Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 73

39K to 42K   out of 217.6K words

na ce to shikkenan.
Na bud'e wayata sakkonin Sahura suka shigo rututu na shiga ina dubawa ina kuma sauraran voice note din da ta turo mini yanzu haka tana gidansu. kuma ta sanyawa gidan sabon kwado Idiris sai dai ya nemi makwanci."
Cike da mamaki na kira wayarta.
Tana d'agawa na ce." Sahura me ya yi zafi haka? yanzu har sai sai ta kai ki ga tafiya gida ba za ki yi hakuri ba."
Ta furta." Amina wallahi na rantse sai dai ya zab'a ni ko matar da zai auro da gaske fa aure zai yi wallahi da idona na ga yana had'a lefe."
Na ce." To shine me wai? ke ba za ki iya ha'kuri na d'an wani lokaci ba Hajiya don Allah kada ki ba ni kunya mana."
Cike da damuwa ta ce." Ke ma kin san babu adalci dangane da abinda Idiris yake ko'karin yi mini ko Amina."
Na danne dariyar da take so ta kwace mini na ce." Na sani to amma ba mu da yadda za mu yi, ba za mu hana shi ba amma ai bari ba shegiya ba ce idan ta shigo kudin suka kare sai ta ga kwakwar da ake ciki a gidan. Ki yi hakuri don Allah ki koma. Yanzu ina yaran suke?"
Ta ce." Suna can gidan Babarsa." Na ce amma abu bai yi dad'i ba wallahi, ki bari da safe za mu yi magana in sha Allahu gabad'aya kin tayar mini da hankali wallahi."
Ta yi 'kwafa ba ta ce komai ba.
Na ce." Da safe zan kira ki in sha Allahu rabbi." Ta ce." To shikkenan."
Na kashe wayar na ajiye Ina mamakin yadda ta tayar da hankalinta wato idan ka ga mutum bai yi abu ba to bai zo kansa ba sai na tuna lukuta da dama da abubuwan da suka shude kai kishiya abar gudu ce, su kuma mazan suna fad'in abokiyar zama ce.

