Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 73

57K to 60K   out of 217.6K words

Hauwa. Yadda take gaya mini cewa tunda take a duniya ba a ta'ba yi mata tozarcin da matar ta yi mata ba shine dalilin da ya sanya take so a d'ora mata jinyya mai tsanani ko kuma a shafe ji da ganinta ta yi mutuwar tsaye babu ji babu gani cikin biyu tace ayi daya. Duk abinda na lissafo maka da farko na saya na kuma fara aikin sai dai ban kammala ba, Allah ya yi mata rasuwa.
K'warai da gaske ya tsorata tun lokacin da mutumin ya fara magana. Mazantaka kawai ya nuna tare da gogewa ta fannin mu'amula bai nuna masa razani ba.
Ya ce." Yanzu ya ake ciki idan ka koma za ka kammala aikin ko kuwa?"
Sai ya gyad'a kansa yana fad'in." Zan dakata gaskiya tunda Allah ya yi ikonsa akan wadda ta sanya ni sai dai da iska (jinnu) muke yi su kuma ba alkawari ne da su ba, idan na gaya musu mu tsaya da yin aikin bai zama lallai su tsaya kai tsaye sai sun gindaya abinda suke buk'ata amma ba zai wuce yanka ba."
Ya girgiza kansa cikin d'an karan mamaki da al'ajabi cikin zuciyarsa tana nanata istigifari. Ya dube shi kafin ya ce." Ka kyauta da ka d'auki aniyyar dakatawa zan kuma biya ka hakkinka. Amma ba yau ba ina so ka dawo bayan sadakar bakwai kud'i hannu da hannu."
Ya risinar da kansa yana ta godiya. Shi kuma ya yi ta nazarinsa cike da madaukakin mamaki gashi cikakken mutum cikin manyan kaya da kamala har da rawani ashe mushiriki ne ta'babbe ne, wato iskokan da suke yi musu aiki sune masu biyan buk'ata ba Allah ba.
Ya sanya hannu cikin aljihu dubu ashirin ya bashi kafin ya ce ." Ka yi kudin motar komawa gida amma kamar yadda na gaya maka bayan an yi addu'ar bakwai ka zo ka kar'bi kudinka."
Ya kar'ba da sauri yasa a aljihu yana ta godiya ya mika masa hannu wai su yi sallama bai kar'ba ba kawai sai ya daga masa hannu yana fad'in "A sauka lafiya." Daga haka ya koma cikin gidan cike da tunani da nazari..
Ya samu Bashir tare da su Salim da Yusi a zaune. Kallo guda ya yi wa yaron ya hangi kama sosai da Maryam domin duk irin fuskarsu daya sai dai shi fuskarsa ta yi duhu sosai da lebensa tabbacin wiwi ta ratsa shi.
Ya dinga sunkuyar da kansa kasa kamar munafiki ya fara gaishe shi cikin ladabi irin wanda suka saba.
Ya amsa yana dubansa tare da fad'in." Ko kaine Bashir din ne?''
Da sauri ya ce." Ni ne, eh ni ne?''
Ya fad'a yana wata dariya da sosa kansa.
Shigowar Alhaji Sulaiman gidan da iyalinsa ya d'auke masa hankali, da kansa ya tafi domin tar'barsa tun kafin ya karaso rumfar da suke zaune.

Tare muka yini da Hajiya azizi da abokiyar zamanta mai suna Hajiya Salamatu da Halisa 'kanwarta da ta ba ni labarinta kwanakin baya. Muka yini dasu a gidan sai wajan uku na rana bayan sun ci abinci sun yi salla muka yi sallama da su kan cewa za su shiga can gidan Maryam din domin yi wa danginta ta'aziyya na yi ta mamaki ashe ba su shiga ba sai yanzu da suka tashi tafiya.
Alhaji Sulaiman ya shigo har gida ya yi mana gaisuwa ni da Hajja ya d'an jima a tare da Hajja suna hira kafin ya yi mana sallama ya fita.
