannan gidan sai ta dinga ɗaga ƙafa kamar wacce take takawa a wuta.


Da suka shiga ciki, sanyin AC ya doke ta. Ta taɓa ƙirjinta da sauri, idonta ya kai ga fitilun da ke sheƙi a sama, ga wani ƙamshi yana yawo kamar kashin furanni.
Sai ta ce da muryar mamaki, “Toh! Ashe haka ake rayuwa a aljanna?!”


A ƙasa kuma ta ga carpet mai laushi kamar soso. Tana taka ƙafa sai ta maƙale, ta yi ƙoƙarin janyewa ta kasa, sai ta durƙusa tana kallon ƙafarta.
Dr Sadeeq ya ce, “Take it easy Indo, kin sa ƙafa ne da ƙarfi — wannan carpet ɗin ba irin ƙasan ku bane.”


Ta ɗaga kanta, idonta cike da mamaki, ta ce da murya mai ɗan kuka, “Na rantse, ai bazan iya tafiya da wannan takalmin ba, ku bari in tafi da ƙafata haka. Wallahi, wannan ƙasan kamar ruwan sanyi ne!”


Dr Kamal, wanda yake gefe yana kallon su da murmushi, ya kasa daurewa. Ya ɗan tabe baki yana dariya yana cewa, “Ya Allah! Wannan dai ba Indo bace — sai ace ta dawo da gidan gaba ɗaya da tambayoyi.”


Da wannan maganar suka fashe da dariya, har Dr Sadeeq wanda ba kasafai yake dariya ba, sai ya kasa jurewa. Indo kuwa ta tsaya tana kallon su da mamaki, ta haɗe hannu tana cewa, “Ashe ba sai an mutu ake shiga aljanna ba! Wallahi wannan wurin aljanna ne kai tsaye. Ku barni, ina so in kira Mama na ta gani.”


Dariya ta sake tashi sosai. Dr Kamal har yana riƙe ciki saboda dariya, yana cewa, “Haba Indo, ki amma kar ki ce mun ɗauke ki zuwa sama!”


Sai Dr Sadeeq ya girgiza kai yana murmushi, ya ce, “Come on Indo, relax. Wannan dai gida ne, ba aljanna ba.”


Ta ɗaga kanta da sauri ta ce, “To amma idan gida ne, me ya sa yake yin ƙamshi haka? Me ya sa ƙasan sa kamar ruwa ne?”


Ya ce cikin raha, “Saboda ana tsabtace shi kullum, Indo. Ki ga, ba kamar ƙauye ba ne.”


Ta juya ta kalle shi, ta haɗe hannuwa kamar mai roƙo ta ce, “Toh don Allah, ka barni in kwana a nan a ƙasa, bazanlalata carfet ɗin da ƙafata ba.”


Sai suka sake dariya gaba ɗaya. Dr Kamal ya ce cikin tsokana, “To ai idan haka ne, dole mu sayar da kujeru — mu saka katifa a ƙasa saboda Indo.”


A wannan lokaci Indo ta yi ƙasa da kai tana murmushi, amma zuciyarta cike da mamaki da tsoro da farin ciki a lokaci guda. Duk inda idonta ya kai sai ta ga wani sabon abu — hotuna masu kyau, fitilu masu kyan haske, kayan daki masu sheƙi. Ta ji kamar mafarki take ciki.


Da suka isa falon baƙi, sai Dr Sadeeq ya ce, “Sit here Indo.”
Ta tsaya tana kallon kujerar, ta ce a hankali, “Toh ai wannan kujerar zata fashe idan na zauna — saboda tana yin laushi.”


Dr Kamal ya ɗan bubbuga kafa yana dariya, “Kai Sadeeq, wannan yarinyar zata bani dariya har yau ta kare.”


A haka dai suka zaunar da ita cikin natsuwa, tana zagaye idanu tana jin kamar sabuwar duniya ta buɗe a gabanta.














NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️🤌












PG 2️⃣8️⃣









Mommy ce ke saukowa daga saman bene tana latsa wayarta a hankali, tana kallon sakon email da aka turo mata daga ofis. Rigarta ta silk ce mai launin sky blue, ƙafarta kuma da takalmi mai laushi amma yana ɗan buga tiles ɗin falon.


A zahiri Mommy mace ce mai nutsuwa, amma idan akwai abu guda da bata jure ba — to shi ne hayaniya. Ita dai ta fi son natsuwa, tsabta, da mutane masu sanin lokacin magana.


Sai kawai taji hayaniya a ƙasan falon, murya cike da dariya da tsokana. A hankali ta tsaya cak tana kallon ƙasa daga saman tangamemen matakala. Idonta ya sauka akan wata yarinya sanye da doguwar riga, zubin ƙauye a gefen jakarta, gashin kanta a ɗaure da ƙaramar zani, tana ta zare ido tana kallon ko’ina kamar wacce aka jefa cikin duniyar da bata taɓa gani ba.


Mommy ta ɗan dafe goshi, ta furta a hankali:
“What on earth… who brought this villager…?”


Sai ta ƙare kallon Indo daga ƙafa zuwa kai, ta girgiza kai a hankali cikin mamaki.
“This can’t be happening in my house,” ta faɗa a ƙasan zuciyarta.


A daidai lokacin, sai ta ji motsin ƙofar waje — su Layla ne, da Nabilaa ‘ya’yanta biyu masu kyan gaske, suka dawo daga makaranta cikin uniform ɗin su masu tsabta, da suka shigo suka tsaya cak, saboda abin da idonsu ya hango.


Layla ta ɗan matsa kusa da yan uwanta ta ce cikin ɓoyayyen dariya,
“Eww… who’s that? She looks like she just came from the farm.”
Nabila ta ɗan ƙara dariya yana kallon Indo da hannu a baki. Indo kuwa ta tsaya tana kallon su da murmushi mara gaskiya, zuciyarta tana dukan doom doom doom saboda irin kallon da ake mata.


Sai Mommy ta nufi ƙasa daga bene a hankali, ƙamshin turarenta ya cika falon. Tana sauka ƙafarta tana yin ƙara tap tap tap a kan tiles, fuskar nan ta cika da mamaki da rashin fahimta.
Mommy ta tsaya cak a tsakar falon, idonta na kan Dr Sadeeq kamar zata huda shi. Tana kallon Indo daga sama har ƙasa, ta hango ƙazantar ƙafarta da yatsun da suka bushe kamar ta ɗan aikin gona. Sai kawai ta dafe kanta tana numfashi da ɗan bacin rai.



Kafin ta buɗe baki, Dr Sadeeq ya fito daga gefe cikin hanzari yana cewa da ladabi,
“Mommy, I need to talk to you about something important, please…”


Amma kafin ya ƙarasa, Mommy ta ɗaga hannu da sanyi amma da murya mai cike da iko ta ce:
“Before that, I need to know — who is that village-like beggar girl standing in my living room?”


Gaba ɗaya falon ya yi shiru. Indo ta ɗan ja baya, ta dafe jakarta, idanunta suka cika da hawaye amma ta daure.


A take zuciyar Dr Sadeeq ta fara bugu doom doom doom doom. Kamal da ke gefe ya yi ƙasa da kai yana murmushi da sauri, yana cewa a hankali, “Oh boy, this one na serious wahala.”


Sai ga ƙarar ƙofa — Daddy ya fito daga ɗakinsa da hula a kai da tasbihi a hannu, yana shirin fita masallaci. Idonsa na farko da ya sauka a falon, sai ya tsaya cak.


Ya kalli Mommy, sai ya kalli Indo, sannan ya ce da muryarsa mai ƙarfi:
“Subhanallah! Sadeeq, Kamal… what is happening here? Who brought this stranger into my house?”


Indo a take jikinta ya fara rawa. Ta kama gefen kujerar kusa da ita kamar za ta ɓuya, zuciyarta ta ce:
“Wayyo Allah, irin kallon nan kamar za su ci mutum da ido.”