To cikin shan k'amshi ya shigo mini ganin haka ya sanya ni ma na kama kaina. Na yi masa sannu da zuwa a takaice bai zauna ba ni ma ban yi masa tayin zaman ba tunda dama sai ya so yake zama har ma ya kwana d'akin nawa. Na dube shi yana ta jin haushi na yi tsai ina nazarin abinda ya sanya shi shigo mini haka idan don na yi wa yara fad'a yake jin haushi to yanzu kuwa na fara wallahi.
Ya juya zai fita yana fad'in." Ina sama ki zo?"
Ban amsa ba har ya fita. Na ja tsaki ina fad'in." Aikin banza harara a duhu. Sai dai ya yi kusan minti ashirin da fita na bi bayansa. Yana can kan kujera daga gefe yana duba Loptop dinshi na shiga. Ya amsa sallamata yana kallona har na je na zauna kujerar dake kallonsa bai d'auke idonsa ba. Ni ma kallonsa din nake yi cikin yatsine fuska. Ya sassauta yana d'an murmushi ya ce." Yau kuma baturiya ki ka koma Amina?"
Na yatsuna fuska ban ce komai ba.
Ya ce." 'Dan taso ki zo nan."
Juyar da fuskata na yi ban ce komai ba kuma ban tashin naje din ba. Dole shi ya kashe Loptop din ya zo inda nake yana fad'in." Irin wannan gayun Amina ai ba zan iya komai ba."
Na ta'be baki uffan ban ce ba. Ashe karyar cin magani yake yi. Ya rike hannuna tare da ko'karin d'aga ni wai sai na tashi tsaye."
Na cire hannuna ina fad'in."Menene haka?" Ya lumshe ido kafin ya ce." To nuna mini kwalliyar na gani, na bawa idona hakkinsa."
Na dauke kaina domin ganin ya fara gigicewa. Ya d'ora hannunsa saman kirjina da suka dan taso ana ganin tsagarsu.
Na cire hannun da sauri ya sake jana da k'arfi har sai da na zamo daga saman kujerar na zauna kasan kafet tare da tankwashe k'afata. Saman kujera ya zauna ya sanya ni tsakiyar k'afafunsa ya rankwafo kaina tare da zuba gabad'aya hannayensa saman kirjina ya ri'ke da kyau. Dole babu shiri na tashi tsaye abinda yake so kenan ya mike shima ya rike hannuwana da kyau yana kallona. Duk sai na tsargu na dinga kame-kame daga nayi yun'kurin zama zai tsayar dani. Cikin iyashege ya fara dukan mazaunaina yana fad'in." Babar mota babbar giwa ba dai yaro. Hajiya da kanta wannan samun irinta sai an had'a da sallar dare."
Duk yadda na kai ga cin magani sai da ya sanya ni dariya na shiga bige hannunsa ina fad'in." Don Allah ka bari dukana fa kake yi a fakaice gaskiya zan rama wallahi."
Ya ci gaba da d'aka mini duka a mazaunai bai bari ba duk da buge hannunsa da na yi yana fad'in.'' Gaskiya na iya kiwo wallahi, wai tur'kashi Allah Ya ba ni wuyan d'auka."
Dariya na dinga k'yalkyalawa shima ya sa dariyar yana fad'in." Haba Hajiya ko ke fa, kin yi lefi kina ci mini kunu haka ake yi."
Ya rike hannuna muka zauna saman kujera yana yi mini wani irin kallo da na kasa tantance ko na menene a hankali ya ce." Kin yi mini kyau yau fiye da koyaushe na yaba sosai kuma zan bada tukwici. Na zuba masa ido ina kallonsa ya ciro wani zuben azurfa da yake yatsanshi na tsakiya zoben tunda na san shi dashi a hannunsa kusan koyaushe kamar k'ara masa kyau da sabunta ake yi azurface gangariya daga tsakiya an yi mata ado cikin wani salo. Da yake siraran yatsu ne dashi ya sanya yana sa mini ya kama ya tsayana wanda ya zauna ya yi cif cif ya yi kyau sosai. Ya sumbaci hannun yana fad'in." Ga tukuici idan bai isa ba sai na sake bada wani abin."
Na dubi yatsana ina dan murmushi na furta." Aikuwa na gode sosai da wannan tukwici ya yi mini ba sai an bada wani ba."
Sai ya hade hannunmu wuri d'aya yana fad'in." Kin san wani abu?"
Na girgiza kai ina kallonsa ya ce." Kada ki sake dukan yaran nan ba ni so, a duk lokacin da wani abu ya shiga tsakaninsu ko suka yi abu na rashin kyautawa a zare musu Ido, a yi musu fad'a amma ban da duka ba na so, domin hakan ba tarbiya ce ba don wasu lukutan dukan yakan kangarar da yaro.
Na daidaita yanayina tare da fad'in. " Wai wanene ya gaya maka dukanta na yi? fad'a fa na yi mata na dan murde mata kunne shikkenan duka."
Ya ce." Ta gaya mini kin dake ta a kanta shin kin san illar duka aka kuwa?"
Raina ya b'aci amma na danne na ce." Sai na dake a kanta domin na illatata ko?"
Ya yi shiru yana kallona. Na ce." Ni ban yi mata dukan da zai firgitata ba a gaban Baba Tabawa komai ya faru. Ba ni son cizo domin yana da illa sosai dole a ja mata kunne."
Ya ce." Ni ma ban hana ba, dukan ne kawai na ce ba na so kada a sake?"
A tak'aice na ce." To shikkenan." Domin maganar ta mutu kawai amma ba yadda za a yi Ina raye kuma ina gani su yi abinda ba shikkenan ba na zauna ina yi musu lako-lako ni kaina ba a yi mini irin wannan tarbiyar ba, ba kuma zan yi wa yarana ita ba.
Na ce." Ina Hauwa na d'auka tare za ku taho?''
Ya ce." Tana can gidansu wai ba zata dawo ba"
Da mamaki na ce." Ba zata dawo ba?"
Ya ce." Kwarai kuwa haka ta fad'a, na ce to shikkenan Allah Ya hada kowa da rabonsa."
Kawai sai na zuba masa ido da mamakin maganarsa wai Allah Ya hada kowa da rabonsa ya fadi hakan cikin kwanciyar hankali tabbacin abin bai dame shi ba. Ni Kam sam lamarin bai yi mini sugar ba. Na ce." Don girman Allah ka yi hakuri."
Ya dube ni da mamaki kafin ya ce." Ha'kuri ai na yi tunda har na mayar da ita amma ta ce a a, kuma ta yi mana shegantaka sai ta sha zamanta abinda ga matan nan da yawa me zai dame ni Amina."
Na ce." Amma dai ba kamar ita ba."
Ya ce." To yanzu ya za ayi?"
Kai tsaye na ce." Ta dawo dakinta don Allah."
Sai ya yi murmushi a hankali ya ce." To ki kira wayarta sai ki roke ta Ina ga haka zai fi."
Daga haka sai ya tashi ya nufi gado yana fad'in." Zo mu yi wata magana."
Na yi jim kafin na tashi na bi shi gadon ya janyo ni na kwanta a gefensa sai ya sanya hannu ya rungume ni sosai a jikinsa yana fad'in."Alhamdulillahi. Sai na rasa godiyar Allahn ta mecece haka dai muka raya daran cikin shau'ki da sakwarkwcewa. Da asuba yana fita salla ni ma sauka k'asa cikin gajiya da bacci a idona.
Sai da na yi wanka tukkuna na yi sallah na nemi gado na kwanta domin mugun bacci ne a idona wanda zai iya zame mini ciwo muddin ban yi shi ba.....✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️

