Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   45 / 73

132K to 135K   out of 217.6K words

da yake gaishe ni girma ya yi mini a ido kwarai ya sake yin fad'i da 'barage mazantaka dai ta bayyana tunda dama tuntuni muryarsa ta fashe an balaga ga wani gemu zororo a ha'barsa. Cikin zuciyata na ce yaron nan dai ya rantse sai ya zama d'an izala
Gashi makarantar da ya yi ta almajiranci ba ni tsammanin ta 'yan alhalissuna ce. Kawai dai abinda ransa ya fi ra'ayi kenan yaro ya nutsu sosai cike da wata iriyar kammala ta mussaman zahirin kammaninsa da mahaifinsa ta fito 'baro-'baro bambamcinsu kawai shi Yaya Aminu ba shi da gemu kuma bashi da kuzarin yaron amma duk wanda ya ga Kamalu a yanzu zai tabbatar da cewa hoton ubansa ne
Hajja ta fad'i take daga Ina kuke cikin wannan rana ta k'arfe d'aya Amina."
Na ce." Wallahi Hajja daga asibiti nake shine na ce bari na biyo mu gaisa kawarki mata ta gaishe ki."
Ta sanya dariya tana jan hannun yarinyar tana sake no'kewa a jikina. Ta ce." Ina fatan dai lafiya ko Amina sannunki da ibada Ubangiji Allah Ya raba ku lafiya."
Na ce." Amin ya rabbi Hajja lafiya lau wallahi abinda sakamako ya nuna kenan.
Ta dinga fad'in." Alhamdulillahi cike da godiyar da Allah da jin dadi kafin ta shiga kwalawa iyami kira mai aikinta wai ta kawo mana ruwa."
Kamalu ya ce." Hajja ni me nake yi bari na kawo mata da kaina.
Ya ajiye lemon zaki da yake hannunsa ya nufi kicin da sauri lokacin Hajja ta d'auki lemon da ya gama 'barewa tana mikawa yarinyar da fad'in." Zo ki kar'ba to tunda kin 'ki zuwa mu gaisa."

kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ta kuwa tafi za ta kar'bo lemon saboda rashin kunya gabad'aya muka fashe da dariya.
Ta ce." Yusi ai yau tun safe ya fita kasuwa da yake ya ce bashi da karatu yau shine ya yi sammakon fita amma nan da biyar da rabi za ki gan shi ya dawo."
Na ce." Ya zama sarkin kasuwa ai."
Tana dariya ta ce." Haka ake son namiji ya kasance ai."
Kamalu ya ajiye mini ruwa da lemo masu sanyi a gabana. Na dube shi ina fad'in." Baka da hankali wanene zai sha wannan ruwan da wannan sanyin."
Yana murmushi ya ce." Mama ai na ga ana rana ne sosai ruwan sanyi zai fi kashe miki ishi."
Na ce"D'auke ka kawo mini mara sanyi."
Da sauri ya yi yadda na ce din ya kawo mini ya bude ya tsiyaya mini a Kofi.
Na d'auka na sha na bawa Minal Tasha na ajiye kofin saman plate din da ya kawo ruwan..
Hajja ta ce me za a sanya Iyami ta dafa muku Amina ni dai ce mata na yi ta saka mini danwake."
Na ce." Aikuwa a yi dani Hajja har na yi sha'awarsa. Tana dariya ta shiga k'walawa iyami kira ta fito ganina ya sanya ta risinawa tana gaishe ni na amsa mata da kulawa Hajja ta ce da ita ta kara garin danwaken ta saka shi da d'an dama. Ta amsa cike da bin umarni ta koma bakin aikinta.
Kamalu ya shiga dakinsu tsayin minti goma ya fito da wasu littafai a hannunsa gabad'aya muka bi shi da ido Hajja ta ce." Makarantar za ka tafi da wuri haka?"
Ya ce." E, Hajja amma kafin nan zan biya gidan Gwaggo."
