Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
zai fi rinjaye."
"Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?"
Shiru kawai na yi Ina kallonsa. Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?"
Na ce." Yadda muke yi mana."
Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta."
Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya.
A daran na gurzu a hannunsa k'warai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni. Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah. Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice. Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba..
***
Bayan kwana biyu da misalin biyar na yammar ranar talata muka yi ba'kuwa a gidan. Hajiya Aziza sunanta matar abokinsu ce Alhaji Sulaiman duk dai abotar tafi karfi tsakaninsa da Alhaji Amadu mai rasuwa dalili shi da girmansu suka hadu ba abotar kuruciya ba ce. Sai bayan rasuwarsa tukkuna abotar ta maye gurbi akan shi da yake ba ni labari. Uwargidansa ce kuma tare suke da maigidan sun zo duba jikin Momi ne tunda ko bayan rasuwar Alhaji Amadun suna yin zumunci dalilin da ya sanya ma kenan Alhaji Sulaiman din yake binbinin abotartasu ta yi karko kamar yadda ta yi da Alhaji Amadun. Shigowarta kenan ya kira wayata ya yi mini wannan bayanin wai ta ce za ta shigo ta gaishe mu kafin su tafi yanzu shi suna tare da maigidan nata a can gidan Momin.
Na ce masa in sha Allahu babu matsala. Sosai na marabceta na sanya Baba Tabawa ta kawo mata abinci tana fad'in a 'koshe take ta ci abinci kafin ta fito nace ta daure ta sanya mini albarka.
Hauwa ta fito suka gaisa sama-sama cikin rashin sakewa ta koma dakinta. Na kira Baba Tabawa domin ta zo ta kwashe kayan abincin da ta jera wanda kad'an ta ci daga ciki. Duk da babu sabo a tsakaninmu amma na lura tana da kirki kuma ta girme mu gaskiya zata iya yin sa'a da Momin ina tambayarta yara ta ce suna nan lafiya biyu suna d'akin mazajensu kenan ta auran da yara biyu akwai hud'u a gida uku maza sai 'yar autarsu mace. Su uku ne a wurin maigidan ita ce Uwargida.
Ta ce." Ai na ga yaran a can gidan Hajiya Maryam twins sun yi wayo sosai sun zama 'yan mata, Ubangiji Allah Ya yi musu albarka."
Na amsa da amin Ya Allah, ai kam duk sun yi wayo."
Ta gyada kanta da d'an murmushi a fuskarta kamar wadda aka tsikara ta ce." Allah dai ya sawwa'ke abinda ba zai shige ba ni Hajiya Aziza."
Kallonta na yi ban ce komai ba. Ta sake yin murmushi kafin ta ce wani abu kira ya shigo wayarta tana d'agawa na ji tana fad'in." Halisa har na fito ma daga gidan, a alhamdulillahi jikin nata da sauki wallahi, eh na gaya mata sa'konki ta ce ta gode." Ta yi shiru tana sauraranta kafin ta ce." To ya za a yi lalura aka ce fa Halisa kin kyauta ai Allah ma yana son masu wannan zuciyar irin taki Ubangiji Allah Ya sa mu fi karfin zuciyarmu."
Daga can ta amsa da Amin kafin su yi sallama da juna ta dube ni tana fad'in." 'Kanwata ce Halisa.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *2K ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*104*
*Whasap Gruop 1K*
Na ce."Allah sarki a takaice ina d'an wani nazari a zuciyata sai na ji maganarta tana fad'in." Halisa k'anwata ce cikinmu daya ai da da rabo kuma Allah Ya yi wa Alhaji Amadu tsayin rayuwa suna tare da Maryam din domin kuwa sun yi soyayya k'warai kuma har iyaye suka shiga maganar har da yarjejeniyar aure a tsakani domin sadaki ne kawai bai biya ba lamarin ya rushe.
