Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   37 / 73

108K to 111K   out of 217.6K words

na buk'aci cewar ta ba ni hayar gidan ta ce wai ita na waje za ta bawa domin tana zargi kada shekara ta zagayo na 'ki biyan ta wanda ni babu hakan a cikin raina wallahi zan biya ta kud'inta dalilin da ya sanya kenan na kira ki idan ba za ta sanya ni domin Allah ba to ki rarrasheta ta ba ni haya ta fad'i abinda ta yanke da shedu da komai a tsakani duk shekara na biya ta kud'inta.......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*140*
Na yi 'kokarin danne dariyar da yake ba ni na ce." Idiris a yanzu dai ba ni da wata hujja mai karfi da zan ce da Sahura ta baka gidanta ka sanya amaryarka a ciki. Akwai gidajen haya da yawa a unguwanni mai zai hana ka sanya dillalai su cigita maka sai ka biya hankali kwance ka sanya matarka a ciki ina ganin kamar hakan zai fi kwanciyar hankali."
Ya yi d'an jim kafin ciki kame-kame ya fara cewa" To shikkenan zan sanya a nemo mini din amma tunda ita ta ce haya zata bayar da gidan mai zai hana ni ta ba ni akan dai ta bawa wani na waje kuma tsakanina da Sahura ai mun zama dayai shekaranmu kusan ashirin da aure yana da kyau a ce ta gane yadda take da matsayi a cikin raina. Karin auran nan na gaya mata nufin Allah ne amma ta ki kwantar da hankali koyaushe idan na je gidanta da rigima muke rabuwa abubuwan nan da take yi mini bana jin dadi wallahi."
Na furta." Sai a hankali za ka ga komai ya wuce amma ni dai a shawarce kawai ka bar mata gidanta ka nemi wani."
Ya amsa da "To a sanyaye muka yi sallama na kashe wayata na ci dariya na koshi lallai Idiris ba shi da kunya wato shi gani yake yi abinda ya yi wa Sahura 'karamin abu ne da bai kamaci ace ta daga hankalinta ba ana sa tunanin kenan kuma yanzu Allah Ya dube ta ya kawo mata d'auki ya lallabo su ci tare har yana so su samu sakewa da walwala da matar da ya auro a kuma cikin gidanta. Shi dai kawai ta bashi ya sanya matarsa a ciki amma babu maganar biyan kudin haya fad'e kawai yake yi mahaukaci ne shi ya d'auki kudi ya bata bayan yana ganin gidajen duka samunsu ta yi a sama ba kudinta ne ya saya mata ba. Ni kaina ba ni goyon bayan hakan domin yadda yake munafikin nan ta sanya shi a gidan watarana sai dai mu ji labari ya sayar mussaman idan ya sake tara yara wahala ta sake yi masa yawa. Kuma dole ta ha'kura ta kyaleshi dalilin yaran da suka ratsa a tsakaninsu .
Daga na yi juyi sai abin ya fado mini nasa dariya har sai da shigo gidan ya fahimci Ina dariya jefi jefi ya fara tambayata menene na bashi labari yadda muka yi da Idiris din.
Tsaki ya ja yana fad'in shima baya goyon bayan hakan tun daga farkon fara neman auran da rikicin da suka dinga yi ya gama fahimtar shine bashi da gaskiya kuma ai duk matar da za a yi wa kishi miji yakan ru'banya kulawa da ita domin dakushe mata damuwa da takaicin abokiyar zamar da za a kawo mata amma shi bai yi ko daya ba ya kuma nuna abinsa nasa ne shi kadai abinta kuma nasu ne gabad'aya mugunta ce tsantsa irin ta wasu mazan.