Ta ce." Yawwa gwara da ka tuna mini shiga kicin ka ce da iyami ta baka garin danwaken nan leda biyar sai ka tafi mata da shi."
Ya ce." To shikkenan. Ta dube ni tana cewa." Abu ne na marmari duk ranar da ta yi sha'awa sai ta tsumbula.
Na yi shiru ina murmushi gefe guda kuma ina kara kambaba mutunci da halin dattako irin nata ga kyauta ga kirki Hajja mutuniyar kirki ce sosai Gwaggo ta zama 'kawarta kuma aminiyarta. Na tsinkayi maganarta tana fad'in." Ai ya sanar da ku d'aurin auransa gobe ne a Bunkure ko."
Na ce." Eh ya gaya mana Hajja Allah Ya sanya alheri."
Ta amsa da Amin. Kamalu ya fito da ledar garin danwaken a hannunsa yana yi mana sallama tare da ce mini zai zo cikin satin nan in sha Allah.
Ta dube ni cikin nutsuwa kafin ta furta." Amina Malam D'aha mutumin kirki ne kwarai da aniya kuma mutumin maigidana ne tare na san su abokai ne kuma masu rufawa juna asiri ta kowace siga. Lokacin da Tajo yake gaya mini kyautar auren 'diya da Malam 'Daha ya ba shi na yi farinciki domin sanin da na yi cewa gidan karamci ne da ilimi da addini gidan yi wa al'kur'ani hidima tabbas had'a iri da jinin Malam D'aha abin alfahari ne tare da fatan samun zuri'a nagartattu. Sai dai kuma jikina ya yi sanyi sosai lokacin da ya nuna mini hoton yarinyar na ganta 'yar karama nama sheda fuskarta tunda itace ta dinga dawainiyar kawo mana abinci a lokacin da Tajo ya kwanta ciwo a gidan. A mizani na tunanina yarinyar ba tsarar auransa ba ce domin ya yi mata nisa sosai babu hadi gabad'aya babu dacewa.
Amma a mizani na shari'a hakan ba haramun ba ne domin manzon Allah s.a.w shi ma ya yi irin wannan aure ya raini Nana Aisha har ta kai munzali kafin ya fara rayuwar aure da ita.
Malam D'aha Tajo ya yi niyyar bawa d'iyarsa kuma na tabbatar da cewa da zuciya daya ya kulla wannan al'amarin ba don samun abin duniya ba na sanshi sosai a can baya abin duniya bai dame shi ba mutum ne mai dattako da sanin ya kamata."
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zucciya. Ni kuwa cikin raina ina fad'in anan dai bai san ya kamata ba Hajja tunda har ya iya bawa dattijo yarinya karama irin wannan ai zamanin annabawa daban da wanda muke ciki yanzu.
Ta cigaba da cewa." Na bashi goyon baya akan ya kar'bi kyautar da aka yi masa da kyakykyawar zuciya ku yi hakuri, ku kara akan wanda kuke yi in sha Allahu rabbi ba za ku samu matsala da yarinyar ba. Itama Hauwa zan kira ta a waya domin na kara tausar zuciyata dama itace fitinanniya ku yi hakuri ku kawar da kan ku na dan wani lokaci komai zai wuce."
Na ce." Wallahi babu komai Hajja ai yarinyar bata da matsala zamu zauna lafiya da juna kuma na yi miki alkawari ba za a samu matsala ta wajena ba."
Godiya da sanya albarka har sai da na ji nauyi da kunya na ce ta daina gode mini domin ban yi abinda ya kai ta yi mini irin wannan godiyar ba a ganina ni ce zan yi mata godiya bisa ayyukan alheran da take yi wa a alhalina.
Biyar daidai na fito da niyyar tafiya har lokacin Yusi bai dawo ba fadi take yi zai ji takaici kuwa idan ya dawo ya ji labarin kin zo.
Na ce." Kawai sai ya zo gida ya same ni Hajja ba zan zauna jiran dawowarsa ba zan yi abinci idan na koma."
