Author : Binta Umar Abbale Category : Read Hausa Novels
ba ce wurin addu'a. Taurarinta suna da tsananin haske dalilin da ya sanya kenan itama ta buk'aci da su yi musharaka wurin haduwar taurarin.
Ya jima yana girgiza kansa da mamakin abin. Ya jima da sanin cewa ana iya amfani da haske da taurarin mutum domin cimma wata manufa wasu lukutan mutum na zaune kaf sai a kwashe masa taurari bai sani ba. Wato malam ka ji tsoron Malaman yanzu da suka kwashe kayansu daga gaban ma'aki.
Kwana da yini suka yi a garin jos duk yadda Malam Isiyaku yake karyar da kai da nuna ya yi nadama bai saurare shi ba. Yana da jama'a sosai duk da wata mu'amula ba ta ta'ba had'a shi da shugaban jami'an tsoron garin ba. Dalilin suna da shahararsa a duniya ya sanya a daran ya gana da commissioner yan'sanda suka cika hannu da Malam Isiyaku zuwa sansaninsu.
Gajiya kam sun kwaso ta daga shi har yaran nasa ga tafiyar mota sai gefen asubahi suka shiga garin abuja ana ta kiran sallar farko.
Ban san ya dawo ba sai da gari ya waye tukkuna na fito na same shi da yaran gabad'aya a falo a zaune. Sun zagaye shi yana ta sauraransu yana murmushi Minal yar lelanshi tana kan cinyarsa. Twins kuma na gefansa a tsaye suna ta tsalle Khalil na saman kujera a zaune. Dukkaninsu cikin tsafta Mairo ta kintsa su. Suna ta 'kamshi.
Na yi murmushi ina kallonsu gwanin ban sha'awa na ce." Cikin dare ka dawo ne?"
Suka juyo gabad'aya suna kallona har da shi ba su lura da fitowata ba sai da na yi magana.
Ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Gefin asuba na shigo Amina. Ya kuke na same ku lafiya."
Na ce." Alhamdulillahi ya su Hajja?" Domin ni ce mini yayi kano za shi kuma zai kwana daya."
A tak'aice ya furta suna gaishe ku."
Ya sauke Minal kasa Yana fadin." Zan kwanta zuwa an jima ki tashe ni."
Na ce." To shikkenan."
Ya haye sama da dan sauri.
Na dube su Usai ta yi saurin janye idonta daga kaina. Na sassauta fuska tare da mika mata hannuna ina fad'in." Zo." Tun ranar da na mur'de mata kunne take ja baya dani. Hassana ce ke iya zuwa kusa da ni har ta yi mini hira. Minal kuwa yar d'akina ce tunda ita dama can akwai ta da saurin sabo."
Ta zo din kamar yadda na buk'ata amma bata kalle ni ba.
"Na ce." Menene?"
"Babu komai."
Na ri'ko hannunta a nutse na furta." Kina jin tsorona ne?"
Ta girgiza kanta. Na d'ora ta saman cinyata ta ai kuwa sai tasa dariya tana kallona abin ya zo mata daban.
Hassana ta taho itama tana bata rai. Na dauketa na sanya a daya gefan suka dinga dariya suna yi wa Minal gwalo ita kuwa mai neman jiran kiris ta fashe da kuka. Khalil yana yin dariya ya ce ni zo na goya ki."
Na ce." Zo nan goyo kike so ko?"
Ta daga kanta. Na ce." To ta kwana gidan sau'ki je ki ce Mairo ta bada abin goyo."
Ta kuwa ta fi da sauri.
Na dire su a kasa ina fad'in." Idan ba ku sanyata kuka ba bakwa jin dadi, kun yi girman banza."
Ina shiga d'aki ta shigo da towel din Sultan tana mika mini na ce." Aiki ya same ni kenan, gashi wanka zan yi yanzu Minal amma muje."
Ta biyo bayana na samu Taburni da yaran tana had'a musu tea na ce." To zauna ki ci abinci idan na yi wanka na fito zan goya ki."
Mairo da ke goge musu kayan makaranta ta ce." ashe da gaske goyon za a yi Hajiya."
Na ce." K'warai kuwa Mairo na juya na fita daga d'akin ina jinsu suna yi mata dariya.
Na sami Adam a falon a tsaye wanda shigowarsa kenan. Muka gaisa yana tambayata Baba ya dawo?"