To alhamdulillahi cikin hukuncin Allah muka isa abuja muka samu gida da jama'ar dake cikinsa cikin farinciki da murnar dawowarmu tun daga kan Hauwa zuwa yaran da masu aiki kowa bakinsa har kunne . Sosai na ga can ji mai kyau tsakaninta da su Taburni da akwai girmamawa da kuma mutunta juna. Na ji dadin hakan na yi addu'a a cikin zuciyata Allah ya sanya hakan ya d'ore.
Kwana biyu ita take dawainiya dashi ya d'an sake da ita babu kallon kyama ballantana hantara kuma bai nemi da na zo na yi masa wani abin ba har sai da ta yi kwana biyunta tukkuna sannan na kar'bi hidimar tasa.

Ranar da muka cika sati daya da dawowa Sahura ta kira ni a waya muka gaisa jin muryarta a cunshe ya sanya ni saurin tambayarta nan take gaya mini Idiris ya sanya an 'balle k'wadon da ta kulle gidanta sun tare da matarsa a ciki itama d'aya daga cikin yaran shagona ne yake gaya mata shine take gaya mini zata d'auko masa 'yan hizba.'
K'warai na yi mamakin da jin haka wane irin karfin hali ne da Idiris ne shin ina kudin da ya samu to ai ba zai ce duka miliyan takwas din ce ta kare gabad'aya wajen neman auran matarsa ba. Lallai bai so zaman lafiya ba domin duk da take matarsa tana da 'yancin da za ta nemi hakkinta wace irin gadara ce wannan da son rai."
Ta fashe da kuka tana fad'in." Amina wallahi saboda yara nake zaune da Idiris ba na so na kunyata Yallabai dan ganin irin tagomashin da ya yi mini amma wallahi na gaji da guma mini takaicin da yake yi hizba zan kai shi kwanaki fa haka ya kira baban yayanmu Alhaji Rufa'i yana gaya masa wai gaba nake yi dashi saboda ya k'ara aure na daina bashi hakkinsa na auratayya sannan ina fita ba tare da izininsa ba idan na yi abinci bana zuba masa idan ya zo gidan wallahi kuma sharri ya yi mini. Abiñci wataran ba shi yake yin cefane ba ni nake yin abina aiki kuma dole na fita tunda dama tuntuni shine yake ri'ke da ni da yara a gidan da bana fita aiki da ba mu kai labari ba. Maganar kwanciyar aure kuwa tuntuni na ajiye a gefe bana kaunarsa wallahi shiyasa ko sha'awar ya zo kusa da ni bana yi."

Na ce." Lallai Idiris ashe bai d'auki shawarar da na bashi ba kenan. Kwanaki fa ya kira ni yake gaya mini kin hana shi gida kin sa kwa'do kin rufe wai na yi miki magana ki bashi hayarsa domin kayan d'akin da aka yi wa amaryarsa suna da yawa can inda ya kama mata haya ya yi matsatsi ya ce ki yanke kudin da zai biya wai na zama sheda duk shekara zai dinga biyanki."
Ta ce." 'Karya yake yi wallahi ta 'karfi da ya ji yake so na bashi gidan akan ban bashi ba ya ce sai dai na ajiye aiki ni kuma na ki ajiyewa shine fa ya gaya yayanmu wai ina fita yawon ma'kota da zuwa kasuwa cefane bada yawunsa ba. Sannan ya bi dare da rana ya buge kwadon da na sanya ya shiga gidan da matarsa suna zaune yau kwana hud'u kenan."
Dariya kamar cikina zai ciwo bakina ya mace na kasa ce mata komai saboda dariyar da nake yi ta hana ni maganar har sai da na ji maganarta a fusace tana auno mini zagi!
Na danne dariyar sosai ina fad'in." Sahura Idiris takadirin mutum ne wallahi malam bahaushe tsantsa to ki kai shi hizba ki kai wa Sahura an zama daya fa ba zan baki shawarar kai shi hukuma ba don Allah ki rabu dashi wallahi muddin yana zalintarki Allah zai saka miki."