Muka yi sallama cikin girmama juna da mutuntawa Magaji direbanta ya d'auke ni a mota har gidana.
Sai da na yi magriba tukkuna na shiga kicin jallop nake sha'awa ta taliya da kifi ita na yi na zuba mana ni da Minal muka ci a kwano d'aya na ajiye wa maigidan 'yar kad'an dalili nasan ko zai ci ba dayawa ba tunda ba cimarsa ba ce taliya da makaroni. Abinda ya fi so dangin towo kowane iri sakawara funkaso ko wainar masa ta bauchi Yana son faten doya ma abinci da miya bai dame shi sosai ba sai ya ce asa masa miya kad'an saman shinkafa. Yana kuma son gurasa da miya sosai.
Wajan goma saura ya shigo tare da Sukairaju ashe tare suka zo garin. Ya d'an tsaya daga bakin kofa ya kar'bi wayoyinsa daga hannuna ya gaishe ni na amsa babu yabo babu fallasa ya juya da sauri ya fita shi kuma ya karaso wajan da nake zaune hannunsa ri'ke dana Minal
A d'an hargitse yake gaskiya tsabar ma baya hayyacinsa gilashinsa a hannu yake abinda bai ta'ba faruwa ba duk rintsi da wahala baya cire gilashin nan na idonsa, sai sau daya lokacin da ya fad'i a garin bunkure yana dawowa hayyacinsa kuwa ya mayar da abinsa kamar wanda aka haifa tare da shi na ta'ba tambayarsa ko yana da matsalar Ido ya ce mini a a yana sanya shine domin kara karfin gani kuma dai ya zame masa jiki idan ma Babu shi a idonsa baya jin dad'i......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA,#700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*149*
Na zura masa ido jikina a sanyaye ga dukkanin alamu akwai matsala. Da kyar na bud'e bakina da ya yi mini nauyi na ce masa barka da zuwa. Ya amsa yana ri'ke hannun Minal da take ta jan babbar rigar jikinsa. Da ya amsa mini bai sake cewa komai ba ya wuce. Na bi shi da kallo cikin lissafi a zuciyata shin menene ya gigita shi hakane? ko dai akwai matsala ta fannin daidaituwar jini shi da yarinyar tunda ya gaya mini zai ce ya d'aukota a yi mata genotype din tunda shi ya sanya nasa As ne kamar yadda nake As. Idan hakan shi ya hadda masa wannan gigicewar lallai ya fito da abinda yake cikin ransa wanda yake ta nuku-nuku da shi yana kuma so ya yaudare mu kan cewa baya son auranta. Alamu sun nuna lallai zuciyarsa ba ta so faruwar hakan ba.
Na tashi na bi shi saman na same shi zaune gefan gado Minal na ta wasa da agogon hannunsa da ya cire ya ajiye shi kuma yana zaune ya dai cire babbar rigar ya ajiye amma har yanzu yana cikin rashin hayyaci.
Motsin shigowata ya sanya shi dubana. Bai janye idonsa ba har na isa kusa da shi na zauna still idona a kansa a takaice na ce." Me yake faruwa ne?"
Ya yi jim kafin dube ni da wani yanayi ya furta "Yarinyar As ce Amina. Akwai matsala tunda ni ma As ne duka d'anjuma ne da d'anjummai, gidan Malam D'aha cike yake da ba'ki na nesa dana kusa sun d'ora manya tukuwane domin abincin jama'ar d'aurin aure dalili shi mutum ne na mutane k'warai da gaske da yawa jamaarsa ta mahaifina ne cikinsu wad'anda suka rage da iyalinsu babu wanda bai san da maganar wannan auran ba. Babban abinda ya fi d'aga mini hankali anan shine yadda zan gaya masa cewa a janye d'aurin auran nan saboda wannan matsalar da bai zama lallai ya yarda da ita ba tunda ke kan ki kin sani abu ne mai wahala ya amince da koyarwar yahuduwa a matsayinsa na malamin addini kuma mutumin karkara."
