Gudun Aure Book 3 Binta Umar Abbale

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 73

36K to 39K   out of 217.6K words

In banda umarni ne na iyaye bai ga dalilin da zai sanya shi zuwa bikon Hauwa ba balle rayuka su b'aci zahiri kuma ba a tara sani ga Allah da ya san abinda zai biyo baya kenan da bai aminta da auranta ba.
Tun mota suka yi magana da Hajja shi ya gaya mata cewa zai wuce Bunkure gidan Malam 'Daha malamin mahaifinsu wato Alhaji Ibrahimu. Yana nan ya tsufa sosai amma da yake tsufan ya wanzu tafarkin addini da karatun al'kurani jin sa da ganinsa duka ba su raunana ba. Sai dai matsalar kafa da ya samu amma baya ga haka babu wani abu da ya samu tawaya a tare dashi sai tsufa wanda wajibi ne ga kowane musulumi. Tun yana saurayi rabonshi da ziyartar malamin yanzu kam ya zame masa dole domin yana buk'atar addu'a bayan wadda yake yi akan kansa.
Sukairaju na sauke Hajiya Saratu a gidanta suka d'auki hanyar kauyen bunkure kamar yadda ya niyyata. Da k'yar ya iya sheda gidan dalili yawanci gonakin da suke garin an sayar an yi gine-gine na zamani tunda yanzu an samu cigaba a ko'ina kusan rabin garin ma ya zamananta da dama wasu na sauya fasalin gidajensu zuwa na zamani.
A can daga gefe Sukairaju ya ajiye motar amma bai fito ba yana ciki a zaune dalilin ganin yadda jama'a suka fara taruwa masu wuce wa suna tsayawa. Ya ce da Sukairaju ya yi sallama a kofar gidan Malam din haka kuwa ya yi ya dinga kwad'a sallama wani magidanci ya fito cikin yar shara da fatanya a kafadarsa. Suka yi musabaha kafin ya tambaye shi. Ya ba shi amsa da eh gidan Malam 'Daha ne. Sai ya nuna masa motar yana fad'in." A gaya masa ba'ko ya yi Alhaji Tajuden ne na Alhaji Ibrahimu dambatta wato abokinsa da ya rasu."
Mutumin ya washe bakinsa kafin ya nufi wurin motar da saurin gaske. Sukairaju ya bi shi cikin gaggawa ya yi saurin tare shi.
Duk abinda suke yi yana kallonsu sai ya sauke gilashin motar fuskarsa a sake ya furta." Sukairaju matsa masa hanya mana mutumina ne."
Da sauri Sukairaju ya bashi wuri shi kuma ya kàrasa bakin motar yana ta dariya tare da mamakin ganinsa. Ya bude motar cikin sauri ya fito ya rike hannunsa yana fad'in." Malam Rabi'u."
Ya ce." Naam Alhajin Allah dama za mu sake ganawa."
Yana dariya ya ce." Allah ya nufa gashi na ziyarce ku, na zo wurin Malam ne."
Ya gyad'a kansa yana fad'in" Ya bayan rabuwa Alhaji ya harkoki da jama'a Ubangiji Allah Ya taimaka ya kara suttura."
Ya amsa da "Amin Malam Rabi'u ya iyali fatan kowa lafiya?" Ya ce." Alhamdulillahi mata na hud'u ina da yara ashirin da biyu."
Cike da mamaki ya ce." Mata hud'u yara ashirin da hud'u Rabi'u?"
Sai ya kyalkyale da dariya yana fad'in." Kwarai kuwa Alhaji yanzu haka akwai shida mata dana aurar da su, suna d'akin mazajensu cikin aminci."