Ta ja hanci tana fad'in." Sai fa hukuma ta shiga cikin lamarin nan Amina na rantse da Allah ba zan lamumci wannan rashin mutuncin ba."
Na ce." Idan kin kai shi hizba suka tura ku kotu ai kin ga duniya ta ji kuma akwai manema labarai ko babu komai mu kyale shi ya ci darajar su Yusra mana Sahura. Kuma a jikina nake jin idan kin kai shi hukuma zai kara fusata ya ce dole ki ajiye aiki kin ga an biyu babu ko?"
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya irin ta b'akinciki da takaici can kuma na ji kittt ta kashe wayar na shiga duba wayata da mamakin abinda ta yi wato bata ji shawarar da na bata ba kenan. To Allah Ya rufa asiri.

***
Wata uku a tsakanin dawowarmu daga Legos cikin da yake jikina ya d'an tasa zuwa yanzu wad'anda muke tare da su a cikin gidan sun fahimci ina d'auke da juna biyu tunda har ya huda zani ya yi kurcici wata biyar kenan ba wasu kwanaki.
K'warai da gaske na yi mutukar mamaki ganin sauyin fuska da mu'amula daga Hauwa sabanin lokacin da muka dawo tana masifar haba-haba da ni da son shiga lamarina da kuma yawan yi mini hira idan muna falon gabad'aya amma tun sa'ilin da ta lura da cikin da nake d'auke shi ta sauya fuska ta kuma rage shiga jikina. Ba mu yin gaba dai tunda tana gaisheni kullum da safe ko da ban fito falo ba ta kan biyo ni dakina mu gaisa amma ba ta zama daga tsaye idan mun gaisa sai ta fita. Ta rage zaman falon sosai ta tsiri na d'aki tunda dama da'biarta ce idan tana nukufurci da jin haushi sai ta rufe kanta a d'aki sai ta ga dama take fitowa.
Jikina ya yi sanyi sosai ganin halin k'uncin da ta shiga duk saboda ina da ciki menene abin damuwa ga matar da take da cikin haihuwa kuma take da mijinta a hannu. Don na d'auki ciki itama rabo yana rantsewa za ta d'auki nata abinda dama maigidan yake buk'ata kenan ni da ita har yanzu ba mu wuce haihuwar ba to ban ga abinda zai sanya ta daga hankali ba a ganina ni zan yi wannan damuwar tunda ta d'ara ni da 'daya har da namiji a ciki ni kuwa nawa duka mata ne kuma ban yi mata ganin kyashi da kishi ba.
Ana haka maigidan ya tafi bunkure dalili an fara gudanar da aikin rushe gidan Malam D'aha kamar yadda ya yi alkawari zai sabunta masa gidan da gini na zamani kuma zai gyara masa tsangayunsa. Ya ce mana zai yi kwana uku ko hud'u domin bayan ya gama da gidan Malam D'aha zai gudanar da wasu al'amuran da duba ma'aikutunsa da suke jahar.
Washe garin ranar da ya tafi ta yi bakuwa. Kallo d'aya na yi mata na sheda ta 'yar uwar nan ta ta ce da muka yi wani zuwa garin nasu domin gaisuwar mutuwa wadda ta dinga shige da fice tana kallona a lokacin har sai da ta magantu.
A falo ta zauna tunda lokacin da ta shigo duk muna zaune a falon gabad'aya muka gaisa sosai da ita ban nuna mata komai a fuska ba take fad'in wai Seminar suka zo garin shine ta ce bari ta zo mu gaisa..
Cikin raina na ce ki gaisa dai da 'yar uwarki. Anan falon ta ci abincin da na sanya Baba Tabawa ta kawo mata sai da la'asar ta yi tukkuna suka tashi suka shiga d'akinta tare.
Ni ma a lokacin na tashi na shiga d'akina domin yin alwala.
Ina idar da sallah da kamar minti biyar kira ya shigo wayata na daga a nutse na gaishe shi ya amsa yana fad'in." An ce mini kun yi ba'kuwa ko?'"