Na yi shiru ina kallonsa zuciya na gaya mini ba wannan dalilin kad'ai ya sanya shi gigicewa ba akwai wani dalilin dai da yake boyewa.
Na ce." Yanzu wace shawara ka yanke?"
Ya yi shiru kawai yana kallona sai da na sake maimaita maganata tukkuna ya furta." Ban yanke ba har yanzu Amina bana jin zan iya dakatar da Malam 'Daha dangane da abinda ya niyyata ya kuma yi gangami a kansa."
Na furta." Za ka bari a d'aura auran kenan ?"
Ya gyad'a kansa yana kallona."
Sai na ce." To idan hakane menene abin damuwa tunda ka ji ka gani me yasa za ka daga hankalinka. Ka bar wa Allah wata'kila sai ka ga kun samar da yara masu lafiya ba irin wanda ake tsammani ba."
Ya ce." Ai ba wani sonta nake ba Amina. Maccan da nake tsoron rabuwa da ita itace nake jin zan yi hakuri na zauna zaman aure da ita idan aka ci karo da wannan matsalar ga misali nan a kanki. Amma ina ji ina gani ba zan yi gangancin ba gaskiya magana kenan."
Murmushin takaici na yi kafin na ce." Akwai zalinci tsantsa idan har abinda ka fada da gaske ne a cikin zuciyarka to bari na gaya maka daka kai har malamin kun zalinci yarinyar nan. Ya kamata duk wani b'oye -boye da kake yi ka fito fili ka yi wa mahukutanku bayani nufi na walliyanku wai shin kai karamin yaro ne? A tunanina saurayi dan shekara a shirin da biyar ba zai yarda a yi masa irin wannan kutsen ba ya yi shiru sai dai dama idan yana so. Idan ka bari aka daura maka aure da yarinyar nan to dama kana sonta a cikin ranka. Soyayyar da za ka nuna mata da iyayenta a yanzu ka fito musu da gaskiyar abinda yake zuciyarsa kuma ka gaya musu babban dalilin da ya sanya ka janye nasan ko wasu basu yarda ba wasu daga ciki za su yarda tunda duka yanzu kai ya waye."
Cike da kosawa ya ce." Na gaya miki Amina Malam D'aha fa ba zai ta'ba amincewa da wannan batun ba. Akwai shi da hujja wadda zai fatattaki duk likitan da na kai masa domin ya fahimtar da shi. Ni dai da bakina ba zan iya furta masa cewa na janye ba saboda ga dalilina akwai hujja mai karfi a wajensa.
Na ce." To shikkenan na ji idan an d'aura menene makomar yarinyar abinda nake so na ji kenan."

na kudi ne don girman Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba

Ya daga kafadarsa yana fad'in." Wallahi ban yanke hukunci ba tukkuna amma dai ina jadadda miki ba ni yin zaman aure da ita. Na bari a d'aura auran domin kada na katse masa hanzari bayan tarin jama'ar da ya gayyato gidansa ana ta hidima. Akwai ciwo da takaici a ce an fasa abin zai yi muni da rashin dad'i."
Na ce." Babban abinda zai yi masa muni shine a daura auran ka bar masa yarinya a gida a jingine wannan shine asalin cin mutunci da wulakanci don haka wallahi kada ka fara."
Ya zura mini ido yana kallona kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta furta." Ya zan yi to Amina na gaya mini dalilai na."
Na ce." Gobe tunda sai an sakko daga sallar Juma'a za a daura ka buga sammako ka d'auki likitan da ya yi muku genotype din ku je dashi gaban malamin ya yi masa cikakken bayani tare da illolin ciwon da yadda yaran da aka haifa suke shan wahala iyayensu ma suke cikin wuya duk a dalilin ciwon. Ubangiji sai ya dubi zuciyarka ya sanya malamin ya fahimci abinda ake so ya gane."
Ya ce." To idan an yi haka mu yi yaya da jama'ar da muka gayawa wasu daga mutanansa fa na ce miki sun zo gidansa a cike yake da jama'a."
Kai tsaye na ce." An yi haka da yawa ai ba a kanku za a fara ba irin wannan idan kaddara ta gifta sai wani ya maye gurbi. Idan hakan ya kasance yadda muke so kun fahimtar da malamin ya gane sai ka yi gaggawar kira na a wayar zan nemawa wani auranta sai a daura da shi kawai."
Ya yi sakato yana kallona na ce." Wannan itace hanya mafi sau'ki da za ka warware matsalarka ni ma zan baka gudumuwa daidai gwargwado amma idan har ka bari aka daura auran da wata niyya a zuciyarka ka cutar da yarinyar sosai kuma ba ka yi wa malam 'Daha adalci ba.
Ya rike hannuna tamau yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode giwa Allah Ya yi miki albarka kaina ya d'aure gabad'aya a yanzu neman mafita nake yi."
Ni ma na sauke ajiyar zuciya a nutse na ce." Na kawo maka abinci ko?"
Ya gyad'a kansa yana fadin." Kawo mini."
Na tashi na fita. Lokacin dana dawo yana bandaki na zauna gefan gado Minal tana tsakiyar gadon nasa a zaune tana ta wasa kira ya shigo wayarsa. Minal ta d'auko wayar ta miko mini tana fad'in." Ana kiran wayar Baba, Mama ana kiran wayar Baba."
Na kar'ba na duba sai na ga mamanta ce Hauwa. Na ajiye wayar har ta katse ta sake kira a daidai lokacin da ya fito da toilet din ya zo da sauri ya d'auki wayar yasa a kunne.
Ya amsa gaisuwar da take yi masa. Jim kad'an ya ce." Malama na ce."A a itama Aminar za ta dawo nan cikinku in sha Allahu."
Ya d'an yi shiru yana sauraranta can kuma ya ce." To shikkenan ku zo ke da yaran gabad'aya ku sauka a gidan Hajja zan yi magana da Ade ku yi duk shirin da za ku yi yau da daddare."
Ya yi shiru yana sauraranta na dan wani lokaci sai ya ja tsaki ya cigaba da cewa." Wai sau nawa zan gaya miki ne gidan ba shi da spece din da za ku zauna ku biyu can gidan Hajja akwai part dina ku sauka a can hakan ya yi ko?"
Ya sake yin shiru dai yana sauraranta ta jima kuwa tana yin magana kafin ya ce." To na ji za a gyara in sha Allahu, zan kira ki da safe kafin ku taho."
Ya kashe wayar yana kallona kafin ya ce." Hauwa ce wai ita dole sai ta dawo kano itama yara kuma can duka suke karatu gobe Juma'a na ce su zo gabad'aya lahadi da sassafe mu koma gabad'aya har dake."
Shiru na yi ban ce masa komai ba. Su zo na ji dadin hakan na kwashi yarana cikin sau'ki komawa kuma sai dai ya koma da ita da yaranta amma ni mun dawo nan gabad'aya a nema musu wata makarantar.
Ganin na yi shiru ban ce masa komai ba sai hankalinsa ya sake kwanciya domin ya d'auka na yarda. Jallop din taliyar da na yi tsammanin ba zai ci da yawa ba wadda na rage masa kaf ya cinyata ya sha ruwan da lemo yana gaya mini tun tea din da muka sha tare a d'akina bai kara cin komai ba.
Abinda ya faru kenan da assuba yana dawowa daga sallah ya fara kimtsawa na yi ko'karin gama abin kari da wuri domin ya karya kafin ya tafi.
Gabad'aya duka a dame yake haka dai ya zauna yana karyawa yana gaya mini jikinsa gabad'aya a mace yake domin baya tsammanin Malam D'aha zai amince da duk wani bayanin da za a yi masa. Na ce." Ka yi ta addu'a Allah Ya zab'a maka abinda ya fi alhari kawai idan har ya amince na gaya maka ka sanar da ni zan nemawa wani auranta ."
Ya

45 / 73