Ya gyad'a kansa yana jimanta karfin hali irin na mutanan k'auye gashi dai bashi da wani karfi irin na su amma ya ajiye mata hud'u da tarin yara."
Ya ce." Ka burge ni da gaske Rabi'u kuma kai namiji ne, yanzu dai ka yi mini jagora wurin Malam na zo mu gaisa ne."
Ya ce." Ka kyauta sosai kuwa domin idan ban mata ba yanzu ka kai sama da shekara asirin rabonka da garin nan tun marigayi yana raye."
Ya furta." Tabbas hakane domin karshen zuwan da muke yi tare da shi ne, tun bayan rasuwarsa kuma Allah bai nufe ni da sake zuwa ba."
Suka nufi cikin gidan a tare suna magana cike da jin dad'in had'uwa. Babu girman kai ko kuma nuna ni isheshshene yanayin yadda ya gaisawa da jama'ar da suka tsaitsaya yana ta d'aga musu hannu haka suka shiga gidan da aka narka 'kasa irin ta da mai d'anko wurin gida shi. Gidan mai yalwa ne sosai irin dai ire iren gidajen Malaman addini mussaman na karkara
har yanzu yana nan inda yake sai dai kwaskwarima da aka yi wa wasu guraran dalilin wasu daga cikin yaransa a ciki suke zaune da iyalinsu. Amma kuma sun gyarawa mahaifinnasu bangaran nasa tunda da alama yana yin manyan ba'ki mussaman abokai ko 'ya'yansu tunda fitacce malamin addinin musulunci ne da har yanzu tafsiri da karatun al'kurninsa ke yawo a wasu gidajen redion.
Koda suka shiga wurin nasa yana zaune kafarsa ta k'wanshe da al'kur'ani kirar warshu a hannunsa yana karatu babu wata gigita ta tsufa ya gane wanene a gabansa.
Rabi'u yana fad'in." Malam ga Tajuden na Alhaji Ibrahimu na kawo maka."
Ya yi dariya irin ta manya kafin ya ce." kuna shigowa na gane shi ai ko baTajudden na Alhaji Ibrahimu ba."
Ya ce." Ni ne Malam ina fatan na same ku lafiya ya bayan rabuwa kuma?" Ya amsa da "Alhamdulillahi ya iyali ya jama'a ya harkokin ina Hajiya Halimatu?" Yana nufin Hajja kenan.
Ya ce." Tana nan lafiya lau ta ce a gaishe ka da kyau Malam."
Ya gyad'a kansa tare da fad'in." Ina amsawa na kuma ji dadin ganinka Tajuden za mu sake saduwa kafin Allah Ya yi ikonsa."
Ya furta." In sha Allahu rabbi zan dinga ko'karin ganin na kawo ziyara Malam abubuwa sai a hankali."
Ya gyad'a kansa yana murmushi kafin ya ce."Allah Ya taimaka ya bada sa'a, na gode sosai Allah Ya yi albarka."
Ya amsa da Amin suma Amin kafin wajan ya d'auki shiru Malam Rabi'u tuntuni ya fita. Malam din ya ce." Akwai abinda yake tafe da kai ne?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kwarai kuwa Malam muna buk'atar addu'a akan komai duk da muna yi akan kanmu, amma a kwanakin nan abubuwa sun yi yawa mussaman 'bangaran iyalina a taimaka mana da addu'a Allah Ya warware mana."
A nutse ya ce." Za a yi in sha Allahu akwai buk'atar ka tsananta addu'a akan kanka, daga nan zan sanya al'majirai yin saukar al'kur'ani tsayin kwanaki bakwai sai ka yi sadaka, Allah Ya warware."
Ya amsa da "Amin Ya Malam na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya furta." Za ka shiga ka gaisa da mutanan gidan ko?"