Na ce." E, bak'uwar Hauwa ce daga bauchi ta zo wata Seminar ne nan."
Ya furta ya sunanta?" jim na yi kamar Sadiya na ji tana kiran sunanta. Ya ce." Ba ni son shige da fice ya yawaita idan ba na gari ku kula sosai."
Na ce." In sha Allahu rabbi ranka ya dad'e." Ya d'an saki ajiyar zuciya yana fad'in." Idan na gama abinda nake yi anan zan wuce maiduguri domin duba Dada ba ki da sa'ko?"
Na ce." Kash! amma ba ka kyauta mini ba wallahi tare fa muka yi da kai za mu je shine zaka zame ka yi tafiyarka kai kadai."
Ya furta." Ki bari ki haihu ki samu lafiya sosai sai ki je in sha Allahu."
Na ce." Shikkenan yaushe za mu yi tsammanin ganinka ?"
Ya d'an yi jim kafin ya furta nan da kwana uku in sha Allahu."
Na ce." To shikkenan Allah ya dawo mana da kai lafiya."
Ya amsa da Amin ki shafa mini kan yarana gabad'aya a ce ina gaishe su."
Ina dariya na furta." Zan gaya musu in sha Allahu rabbi."
Sallama muka yi na ajiye wayar ina murmushi wanda na kasa tantance ko na menene.
Yau su Baba Tabawa Jallof suka yi na shinkafa da tafiya sai suka yi amfani da bushashan kifi ta ji alayyahu da albasa ta yi kyau ainun a ido kuma na tabbatar da cewa za ta yi dadi amma bata ni sha'awa babdon ko da ta kawo ta ajiye mini ita a gabana sai na ji tana tashin karnin kifi wanda na tabbatar da cewa hancina ne kawai da kuma tsagunaguni na mai juna biyu.
Ko loma daya ban iya ba na ce ta d'auke plate din ta yi yadda nace din ta zo tana tambayata ko akwai abinda nake buk'ata tunda da sauran dare sai ta yi mini."
Na dube ta tausayi suke ba ni dattijan kwarai da gaske har gwara Taburni ta haihu har da jikoki ita kuwa Baba Tabawa bata ta'ba haihuwa ba sai jigila take yi da mu da yaranmu ga shekaru jiki da jini don ma jikin ya horu da aiki ni dai sai nace tunda nake da ita ban ta'ba ganin ta kwanta ciwo mai tsanani ba hana karya lokacin da muke kano ba ta jima da zuwa ba ta ta'ba wani ciwon kai wanda ya d'auketa tsayin kwana uku a kwance tunda na kaita asibiti aka duba ta da maganguna ta warware daga lokacin ban sake jin ta ce mini ba ta da lafiya ba.

Paid book ne wannan littafin kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Na ce kawai ta bar shi idan zan kwanta zan sha tea wannan ba shi da matsala da kaina ma zan hada abina.
Ta amsa da to kafin ta juya domin komawa dakinsu. Hauwa ta fito ganina a falon ni kadai sai ta tsaya tana fad'in." Ni kuwa Amina wanene ya gayawa maigidan Sadiya ta zo?"
Na dube ta a tsanake kafin na furta. Kya tambaye ni Hauwa ko kuwa ni kadai nake rayuwa a gidan kin manta tun daga bakin gate gidan cike yake da masu tsaro saboda kin yi bakuwa sai na kira shi na gaya masa kenan?'
Ta fara dariya irin ta kare kai tana fad'in." Haba Amina ni ban tambayeki domin na fusataki ba ya kira ni ne da fad'a yana cewa mu kula da masu shigowa sai naga tunda na zo gidan nan babu wani d'an uwana da ya ta'ba zuwa sai yanzu Sadiya ai ba bare ba ce 'yar uwata ce da babanta da mahaifina uwa daya uba daya suke."