Dr Kamal ya ɗan share gumin goshinsa yana murmushi cikin tsokana, “Sir, take it easy… she’s not a stranger exactly—”


Kafin ya ƙarasa, Mommy ta ɗaga hannu cikin gaggawa:
“Please, Kamal, keep quiet. I’m talking to Sadeeq now.”


Dr Sadeeq ya ɗan nisa da ƙasa, ya ce da tausayi,
“Mommy, Daddy, please… bari in faɗa muku komai. Ba kamar yadda kuke tunani bane. She’s… she’s someone special — kuma akwai dalili da yasa ta ke tare da mu.”


Mommy ta ɗan ɗaga gira, ta ce cikin murya mai taushi amma da sanyi:
“Special? In this house? Sadeeq, you know how we live. We don’t bring anyone without class into this family.”


Sai Daddy ya kalle shi da mahaukacin kallo, ya ce:
“Bari in dawo daga masallaci, amma ka tabbatar da wannan yarinyar ba ta kwana a nan sai mun gama magana.”


Ya fice daga falon a hankali.


Indo kuwa, sai ta zame gefe ta zauna, jikinta har rawa yake, tana kallon falon da hawaye a ido. Tana faɗin a zuciyarta:
“Ashe nan Abuja ɗin ma akwai mutanen da zasu ɗauki mutum kamar ƙasa.”


Sai ta ɗan share hawaye da gefen zaninta, ta ɗaga kai tana murmushi mai rauni.
Dr Sadeeq kuwa ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa cike da tausayi — amma ya san lamarin ba zai zama mai sauƙi ba.


Dr Kamal ya ɗan matsa kusa da shi, ya furta a hankali cikin raha:
“Welcome to the war zone, my friend. Mommy’s not gonna let this one go easily.”


Sai Sadeeq ya ce da murya mai taushi,
“Then I’ll fight for it. Because I know she deserves better.”








“Sadeeq,” ta kira sunan nasa a hankali, amma cikin murya mai ɗauke da umarni.
“Ka fita da wannan ƙazantar ɗakin nan. Please! Kafin insha’e prayer — mu haɗu sannan zaka yi magana. I don’t want to see her here again, do you understand?”


Tana faɗin haka ta juyo ta haura sama cikin fushi, ƙamshin turarenta ya biyo bayanta. Su Layla suka bita da dariyar da suka ɓoye, suna taɗi da TikTok slang kamar suna kallon wacce suka rasa ko mace ce ko jaruma.


Indo dai ta tsaya cak, ta kasa motsi. Idonta suka cika da hawaye, zuciyarta tana tsalle kamar ana danna ganga a ciki. Cikin firgici ta kama gefen rigar Dr Sadeeq da hannayenta biyu kamar wacce ke neman tsira daga wani hatsari.


“Wayyo Allah… ban yi komai ba,” ta furta a hankali da rawar murya.


Sadeeq ya ja numfashi ya dan taɓe baki, yana kallonta da tausayi.
“Indo… calm down please. Ki kwantar da hankali. Mommy ba ta daɗe tana fushi ba, zata fahimta daga baya.”


Sai ya kalli Kamal da yake gefe yana ɗan dariya da kyar ya ɓoye, ya ce masa,
“Kamal, muje part ɗina Bari ta huta kafin sallah.”


Kamal ya ɗaga kai da murmushi, yana dariya a zuciya.
“Okay boss, amma this is just the beginning oh.”


Suka fito a hankali daga babban falo suka shiga wing ɗin sa
Gidan nan ya cika da kayan alatu — wall frames, dim lights, da leather seats masu laushi. Indo ta kasa ɓoye mamakinta, tana kallon komai da bakin buɗe, kamar wacce aka kawo gidajen sama.


Sadeeq ya nuna mata kujera ya ce da sanyi:
“Zauna anan, ki huta. Kafin mu je masallaci.”