Shiru na yi ban ce mata komai ba. Ganin haka ya sanya ta cigaba da ce wa." Alhaji Amadu ya so Halisa sosai kuma ya yi mata hidima k'warai farko a gidana suka had'u ya nuna yana sonta sanin halin tsananin kishin matarsa ya sanya da maigidanmu yake sanar mini da buk'atar abokinsa na ce a a gaskiya dalili na farko Maryam k'awata ce muna zumunci sosai saboda abotar mazajenmu. Duk da ba mu zaune a gari daya amma muna ziyartar junanmu sa'i da lokaci kuma muna yin zumunci ta waya bayan haka kuma tsaye take a kan yarana kamar yadda ni ma nake tsaye akan yaranta. Shiyasa ban yi mamakin ganin yaranku a gidanta ba domin zahiri macace mai son yara da gaske da hidima su.
Da yake 'yar kasuwa ce mai zafin nema ba zan manta ba tasha yi mini fad'a sosai idan muka hadu tana fad'in ko ba zan nemi kudi don yarana ba dalilin ubansuya tara musu na tashi na nema domin iyaye da 'yan uwa da kuma gajiyayyu.
A duk lokacin da wani abu ya fito na ya yi muddin ta yi odarsa to kamar yadda za ta d'ibarwa Nusaiba kaya haka zata d'ibarwa Asiya da Madina kaya irin na yarinyarta babu bambamci ko kad'an. Sosai take yi mini kara akan komai ni kaina na sheda tana da kyauta da kirki daidai gwargwado Maryam duk wanda ya ra'be ta zai dandali arzikinta. Sai dai kin san an ce d'an Adam tara yake bai cika goma ba nasan dai tuntuni Maryam ba ta son kishiya tasha gaya mini a rayuwarta abinda tafi tsana kenan dalilin da ya sanya lokacin da maigidanmu zai 'kara aure ta dinga ba ni shawarwarin yi masa tutsu da wasu dai shawarwarin da nake ganin za su iya kaini ga halaka. Lokacin na tsananta da addu'a sosai domin mu gaskiya gidanmu gidan malamai ne Amina ba mu ta so mun ga iyayenmu na yawon bin malamai ba. Addu'a dai da yin nafilar tsakiyar dare ita iyayenmu suka koya mana tare da azkar a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro mana. Gaskiya ban yarda na bi sharwarin da take ba ni ba na dai dage da addu'a sosai akan idan auran da mijina zai yi akwai alheri ina rokan Allah Ya hada ni da abokiyar zama tagari dalili tunda?a na ta so gidanmu mata hud'u ne a ciki kuma mahaifinmu tsayayye ne da wuya ma a cikinmu wata ta kaso auranta ta dawo masa gida da zumar yin zawarci daidai gwargwado mun samu kula da tarbiya.
Sosai Alhaji Amadu ya makance da soyayyar Halisa ya zama duk bayan sati biyu daga nan abuja sai ya je Jigawa gidanmu hira wurin Halisa a lokacin itama bai kwanta mata a rai ba ta zo tana gaya mini abinda yake faruwa ni lokacin ma ban san yana zuwa zance ba tunda mun gama magana da Babansu Madina akan zai gaya masa cewa ta tsayar da wanda zata zaura kuma gaskiya ne akwai wanda suke soyayya a lokacin sai dai bai kai ga turowa ba, Amma dai gidanmu sun san da maganar mahaifinmu ma sun yi magana da mahaifinsa akan hakan.
Na dinga mamaki sosai sai dana tambayi Babansu Madina akan mai yasa bai gaya masa ba sai yace ya gaya masa ya'ki ha'kura ya ce tunda har yanzu shi wancan din bai fito ba shi ba zai janye ba.
Na kira ta zo na ce da ita duk lokacin da ya sake zuwa kada ta fito ta yi masa kora da hali domin a gaskiya ba ni son abinda za a yi shi daga baya rai yana b'aci Muna mu'amula da Maryam sosai a tsukin na tabbatar da cewar ba ta san abinda yake faruwa ba, kuma ba na son abinda zai ta'ba zumuncinmu. Idan lallai ya zama dole mijinta ya kara aure to ya nema a wani wurin amma ba daga b'angarena ba.