Na ce.'' Wannan kuma damuwarki ce Hauwa kina so ki gaya mini cewa ni nawa 'yan uwan tarewa suka yi a gidan kenan ko?"
Ta girgiza kanta tana cewa." Na ga kin hasala daga tambaya sai cibi ya zama 'kari Amina ko dama haushina ki ke ji ne ban sani ba ko kuwa zuwan Sadiya ne bai yi miki dadi ba."
Na ce." Me yasa zan ji haushin Sadiya me ta yi mini Hauwa wai ke don Allah an gaya miki kowa yana da tsatsar zuciya ne. Bayan Sadiya ki kawo wasu gidan nan su zauna bai dame ni ba Hauwa."
Murmushi ta yi bata sake ce mini komai ba ta nufi kicin. Ina nan zaune ta fito da wasu madaidaitan mazuban abinci ta wuce ni. Tsaki na ja can k'asa na tashi na shige d'akina. Wai tambayata take yi wanene ya gaya masa ta yi bakuwa saboda raninin hankali yadda ya kira ta a waya yana tuhumarta ni ma haka ya kira ni ita dai har yanzu ta'ki zama da ni da zuciya daya.
Can wajan sha d'aya na ji yunwa ta yun'kuro mini tabbacin tea din da na sha ba zai d'auke ni ba.
Na tashi da azama na nufi kicin din fatan doya nake sha'wa wanda ya ji attaruhu.
Daf da zan shiga kicin din na ji kamshin wainar k'wai.
Na ji muryarta tana fad'in." Kina nan da cin dad'i dai Sadiya ba kya gajiya da ciye-ciye tsakani da Allah cikin daren nan kin tashe ni da soya kwai "
Na ji maganar ita Sadiyan tana fad'in." Laulayi ne ya sanya ni a gaba Hauwa dama ya ya lafiyar kura da kwad'ayi tunda na samu cikin nan yake cin kudi wallahi kullum sai Babansu Haidar ya sayo mini balangu."
Ta ce." Wai ba wani sirri da za ki ba ni ne Sadiya wani lamari ne yake damuna wallahi na rasa yadda zan yi na shawo kan matsalar nan ina cikin damuwa mai tsanani.
Na ji tana cewa." Menene kuma ke dai kullum cikin korafi kike Hauwa yana da kyau don Allah ki yi amfani da shawarwarin da muke ba ki. Na gaya miki ko kin sanya ana yi miki taimako dole sai kin had'a da kissa da addu'a kuma. Sannan na fahimci matar nan ba ta da hayaniya kuma tana da kirki daidai gwargwado don girman Allah ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya da juna."
Ta ja tsaki tana fad'in." Duk ina ko'karin yin haka Sadiya amma ba zan boye miki ba wallahi ina tsananin kishin amina. Tabbas abinda ki ka fada a kanta gaskiya ne macace mai kirki da kawaici kuma bata da mugunta ko kad'an wallahi duk lokacin da ta lura na yi fad'a da maigidan ta dinga kokari sasanta mu kenan amma duk da wannan abin da take yi ba na jin zuciyata za ta daina jin zafinta dalilin yadda maigidan ke nuna mini cewa ya fi sonta wannan zahiri ne na tabbatar da haka yana mutuwar sonta ko alwashi ya ci akan abu idan ta yi magana sai ki ga ya sassauta. Sai abu na biyu yau watana kusan hud'u da dawowa gidan nan har yanzu bai yi auratayya da ni ba. yana dai yi mini magana har na kai masa abinci ya ci amma zamu kwana d'aki daya baya kallona duk yadda na kai wajen janyo hankalinsa wallahi ba ya sauraranta Sadiya abin yana yi mini ciwo sosai na kai kaina wurinsa ya fi a kirga na yi shigar da zata sanya ya ji sha'awata amma ko gezau ba ma ya kallona balle na

37 / 73