Ta zauna da natsuwa amma har yanzu tana girgiza kai, tana faɗin a hankali:
“Wayyo Allah, ba na son ta min fushi. Na ga idonta kamar na zakara.”


Dr Kamal ya yi dariya da kyar ya ce,
“Don’t worry Indo, idan kin saba da Mommy, sai kice itace mafi kyau. Amma yanzu dai… sannu. Ki zauna lafiya.”


Sadeeq ya nuna mata toilet ɗin da ke cikin parlour ɗinsa
“Ga bandaki can, Indo keje ki ɗauro alwala, sai mu shirya sallah.”


Amma ai bai kai ga ƙarasawa ba, Indo ta ɗan ƙanƙame jikinta, ta kalle su da mamaki.
“Alwala kuma? Wacce irin macece wacce ake ce mata ta ɗauro wudhu ? Ni fa ba wani ruwa zan sha ba idan ban ga guga ba…”


Kamal ya kalli Sadeeq ya kafe da murmushi, yana ɓoye dariya.
“Wallahi this is gonna be fun, my guy.”


Sai Sadeeq ya rufe fuska da hannu yana nishi.
“Oh my God… Indo please, bari in nuna miki. Ki kalli yadda ake.”


Ya tashi cikin nutsuwa, ya nufi bandaki, ya janye labule, ya kunna tap. Ruwan ya fara fita daga sink yana yin shhhh… Indo ta ja da baya cikin firgici.


“Wayyo Allah! Ruwan nan daga sama yake fitowa? Babu guga, babu kwano?!” Kamal ya fashe da dariya yana jingina da bango.
Sadeeq kuwa ya kalleta da natsuwa, amma yana jin wani irin nauyi a zuciya — tsakanin dariya, tausayi, da gajiya.


“Ki kalli yadda ake, Indo,” ya ce cikin ladabi, “Babu hatsari, ruwan nan daga famfo yake fitowa, ba aljani ke jefa ba.”


Indo ta ɗan ja tsaki tana kallon ruwan kamar za ta tambaye shi sunansa.
“Toh idan ya cinye ni fa?”
“Don Allah ki hanzarta kafin Daddy ya dawo.”


A haka suka ci gaba — shi yana nuna mata yadda ake wudhu, ita tana ɗan kwabe fuska tana kwaɗayi ta tambaya me ake yi da ruwa haka da dare.
Bayan wani ɗan lokaci, Sadeeq ya ɗan nisa da numfashi ya ce:
“Good. Yanzu ki je ki yi sallah, Indo.”


Sai ta ɗaga kai da jinƙai, ta ce da dariya:
“Ni dai ina so in gama karatun nan da aka ce zanyi, amma wallahi Abuja ta ban tsoro.”


Suka kalli juna suka yi murmushi.
Dr Kamal ya ce da raha, “Abuja fa kawai ce… Amma Indo, yanzu dai kin fara sabon labari — kuma ni ina jiran episode ɗin gaba.”


Suka fitta suka barta da cewa taye sallah.........





NI KUWA NACE SU MOMMY WAI ZAKI FARA HAYANIYA IDAN DAI KINA TARE DA INDO ,, DON MA TAYE SANYI GA KUMA TSORON BIRNI .......















PG


2️⃣9️⃣











Dukkan gidan ya lullube da shiru mai nauyi. Fitilun falon suna sheƙi, kamshin turaren oud da bakhur yana yawo cikin iska, yana haɗuwa da sanyi mai ɗan ɗaci daga AC.
Daddy yana zaune a babban kujerarsa mai launin cream, Mommy a gefe tana kallon TV, su Layla suna zaune suna ta latsawa wayoyinsu da murmushin rainin hankali.


Kofa kawai sai ta buɗe.
Dr Sadeeq ya shigo cikin natsuwa, Dr Kamal yana bayansa yana ta wani ɗan murmushi, sai kuma Indo — cikin riga mai sauƙi, kanta ɗauke da ɗan gyale, ta tsaya kamar wacce ta shiga kasuwa ta rasa inda zata kalli kaya.