Na ce masa ya dawo amma ya kwanta sai zuwa an jima ya dawo lokacin ya tashi.
Ya ce to cikin sanyin jiki kafin ya juya ya fita na bi shi da kallo gwanin ban tausayi.
Wajan daya da rabi na tashe shi domin yin sallah.
Ya tashi zaune yana kallona goye da Minal a baya. Ya ce "Wacece a bayanki?"
A tak'aice na ce." Name sake dina ce."
Sai ya yi murmushi ya ta shi ya shiga bandaki ina zaune ya fito d'aure da alwala na ce." Adam kuwa ya shigo nemanka d'azu."
Ya ce." Zuwa an jima zan nema shi. Sallah zan yi yanzu ki kawo mini abinci.".
Na tashi na sauka kasa na had'o masa abincin da abinda zai buk'ata na koma na same shi ya idar amma yana gyangyadi a saman daddumar hakan kuma ba dabi'arsa ba ce.
Na ajiye tiran ina tashinsa ya tashi ya nufi bed yana fad'in." Baccin zan sake komawa.
Da mamaki na ce." Abincin fa.''
Ya rufa da bargo yana fad'in." Sai na tashi tukkuna.
To wasa-wasa haka ya wanzu tsayin kwanaki hud'u yana wannan baccin gabad'aya yin ibada ne kawai yake tashinsa idan ya gabatar ya ce zai koma ya kwanta da rigima sosai yake cikin abinci ya zama kamar wani sususu jikinsa babu kuzari sai bacci sai kace wani rik'akken d'an 'kwaya.
Hankalina ya fara tashi domin na ce masa ya kira likitansa ya duba shi bashi da lafiya ya ce na kyale shi a hankali zai warware kawai dai na cigaba da kunnansa karatun al'kurani. Ganin abin nasa ya'ki sau'ki na fara kuka domin tunda ya yi tafiyar nan ya dawo bai kwanta da ni mun yi sunna ba kwana biyar yanzu wanda a tarihin rayuwarmu hakan bai ta'ba faruwa ba.
Muka dinga rigima akan na ce zan gayawa Hajja ba shi da lafiya a ganina ai mai matsalar aljanu da farfadiya ya kamata ace ana kunnawa akaratun al'kur'ani a saitin kunne, ga yanayin jikinsa ya nune babu kuzari amma ya ce shi lafiyarsa lau wace irin gajiyace wannan da zata mayar da shi d'an maye kullum bacci....✍️
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop 1k via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*124*
A cikin kwanakin da ya kasance cikin wannan yanayin ki'ba ya yi ta fuska sosai ban sani ba ko baccin da yake yi ne ya janyo faruwar hakan oho! tunda gaskiya ba abincin kirki yake ci ba ballantana na ce tun asali ma mutum ne shi da bai fiye tasa abinci a gaba ya yi ta narka ba, kuma ba shi da irin ciye-ciyen nan na masu kudi.
Cikin dare na tashi na yi sallah raka'a biyu na tsananta addu'a sosai domin abin ya fara daga mini hankali yanzu kuma na gano babu shakka akwai abinda ya faru wanda yake b'oye mini.
Gefan kansa na zauna na bud'e alk'uranin izifi sittin din da yake hannuna daga sama na fara a cikin nutsuwa har aka fara kiran sallar farko wanda ya yi daidai da lokacin ya motsa. Ya tashi zaune yana kallona na rufe al'kur'anin muka dubi juna na dan wani lokaci kafin ya kira sunana na amsa.
Sai ya zura k'afafunsa kasa domin sauka yana fad'in." An yi kiran sallah ko?''
Na ce." Za a yi yanzu dai."
Toilet din ya nufa na bishi da kallon nazari kafin na tashi na bi bayansa na ga yana had'a ruwan zafi dana sanyi wanka zai yi ban hana shi ba kawai na ja masa k'ofar na fito na zauna har ya kammala ya fito d'aure da towel ashe ba iya fuska ya murmure ba har jikin gabad'aya.
Ga mamakina da kuzarinsa ya kintsa ya fita massalaci wanda ya d'auki kimanin kwanaki biyar rabon da ya sanya kafarsa a waje duka sallolinsa a gida yake yin su ya koma ya lafke a gado.