idan kin san kina karanta book din nan ba ki biya ni hakkina ba to Ina binki bashi.

Ya yun'kura domin tashi Yana fad'in." E, zan shiga Malam zan yi magana da Rabi'u akan abin sadaka sai mu ga yadda za a yi."
Har ya juya zai fita ya dakatar da shi ya tsaya sai ya ce." Ya iyalin Tajuden su nawa ne yanzu yaranka kuma nawa?"
Ya ce." Allah shi gafarta Malam su uku ne yara kuma ina da biyar rayayyu d'aya ta rasu."
Ya ce." Alhamdulillahi Alhamdulillahi Ubangiji Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya raya mana su bisa tafarkin addinin islama. Idan har kana da buk'atar cika sunnar Annabi tunda su uku ne ka zo nan na zaba maka daya daga cikin yarana biyu da suka rage mini. Hakika ina sha'awar tabbatuwar zumuncina da Alhaji Ibrahimu. Duk da fad'in Allah ne kuma sunna ce mai kyau amma ba wajibi ba ne, abinda magabatanmu suka d'ora mu akai kenan lallai k'arshen duniya mata za su yawaita yayin da mazan auran za su yi 'karanci ko rashin ikon ga masu niyya. masu iko idan kuna da d'aya ku kara da ta biyu, masu biyu ku 'kara da ta uku, masu uku ku k'ara ku yi hud'u domin dakile mas'aloli masu yawa. Idan har ka niyyata tunda kana da iko kada ka manta ka zo nan zan had'a ka aure da nutsatstsiyar yarinya ko ba daga cikin yarana ba."
Cikin wani yanayin ya furta." To shikkenan Ya Malam idan da yiwuwar hakan in sha Allahu zan zo sai a san yadda za a yi na gode sosai, Allah Ya saka da alheri"
Ya amsa da "Amin cikin nutsuwa yana yi masa fatan alheri da sauka lafiya.
Yana fita ya ciko karo da Rabi'u a tsaye ya ce ya yi masa jagora cikin gidan domin su gaisa. Ya dinga mamakin yadda gidan Malam 'Daha
ya cika da tawagar yara 'yan mata da masu tasowa maza da mata sai iyayen tukuwane kangama-kangama dama can sanin da ya yi masa mutum ne mai arzikin gona ki a k'auyen don haka matsala ta abinci ba zata ta zama barazana a gare su. Malamin mahaifinsa ne kuma akwai abota sosai sai dai kowa tsarinsa daban. Mahaifinsa ko a can baya yana da wayewa sosai ta fannin boko da kuma addinin daidai gwargwado Hajja ita kad'an ta rayu bai ma ta'ba yun'kurin karin aure ba har ya rasu su biyu ya haifa. Shi kansa bai taba tunanin zai iya ajiye mata uku ba domin yadda ya tsara rayuwarsa tun daga kuruciya Samira kadai ta ishe shi, sai gashi Allah Ya na ta juya lamarinsa.
Har gajiya ya yi da amsa gaisuwa domin dai daga sashe sashe ake zuwa gaishe shi. Rabi'u ya riko hannunsa suka fita duk da haka wasu daga cikin yaran sai da suka biyo bayansu.
Bakin motarsa kuwa jama'a ne a tsaye Sukairaju yana ta fama da su. Daga bakin kofar gidan Malam din suka tsaya a dan gajiye yake fad'in." Rabi'u kana da asusun ajiyar kudi ko?"
Ya ce." E, da akwai sai ya fito da wayarsa ya mika masa yana fad'in." Bismillah yi sauri sanya mini lambar a nan zan tura abin sadaka a bawa Malam sannan abinda ya yi saura ka yi amfani dashi a kuma sallami iyayenmu da k'annanmu da suke cikin gidan a ba su su sha ruwa."
Ya kar'bi wayar da sauri yana fad'in." To Allah Ya saka da alheri mun gode Allah Ya kara arziki Alhaji."
Bai ce komai ba har gama ya mika masa waya ya kar'ba a tsaye a wurin ya tura dubu dari biyar sannan ya bashi wayar a gain ya ce ya sanya masa lambar wayarsa domin su dinga gaisawa."
Ya kar'ba a karo na biyu ya sanya masa lambar shi kuma ya yi serving da Malam Rabi'u Bunkure.
Da haka suka yi sallama cike da girmama juna. Sai da suka fita daga karkarar tukkuna Sukairaju yake tambayarsa ina suka nufa domin shi duk a tunani shi zai sake kwana a kono din ganin bai fiye son tafiyar mota ba. Ya ce." Mu d'auki hanyar gida kawai yau komai dare a gidana zan kwana Sukairaju na huce gajiyar gabad'aya."