Daf da magriba mun d'an samu sau'ki shige da fice na mutane domin duk wanda ya je can gidanta ya yi gaisuwa sai ya shigo mini mussaman mak'otanmu dama wad'anda muke cikin estate din a tare.
Na shiga d'aki sallah na samu Anti Yagana har ta idar ta kashingida tana fad'in." Gobe ana yin addu'a da safe zan d'auki hanya da wuri Amina."
Na ce" Ba za ki ta ya ni zama ba anti Yagana kina ji su Hajja ma fa gobe suke cewa za su tafi."
Ta furta." Na so hakan Amina Amma hankalina ya yi gida saboda Fadila ban san a wane yanayi take ciki ba tunda an ce har da karin ruwa."
Na ce." Hakane kuma to shikkenan Allah ya kaimu zan gayawa maigidan idan ya shigo in sha Allahu."
Ba tace komai ba. Na shige band'akin domin d'aura alwalar sallar magriba.

Har bayan isha'i muna tare da anti Yagana a d'aki muna tattauna mas'aloli masu yawa. Hajja ta shigo d'akin da kanta tana fad'in." Yagana tun safe da ki ka fito mu ka gaisa ki ka auri zaman d'aki ko ba kya jin dadi ne."
Ta mike zaune tana yar dariya kafin tace." Wallahi lafiyata lau Hajja kawai gajiyar tafiya ce bata sake ni ba."
Itama da murmushi da kulawa ta ce." To ku fito mu ci abinci, ke Amina kema tun d'azu nake hankalce dake kowa ya ci abincin rana babu ke, maza ku fito mu had'u mu ci abinci yanzu nan Tabawa ta kammala har ta fito mana dashi."
Na ce." To shikkenan Hajja.''
Anti Yagana ta yi murmushi bayan fitarta daga d'akin tana fad'in."Baiwar Allah nan tana sona Amina, ko da yake k'aunar da take yi miki ne ta shafe ni."
Na ce." K'warai kuwa na sheda soyayyata da Hajja ta daban ce, amma shekarun baya anti Yagana an so a juyar mata da hankali wallahi na d'an fuskanci gizago daga wurinta da na ri'ke addu'a kuma sai abin ya shud'e kamar ba a yi ba."
Ta ce." Muddin baka nufi kowa da sharri ba Amina to ko shi ya nufe ka dashi ba zai yi tasiri ba, addu'ar nan dai da ki ka rike ki ajiye a ranki cewa itace makaminki."
Na ce." In sha Allahu anti Yagana."
Tare muka fito falon duk suna zaune wannan karon Sultan yana hannun gwaggo tana d'an jijjigashi.
Kafin na zauna na ce." Gwaggo yau kece ki ke auran kenan." Tana dariya take fad'in.'' E, ai yau yace da ni yake auran."
Ina Uwani ta yi murmushi tana cewa." An jima kadan zai ce da tsohuwar zuma ake magani ni ce uwargidansa. Hajja da tunda suke maganar ba ta sanya musu baki ba sai yanzu ta ce." Duk ku gama yin jigila dashi yace ni yake so ko Tabawa." Aka yi dariya gabad'aya cikin raha da barkwanci.
Cikin wannan yanayin ya shigo tare da Kamalu dama a tare nake ganinsu duk lokacin da suka tashi daga kar'bar ta'aziyyar.
Ya tsaya suka gaisa da su Hajja kafin ya haye sama. Shi kuma Kamalu ya zauna a cikinmu Hajja ta ce Baba Tabawa ta zuba masa abinci.
Saman na bi shi ina shiga d'akin na same shi ringine a gado. Na k'àrasa na zauna gefan kafafunsa. Ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya." Na gaji tubis Amina ga'bobina ciwo suke yi mini wallahi na jima ban yi gajiya irin ta wannan lokacin ba."
Na sauke ajiyar zuciya Ina fad'in." Ya za a yi abu ne da aka asassa shi amma da yawa wasu ba sa yin wannan zaman."
Ya ce." K'warai kuwa gobe idan an yi addu'ar uku zan sanya a cire rumfunan da aka kafa kowa ya tafi kuma haka ya isa ranar bakwai zan sanya masallatai a yi mata addu'a."
