Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
na yi kokarin ganin na koma hannun uban yarana har yana jaddada mini cewa idan ba tsautsayi ba babu wani dalilin da zai sanya shi rabuwa da matarsa saboda rayuwar yara na shiga garari."
Inna Uwani ta dinga galla mata harara kafin ta ja tsaki ta furta." Ke har wani shiga garari kike hangowa yaran da suke da uba irin Alhaji Tajo. Suke kuma da uwar riko irin Amina. Wannan ba hujja ba ce amma tunda kin ce haka ba zan hana ki ba wata'kila gaskiya ne yana buk'atar kudin ne domin d'orawa akan kasuwancinsa tunda har ya amsa tayin da ki ka yi masa sai ku yi abin a sirrin ce yadda babu wanda zai gane da wata manufar kuka shirya auran...........✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *🔚 ALHAMDULILLAHI*
*177*
*SADAUKARWA GA IYAYAN DA ALLAH YA JARABTA DA FITINANNUN YARA IYAYEN DA ALLAH YA JARABTA DA HAIHUWAR YARA MASU DAUKE DA LALURAR JINI SIKILA. SADAUKARWA GA JAJURTATTUN MATAN DA SUKA YARDA DA RUSHEWAR FARINCIKI SU DOMIN JIN DADIN YARANSU. SADAUKARWA GA MAZAN DA SUKE HAKURI DA JIMIRIN RIKON MARAYA. SADAUKARWA GA ILAHIRIN MASOYA MAGOYA BAYANA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA BINTA NA GODIYA NA SAKE GODIYA ALLAH YA SAKA DA ALHERI LITTAFIN GUDUN AURE BIYU NE A MADADIN DAYA DOMIN YA YI MUTUKAR TSAYI SOSAI YA ZAMA COMPLETE A TELEGRAM 2K DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA SHI*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*177*
Wannan shine tunanin Hauwa wanda babu technology ko kad'an a cikinsa. Lokacin da maganar ta fasu a cikin danginsu sun yi mamaki da k'ananun maganganu amma ganin yadda Sadiya ta goyu da bayan auran ya sanya kowa bakinsa ya mutu. Ita kanta Hauwan ta yi mamaki sosai amma da ta tuna cewa auran kwangila ne sai hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko mijin nata ya gaya mata yadda suka shirya wata uku kacal za su yi su rabu. Gabad'aya lokacin idonta ya gama rufewa babu abinda take da buri illah a dauran auran wattani uku suka cika ya saketa kamar yadda suka yi alkawari zuciyarta bata ta'ba yi mata kokwanton wani lamari zai iya kasancewa ba.
Ba mu da labari daka ni har maigidan sai saura kwanaki biyu d'aurin auran Hajja ta kira shi a waya muna tare a dakinsa take gaya masa Hauwa za ta yi aure Inna Uwani ta kira tana gaya mata nan da kwana biyu za a d'aurin auran. Bai shiga wata wata damuwa ba ya yi fatan alheri suka d'an ta'ba hira kad'an kafin su yi sallama ya kashe wayarsa.
Na d'auka zai d'an nuna kishinsa ko yayane tunda sautari wasu mazan sun tsani su saki mace su ji da gaggawa ta yi aure duk da nasan babu wata soyayyar kirki a tsakaninsu amma ai sun haihu zai d'an ji wani iri sai kawai ma na ga ya d'auki Mufida yana yi mata wasa yarinyar ta yi gwa'bi babu lefi amma dai da mutukar bambanci a hallita a tsakaninta da yan uwanta tun bayan haihuwarta sau biyu kacal ciwon ya motsa mata dalili muna mugun kiyayewa da bin ka'ida cikin kowane yanayi koyaushe tana hannuna na ri'ke na goya idan ta kama. Allah Ya jarrabe shi da masifar sonta sosai saboda dalilai bambamta sunan Mamansa sannan kuma 'ya macace mai rauni mai kuma rangwamin lafiya. Zahiri ya so Minal amma kamar yadda Khalil ya fad'a kwanakin baya yanzu dai Mufida ce ke kan karagar mulki don ni kaina idan muna tare bai fiye ba ni lokacinsa ba. Idan ya d'auketa sai su yi ta wasa itama ta yi sabo dashi tana ganinsa za ta dinga mik'a hannunta tana 'bangale baki ga shi kamarsu daya bayan yanayin ciwonta ta kwashi yanayinsa ta kowane sashi mussaman k'aramin jikin shiyasa abin ya yi yawa 'kank'anuwa ce sosai amma dai babu rama ta tashin hankali a jikinta a murmure take.