Kasa sauka 'kasa na yi har sai da gari ya yi haske ya dawo. Ya gan ni a zaune bai nuna mamaki ba na zuba masa ido har ya zo ya zauna kusa da ni wanda na yi zaton kwanciyar zai sake yi sai naga akasin haka muka gaisa ya ce mini na d'auko masa Loptop dinsa dake ajiye can wurin da yake zama. Cike da jin dad'in ganinsa a haka na tashi da azama na je na d'auko masa har ya bud'e ya kunnanta sai kuma ya kashe ya janyo ni jikinsa.
Ga mamakina na ga yana ko'karin cire mini hijabin dake wuyana. Muka kalli juna ya kanne mini ido cikin wata kalar murya ya ce." Mu 'dan yi wani abu ko."
Kasa ce masa komai na yi domin ni hakan ma jefe ni ya yi a farinciki ganin ya fara dawowa hayyacinsa. Na biye masa kimanin minti talatin muka d'auka kafin komai ya kammala.
Ya riga ni yin wanka ko da na fito sai na same shi yana yin waya na ji yana kiran sunan wani Malam Rabi'u akan zai tura masa da abin sadaka a sake yin saukar al'kur'anin da aka yi a watannin baya.
Sai da suka gama tukkuna na sake gaya masa Adam ya shigo jiya da shekaran jiya wurinsa.
Yana sake ko'karin kunna Loptop din a karo na biyu ya ce." To zan neme shi na ji menene nasan ba zai wuce maganar Nabila ba ita take turo shi wai zata zauna tare da su."
A tak'aice na ce." Hakan yana da kyau ai."
Na tashi na sauka kasa domin had'a masa abin kari.
Kafin na shiga kicin din d'akin yaran na fara dubawa duk sun yi shirin tahafiz yau asabar da lahadi tun takwas na safe suke tafiya sai shida. Ranakun da suke da boko kuma suna shiga k'arfe uku. Dukkaninsu cikin uniform a tsaftace kamar yadda dai suke yi musu hidima a gidan Momin Taburni da Mairo kowanne da lunchbooks dinsa. Ganinsu ya saukar mini da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a raina na tsinci kaina cikin nishadi da annashuwa suka fara gaishe ni ina amsawa tare da tsokanar Minal yau sai makaranta.
Falon muka fito tare na ce." Mairo ta kira mini Masa'udu. Kamar yadda suka bar gidan Maryam ba ni son abinda zai sake dangantasu da gidan duk kuwa da cewa direban da yake jigila dasu yana nan tare da masu gadin amma ba ni son abinda zai sake kai yaran gidan ina so su fara gina sabuwar rayuwa mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ya shigo tare da risinawa yana gaishe ni na amsa na ce.'' Daga yau za ka cigaba da kai yara makaranta kafin Babansu ya samar musu da sabon direba."
Ya amsa da "To shikkenan in sha Allahu Hajiya."
Ya tasa kan su gabad'aya har Khalil suka fita suna yi mini bye-bye Mairo ta bi su da jakkunansu da kayan abincinsu.
Na leka d'akinsu Baba Tabawa muka gaisa sosai suna tare da Taburni da alama ta su ta zo daya tunda duk dattijai ne. Sultan na ta bacci cikin net din shi sun shirya shi tsaf.
Har na juya zan fita Baba Tabawa ta ce." Hajiya Amina kina jin mu da Taburni ko wai tafiya gida za ta yi."
Na juyo da sauri ina fad'in." Me yasa Taburni ko an yi miki wani abin ne? ko kuma ba ki jin dadin zama da mu."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Ko daya wallahi Hajiya ina so na je na ga yarana da iyalinsu idan hali ya yi zan dawo suna can suna jirana tunda sun san uwar rikon nawa ta rasu wasu daga cikin iyalina ma sun zo gaisuwa."
Na ce." A a gaskiya ba za ki saki aikinki ba Taburni za ki zauna da mu in sha Allahu a madadin marigayya kuma za mu ninka miki albashinki, zuwa ganin gida wannan ba lefi ba ne, amma ina jin dad'in ganinku a tare ga yara sun saba daku."
Kwalla ta cika kwarmin idonta tana fad'in." Shikkenan Hajiya Amina na gode sosai Ubangiji Allah ya saka muku da alheri cikin satin nan zan je na dawo."
Na ce." Zan sanar da maigidan in sha Allahu nasan zai sanya a aiki kuma aje a dauko ki."