Shiru na yi ban ce komai ba.
Gabad'aya tunanina na kan yaranmu. Amma har yanzu ban ji yace komai ba akansu. Ba ni son na yi magana ta zama fitina zan d'an jira shi daga nan zuwa ranar da za ta cika kwanaki bakwai duk wacce za mu yi sai mu yi.
Ya yun'kura zai tashi sai ya koma ya zauna. Na ri'ko hannunsa cikin mamaki ina kallonsa lallai da gaske ya gaji. Hannunsa da na ri'ke na ji d'umi ba kamar koyaushe ba. Sai kawai na ta'ba wuyansa zafi rad'au zazza'bi ne.
Na ce." Zazza'bi kake yi fa Baba?"
Ya ce." Zazza'bi ne ko?''
Wai tambaya yake yi. Na ce." K'warai kuwa zazza'bi ne ya kawo maka sagewar gabobi da ciwon jiki, ya kamata ka samu hutu fa."
Ya sake yun'kurawa a karo na biyu yana fad'in." Bari na yi wanka zan kira likitana yanzu ya duba ni tun wajan sha biyu na rana na ji yanayin jikina ya canza ina dan jin ciwon kai ma."
Na kama hannunsa muka nufi bandakin tare na hada masa ruwan wankan ina fad'in.'" Wankan ma da ka bar shi tunda ka yi da safe. " Ya ce." Ai ba zan iya bacci ba idan ban yi shi ba Amina, kada ki damu bari na yi na fito ki kawo mini abinci."
Na ce." To a sanyaye na fito na bar shi a toilet din na sau'ka kasa cikin 'yar damuwa ya jima kuwa bai kwanta ciwo ba tun bayan zazzafar murar da ya yi a gidana sakamakon ruwan saman da ya dake shi a shekarun baya.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Gudun aure paid book. 2k complete on telegram. What'sappa Gruop 1k Via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*121*
Lokacin da na koma d'akin bai fito ba na zauna ina jiransa ya fito a rikice da d'ari irin na zazzabin ya sake ninkuwa kaya masu d'an kauri na d'auko masa ya kar'ba yana ko'karin sanyawa ya ce na d'auko masa hular sanyi duk a cikin kayan nasa ina fad'in." Abinda nake ta gudu kenan. Ya gama sanya kayan jikinsa ya zauna gefan gado cikin yanayi na ciwo da kaina na shafa masa basiline a jikinsa gabad'aya. Ya sanya hular har ta rufe kunnuwansa. Kafin na fara zuba masa abincin ya d'auki wayarsa ina jin ya kira likitansa ya yi masa bayani ya bashi tabbacin cewa gashi nan zuwa yanzu.
Cokali biyu ya iya ci na abincin ya dakata. Gabad'aya ni ma sai na ji zazzabin yana nema ya rufe ni. Babu zato ba tare da tsammani ba na ji yana fad'in." Kira mini Hauwa a wayarki Amina."
Da mamaki mai yawa nake dubansa. Ya d'an lumshe idonsa kafin ya bud'e yana gyad'a mini kai.
Ban iya cewa komai ba na tashi a hankali na sauka kasa da nazari a k'wanyata. To ko dai an daidaitasu ne ban sani ba wata'kila kafin mu fito daga d'aki ni da Sahura mahaifiyarsa ta zauna dashi akan hakan zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sa'ke. Na koma d'akin na same shi a takure a gado ga blanket din bai rufa ba.
Na zauna tare da rufe masa k'afafunsa har zuwa saman kirjinsa sannan a tsanake na fara neman layin Hauwa. Bugun farko ta daga ta kama sunana. Na amsa kafin mu gaisa ban ji ta sake yin gaisuwa ba kawai ta yi shiru sai na daure na ce." Maigidan ne yake son magana dake?"
A yatsine tace." Kamar yaya menene a tsakanina da shi, kuma ai yana da lambata mai ya sanya sai kece za ki kira ni.''
Na danne b'acin ran da nake ji yana taso mini na furta." Haka dai ya ce ni na kira ki Hauwa."