Na kasance sosai cikin nazari da tunanin auran gaggawar da Hauwa za ta yi k'asa da wata hud'u da mutuwar auranta babu abinda zuciyata ba ta gaya mini ba akan haka. Wani sashi na zuciyata na gaya mini wata'kila ta samu wanda take sone kuma mai wadata da wannan nazarin na yi ko'karin ganin na mantar da kaina lamarinta tunda Ubangiji ya datse alakarmu domin ba ni fatan ta sake dawowa cikin rayuwarta har abada addu'ar da a koyaushe nake yi kenan. Ina ganin status dinta jefe jefi tunda har yanzu muna da serving din lambar juna ban goge ba itama bata goge ba amma ba mu ta'ba yin magana ba idan ta d'ora ma ba ni dubawa saboda har abada ba ni buk'atar abinda zai k'ara had'a ni da ita. Dalilin da ya hana ni goge lambarta kuwa saboda yaranta a duk lokacin da Khalil ya buk'aci magana da ita zan bashi lambar tunda duk tsiya ai ba canzawa towo suna dole itace uwarsu kuma ba zan d'auki aniyar datse alakar da take tsakaninsu ba kamar yadda koyaushe Babansu ke gayawa yaron ko za su je bauci wajenta sai sun girma ba yanzu ba yaron har ya gaji da bibiyar lamarin ya ha'kura abin yana yi masa ciwo ainun yadda ya damu da ganin irin rabuwar da iyayen nasa suka yi wadda duk wanda zai bud'e baki zai gaya masa cewa babu sauran gyara kuma sun karanta karatun a islamiyya.
****
To wani abu da Hauwa ba ta sani ba shine har yanzu Naziru yana sonta dama a rashinta ne ya auri Sadiya tunda a wancan lokacin ta raina samunsa k'aramin 'dan kasuwa ne yana sana'ar sayar da leda a kasuwa da abinda ya danganci buhu da bacco sai dai inda Allah ya taimake shi shagonsa ne ba haya yake yi ba. Kuma ya yi kokarin ganin ya gina gidansa mai d'akuna uku da shago a waje d'aya yake kiwon kaji biyu Sadiya take amfani da su shagon waje kuma yaransa da yake duk maza ne yanzu sun zama samari su hud'u suna amfani da shagon amma dai band'aki d'aya ne duk da shi suke amfani a cikin gidan. Haihuwar da ta yi ne a yanzu ta haifi mace wadda gabad'aya suka d'auki son duniya suka d'ora mata.
D'akin nan da yake kiwon kaji shi ya gyara mata aka yi sabon fenti da sumintin kasa amma dai duk da haka d'akin yana warin kaji tunda ya jima yana kiwon shekara da shekaru d'akin ya game da wari abin sai addu'a.