Idanunta suka fara bin falon — carpet ɗin, kujeru masu sheƙi, gilashin chandelier mai kyalli kamar rana, sai ta ɗan turo baki tana ambaton zuciyarta,“Innalillahi... to ashe haka gidan Aljanna yake...” ta ji idanu suna binsu kamar wuta.
Layla ta ɗan murmusa cikin raini, tana ƙarasawa kusa da Mommy ta faɗa mata a hankali:
“Mommy, who brought that village looking girl here? Look at her feet, she’s even barefooted.”






Mommy ta ɗaga kai daga wayarta, idonta ya sauka a kan Indo. Kallo ɗaya ya wadatar wajen bayyana yadda take ji — ƙyama, raini, da mamaki.


Dr Sadeeq ya ja numfashi, ya kama hannun Indo yana ƙoƙarin ya sa ta zauna kusa da kujerar sa.
“Please Mommy... Daddy... just let me explain. This is—”
“No!” Daddy ya dakatar da shi da ƙarfi, murya ta cika falon.
“This will never happen in my house. What nonsense is this, Sadeeq? Who is she?”






Indo a take ta firgita, ta yi baya tana zare ido, har sai Dr Sadeeq ya sake riƙo hannunta, yana cewa cikin sanyi,
“Calm down Indo... nothing will happen. Just sit.”






Amma muryar Daddy ta kara tashi:
“You dare bring this thing into my home? Look at her! Who is she to even step her foot here? I said she must get out!”






A lokacin ne Indo ta shiga girgiza kai, idonta ya cika da hawaye, ta ce cikin rawar murya:
“Don Allah kuyi haƙuri... ban san komai ba... wallahi ban aikata komai ba...”






Kafin ta ƙarasa, sai Daddy ya ɗaga hannu cikin bacin rai, yana cewa:
“Shut up! You don’t talk when elders are speaking!”






Zuciyar Dr Sadeeq ta buga kamar ana bugun ganga. Idanunsa suka ɗan sauya launi, bai taɓa ganin mahaifinsa cikin irin wannan fushi ba.
Indo ta yi ƙasa da kai, ta soma kuka a hankali, sai kawai ta matsa kusa da shi tana ɓuya a jikinsa, tana girgiza kai


A lokacin Mommy ta miƙe tsaye, da wani kallo mai ƙarfi — tana nuna su da yatsa,
“Sadeeq! You let that dirty girl touch you? Are you out of your mind? This is disgusting!”


Layla ta rufe baki tana dariya a gefe, tana faɗa wa Na’iba: “Maybe he brought her for some village experiment.”






Dr Kamal dai ya sunkuyar da kai yana danne dariya da tausayi, amma idonsa na nuna masa cewa bata fiye daɗe da halin nan ba.


Sai Daddy ya ƙara da cewa cikin tsawa:
“Take her out of my house right now before I lose my temper! I won’t allow this kind of shame under my roof!”






Dr Sadeeq ya dafa kansa, zuciyarsa na bugawa, ya ɗan ɗago yana kallon su duka.
Muryarsa ta yi sanyi amma cike da ɗaci“Daddy, please... you don’t understand yet. She’s not who you think she is. Just let me explain... please.”


Sai Mommy ta ƙara harararsa da cewa:
“You brought a filthy village girl here, holding her hand in front of us, and you expect us to listen? You’ve embarrassed us enough, Sadeeq!”






Indo ta kai hannu ta share hawayen ta, "Don Allah kuyi haƙuri ne marainiyya ce Dr Balarabe" kafin ta karasa yasa hannu ya rufe bakin ta "just shut up Indo"




Wannan kalmar ta janyo shiru.
Daddy ya ɗan dakata, ya sauke numfashi, amma kafin ya ce komai, sai Mommy ta ce cikin ɗaci:“So now we are turning this house into an orphanage?!”






Dr

15 / 48