Ta ja siririn tsaki wanda ya yi mini ciwo sosai a rai amma ban katse wayar ba na mik'a masa yana daga kwance don bai tashi ba ya kar'bi wayar yasa a kunnansa. Sunanta ya kira ta amsa a dakile.
Ya d'an yi jim ban sani ba ko yana jiran gaisuwarta ne ko kuma yana jiran ta yi masa ta'aziyya ko daya dai ba ta yi ba.
Ya furta." Kina lafiya ko?''
"Umm" Ta ce cikin basarwa. Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya furta." Idan kin ji wani canji ko yaya ne a jikinki kada ki yi shiru."
Na yi zugum ina kallonsa da mamaki wai yau Hauwa yake rarrashi har yana fad'in idan ta ji canji na ciwo a jikinta kada ta yi shiru ta sanar da shi. Duk ina k'iyayyar da yake fadin yana yi mata. Mamaki ya kasa bari na janye idona daga kansa har sai da suka yi sallama ya miko mini tare da lumshe idonsa. Na daure ina fad'in." Alhamdulillahi na ji dadin wannan abin da ya faru, Ina fatan Allah Ya sa ya zama na karshe."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Ni ma na yi shiru ina d'an duba wayata sai dai can kasan zuciyata wani takaici ne na dinga tunanin daga ina yake ai ni nake so Hauwa ta dawo mu cigaba da zama to mai zai sanya don ya yi waya daya da ita yau na ji haushi idan hakane kuwa gaskiya zuciyata bata kyauta mini ba.
Ban iya tashi na fita daga d'akin ba har sai da likitansa ya zo ya duba shi sosai ya yi masa BF domin yana kuka da ciwon kai sosai jininsa ya haura amma ba sosai ba, dama kuma yana da hawan jinin sai dai ba kasafai yake tashi ba sai da damuwa kamar shakarun baya da ya motsa masa lokacin ina amarya yana neman hanyar da zai samu kaina ni kuma na'ki bada fuskar hakan tun zamana na farko Legos kenan a iya sanina tun daga lokacin bai kara motsa masa ba sai yanzu.
Suka yi sallama yana fad'in " Za su tafi da Sukairaju yanzun domin ya bashi magunguña. Ya ce mini lallai ya ci abinci sosai kafin ace ya sha maganin.
Da kyar da jibin goshi kamar wani yaro ko d'an yayen da yake rigima ya ci cokali biyar bayan biyun da ya ci da farko yana fad'in bakinsa babu dad'i, ba zai iya ci da yawa ba. Haka nan na ha'kura na kyale shi tunda iya naci da magiya na yi masa akan ya kara yace a a.
Sukairaju ya kawo magunguñan ya tsaya ya yi masa sannu kafin ya fita. Na duba kowanne akwai yadda za a ba shi.
Na dube shi idonsa biyu rufe idon kawai Yayi kamar mai bacci.
Na ce." Ka tashi kasha maganin to."
Bai yi mini jayayya ba ya tashi na d'auki ruwa na tsiyaya a cup na mik'a masa ina ciro maganin ina bashi yana sha tsaf ya gama ya ajiye zai kwanta na ce." Ka dan bari ya fad'a maka." Bai ji ba ya yi kwanciyarsa minti biyu kuwa sai yun'kurin amai. Ya tashi da azama ya nufi toilet ya fara watso shi duk abincin da yaci da maganin da sha suka yo waje.
Na rasa yadda zan yi gabad'aya damuwa ta dabaibayi ni. Haka nan na tarairayo shi muka fito ya je ya kwanta ya nishi. Na lura baya son ciwo kuma bashi da wani dauriya idan bashi da lafiya haka ya yi mini lokacin da ya kwanta ciwon mura a gidana na kuntau na sha dawaniya.
Toilet na gyara na fito na same shi bacci ya d'auke shi sosai. Aikuwa ba zai yiwu ba, tashinsa na shiga yi ya bude idonsa na ce." Dole fa sai ka tashi ka sake cin wani abincin da maganin idan yaso sai ka yi baccin."
Bai ce komai ba ya gyara kwanciyarsa ya rufe Ido.