Ranar da aka d'aura auran ta tare suka kwana a daddafe shi a wajansa hakan ba komai bane tunda ya saba sha'kar warin k'ashin kajin da yake kiwo wanda suka hadu da dusar abicinsu. Ita kam a wajanta sabon lamari ne da take ganin ba za ta iya jura ba mussaman da wata gaisuwar kirki bata ratsa tsakaninta da Sadiya ba da gari ya waye ta yi tafiyarta wajan aiki gidan kaca kaca gashi bashi da wani girma k'udaje sai shagalinsu suke yi daga cikin d'akinta tana iya jiyo zarnin fitsarin samarin gidan da ya had'u da warin masai yake fitar da wata irin k'alla tunda na gargajiya ne. Sai shi da kansa ya zuba ruwa a bokiti ya wanke bandakin tukkuna ta iya shiga ta yi wanka yadda ya nuna ai hakan ba komai ba ne tunda ya riga ya saba Sadiya ba ta yin aikin gida sai ta dawo daga aiki to balle kuma yanzu da take ganin ba ita kad'ai ba ce matar gida. Da wannan matsalar aka fara domin dai rige-rigen shiga band'anki ake yi a gidan samarin yaransu duk nan suke uzurinsu har ma da abokansu idan sun zo wataran ma tana ciki tana uzuri za ta ji ana buga mata kofa wai ta yi sauri ta fito. Yaran da ada can suke ganin girmanta dalilin amincin da yake tsakaninta da Mamansu yanzu ko kallo ba ta ishe su balle su gaisheta. Aka dinga fafata rigima sadiya ta yi duma ta barta da yaran sai rashin kunya suke yi mata ita kuma duk abinda take yi na kasuwancinta bata fasa ba gari yana wayewa za ta tafi aiki ranar hutu kuma ta shiga kasuwa sare sare kayan da take sayarwa.
Sai ya zamana Hauwa ke aikin gida ta yi girkin rana da dare koyaushe idan ta yi masa korafin cewa babu ajadanar haka a shara'din auransu sai ya bita da lallami da dadin baki yana ce mata idan bata saki jikinta ta nuna auran soyayya suke yi ba mutane za su fahimci manufarsu. Hakan ya sanya take gyara gidan har ta yi griki ta kuma wanke bandaki Sadiya na wajan aikinta ta dawo kuma ta d'ibi abinci ta ci ta k'oshi ta yi mata duma kamar babu sanayya a tsakaninsu
Babu wata maganar arziki sai kame-kame sai hakan ya kara tayar mata da hankali gashi tun farkon tarewarta ta bashi dubu dari biyu da hamsin akan ya kama mata haya koyaushe idan ta yi magana sai ya ce mata gidan ne ba a samu ba. Haka ta yi wata biyu a daddafe a gidan lokacin sun yi fito na fito da Sadiya uwarka ubanka sun kuma yi wa kansu tononan silili har Sadiyan na fad'in indai Naziru ne gata nan gashi nan ai ba tomo ba ne kuma ta kama kafar wala tunda duk mazajen da suke gari ta rasa da wanda za ta yi auran kisan wuta sai da mijinta.
Lokacin ne maganar ta fasu a dangi iyayensu maza kowa ya san dalilinta nayin auran kisan wuta don ta koma gidan tsohon mijinta ne. Inna Uwani sai da fita ta gagareta saboda kunya da tashin hankali irin lalataccen kallon da 'yan uwan mijinta ke yi mata sai ta zama abin kallo ma domin
har gida aka dinga zuwa ana yin ala wadai da irin yadda ta bada goyon bayan aikata abinda Allah Ya haramta shi kuma Naziru ya riga ya gayawa mahaifiyarsa cewa bai auri Hauwa don ya saketa ba. Amma kuma ita sai ya ce mata idan har tana so ya saketa sai ta kara masa miliyan biyu kudi sun kama miliyan biyar da yake hankalinta a tashe yake da barin gidansa babu ja'inja ta kàra masa. Da wannan hanyar ya dinga kar'be mata kudi har sai da ya zama ya tatiketa tsaf kuma ya ce ba zai saketa ba saboda yana sonta dangi kuma kaf suka goya masa baya. Lamarin da ya janyo mata mummunan ciwo jininta ya hau aka dinga tiri-tiri da ita don har kwanciya ta yi a asibiti a lokacin ne muka samu labari ni da shi mun je kano hutu zai d'an gudanar da wani aiki Hajja take gaya mana halin da ake ciki domin dai duk yadda lamarin ke yi mata zafi a ranta sai da ta je har can bauchin ta duba jikin Hauwan ta kuma ce masa lallai ya tura mata da kud'i domin jinyya saboda babu tunda har ya yi rantsuwa akan janye kyautar kamfanin da ya yi mata ya ce babu amfanin mallakawa ma'kiyi abinda zai kawo masa cigaba a rayuwarsa. Mutum ne mai bala'in riko da tsananin gaba do dai yanzu an sake girma amma dai yadda ya'ki jinin Hauwa haka ya'ki jinin mutuwarsa sunanta 'yar ta'adda a wurinsa yana rangwatawa ne kawai saboda Hajja ta nuna tsananta gaba da kiyayyar bashi da amfani tunda an riga an hadu babu yadda za a yi da juna.