Na fita daga d'akin cikin nazari. Idan Taburni ta tafi baba Tabawa ba zata ji dad'i ba sun saba ga yaran ma idan Mairo na wani uzuri wajanta suke zuwa kuma macace mai hankali.
da kaina na shirya masa abinda zai ci farfensun kifin na sake yi masa tunda na ga ya yi masa dadi kwanaki na hada masa da funkaso da tea wanda nasan dole zai bukace shi domin dumama cikinsa.
Ya kuwa ji dad'i sosai kuma ya ci da yawa ya dinga yi mini godiya ina jin dadi a raina ganinsa ya fara nutsuwa har ma yana ta rage ayyukan da ya jima bai yi ba.
To shi din ma da na gaya masa cewa Taburni za ta koma garinsu bai bada goyon baya ba ya ce yara sun saba da ita sosai idan har ba a takura mata ba to na gaya mata ta zauna zai dinga biyanta fiye da yadda tsohuwar uward'akinta take biyanta.
Yinin ranar haka na yi shi babu komai a cikina domin duk abinda na tunkara da zumar kaiwa bakina zan ji zuciyata na tashi abu mai tsami tsami shi na fi sha'awa tun da na fara jin haka kuwa akwai matsala daf nake da yin al'ada idan ba ta zo ba kuwa ciki ne.
Duk yadda na kai ga daurewa kuwa kasawa na yi domin da daddare amai na dinga kyalayawa Allah ya sa a d'akina ne na yi na gama na gyara toilet din na fito na kwanta lamo cikin kasala sallar Isha'i ma a zaune nayi ta saboda yadda jikina ya mace lokaci k'an'kani.
Sai wajan goma da arba'in na dare na iya fitowa falon shiru yaran duk sun shiga sun kwanta. Na nufi saman abin mamaki hawa daya biyu zuwa uku sai da na zauna na huta. A haka na kàrasa hayewa zuwa d'akin nasa.
A bud'e yake tunda dama yana tsammanin shigowata na same shi yana waya da harshen larabaci karo na biyu kenan da na ji shi yana magana da harshen. Ranar da aka d'aura auranmu a makka da kuma yau. Ban jima da zama a gefansa ba ya gama wayar ya dube ni yana fad'in." Hajiya yau mantawa ki ka yi da ni ne?"
A tak'aice na ce." A a gani na yi ka ji sauki ai."
Ya ce." Sai ba ni da lafiya za ki zo wajena har ki d'ora kaina anan." Ya fad'a tare da dora hannunsa saman kirjina.
Murmushi kawai na yi ban ce masa komai ba kaina ne ma yake yi mini ciwo.
Ya ce." Tunda magriba da ki ka kawo mini abinci ki ka sauka ba ki dawo ba ko na yi wani abin ne?"
Ya fad'a cikin rausayar da kai."
Na ce." Babu abinda ka yi kawai na ga kana aiki ne shine na ce bari na dan baka wuri ka kammala."
Kira ya shigo wayarsa ya d'auka na ji yana fad'in." Lafiya ya kike ina Uwani." Daga nan na fahimci Hauwa ce. Sai na juyar da kaina gefe to da yake hands free wayar take na ji tana fad'in." Yau kwana uku Ina neman wayoyinka bata shiga."
A tak'aice ya ce."
"Ba ki da number Amina?" Ya bata amsa da haka.
Ta ce." Itama ba ta shiga."
Da mamaki na kalle shi wayata kullum a kunne take wannan ba gaskiya ba ne ba ta kira ni ba.
Ya ce mata." Ok
Ina fatan lafiya ko?"
"Ba ni da lafiya ne?" Ta fad'a cikin 'yar k'aramar murya."
Babu wani gigita a tare da shi ya ce. Sannu idan kin je asibiti sai ki sanar da ni abinda ya kasance na sayan magani zan sa miki."
Daga haka bai jira jin abinda za ta sake cewa ba ya datse wayarsa ya ajiye.
Ya dube ni muka had'a Ido sai ya kanne mini idonsa yana fad'in." Ina labari?"
Gudun aure paid book ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Na ce." Kai zan tambaya domin cikin kwanakin nan ka jefa ni cikin rudani"
Ya sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba sai ya d'ora kansa saman tudun kirjina. Ni ma da taya 'bera 'bari na tallafe masa kan ina shafa shi. Ai sai na kunna shi ya sake ma'kale ni tare da zura hannuwansa duka biyun ya kewaye 'kuguna. Mun jima haka Ina ta shafa saman kansa a hankali