Aikuwa da azama ya d'auki hanyar garin abuja kamar yadda aka bashi umarni.
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya d'an gyara zaman shi a mota yana nazarin maganar Malam 'Daha wai ya zo cikin karkara ya nemi aure domin cika ta hud'u. Gabad'aya ma shi yanzu babu wannan lissafin a tare da shi bai sani ba ko nan gaba. Gabansa ya fadi lokacin da ya tuna iya rigimarsa Amina tunda suka yi sallama jiya sau daya suka yi waya da daddare kafin ya kwanta ya kira ta domin gaya mata ba zai dawo ba sai gobe. Yana duba wayar ya ga kiranta ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya sanya wayar a kunnansa Amina ta tsaya masa ransa sosai shi kansa ya tabbatar da haka...✍️
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 9:19 AM] Ummu Safwan: *Gudun aure paid book complete 1k akan telegram normal What'sapp group kuma #700....via 0542382124.... Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*114*
Muna tare da yara falo wai sun zo ganin 'kaninsu domin babansu ya gaya musu sunansa Sultan falon ya kacame Husaina da Minal har da kokawa ban ankara ba sai kukan Minal na ji da k'arfi lokacin ya yi daidai da fitowar Baba Tabawa daga d'akinta. Kukan Minal din ya zaburar da yaron shi ma ya tsanyare da kuka Baba Tabawa fadi take "A kul cizo ko Usai ba ki san 'kanwarki ba ce, ka da na sake gani kin yi cizo."
Na juya da mamaki ina kallonta yayin da nake jijjiga yaron na ce." cizonta ta yi?"
Hassana dake tsaye a gefe ta ce." E, ni ma tana cizo na ko Yaya?" Ta fad'a tana kallon Khalil da yake zaune hankalinsa kan tibi domin shi duk rigimar d'aukar yaron da suke yi ban dashi da suka shigo dai ya zo ya tsaya kusa da ni bayan mun gaisa har yana tambayata sunansa Sultan ko na ce masa eh daga haka sai ya je ya zauna. Yana da nutsuwa sosai kuma bashi da hayaniya irin ta 'kuruciya.
Ya yi shiru bai ce komai ba wata'kila bai ga lokacin da ta yi cizon ba shiyasa bai yi magana ba.
Na ce." Kai cizo take yi dama?"
A hankali ya ce." Idan suna fad'a ba, itama Hassana ai mazilinciya ce ita ta koya mata cizon don ta fi k'arfinta"
Na dube ta ta yi tsuru-tsuru! domin da alama ba a saba yi mata fad'a ba ko nuna mata abinda take yi kuskurene. Fad'an da Baba Tabawa ta yi mata ya sanya ta kyakykya'be fuska za ta yi kuka.
Cikin tsawa na ce." Zo nan!" Ta'ki zuwa hawaye tuni sun 'kwace mata. Na ce." Ba za ki zo ba?" Ta ma'kale kafada tana kuka."
Na mi'kawa Baba Tabawa yaron ina fad'in." Ki mayar da shi baya wata'kila ya koma baccin." Hassana ta je da sauri tana fad'in." Baba ba ni shi na d'auke shi."
Cikin zare ido na ce." Matsa ki ba ni wuri babu wanda zai d'auke shi ai tunda ba za a ce ku bari ba."
Ta koma ta zauna jikinta a sanyaye. Na janyo Minal da take shashshekar kuka na d'orata saman cinyata Ina rarrashinta har ta yi shiru na bud'e mata game a wayata tana wasa.
Yadda suka takure a wuri d'aya hakan bai sanya ni na ji tausayinsu ba abinda ya dame ni shine rashin jin magana d'aya domin tun kafin a kai ga cizon nake ce musu su nustu zan bawa kowa yaron ya d'auke shi ban ankara ba har an kai ga cizo.
Na mik'a hannuna da sauri na janyota gabad'aya ba su ankara ba sai suka fasa ihu a tare domin yadda na janyo Usai din shi ya zaburar da 'yar uwata Abinda ba su saba dashi ba kenan
Khalil ya zubo mini ido da yanayi na damuwa kamar ya hana ni. Na kama kunnanta na mur'de shi da k'arfi. Ta tsala ihu! sai hawaye shar-shar! Baba ta fara ko'karin kwaceta. Na kai mata rank'washi da d'aya hannuna ina sake murde fatar kunnan na ce." Wallahi duk ranar da na sake ji an ce Usaina ta yi cizo zan sanya reza na yanke harshenta Khalil ka zama sheda idan ta yi ko a gidan Momin ne ka zo ka gaya mini." Da sauri ya ce. "Ba za ta sake ba Mama ki yi hakuri kin ji."
Na cika mata kunnan ta matsa gefe kusa da 'yar uwar da take tayata kukan suka jeru suna yi cikin jan hanci da sauke ajiyar zuciya."
Kiran da ya shigo wayata ya katse maganar da muke yi da Baba Tabawa akan abin duk yaro mai cizo ai babu yadda za a yi yayi farinjini ko yanzu hannun Minal ya yi shedar ha'kora ina dalili.
Koda na duba maigidan ne. Na daga lokacin kukan yaran ya hana ni jin abinda yake fad'i mi'kewa na yi na nufi d'aki ina fad'in." Ina jinka ina yini?"
Ya amsa a tak'aice kafin ya ce." Wacece take kuka Hassana ko Usaina?" Kai tsaye na ce." Dukansu ne?" Ya yi Jim kafin ya furta." Akan wane dalili Amina?"
Na ce." Fada suka yi har da cizo shine don an yi musu fad'a suka had'a kai suna kuka?"
"Idan wannan fad'an ne a junansu sun saba yi ai."
Ya fad'a da yanayi na b'acin rai a maganarsa.
Na ce." Da sau'ki idan a junansu suka yi tunda tare suka rayu ko a ciki daya. Usai ce ta ciji Minal a hannu?"
Ya yi shiru bai ce komai ba haushi ya ji da alama sai abin ya ba ni mamaki da dariya. A gajarce na ce." Ka taho ne?"
"E, kin ga Amina kada ki sake dukan yaran nan ba na so na gaya miki?"
Na ce." Haka na ce maka na dake su? fad'a fa kawai na yi mata ita mai cizon shine ita abokiyar tagwaitakartata take tayata kuka bayan Kuma ita din ta tabbatar mini da cewa dabi'ar yar'uwartata kenan cizo a ganinka d'abia ce mai kyau?"
"Na ce dai kada ki sake dukansu ban ce dabi'a ce mai kyau ba fad'a ya isa ban da duka."
Na ce." To." kawai na yi shiru ina mamaki.
"Gani nan kan hanya in sha Allahu ki yi mana addu'ar sauka lafiya."
Na ce." Allah Ya kawo ka gida lafiya."
Ya amsa da "Amin. " Kafin ya kashe wayar na fita falon ina mamaki ashe zai sake ru'banya domin babu kowa a falon har Khalil din. Na bi Baba Tabawa kicin ina fad'in.'' Ina yaran suke?"
Ya juyo tana kallona kafin ta ce." Au ko sun tafi babu sallama."
Na ce." Da alama gashi na fito babu su a falon.
Sai ta sanya dariya tana fad'in." Kai jama'a yaran yanzu ba sa son fad'a, wato fushi suka yi."
Na gyada kaina ina fad'in." Kada Allah Ya sa su 'kara shigowa gidan." Na fita daga kicin din raina a b'ace ni ba za a yi wannan sakarcin da ni ba. Daga jin kukan yara ya yi wani kicin-kicin yana fad'in magana a kumbure kada a dake su, aikam sai dai ba su yi abin dukan ba.

Ki karanta baki biyani hakkina ba ina binki bashi

Shigar k'ananun kaya na yi domin tar'barsa ina da ragowar kwana daya tunda shekaran jiya kawai muka kwana dole anan wurina zai kwana. Na tsaya gaban madubi ina duba kaina na juya nan na juya nan har abin ya so ya ba ni dariya ni kaina ba kasafai nake son sanya rriga da wando matsatstsu ba don sai na dinga ganina kamar wata inyamura yanzu na dinga kallon kaina a madubi ina tuna wata jarumar finafinan kudu na manta sunanta amma tana da wani irin hips mai tudu da mutukar daukar hankali. sam bata da kyawu a fuska amma tana da dirin jiki mai kyau. Kai na ji dadin maganin tumbin nan da nayi amfani da shi domin yanzu ina yin gayu sosai na matse ko'ina na jikina ya fita yadda ake so maganin ya daidaita mini yanayin jikina kwarai......08089965176 ga masu buk'atar su tuntubi wannan lambar.

Misalin tara da arba'in na dare ya kira ni yana gaya mini ya d'an jima kad'an da dawowa yana gidan Momi zai shigo zuwa an jima

13 / 73