To ita ga da niyyar da ta yi aure amma ga yadda kaddarar takasance
A lokacin kuwa ya tura mata da dubu dari biyar ya kuma kira wayarta tun bayan rabuwarsu wata biyar kenan suka gaisa 'kasa k'asa nake yin maganarta tana magana a hankali ya dubata da jiki sosai sannan ya ce ta duba ya tura mata sa'ko. Ya mi'ko mini wayar wai tana son mu gaisa babu yadda na iya haka na kar'ba nasa a kunnena na ji maganarta a raunane kamar ma kuka take yi. Zuciyata ta d'an karye kad'an amma ban bari ta gane ba muka gaisa sosai na yi mata ya jiki ta tambayi yaran gabad'aya har da k'aramarsu Mufida na ce duk nuna nan lafiya lau.
Jin ta yi shiru ya sanya na mik'a masa wayarsa na ji yana gaya mata idan da buk'atar wani taimakon gaggawa ta sanar dashi daga haka ya kashe wayarsa.
Ko da muka keb'e bai bai tashi zancan ba sabgoginsa kawai yake yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tun kafin mu zo nasan dalilin zuwan tunda bai gaya mini ba ni ma ban nemi jin karin bayani ba Hajja ta kira ni a waya ta gaya mini yana yi wa Kamalu gini amma bata gaya mini wane iri bane shin na gida ne ko kuwa na makaranta.
Sati daya muka yi a kano muka koma abuja cikin yaranmu da suke samun kulawa wurin masu aikin da a yanzu nake ganinsu kamar 'yan uwana saboda yadda sha'kuwarmu da su ta kara tsananta. Babu wani sa'bani da ya sake giftawa tsakanina da shi tun bayan fitar Hauwa muka samu wani irin daidaito da kara kusanci ga juna gabad'aya hankali da tunaninnmu yana kan yaranmu mussaman ita wannan din da muka samu daga baya. Ban ta'ba jin ya yi wata magana da ta danganci neman cikin gurbin da Hauwa ta bari ba abinda na lura da shi ma a yanzu ba wannan ne a gabansa ba amma ta fannin abinda ya danganci mu'amula ta aure babu wani abu da ya yi rauni muna shan soyayya launi-launi domin ni dashi gabad'aya mun 'ki bari kanmu ya yi murfi yadda koyaushe yake d'okantuwa da ni haka nima nake kasancewa da shi kamar wata sabuwa dalili ina kasancewa cikin gyara kaina ciki da waje yadda zai ji dad'i ya kuma yi alfahari dani tare da dakushe masa sha'awar duk wata 'ya mace.