*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa

*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
Kirana da aka yi a waya shi ya tashe ni wajejan goma da ashirin da biyar na safe. Koda na duba lambace babu suna na daga tare da sallama sai na ji muryar Idiris mijin Sahura nan da nan na daidaita yanayina. Domin zahirin gaskiya ni ma haushinsa nake ji dangane da abinda yake ahirin aikatawa. Tabbas nasan kiran nasa baya rasa nasaba da matsalarsu. Muka gaisa jikinsa a sanyaye ya fara yi mini bayanin halin da ake ciki Sahura ta rufe gida sannan ta tattara yara da kayansu ta kaiwa mahaifiyarsa bayan tasan bata da k'oshin lafiya. Yanzu haka sai a shagon dake jikin gidan ya kwanta shagon da yarana suke d'inki kenan yana jadadda mini a cikinsu ya kwanta cike da alhini da damuwa. Ban katse shi ba har sai da ya kammala tukkuna na ce." To wallahi ni dai Idiris ba ni da tacewa akan wannan lamari. Ina ganin ka kyaleta kawai tunda tafi buk'atar rabuwar sai ka je ka yi rayuwarka da sabuwar amaryarka yara kuma ai duk sun girma babu wanda za a yi wa wahala a cikinsu."
Da damuwa ya ce." Saboda fa kusancin da yake tsakaninku ya sanya na kira ki Amina, me yasa za ki gaya mini haka ke don Allah idan na ce zan rabu da Sahura ba za ki yi mamaki ba?"
Na d'an yi murmushi babu nisha'di na ce." Babu mamakin da zan yi Idiris abinda aure na mutum biyu ne idan ka gaji da ita zaka sawwa'ke mata mana ko kuma ka nemi hanyar da za ka k'untata mata."
Ya ce." Yanzu dai don Allah ki rarrasheta wallahi ba wai don na wulakantata zan yi auran nan ba. Ina son Sahura ina kuma buk'atar cigaba da zama da ita ki rarrasheta ki bata ha'kuri ta dawo mu cigaba da zama in sha Allahu babu abinda zai faru domin itama yarinyar da zan aura bata da matsala 'yar gidan tarbiya ce wallahi bata da fitina."
Na yi dariya ina mamakin maganarsa tun bai zauna da yarinyar ba yana shedar halayenta tabbaci kenan ba zai janye ba. Na ce." To shikkenan zan yi magana da ita zuwa an jima in sha Allahu."
Da sauri ya furta." Zan kira ki domin na ji abinda ku ka yanke amma don girman ki tausheta ta dawo na ware mata turmi biyu daga cikin lefen da nake had'awa sannan zan bata dubu hamsin sai ta sayi kayan kwalliya."
Na ce." To shikkenan. Da takaici na katse wayar ban tsaya na kàrasa sauraran karshen maganarsa ba. A tunana ai Sahura tafi karfin turmin atamfa biyu da dubu hamsin, ita wahalar nawa ta yi masa tunda suka yi aure har yanzu ma cikin yi masa hidima take.

Da yammacin ranar muka yi waya da ita na gaya mata Idiris ya kira ni a waya akan abinda yake faruwa. Kamar yadda ya buk'ata din na fara rarrashinta da kawo mata misalai ta yi shiru tana saurarena don har ina murna ina cewa ta sauko a zuciyata sai da na gama maganata tukkuna ta ce ." Ba ni buk'atar atamfofinsa ya ri'ke har da k'udin ya k'arawa amarya Amina, takarda zai aiko mini da ita yanzu zaman da nake yi kenan."
Na ce" Sahura akan kishiya dai idan ki ka kashe auranki na kusan shekara ashirin da wani abu wallahi kin ba ni kunya kuma na raina wayonki, ki bari ta shigo mana ki ga kamun ludayin zaman. Haba don Allah ki jure mana."
Kashe mini wayata ta yi ta barni ri'ke da tawa a kunne da mamaki.