Sati uku da yin wannan maganar ta sake zuwa gidana tana kuka sosai ta ce mini ya sake zuwa kuma Babanmu ya saurare shi. Wata dabi'a ce ta mahaifinmu son bawa mai aure d'ansa. Ni kaina don dai lokacin da maigidan nan ya fito da niyyar aurena da gaske yake domin gabad'aya ya shigo da na tabbatar da cewa mai mata Babanmu zai bawa ni. tana gaya mini sun yi magana sosai da Babanmu har ya ce ya jira shi zai yi magana da iyayen Murtala saurayin da suke soyayya idan har da gaske yake yi to ya fito a cewarsa masu son auran da gaske suna fitowa ba za a ce za a zauna jiran wani lokaci ba. A lokacin shi Murtala din baya gari ya tafi can kudu Benin suna harkar gwangwani. Amma ya ce mata yana dawowa zai yi magana domin a zo a kawo kudin aure. Da ta gayawa Baban namu haka ya ce sai ya ji ta bakin mahaifin Murtala din tukkuna zai yanke hukunci.
Dole ta ha'kura ta tsaya sauraransa. Lokacin Malam Shu'aibu bai rufe komai ba ya gayawa Babanmu cewa. Har yanzu Murtala ba shi da taku daya wanda idan ya yi aure zai ajiye iyalinsa. Can kudu (Benin) da yake zuwa tare da abokansa sana'a suke yi ta inada da 'karafuna da robobi, wannan shine amma tunda manemi ne arziki na Allah ne. Shi ba zai hana idan mijin aure ya fitowa yarinya ta yi auranta ba domin tauye hakki ne a ce mace ta zauna jiran namijin da bai zama lallai ya yi mata adalci a gaba ba, tunda da yawa hakan ta faru samari su yi alkawarin aure da budurwa su tafi neman kudi idan sun samo sun dawo gida sai su ga ai sun fi karfin ajin wannan budurwa da suka bari a gida.
Wannan maganganun na Malam Shu'aibu maihaifin Murtala ya zaburar da Babanmu a cikin satin da Alhaji Amadu ya je gidan namu suka yi magana ya ce idan har da gaske yake kuma ya shirya auran ya turo magabantasa. A tak'aice dai Amina na gaya miki da ni da Halisa sai ji muka yi an kawo kudin auran dubu dari biyun shekarun baya mai d'anko. Kuka sosai Halisa ta zo gidana ta na yi mini kamar ranta zai fita tana fad'in ita kwata kwata bai yi mata ba tsoho ne. A lokacin da take wannan koke-koken babu abinda nake tunani sai yadda za ta zauna da Maryam domin na fi kowa sanin yadda ta k'yamaci kishiya a rayuwarta.
Sosai na tausheta da rarrashi da ban baki har Babansu Madina ma da ya dawo ya sanya bakinsa yana ta kwarzanta mata nagartar abokin nasa yana fad'in ta kwantar da hankalinta ta yi mijin da za ta yi alfahari da shi. Muka rarrasheta sosai ta ha'kura kwanta uku a gidan namu da yake duk gari daya muke gidan iyayenmu na kazaure gidana kuma a dutse a kwana na hudun Alhaji Amadu ya zo gidan wata'kila ya je can gidanmu aka ce masa tana nan
lokacin da rarrashi da ban baki na tursasa Halisa sauraran Alhaji Amadu suka dan jima a d'akin bakin maigidan suna hira kafin su yi sallama ya tafi ta shigo mini da kwalin waya sabuwa dal black berry mai kyau da tsada da kudi dubu hamsin wai kudin zance.
Na taya murna sosai a lokacin na kuma bata sharwari akan ta dage da addu'a domin duk lamarin da Babanmu ya kar'be shi da hannu biyu to tabbas ya yi istahara a kai ya gano alherinsa don haka idan tace zata tayar da fitina za ta fita zakka a cikinmu tunda ba ita kadai aka ta'ba yi wa irin haka ba.
Sannu hankali soyayyar Alhaji Amadu ta kar'bu a zuciyar Halisa yadda shi ma yake hidima da ita da gidanmu na tabbatar da cewa da gaske lallai auranta zai yi domin duk bayan sati biyu ko kwana goma yake zuwa wurinta har aka tsayar da maganar daurin auransu wata shida farkon watan maulidi.