MURFI
Bayan shekaru biyar abubuwa da yawa sun faru masu dadi da marasa dad'i mun yi rashin Hajja haka zalika mun yi rashin Dada mata uku da suka taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu Gwaggo Hajja Dada duka sun amsa kiran Ubangiji suna masu tuba da tabbatar da ya'kini ga Allah. Yadda kowa yake ha'kuri idan ya yi gagarimin rashi haka mu ma duka muka yi hakuri 'ya'ya da jikoki masu aiki da hadimai tare da abokanan arziki. A cikin dai shekarun ne Kamalu ya taka mataki na mussaman fannin addini tauhidi tare da da'awa. Yaro ya yi bazata to amma ba abin mamaki ba ne idan har an yi duba da irin kalubale mabambamta da aka riska tun daga farkon kuruciya har kawo wa yanzu da aka cimma manufa babu shakka addu'ar iyaye tana da tsananin tasiri akan yaransu ba ma su kad'ai takewa tasiri ba har da wad'anda ke abota da su. Na ga zahiri domin ita addu'ar a yanzu na tabbatar da cewar itace take ri'ke da ni har na riski wannan lokacin cikin nutsuwa da hayyacina. Gwani Kamaludden Aminu Salihi a yanzu yana da masters degree (gwani) bayan fafutukar da aka sha wajan neman ilimi littafan addini tun daga kan al'kur'ani mai girma babbbak'u farfaru haddace shi da kuma rubuce shi. Idan muka zo kan kan litattafan addinin musulunci irinsu fi'kihu ahlari ishmawi iziya risala askari muwad'da malik muddawara kulasatunurulmubin, arba'una hadis, zadizzaujen. Wad'annan littafan addini ne da duk wani mai neman ilimi fannin da'awa ya karance shi Gwani Kamalu ya zauna zaurukan malamai da yawa domin k'arin sani kafin malamansa su bashi izinin zama kan mumbari a katafariyar makarantarsa da uban rik'onsa ya gina da sunansa mai suna *Gwani Kamaludden tahafizul-kur'an* Ya k'ara da gina massalaci kusa da makarantar domin zaman tafsiri da warware wata mas'alar idan ta taso wadda ta shafi addinin musulunci a k'arshe kuma ya ce ya nemo aure gidan mutunci da tarbiya domin k'ara samun goyon baya da nutsuwar gudanar da al'amuransa.
To rasuwar Hajja ita ta gyara zazzafar gabar dake tsakanin Inna Uwani da Hajiya Saratu domin dai Inna Uwani kuka take yi sosai da Hajiya Saratu a ganinta itace take zuga Hajja ta'ki yafe musu ta zo ta sake zuwa wurin Hajja domin neman gafara da kuka da ro'ko ba a rabuwar arziki a tsakaninta da Hajiya Saratu domin cikin ikon Allah duk zuwan da za ta yi sai ta risketa a gidan su yi ta babu kyau babu dadi ita Hauwa na can babu wadatacciyar lafiya domin yawan hauhawar jininta ya sanya mata nakasa k'afarta daya ta lanjare da 'kyar take janta a gidan Naziru ma gabad'aya ta zama maririya domin babu wani abinda take iya aiwatarwa tunda babu lafiya kwanciyar aure wannan ba kasafai yake yi da ita ba saboda babu nutsuwar yin kullum cikin ciwo yau da lafiya gobe babu adalci d'aya da ya yi a lamarinta da ya cigaba da zama da ita a hakan bai saketa ba. Ko saukar al'kur'ani da Khalil ya yi Inna Uwani ce kawai ta samu damar zuwa nan abujan tunda ran Hajjan aka yi wannan bada'kala domin kuwa da kuka ta bar gidan sakamakon irin k'yama da gudun da yaran Hauwa ke yi mata ga Hajiya Saratu ta hana ta motsi a lokacin ne Hajjan ta tsawatar mata tana gaya mata ko bayan ranta bata yarda da wannan matsanaciyar gaba ba babu yadda za a yi da juna tunda an hadu abinda ya riga ya faru sai a bar wa Allah tunda ya wuce yara kuma kada a kuskura a dasa musu kiyayyar uwarsu..
Bayan rasuwar Hajjan ne na ga sun d'an daidaita domin dai mutuwar ta ki'dima mutane da yawa. Har ita Hajiya Saratu ta je can bauchin ta duba Hauwa data na bani labarin halin da take ciki sai da ruwan hawaye ya ciko idona lallai dan adam ba abin komai yake ba Hauwa ta had'u da jarrabawa da kuma ciwo mai tsanani wanda a halin yanzu maigidan ne ke hidima da maganinta mijinta kwabonsa bata ciwon kai ina ma ya ga kudin. Gidansa dai babu yunwa zai kawo ko babu dadi Sadiya ta dafa ta sammata a kwano amma ita da yake Hajiya ce ta fi Hauwan kudi takan yi miyarta ta kaji ko ta namar rago duk ranar dai bai yi cefane Mai kyau ba ta tsakura ta ci ita da yaranta abinda ya kawo shi take bawa Hauwa tunda