Na ce." Ka tashi don Allah ka ji.''
Ya yi mini shiru bai motsa ba. Kawai sai na zuba masa ido tsabar takaici da damuwa na ce." Shikkenan gaskiya zan sanar da Hajja an ta'ba yin ciwo ba cin abinci da magani."
Ya bude idon yana kallona yace." Wai ba na ci ba ne?".
Na ce." To nawa yake wanda ka ci, kuma duk ka amayar dashi da maganin."
Ya tashi zaune tare da tallafe ha'barsa. Sosai na zura masa ido ina nazarinsa sai nake ganin kamar bayan ciwon da yake damunsa akwai wata damuwar. Zuciyata ta fara raya mini ko ya fara kewar matarsa ne da ta rasu. Wani sashe na daban yake ce mini 'Anya kuwa' ai an yi masa mace-mace da yawa ya ha'kura kuma bai ta'ba yin wani ciwo ba, kawai dai ciwon ne ya zo masa akan ga'ba ne.
Nasa hannu na cire hannunsa da ya tallefe ha'barsa da shi a d'an sanyaye na ce." Wai menene don Allah, kada ka jefe ni cikin tashin hankali, yau kana tallafe ha'ba ko akwai wani abu da yake damunka?"
Ya dube ni. Muka tsirawa juna ido sosai mun jima a haka bai ce komai ba sai ni na janye idona na sake zubo masa abincin da kaina na dinga bashi cikin ikon Allah kuwa ya ci da yawa da kamar minti goma tukkuna na sake bashi maganin a karo na biyu, ban yarda ya kwanta ba sai da muka yi zaman kimanin minti ashirin har ya fara gyangyadi sannan ya kwanta ni kuma na sauka k'asa.
Na samu anti Yagana ta jima da yin bacci. wanka na yi a gurguje na sanya kayan bacci tare da a turare a jikina na koma saman. Lokacin baccinsa ya yi nisa sosai, na shiga cikin bargon kusa dashi sosai na kwanta kafin na fara yin addu'ar kwanciya bacci.
Da asuba da d'an kuzari ya tashi domin ya riga ni ma tashi motsinsa na ji a bandaki na yun'kura da sauri na dira daga gadon domin ina tsoron ya ce zai watsawa jikinsa ruwa. Na same shi yana alwala sai na sauke ajiyar zuciya na tsaya har ya kammala tukkuna ya fita zuwa massalaci sannan shiga toilet din sosai domin yin nawa uzurin.

Tun bayan da ya fita da asuban bai dawo ba sai wajejan goma da arba'in na safe. Na d'an shiga yar damuwa saboda yanayin jikinsa. Amma nasan abinda ya zaunar dashi bai wuce yin addu'a ba kamar yadda aka yi duk ranar da mamaci ya cika kwanaki uku da rasuwa.
Anti Yagana Hajja da inna Uwani Gwaggo sun shirya tsaf da Shirin tafiya muna falo da su gabad'aya domin jiran shigowarsa Kamalu ya riga shi shigowa da kusan minti goma kafin ya shigo.

idan kin karanta ba ki biya ni ba ina bin ki bashi.

Cikinmu ya zo ya zauna kujera kusa da ni. Suka gaisa sosai. Hajja ta gaya masa tafiya za su yi. Na d'auka zai ce su yi hakuri su bari ayi bakwai sai bai nuna damuwarsa akan hakan ba ya ce ." Ita anti Yagana ta bari zuwa an jima kadan Sukairaju ya dawo sai ya d'auketa a mota ya kaita har gida. Hajja kuwa dama a babbar mota suka zo da direbanta duk zai kwashe su har Hajiya Saratu Kamalu da Yusi da Shima shigowarsa kenan yanzu a lokacin da suke maganar cikin shiri tunda ya san da tafiyar tun jiya 'dan uwansa ya gaya masa
Cike da damuwa muka yi sallama na kasa daurewa sai da na yi kwalla na d'auko hijabi muka bi bayansu harbar gidan ni da anti Yagana har sai da suka shiga

20 / 73