Abinda ya fi tsaya mini a raina dangane da al'amarin shine yadda mu'amulata da Maryam bata raunana ba na shiga mamaki sosai jikina kuma ya yi sanyi k'warai na tabbatar da cewar duk wannan abinda yake faruwa Maryam bata sani ba domin kuwa da ta sani dole zan ga canji daga wurinta dalili kuwa shine na fi kowa sanin abinda tafi kyama kenan kishiya. Na gayawa Babansu Madina cewa ni fa hankalina gabad'aya bai kwanta da neman auran nan ba, domin kuwa ina zargin abokinsa da munafurtar uwargidansa. Da ya tambayeni mai yasa nake zargin hakan na ce masa naga ko kad'an ban ga canji a wurinta ba muna zumunci sosai domin ma a satin da aka sanya ranar daurin auran ta aikowa da yara kaya kowanne set biyu da muka yi waya ta ce mini sabuwar order ce shine ta d'ibar musu.
Shi kansa ya jinjina al'amarin sosai amma daga lokacin bai kara tayar da maganar ba ni ce dai abin ya dame ni a zuciyata domin sai nake ganin kamar duk ranar da ta san abinda yake faruwa za ta yi mini kallon munafuka ko kuma mai sonta kanta, ba kuma zata ta'ba yarda da cewa mijinta ne ya ga Halisa yace yana so ba za ta yi zargin cewa ni ce na had'a su.
Wallahi na shiga damuwa sosai da sosai domin kuwa ga'barar da Alhaji Amadu ya d'auka ta neman auransa ba mai kyau ba ce a ganina yafi alheri ya fito ya gaya mata akan ya 'boye mata.
Na kasance cikin zullumi da tunani a koyaushe nazarin da nake yi shine idan har Maryam ta samu labarin mijinta zai auri k'anwata wane kallo za ta yi mini.
Katsam watarana na ga text message d'inta ina dubawa na ga ta rubuto mini Aziza na gode sosai ashe tsakanina dake ba zaman amana, kema kin boye mini abinda yake faruwa, na d'auka ni dake yanzu mun zama 'yan uwana na ji don kin gaya mini mijina na neman auran k'anwarki Halisa menene ko kin d'auka zan tsananta kishi a kanta, ai abin gudu a kishiya shine a d'auko maka kwarkwasa wadda ba ka san ni ba, amma ni kam na sheda halinki kuma ina fatan haka Halisa take da kyawawan halaye idan har da akwai alheri a zamana da ita Ubangiji Allah Ya kawota cikin gidana, ke kuma na gode da 'boye mini da ki ka yi."
Jikina ya yi sanyi sosai da na gama karanta sakon data turo mini na zauna ina ta tunani da mamaki. Dama nasan tuntuni ba ta san abinda yake faruwa ba sai yanzu da daurin auran bai wuce wata biyu da kwanaki ba sannan ta samu labari. Hakika kowacce aka yi wa haka dole zuciyarta ta sosu Amma sai na dinga mamakin yadda ta sadada har ta samu damar yi mini text kuma cikin nutsuwa bata kalubance ni akan had'a baki muka yi da mijinta ba.
Na kwana da tunanin hakan a raina sai da gari ya waye tukkuna na kira ta a waya ta daga babu jinkiri muka gaisa sosai cikin ko'karin kare kaina na fara yi mata bayanin abubuwan da suka faru tun farkon neman auran har zuwa yanzu. Ta dinga fad'in ai na d'auka ni dake babu rufi Aziza babban abinda ya ba ni haushi kenan yadda kike biye masa kema ki ka yi mini shiru wato sai dai kawai na ji an d'aura auran kenan kun yi mini adalci.
Na shiga bata ha'kuri da tausarta Ina nuna mata cewar ban san ta yadda za a yi na iya tunkararta da maganar ba domin ni duk a tunani na mijinta ya gaya mata.
Ta ce mini bai gaya mata ba ita ta fahimta da kanta yana neman aure da kuma ta yi bincike ta gane Halisa ce k'anwata.
Yadda muka fahimci juna sosai a wayar ya sanya mini kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata na amince da cewa Maryam ta sakko ta kuma yi na'am da cewa kishiya abokiyar zama ce kuma hukuncin ne na Allah....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: 🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu