Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   32 / 73

93K to 96K   out of 217.6K words

ta 'kara zuwa domin ita najasa ce da mahaifiyarsu.
Voice na biyu kuwa kuka take yi tukuru tana fad'in. Anti Amina don Allah kada kema ki k'yamace mu don Allah kada lefin da mahaifiyarmu ta yi ya shafe mu wallahi tallahi ba mu ta'ba sanin abinda take aikatawa ba kenan, ta rasu ta dasa mana tsangwama da k'yama a wajan mutane ba mu da lefi kada ke ma ki tsane mu antina......✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Gudun aure littafin kudi ne complete 1k akan telegram via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*134*
Ina tsaka da mamakin abinda Hauwa ta aikata ya shigo dakin ransa a 'bace ganin haka ya sanya ni daidaita yanayin fuskata. Fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba duk akan na d'auki magani na bawa Hauwa kamar zai mangareni da duka. Na yi shiru kawai ina jinsa ban tanka masa ba ya gama da fad'in na tashi na je na kar'bo masa maganinsa. Nan fa d'aya na ce ba zan je ba na nemi waje na kwanta raina gabad'aya a b'ace wai shin yaushe za mu samu zaman lafiya ne a gidan nan. Ni a ganina abinda na yi shine daidai da adalci ban d'auka cewa zai zama lefi tunda ai shima yana son lafiyarsa
Me yasa ya amsawa mahaifiyarsa ya san bai shirya cigaba da zama da ita ba. Ba ni so daidai da kwayar zarra hakkinta ya kama ni. A yanayinta dai sulhu da sasanci take nema tunda har ta iya yin ado da kwalliya dominsa ta kuma bi shi dakinsa to ai sai ya yi hakuri ya yafe tunda zahiri shi ma yana yi mana lefin kuma ha'kuri yake yi da ita.
Ina kallonsa ya shiga toilet dina ya yi uzurinsa ya fito d'aure da alwala ya zauna saman dadduma ya bude Al'kur'ani mai girma yana karantawa daga tsakiya suratul-kahfi sai da ya kammala ya rufe al'kur'anin bai nade daddumar ba ya kwanta a samanta tare da takurewa kamar wani maraya.
Na tashi zaune ina duban bayansa da mamakin abinda ya yi akan ya yi wa Hauwa magana ko ya kwana d'aki daya da ita gwara ya kwanta a kasa bisa dadduma wace irin zuciya ce wannan ta riko da gaba mai tsanani.
Ina ta yi masa magana ya yi mini shiru kuma idonsa biyu tunda ina ganin haske wayarsa yana dubawa.
Na sauko daga gadon hijabina na sanya na bude d'akin na fita dole na kar'bo maganin na shafa masa tunda na lura shi akan hakan sai dai duk abinda zai faru ya faru ga lafiyarsa amma ba zai kwanar mini a d'aki ba balle ta fahimci haka ta ji haushi ko ta zarge ni.
Na bubbuga kofar d'akin nata ta zo ta bude mini ta yi sabon wanka cikin kayan bacci tana kamshi na ce." Maganin nan za ki ba ni."
Sai ta yi kasa'ke tana kallona cikin nazari na yi kasa da kaina ina jinta tana fad'in." Yanzu nan fa na gama shiri zuwa saman ya dawo ne?''
A tak'aice na ce." E, shine ya ce a bashi." Ta juya jikinta a sanyaye ta d'auko mini na kar'ba na ja mata kofar.
A zaune na same shi yana waya ya gama ya koma ya kwanta bai dube ni ba.
Na daura tare da furta." Ga maganin na kar'bo."
Ya yi mini shiru bai ce komai ba.
Shiru d'akin ya d'auka kusan minti goma sha biyar ba shi da niyyar tashi ya d'auki maganinsa ya fita.
Na ce." Ni fa wallahi ba zan yadda da wannan rayuwar ba. Ba zan ta'ba amincewa na zalinci wata ba mu yi maganar gaskiya a tsakaninmu kada ka so zuciyarka akan duk abubuwa da suka faru Hauwa matarka ce kuma 'yar uwarka ni kuma na dauketa abokiyar zamana tunda ka ce na kar'bo maka maganinka gashi ka tashi ka tafi wajenka ta sameka a can shi yafi alheri."
Uffan bai ce mini ba sai ya mika hannu ma ya d'auko fillo daya daga cikin wad'anda suke jere a saman gadona ya gyara kwanciyarsa.
raina ya b'aci sosai na kwanta jikina a sanyaye ina kallon bayansa da tarin mamakin abinda yake yi. Ni dai anan ban ga lefin da na yi ba kuma da zai tsiri jin haushina.
Damuwa ta cunkushe mini da fargaba domin yadda ya yi zuciya da kallon inda nake haka yake so ya yi wa lafiyarsa mugunta.
Kaina ya fara sarawa tsabar takaici na rintse idona domin kirkiro bacci amma nasan ba zai ta'ba zuwa ba.
Can na fara jin saukar numfashinsa alamar bacci ya d'auke shi. Na tashi zaune da sauri da mamaki da gaske yake yi
Na zuro 'kafata kasa ina le'ka fuskarsa bacci yake sosai kuma cikin kwanciyar hankali. Na tashi na je na d'auko kayan maganin na zauna kusa da shi tare da d'an bubbuga fillon da yake kwance ya bud'e Ido yana kallona da yanayin bacci. Na ce." Ka tashi na shafa maka."
Ya tashi kamar yadda na umarce shi da kansa ya cire kayan jikinsa. Ban ce komai ba na fara shafa masa yana ta bina da kallo har na gama bai yi magana ba ya mayar da rigarsa da wandonsa na ciki ya koma ya kwanta.
A haka muka kwana a d'akin kai da gindi. Sai da asuba ya fita bai kuma kula ni ba. Na kasance cikin mamaki sosai shikkenan daga gyara kayanka Allah Ya sawwa'ke.
A haka kwana biyun da Hauwa ya kamata ta yi da shi suka shud'e a banza ba ma ya yarda ya kwanta a dakinsa balle ta biyo shi sai ya taho nawa ya kwanta kuma ba zai mini magana sai dai idan na gaji na yi masa idan na zo na shafa masa maganin sannan yake amsa mini amma bai ri'ke mini hannu ba balle ya ce zai nemi wani abu.
ranar da na kar'bi girki da yamma na shiga kicin domin hada masa fruit-salad kamar yadda ya buk'ata. Baba Tabawa da Taburni suna ta hidimar abinda za a ci daddare.
Muka gaisa kafin na ji maganar Baba tana fad'in. " Ban da abinki Taburni ai ba ita ta d'auke ki aiki ba to me zai sanya ki damu da abinda ta ce don Allah ki yi hakuri me yasa za a yi ta maimaita magana d'aya."
Na ce." Menene kuma?''
Murmushi ta yi tana fad'in." Ita da Hajiya Hauwa da alama jininsu bai hadu ba tun bayan dawowarta kafin ku dawo ke da maigidan su ka d'an yi sa'insa abin dai babu arziki da b'angaran Hajiya Hauwa kamar yadda ki ka san halinta na cin mutunci wallahi har da zagi wai zamansu ba shi da amfani mun had'u har da ni munafurcin banza. daga lokacin ko Taburni ta gaisheta ba ta amsaw.........." To me zai sanya ni amsawa Tabawa"
Muryar Hauwa ta katse maganar Baba Tabawa gabad'aya muka juya muna kallonta. Ni mamaki ne ma ya kama ni yadda yau ta kira Tabawa kai tsaye babu ma Baba dukkaninsu dattijai ne cikinsu babu wadda ba ta haife mu ba ai rashi ba hauka ba ne don suna masu aiki sai su zama wulakantattu."
Ta shigo kicin din sosai tana fad'in." Baba Tabawa tunda Amina ta dawo ki 'kara kuzarin gulma da munafurci yanzu don Allah ba ki ji nauyi da kunya ba da girmanki da shekarunki?
saboda ni ba ni da kudi ba na baki toshiyar hanci shiyasa ba ki d'auke ni a matsayin matar gida ba. Matsiyaciyar matar can wadda ta yi mutuwar wulakanci tun tana raye kike maula da yi mata fadanci kada ki ce na manta duk abinda zai faru ba ki ta'ba goyon bayana ba Amina da Maryam sune mutane tunda suna sinna miki. To a shirye na dawo na gaya miki kowane sakarai da sha'kiyyi zan daidaita masa zama wallahi na kuma fad'a Mairo da Taburni sai kun bar gidan nan domin duk wani abu da ya danganci matsafiyar matar can najasa ne ba za ku hana mala'ikun rahama shigo mana gida ba."
Baba Tabawa duk yadda ta kai ga daurewa sai da ta fashe da kuka ta sanya tafin hannunta ta 'kunshe bakinta hawaye share-share a kumatunta. Tunda na d'auki baiwar Allah nan aiki tsayin shekaru kusan biyar tsakanina da ita alheri ne da kyautatawa da wasa da dariya amma yau Hauwa ta dubi tsabar idonta tana kiranta da munafukai shakiyya sakarai.
Taburni ta jingina a jikin wardrobe din kicin din tare da sunkuyar da kanta.
Bakincikin da nake ciki ya sake hauhawa ai na d'auka ta yi sanyi ta dawo ne domin ta gyara kuskuran da ta yi mu zauna lafiya ashe ba haka ba ne a zuciyarta da wani shirin ta zo.
Na dube ta sosai ina fad'in." A matsayinki na wa za ki sanya su barin gidan ko ke ce ki ka d'auke su aiki ki ke biyansu?"
Ta gyad'a kanta tana cewa." A matsayina na matar gida kamar yadda ki ke matar gida ko da bambanci ne a tsakaninmu."
Na ce." Da bambanci kwarai da gaske Hauwa Ina so na gaya miki ki gyara kalamanki akan wad'an nan dattijan Annabi Muhammadu s.a.w ya ce ka girmama furfura ko ta wacece ke yanzu don Allah ba ki ji kunyar duban tsabar idon Baba Tabawa kin gaya mata wannan maganganun ba."
Ta ta'be baki tana fad'in." Ita ba ta ji kunyar abinda take yi ba ai munafukar tsohuwa ce."
Na buga mata tsawa sosai ina fad'in." Wallahi tallahi Hauwa za mu yi ta dake gidan nan akan wad'an nan da suke tsaye na gaya miki."
Ta girgiza kanta tana fad'in.'' Na ji duka to Amina na ce ki rufe ni da duka."
Na ja tsaki kawai ban sake wata magana ba na juya bangaransu ina ba su ha'kuri zuwa lokacin itama Taburni kukan take yi tana fad'in." Shiyasa na ce fa tafiya zan yi cikin iyalina na yi abinda na yi Hajiya Amina ba na so a kaskantani ki yi hakuri ni ba ki yi mini komai ba amma don girman Allah ki sanya a mayar da ni k'auyenmu.
Na ji 'kwalla ta ciko kwarmin idona na dubi Baba Tabawa da take goye da Sultan a bayanta yana ta bacci idonta duk ya kumbura tsabar kukan da ta jima ba ta yi irinsa ba. Na gyad'a kaina in banda rashin mutuncin Hauwa matar da ta rungumi d'anki da ki ka dangwarar ki ka tafi take yi masa wahala itace abar zagi da aibatawa. Lallai da gaskiyar Hajja Hauwa ba ta da kunya yau na sake gasgazatawa tunda ita duk girma da shekarun mutum furfurasa ba ta hana ta yi masa diban albarka.
Da kyar na iya had'a fruit-salad din ina yi ina basu baki Hauwa ba su kadai ta ci mutunci ba har da ni da maigidan gabad'aya ta tsinka. Na had'a masa abinci tsaf tunda lokacin su ma sun kammala na kai samansa na jere inda yake zama.
Na yi wanka da sallar magriba na shirya na zauna kaina ya kulle gabad'aya na rasa ta yadda za a yi na fara yi masa bayanin abin nan da yake faruwa wanda na tabbatar da cewar wani sabon tashin hankalin ne zai sake faruwa a tsakaninsu tunda haushinta yake ji dama.
Ya kira ni a waya na tashi na je na same shi ya sake sosai ya daina gabar yana ba ni labarin Bashir kanin marigayiya cewa an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara goma sha biyar tare da horo mai tsanani babu kuma biyan tare tunda dama tsohon mai lefi ne nemansa ake yi ruwa a jallo dilan wiwi da 'kwaya ne ga 'yan sace-sace yana ta'bawa.
Jin sa kawai nake yi hankalina baya kansa amma dai na yi kokarin aro jarumta ban bari ya fahimci cewa akwai rikici ba.
Da asuba yana fita salla na sauka kasa. Kai tsaye d'akin yaran na leka tare suke da Mairo dama har ta yi musu wanka tana shiryasu da kayan makaranta. Khalil da yake ya girma shi da kansa yake shiryawa. Muka gaisa da su na wuce wajansu Baba Tabawa na same su suna dambarwa Taburni ta had'a kan kayanta ta 'kulle a d'ankwali tamau wai tafiya za ta yi rarrashinta ya hana Baba Tabawa shiga kicin kamar dai koyaushe. Ganin da gaske take ya sanya hankalina ya tashi ba ni son rabuwa da matar gabad'aya ita kuma yadda ta yi fushi koda an bar ta tafi garin nasu ba lallai ta dawo ba.
Gabad'aya muka fito fallo na yi na yi da ita ta yi hakuri ta'ki Mairo da yaran gabad'aya duka suka fito aka yi cirko-cirko. Minal ganin Taburnin tana kuka sai itama ta fashe da kuka da kar'fi don da alama hayaniyar da ake yi da kukan da suke yi su biyu ya tsorata kukan ta ya yi daidai da lokacin da ya shigo ya fara fadin." Lafiya a d'an ki'dime yana kallona domin neman karin bayani."
A tak'aice na ce." Taburni ce za ta tafi." Ya sunkuya ya d'auki Minal din yana rarrashinta da yanayi na damuwa ya furta.'' Taburni ke da na ce miki muna buk'atar zama tare dake yara sun yi sabo daku yanzu ki duba ki ga yadda Minal ke kuka ganin kina yi, ki yi hakuri ki zauna tare da mu duk abinda ya kamata na kulawa za a yi miki daidai gwargwado."
Ta sa gefan mayafinta tana fad'in." Dole ce ta sanya ni tafiya Alhji amma ni ma ina son zama daku."
Ya ce." To shikkenan ki gaya mini me aka yi nasan lallai ruwa baya tsami banza."
Shiru falon ya d'auka babu wanda ya yi magana. Sai da ya sake maimaita maganarsa tukkuna a sanyaye ta furta." Amaryaka da ta dawo ita ce bata buk'atar zamana a gidan."
A dan daburce ya ce." wace amaryar tawa kuma Taburni?"
Ta yi shiru tana jan hanci. Can kuma da ya gane Hauwa take nufi sai ya ja tsaki bai ce komai ba ya nufi dakinta da d'an karfi ya buga kofar d'akin ta yi magana ya ce." Bud'e malama."
Minti biyu ta bud'e ta fito da yanayi na bacci a idonta wato duk wannan dambarwar da take faruwa a gidan ita baccinta ma take yi.
Na tausaya mata k'warai da aniya yadda ya fara yi mata tijara da kausasan kalamai wanda ke nu ni da cewa ya fi buk'atar zaman Taburni a gidan a kan zamanta idan ba za ta iya zama ba hanya a bud'e take ta 'kara gaba. Ta muzanta ainun domin ya yi bala'in tsinkata ya kuma nuna mata cewa masu aikinsa sun fiye masa ita tsit! falon ya d'auka na yi 'kasa da kaina ina jajanta mata ina kuma jin wani iri a raina yanzu me ya fi wannan takaici. Babu abinda ya fi zaman lafiya dad'i a gidan aure Hauwa da za ta d'auki shawara sam tashin hankali bai kar'be ta ba bata ta cin riba ko kad'an sai fad'uwa a gigice da borin kunya ta nufi dakinta tana kuka mai cin rai......✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *PAID BOOK 1K ON TALGRAM VIA 0542382124... BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*135*
Ya wuce mu ya hau samansa da tsananin 'bacin rai a fuskarsa wannan ya sake nuna mini cewa dama kiris yake jira da ita a gidan don dai haka siddan ba zai yi mata rashin mutunci ba ne sai da dalili amma yanzu da ya samu mafaka ya yi da hujja! ita aka yi wa amma ni nake jin kunya da nauyi wai hausawa suka ce sandar da ta daki uwargida da ita ake dukan amarya.
A ranar kuwa yini ya yi yana 'kuncin rai tabbacin ta gama 'kona masa rai da kuma damuwoyin mas'aloli masu yawa a tare da shi
har ni da nake ta ko'karin sasanta al'amarin haushina yake ji. Hakan ya sanya ni rabuwa da shi na sauko na yi kwanciyata a d'akina gidan ya kasance shiru tunda ranar makaranta ce yara tun safe idan sun tafi sai yamma likis za su dawo. Da k'yar dai muka rarrashi Taburni ta janye k'udirinta ta ha'kura da tafiyar har suka shiga kicin da Baba Tabawa a tare.
Sai da daddare tukkuna wajan sha d'aya na yi shirin kwanciya na sake komawa saman. Na same shi zaune kan dadduma yana ta karatun al'kurani abincin da na jere masa bana tsammanin ya ci. Sai da ya kammala tukkuna ya juyo yana kallona muka had'a Ido. Ya d'auke kansa yana fad'in." Zuba mini abinci kad'an amma."
Ban ce komai ba na tashi na isa wurin abincin kamar yadda ya buk'ata shinkafa ce da taliya da miyar kifi masu girma.
Ya zo ya zauna da babbar wayarsa a hannu ya d'auki flat din abincin ya tallafe a hannunsa kamar yadda yake yi wasu lukutan ya fara da Bismillah sai da ya kusa cinyewa ya ajiye flat din ban ce komai na sanya a hannu cikin abincin na fara gyara masa kifin da bai ci ba duk da manya ne marasa k'aya amma dai ba a rasata ko yaya ne. Ya ci kifin sosai don da alama ya fi bukatarsa a kan nama idan shine ba zai yi masa irin wannan cin ba.
Na tsinci maganarsa yana fad'in.'' Amina Hauwa tana ganin tana da wani matsayi mai girma a gidan nan ko?'
Na yi shiru ban ce komai ba domin ni gabad'aya ma al'amarinsu ya ishe ni. Ya cigaba da cewa." Yara da suka ratsa tsakani na da ita ne kadai suke ri'ke da ita amma wallahi zan fad'a miki gaskiya ba ni son na bud'e idona na ganta cikin gidan nan nawa sai dole akan wad'an nan dabi'un da ta fara za ta sake fita domin ba ni had'a kowa da masu aikin nan mussaman Mairo da Taburni ina ganin 'kima da mutuncinsu duk wanda zai tsaya tsayin daka akan abinka ai masoyi ne."
Na ce." K'warai kuwa amma ita Baba Tabawa saboda ni na kawo ta bata da muhimmanci da zamanta da babu a gidan duk daya ne a wajenka ko."
Ya dube ni yana fad'in." Ban ce ba Amina ai ban ware ba har da ita na ke nufi."
Ya mutsa fuskata na yi ban ce komai ba. Ya gama cikin kifin na tattara kayan abincin na sauka da su k'asa na wanko hannuna tsaf na sake komawa saman na same shi zaune a wajen bai tashi ba.
Na dube shi sosai ina fad'in" Yau bacci ne a idona sosai za a shafa maganin

32 / 73