Bayan magriba Idiris din ya dinga kira wayata ina kan daddauma ina jan carki kamar yadda na saba. Koda na duba na ga shine na ajiye wayar kawai na cigaba da abinda nake yi shi kuma bai fasa kira ba. Hakan ya yi daidai da shigowar maigidan wanda shi ma tunda ya fita da asubahi bai sake shigowa ba.
Ya d'auki wayar yana dubawa sai ya kalle ni kaina a sunkuye kawai sai ya daga tare da sanyata a kunnansa jin muryar namiji na ji yana fad'in." Wanene?" ban ji abinda Idiris din ya ce masa. Na ji yana fad'in." Mijin Sahura ne to bari ta kammala tana azkar ne zuwa an jima sai ka kira."
Ya yi shiru na d'an wani lokacin kafin na ji yana fad'in." Amin Ya Allah, ma sha Allah, ka kira zuwa an jima kadan." Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye har na kammala na juyo ina dubansa ya ce." Mijin Sahura ne ya kira ki a waya ina fatan lafiya?"
A tak'aice na ce." Lafiya ba lafiya."
Ya dube ni sosai yana fad'in." Suna da matsala ne?"
Ina ko'karin cire hijabin jikina na furta." Aure zai ka'ra shine take bore har ta tafi gida."
Ya yi d'an jim kafin ya furta." Na kan rasa inda tunaninku yake tafiya wataran Amina, daga zai kara aure domin raya sunna sai ta ta tafi ta bar dakinta menene amfanin hakan."
Cike da takaici na ce." Ai ba a ce kada ya kara ba, ya bari ya tsaya da k'afafunsa tukkuna bashi fa da cikakkiyar
sana'a, wallahi Sahura wahala take sha a hannunsa kuma ta yi masa hallaci tunda suka faru a gidan haya suke shekara kusan ashirin da uku da auransu buge-buge yake yi itace karfin kula da gidan tun kafin ma ta samu aiki a kamfaninka haka take gwagwarmaya. Amma shine daka kawai an yi musu rabon gado ya samu miliyan takwas ko wata biyu fa ba a yi da raba musu kudin ba ya fara yun'kurin karin aure har yana tara lefe a dakinta. Ita kuwa ta kulle gidan ta gudu ta kai masa yaransa wurin Babarsa."
Dariya ce ta sub'ce masa ya dinga yi har ina mamakinsa na d'auka ai zai cigaba da goya masa baya. Ya ce." A lallai bai kyauta ba kuma da gaske bai yi adalci ba. Yadda ki ka gaya mini yanzu ai ita ta yi masa hidimar da ta zarce ta miliyan takwas to me yasa tunaninsa bai kai ya saka mata da alheri ba sai da kishiya. Bai kyauta bai kuma yi daidai ba, in banda rashin tsinkaye ai ba aure ya kamata ya yi ba a yanzu ko?"
Da sauri na ce." Kwarai kuwa abinda itama take ji wa haushi kenan zai bata turmin atamfa biyu da dubu hamsin abinda ya kara ba ni haushi dashi kenan."
Ya ce." Kin ga kira mini Sahurar yanzu na yi magana da ita."
Na zauna gefansa ya miko wayata na lalubi lambata bugun farko ta daga cikin bala'i ta fara fad'in." Amina ki kyale ni don Allah idan har kin san ba maganar arziki za ki gaya mini ba, na gaya miki na gama yanke hukunci, idan kema za ki goyu da bayan Idiris din sai nasan a wani aji zan ajiye ki."

Ina binki bashi idan kin karanta ba ki biya ni hakkina ba

Na ce." Yi ha'kuri mai da wukar sis, Yallabai ne zai yi magana dake." Ta yi shiru ba ta ce komai ba sai na mik'a masa wayar da sauri ya kar'ba a nutse ya kira sunanta "Sahura."
Ina ji ta amsa cikin ladabi." Na'am ranka ya dad'e ina yini?"
Ya ce." Lafiya lau ya kuke ina yara?"
Ta ce." Kowa lafiya lau Sir."
Shiru ya d'an biyo baya kafin ya yi gyaran murya ya ce." Kin san abinda nake so dake?" Ta ce." A'a. "
Ya ce." Amina ta yi mini bayanin duk abinda yake faruwa, ki yi hakuri ki koma dakin mijinki ki cigaba da kula da yaranki, shi kuma ki kyale shi idan har kina da hakki sannu a hankali Allah zai saka miki. Ni kuma zan yi

14 / 73